Showing 18001 words to 21000 words out of 47460 words

Chapter 7 - In Da Rai Book 2 Complete By Garkuwa.pdf

Advertisement

06 Jul 2025

6544

kuma ya ɗan juyo ya kalli Ishmah dake
gaidashi yace.
“Barka dai amarya, Allah ya sanya alkhairi yabada zaman lafiya”.

A tare Taj da Garkuwa suka amsa, ita kuwa Ishmah ƙasa tayi da kanta tare da ɗan kaɗa kanta

jin Garkuwa dake shiga motar nace mata.
“To sai da safe, zamuyi waya”.

“Allah ya bamu alkhairi”.
Amin suka amsa kana yaja motar suka tafi.

A hankali ta ɗan juyo ta kalleshi, da sauri tayi ƙasa da kanta ganin shima ɗin ita yake kallo.
Cikin sanyi murya tace.
“Ya ƙafarka?”.
A hankali ya ɗan matso kusa da ita, murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Alhamdulillah”.
Ya faɗa tare da ɗan ƙara matsowa jikinta.
Sai kuma ya ɗan jujjuya kanshi yana ƙarewa harabar gidan kallo ba kowa.
Hannunshi yasa ya jawota jikinsa sassauƙan rugguma yayi mata tare da ɗan manna lips inshi
kan goshinta ya dire mata sassayan kiss murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Ki yafewa Tajj ɗinki Ma'eesha”.
Cikin sanyi ta ɗan lumshe idanunta kana ta buɗesu a hankali. Sai kuma ta ɗanyi saurin
matsawa baya, saboda hango Yah Muhammad.
A hankali ta nufi cikin gida.
Shi kuwa Taj BQ ɗin ya wuce shida Yah Muhammad.

Washe gari da safe, cike suke a Parlour Daddy.
Cikin sanyi Ishmah ta kalli Yah Rabi'u ɗan Bappa Bello dake zaune ba tare da ya fara cin abinci
ba.

“Yah Rabi'u kaci abinci mana”.
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da cewa.
“Ina azumi ai”.
Da sauri Rahama tace.
“Kai Yah Rabi'u dan Allah ka karyashi muna haɗe kowa nacin kai kuma ka wani ce kana
azumin”.
Cikin mutuntaka da nagarta yace.
“Azumi mukeyi dani da Yah Abubakar wanda mukayiwa Allah al'ƙawarin duk randa Ishmah tayi
aure, zamuyi azumi uku uku domin gode mishi”.
Cike da tarin mamaki ta kalleshi.
A ranta tace.
A kaina, shin dama ashe har haka rashin aurena ke ciwa yan uwa tuwo a kwarya.
A fili kuwa sunkuyar da kanta tayi, yayinda wasu siraran hawayen ke zubo ma.
Cikin sanyi kuma duk suka kalli Adam daya saki wata doguwar ajiyar zuciya murya cike da rauni
yace.
“Ni saboda aurenta nake azumi uku cikin ko wanne wata, sai gashi yanzu kuma da auren yazo,
ji nakeyi tamkar ace an fasa saboda, bana son tayi nesa damu, domin itace ta meye mana
gurbin Daddy a gidan.

Ita muke gani muji sanyi itace ta danne maraicinmu, mukan shiga ɗakinta muyi tamkar yadda
mukeyi a ɗakin Daddy”.
Da sauri Yah Abubakar ya ɗan dafa hannunsa dake kusa da nasa tare da girgiza mishi kai.
Sai kuma duk suka kalli Hamisu wanda ya miƙe tsaye tare da ficewa yana zubda hawayen
tunowa da Mahaifiyarsun da kuma nesa da yayarsu zatayi dasu.
Da sauri kuma duk suka kalli Rahma yar auta data saki shesh-sheƙan kuka murya na rawa take
cewa.
“Yanzu zamu ƙara fuskantar maraici, ni bazan ma zauna a gidan nan ba in ta tafi”.
Da sauri Yah Muhammad ya jawo hannunta tare da cewa.
“Zo nan auta, ba gamu ba, duk abinda kikeso zamuyi miki”.

Ita kam Ishmah tuni take zubda hawaye masu zafi.
Sosai take jin rashin mahafiyarsu ya sabunta garesu.
Yah Rabi'u ne ya gyara zamansa cike da hikimar Addini ya fara yi musu nasiha mai ratsa jiki
wacce tasa gaba ɗaya suka fara samun nitsuwa.


Ethiopia
Cikin sanyi Abpu ya koma ya kishingiɗa jikin kujerar dake bayanshi.
Tare da fesar da zazzafan numfashi cikin alamun rashin ƙoshin lfy yace.
“Zuwa yanzu dai dole in cire batun auren Adaya a raina.
Wata ƙil itace Allah ya bani Zakka a cikin yayana.
Allah yaji ya gani nayi iya iyawata shine shaidata, kamar yadda shine mai shiryawa,
To ina fatan ya shirya min ita fiye da bada tarbiyata in tana da rabon shirya,
In kuma bata da rabon shirya ina roƙon Allah ya yafe min kada ya kamani da zunubanta”.
Ya ƙare maganar murya cike da rauni.
Yah Ma'aruf dake gefene ya ɗanyi saurin motsawa kusa dashi.
Aminullah kuwa ƙaninta hawayene suka tsinko mishi.
Ummi kuwa murya a sarƙafe tace.
“In sha Allah zata shirya, tunda kace Allah.
Ta dire mgnar tana nazari yau kwana uku kenan Adaya bata fita ko tsakar gidaba tun randa
wanda akace mijinta ne yazo ya saketa.
Yah Ma'aruf ɗinne yaci gaba da tausa sa Abpun.
Mamanshi kuwa k’waffa tayi ƙasan lips tare da juyawa ta fice Allah ya sani lamarin Adaya ya
fara damunta, dan yana damun mijinsu kuma itama duk inda taje sai ace ƴarsu cikin takaici
tace.
“Shegiyar yarinya mai kama da ifiritu minaljinni, ta buwaye mu ai ta nuna mu, Allah ya shirya.”

A dai-dai lokacin a can Parlour Abba kuwa.
Sheykh Tajuh Usman Bauchi ne tare da Babban ɗansa Sheykh Tijjani Usman Bauchi.
Sai Uncle Bello.
Da kuma Taj dake tsakiyarsu.
Bisa dukkan alamu magana mai mahimmanci suke tattaunawa

Bayan sun gama duk tattaunawar tasu, sun tsaida matsayar tafiya da masuyin rakiyar kai
amaryar.

Sai ƙarfe goma su Sheykh Tajuh Usman Bauchi, suka fita tare da tawagar zakiransu, suka
kama hanyar Bauchi, bayan ya ƙara kebewa da Taj ɗin.

Cikin sauƙe numfashi Uncle Bello ya kalli Abba da kuma sauran yaran nasu kana yace.
“To Alhamdulillah, abu yazo mana a lokacin da bamuyi zaton zai-zo mana a hakanba.
Sai kuma ya ɗan kalli Yah Muhammad tare da cewa.
“Masu zuwa rakiyar nanfa, bazasu wuce 6 ba, ni in a son samu nane ma mutum biyu kacal”.
Kai Yah Muhammad ya jinjina tare da cewa.
“Toh gsky nima hakan naso, toh shi ɗin ne yake nunin da aje ɗin saboda wai hankalin Ishmah
zaifi kwanciya, kuma Abba ma zaifi samun nitsuwa in ya san inda Boɗɗinsa take”.
Murmushi ya ɗanyi kana yace.
“To ka kira Goggo Dijan ku. ƙanwarsu Abba kenan. da takwararta Khadijah ƙanwar Ishmah
kenan mai Binta.
A gefen mu su zasuje, sai kuma ummarku ɗaya.
Sai kuma matarka ko matar Abubakar, sai kuma uwar ɗakinta Garkuwa.
Biyar kenan ko?”.
Da sauri Yah Abubakar yace.
“Eh”.
Yana gyara zamansa yace.
“To sai ita Ishmah da mijin nata, bakwai sun fito ba.”
Cikin sanyi Taj ɗin yace.
“Eh yanzu mukayi waya da Sheiykh yace, min yayi magana da wani ƙaninsa cewa, za'a samu
Visa, sai dai na mutum takwas za'a samu kuma ranar Laraba jirgin zai tashi.”
Cikin sauke numfashi Yah Abubakar yace.
“To sai asa Adam cikon na bakwai ɗin, kar suje ba namiji ko ɗan aike zai musu, kuma Aunty
Nana taje, In sha Allah daga baya zanje da Maryam kam”.
Cikin gamsuwa Abba yace.
“To Allah ya sanya alkhairi aje lfy a dawo lfy.
Khadijah ma da Dija sun cemin sun taso suna hanya ma”.
Shiru sukayi jin Yah Muhammad na cewa.
“Toh Amman Uncle Bello ko dai Ummace zataje madadin Nana”.
Da sauri Uncle Bello yace.
“Wannan tunda muka dawo Umrah take fama da mura, gashi matar Rabi'u nada tsohon ciki.
Baza muso a barta ita ɗaya a gida ba babba ba”.
Cikin gamsuwa yace.
“To Allah ya sauƙeta lfy”.
Amin suka amsa sai kuma yace.
“To sai kaje ka amso E passport ɗinsu duk masu zuwan dan ayi duk abinda ya dace”.
Daga nan dai suka gama tsara komai.

A Parlour Daddey kuwa cikin murmushi Yah Muhammad yake kallon E passport ɗin Ishmah tare
da cewa.
“Masha Allah saura wata uku yayi expire, da yanzu sai munyi sungular sabunta shi, Kinga
yanzu an huta mijinki yayi sungular in kunje.”
Ba tare da ta fahimci mgnar saba, ta juyo tana kallon Aunty Maryam dake miƙo mata bowl ɗin
data zuba mata dahuwar jan naman.
Amsa tayi tare da cewa.
“Amman sai anjima yanzu bana jin yunwa”.
Cikin kulawa Yah Muhammad yace.
“Toh me kikaci ɗazumafa ina ganinki ba abinda kikaci”.
Cikin sanyi tace.
“Ji nake ina ƙoshe”.
Kai ya jujjuya mata tare da cewa.
“A'a Goggani kada kiyi haka”.
Da yake yakan kirata da goggini a wasu lokutan yadda Khairat ɗinsa ke kiran Ishmah kafin ta
gama iya magana.
Kujera ya nuna mata tare da cewa.
“Zauna kici, ke baki ga kin zama yar lelenmu ba”.
Kai ta ɗan sumkuyar tare da cewa.
“Toh”.
Daga nan ya fita yana faɗin bari inje in amshi na Aunty Amina da Garkuwa.
Cikin sauri Aunty Nana tace.
“Abban Ikiram ya yarda zata je?”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Eh Amman fa saida Abba da Sheykh Tajuh da Tajj ɗin sukaje har wurinsa tukun ya yarda”.

Adam kuwa da bashi da E Passport Abubakar yasashi a gaba sukaje ayi mishi.

Hakan kuwa akayi.
Cikin kwana biyu aka gama komai, to abune na kuɗi da kuma sa bakin manya, shiyasa tuni
komai ya kankama ya haɗu.
Aunty Maryam kuwa da Garkuwa wani irin shiri da tsumi na musamman sukeyiwa Ishmah da
har yau mgnar kalmar auren nan bai haɗata da kowaba.
Har gobe jin kalmar take a baƙuwa a cikin kunnuwanta.

Taj kuwa tamkar ma gudunsa takeyi, ko sun kasance wuri ɗaya ma kuma zama take tamkar ba
itace surutacciyar abokiyarsa nan mai tsananin shaƙuwa da shiba sai dai tana kula da ƙafarsa
duk dai har yanzu yana ɗan ɗingisa ta.

A tsakanin kwana kin kuma ya amsa gayyatar sauk’an karatun wasu ɗalibai a jihar Bauchi a
ƙaramar hukumar Azare.

Ita kuwa Ishmah gani take Taj ɗin tamkar ba Taj ɗinta bane, kamar wani ne da ban aka ajiye

mata.
Saboda tsananin nauyin shi da takeji wanda yasa ko sunanshi nauyin faɗi yake mata.
(girma da darajar aure kenan.)

Khadijah da Goggo Dijan kuwa da Aunty Maryam tuni suketa shirya komai na tafiya.

Ethiopia
Yau talata Ummi ce zaune tare da tsurawa Adaya idanu tana kallon yadda take tahowa wurinta
cikin sanyi da lallaɓa takun ƙafar tamkar ba Adayarta data sani a bayaba wacce ko tafiya take
sai ta rausaya ba.
Numfashi mai nauyi ta fesar dai-dai lokacin da Adaya ta zauna gefentan a hankali tace.
“Adaya nafa ce Miki, na san akwai abinda kike ɓoye min, ki faɗa min menene matsalar ki?”.
Cikin sauri da karsashi tace.
“Ummi ba abinda ke damuna fa! Kawai zazzabin da nayine, kuma na gaya miki faɗuwar da nayi
a BQ lokacin da zan fita ne, ƙuguna ya bugu shiyasa nake tafiya a hankali dan har yanzu yana
min ciwo, shiyasa ma ko fita rihazal banayi”.
Cikin rashin gamsuwa Ummi tace.
“Toh Allah ya sauwaƙa”.

Gidansu TAJJ.

Ummey ce zaune gaban Addawa cikin sanyi tare da tsiyayar da hawaye masu zafi
Murya na rawa cike da rauni tace.

“Ko ina yayi min zafi a duniya ji nakeyi, bani da wani sauran farin ciki tunda Malam ya nesantani
da Afif ya cika zuciyata da duniyata da baƙin ciki mara yankewa.
Nayi niyar zanyi mishi mgnar Afif in yaso ta zama sanadin aurena, in rabu dashi inje in
kansance tare da ɗana, in killace shi in cire mishi ƙuncin rashin mahaifin nasa.
Amman kin hanani kana kin ƙara min wuta a kan ranar da malam ya sani”.
Cikin sanyi Addawa ta ƙara matsowa kusa da ita.
Sassayan numfashi ta fesar tare dasa hannunta ta sharce mata hawayenta da wani ke korar
wani cikin hikima da hangen nesa na manyan mutane tace.
“Eh ko yanzu zan ƙara jaddada Miki ban amince ki kira masa sunan Taj a gabansa kamar yadda
yace ba”.
Har suna haɗa baki ita da Halima sukace.
“Toh saboda me?”.

“Saboda yace in kin kira masa sunansa a gabansa ko kinyi alaƙa dashi a kan aurenki”.
Da sauri tace.
“Toh me zanyi da auren Malam me ya rage min dashi”.
Tana maida hawayenta dake tsatstsafowa tace.
“Nasan idan har kikayi mgnar Afif a gabansa tabbas zai sakekin, sakinki kuma shine abinda zaifi
yiwa Afif ciwo fiye da komai, yace min bazai taɓa yafewa kansaba in har ya zama sanadin

rabuwar auren iyayensa.
Sannan kuma ai in kikayi abinda zaku rabu da Malam kin yiwa magauta abinda suke so, shike
nan sunyi nasarar korar ɗanki. Kema sun fidda ke gidan Zakiya nayin aure shike nan baki da ko
tsuntsu a gidan
Zai kuma tabbata cewa Afif ya aikata laifin kenan?!”.
Da sauri Ummeeyshi ta saki shesh-sheƙan kuka.
Dafa kafaɗarta Addawa tayi tare da cewa.
“To in dai bakya son haka ya tabbata, to kiyi haƙuri kada ki sake mishi mgnar Afif, kuma daga ke
har su Maryam kada kuyi alaƙa dashi, saboda kada Allah ya isan mahaifinsu ya hau kansu”.
Cikin kuka Halima tace.
“Yanzu shike nan an rabamu da ɗan uwanmu an maraitar dashi duk da yawan danginsa!”.
Cikin ƙarfin hali Addawa tace.
“Tajuddeen bazai maraitaba, zan kasance tare dashi, kamar yadda na gaya muku dani da
Laylah, da Zulaihat yau da dare zamu tafi Qatar zamuje can.
Yace min shima zuwa dare baƙi zasu isa in rigasu isa in marabcesu, sai dai bansan wasu baƙin
bane, kuma bansan ina yake ba.
Dan haka ki kwantar da hankalinki zanje in kasance dashi zan bashi dukkan kulawar da kikega
in kuna tare zaki bashi.
Wani sassayan kuka Ummeeyshi ta kuma sakewa tana faɗin.
Yanzu ko a waya kenan ya haramta inyi mgn da ɗana”.
Da sauri Addawa tace.
“Kwarai ma kuwa, don kiyaye igiyar aurenki, ki zauna a nan mu jira ranar da gsky zatayi halinta
domin ai INDA RAI to tabbas da Rabo.
Ki zauna a gaban idonki gsky zatayi halinta kiga yadda kwayar idanun magautansa zasuyi.”


Nigeria.
Yau Laraba tun safe suke gama shirin su, duk masu tafiyar sun haɗu.
Garkuwa, Aunty Amina, Aunty Nana, Khadijah, Adam Goggo Dija.
Kasan cewar ƙarfe tara jirginsu zai tashi daga Adamawa to Lagos.

Ƙarfe biyu dai-dai kuma zasu tashi daga Logos Nigeria to Doho Qatar.

Cikin sanyin da tunda gari ya waye ta tashi dashi, da ji take da ganin abin kamar wasa ko
almara koko mafarkin da zata farka ta ganshi a sawarware.
Rauninta yayi ruɓanya da kaso 90 bisa ɗarine, a lokacin da taga anata fidda dukkan
kayayyakinsu durƙushe take a gaban Abbanta da kuma Uncle Bello sai Yayunta.
Wani irin sassayan kuka take yi mai tsuma zuciyar duk mai imani.
Sai kuma kawai ta rarrafa a hankali ta ɗaura kanta bisa cinyar Hajia kakarta wacce tun safe
tazo don yin sallama dasu.
Sunkuyar da kai Abba yayi domin shima kansa hawayen ke zubar masa.
Da sauri Rahama tazo ta raɓa jikinta jin tana cewa.
“Yanzu in na tafi waye zai zauna dasu Rahama, waye zaike hanasu kewa da maraicin Daddy,

Waye zai rinƙa hana Hamisu kuka in ya tuno Daddynmu”.

Wani irin azabebben numfashi Taj ya fesar a hankali, tare da rumtse idanunsa ji yake yi kukanta
na ƙona mishi ƙahon zuciyarsa tamkar zata narke.
Uncle Bello ne ya ɗanyi ƙarfin halin farayi mata faɗa mai haɗe da nasiha nasiha.
“Toh Shatu YAR FULANI. Kin mance cewa Duk wanda baya yarda da ƙaddara MI WASMITI
shine kalmar da zata yi abota da harshensa.
Ki tuna fa cewa NAMIJI BAYA KAƊAN.
Ai duk sonki da su Hamisu iyakar na BANDIRAWO ne baki kai Allah daya haliccesu sonsuba.
kuma dai TAUSAYAWA JUNA da kuke bazai hanaki yin aure ki raya sunnar Manzon Allah ba.
Tunda da baku isa ku kauda RUBUTACCAN AL'AMARI ba.
Mutuwa kuwa ai RIGAR KOWA ce, Mamana ya zamuyi Allahn da ya bamu ita shi ya ɗauke
mana ita, kuma ya fimu sonta.
To ma wai zakiyi butulci da HUKUNCIN ALLAH ne Mamana?
Kin sani cewa Babu Maraya sai rago ko, to ai ko NAKASA MA BA KASAWA BACE, bare kuma
ga
Ga yayunku da mahaifinku wanda yake GARKUWA a gareku.
Kuma TUBALIN jin daɗi rayuwarku.
Kada ki mance cewa Allah yayi miki SAKAYYAH nefa da maɗaukakin aure a bisa haƙurinki da
kikayi tsawon shekaru kina riƙe da kanki
Dan haka ki share hawayenki ai INDA RAI to ai ana tare duk inda kike a faɗin duniyar nan.”
Ina ta kasa tsaida hawayenta saboda jin murya Khalid wanda Hamisu ya ɗaukosu dan suzo
suyi sallama da ita wani irin sassayan kuka yaron yakeyi harda Shesh-sheƙan kuka.
A hankali Taj ya jawoshi jikinsa cikin son yaron tare da jin tausayinsu zai ɗauke musu uwarsu ya
nesantasu da ita.
Wani irin tausayin Minat dake gefe tana sharar kwallane ya rufeshi.
Ji yake yi shi da yake babba ma daga shi sai Allah ne kaɗai suka san irin ƙunci da ciwon da
yakeji na rabuwa da iyayensa da yayi, inaga su yara.
Cikin sanyi yace.
“Zo nan my Daughter”.
Ya ƙare maganar yana jawo hannunta a hankali ta matso gareshi sai kuma ya jawo Mahamud
da yayi ƙasa da kanshi cikin sanyi yace.
“Kada kuyi kuka, kuyi mana addu'a, kai My boy kana gama Secondary School zaka dawo
wurinmu kaci gaba da Karatu.
Kema My Daughter zaki dawo kuyi karatu tare da Laylah ɗinki ko.
Kai kuma Mahmoud ai kama kusa tafiya Mexico kayi karatu a can ko?”.
Cikin jin daɗi duk sukace masa.
“Yess Uncle Taj”.
Yana sharewa Khalid hawaye yace.
“To kuje ku rarrashi Amminku kuce tayi haƙuri”.
Kusan a tare suka koma gabanta da sauri ta ruggume su.
Sai kuma tayi murmushi mai haɗe da hawaye jin Khalid na cewa.
“Ammi ki dena kuka, nima ina gama Secondary School zan taho Qatar mu zama larabawa”.

Kanshi Abba ya shafa tare da cewa.
“Yauwa Khalid haka nake son ji”.
Da sauri duk suka ɗaga hannayensu jin Uncle Bello na cewa.
“To muyi musu Addu'a.”
Nan fa yayi ta kwararo musu addu'o'i.
Bayan sun shafa ne, kuma Ishmah ta sake sakin wani kukan.
A hankali Abba ya miƙe tsaye tare dasa hannunsa ya kamota ya tsaida ita cikin kuka tace.
“Abba wa zai zauna da Rahama da Hamisu”.
Da sauri ta sauƙe nannauyan numfashi jin Hajiabna cewa.
“Ki kwantar da hankalinki Ni zan zauna dasu, sai Abbanku yayi aure zan koma gida”.
Cikin jin ɗan sanyi a ranta ta ruggume Hajia.
Yah Muhammad ne ya ɗan sharce hawayen da suka zubo mai gami da cewa.
“'Lokacin tashin ku ya kusa fa”.
Aunty Amina ce ta kamo hannunta suka fito ganin alamun bazata saki Hajia ba.
Cikin sanyi da tsokana Maryam ta sharce hawayenta tare da cewa.
“Fisabilillahi ke ba yarinya ba duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login