Showing 21001 words to 24000 words out of 47460 words
Chapter 8 - In Da Rai Book 2 Complete By Garkuwa.pdf
kiyi ta samu kuka da shogwabarki ki karya mana zuƙata.”
Ruggume Maryam ɗin tayi tare da cewa.
“Aunty Maryam zanyi missing naku ga amanar su Rahama”.
Sai kuma ta sake Maryam ta ruggume Hamisu.
Murmushin ƙarfin hali yayi tare da kamo hannunta suka nufi motar Abba buɗe mata yayi ta
shiga kana ya sunkuyo a hankali ya raɗa mata wata kalma.
Kawai sai gani akayi tana Murmushin tare da dukan kanshi.
Daga nan duk saura suka shiga motocin akaja aka tafin.
Suna zuwa Airport ba dadewa suka tashi, suka yi Lagos.
Suna shiga cikin jirgi a jere cike da nitsuwa wayace maƙale a kunnensa bisa alamu da Addawa
yake mgna.
“Mu yanzu zamu tashi!”.
Tana gyara zamanta bisa ɗaya daga cikin hamshaƙan kujerar tace.
“Mufa tun sha biyu muka isa”.
Kai ya ɗan jinjina tare da cewa.
“Eh ai ba nisa Ethiopia to Qatar 3 Hours and 18 minutes ne!”.
Tana lumshe ido alamun bacci tace.
“Kuma zaku iso kafin la'asar ko?”.
Suna haurawa saman first class, ya ɗan girgiza kai tamkar yana gabanta kana a hankali yace.
“Nanfa Nigeria to Qatar 8 Hours and 55 minutes ne, kin ga tafiya ce mai nisa sosai”.
Ya ƙare maganar tare da zama bisa kujerar dake gab da window, a hankali Ishmah kuwa data
lumshe idanunta hawayen da suke ciki suka zubo, Saboda jin irin nisancin da zatayi da ƙasarta
da yaranta mahaifinta Yayunta da kuma ƙannenta hakan yasa kukanta ya sabunta,
Tana mai zubda hawayen ta zauna.
Yayinda Garkuwa kuwa da Aunty Amina suke gefen daman su.
Sai Khadijah da Goggo Dijan dake bayansu.
Adam da Aunty Nana kuwa na can baya.
Shi kuwa Taj a hankali ya ɗan gyaɗa kansa tare da cewa.
“Uhmmmm”. Saboda jin Addawa na cewa.
“Kace inyi baccina sai tsakiyar dare zaku iso, ni da nufina zan jira isowarku ai”.
Ƙosawa da surutunta ne ya sashi katse kiran tare da kashe wayar saboda sanin dokokin su na
cikin jirgi.
Ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga zuwa Qatar.
Wani irin kukane mai sassayan sauti ya kubcewa Ishmah lokacin da taji jirginsu ya rabu da
ƙasarta ta haihuwa.
Lallai wanda baiji tsoron Allah ba ya wahala.
Cikin kwanaki biyar rayuwarta ta sauya salon ƙaddararta ya juye yazo mata a baibai, ko kusa ko
zato ko tsammani fita ko cikin Jimeta batayi ba sai gashi wai ƙasar zata bari Bama ƙasar ba
Africa baki ɗaya.
Dama ace Ethiopia ne da tasan ko ba komai yankin nahiyarta ne Africa.”
Shi kuwa Taj a hankali ya lumshe idanunsa, tare da fara tariyo shekarun baya, yana mai tunowa
haɗuwarta dashi da halin da ta shiga, tuno da wannan ne ya sashi ɗan gyara zamansa tare da
ɗan matsowa kusa da ita.
Dai-dai lokacin kuma tayi saurin rumtse idanunta da ƙarfi saboda jin hanjin cikinta sun fara
walle-walle irin dai yadda taji a shiganta jirgi na forko a rayuwarta.
Murya cike da rauni tace.
“Innalillah”.
Da sauri yasa hannunsa ya kamo nata ganin ta yunƙura bisa alamu so take ta kafa goshinta a
jikin set ɗin da yake gaban nata.
Da ƙarfi ya ɗan matse hannun nata cikin nashi tare da sarƙafe yatsunsu wuri ɗaya.
Sassayan numfashi ya fesar tare da ɗan jawota gefenshi, dai-dai lokacin kuma jirgin ya ɗanyi
marisar ɗaukar asalin hanyarsa.
Cikin tsananin tsoron ta raɓa jikinsa gefen kafaɗarsa ta manna kanta bisa damtsenshi tare da
rumtse idanunta da ƙarfi.
Shi kuwa Taj cikin fesar da sassayan iska ya ƙara matse hannunnata tare dasa hannunshi ɗaya
ya gyarawa kanta zama, cikin sanyi ya lumshe idanunsa tare da ɗan sunkuyar da kanshi kaɗan
lips inshi ya manna bisa goshinta tare da liƙa mata wani amintaccen kiss mai sauk’ar da
nitsuwa. Ajiyar zuciya mai nauyi taja kana ta sauƙe tare da direshi da ƙarfi, saboda wani irin sanyi da
taushin lips inshi da ya ratsa mata goshi.
Shi kuwa Taj a hankali ya ɗan ƙara matsowa kusa da ita, sai kuma ya ɗan sunkuyo ya leƙa
fuskar ta ganin hawaye na zubowa ne yasashi sa yatsunsa biyu ya sharce mata hawayenta, sai
kuma ya ɗan ƙara sunkuyowa sosai ya kai bakinshi dab da kunnen ta.
Sassayan numfashi ya shaƙa tare da motsa lips inshi a hankali murya cike da raɗa yace.
“Shima iri ɗaya ko Ma'eeshah!”.
Sai kuma ya ɗan cije gefen lip inshi na ƙasa yana mai ƙara yarda cewa haɗinsu daga Allah ne,
shiyasa komai nasu yake zuwa iri ɗaya, jin hawayenta na ɗisa bisa cinyarsa ne yasashi ci gaba
da cewa.
“Allah ne ya ke kusanta ƙaddarorinmu da kamantasu, kin rasa Daddy a lokacin ban alaƙan ta
kamanceceniyar ƙaddararmu ba, sai gashi ni ƙaddara ta rabani da Ummey na, wanda gwara ke
mutuwace ta rabaku”.
Haka nan taji hawayenta sun tsananta domin tunda yazo basuyi wani zaman kirkiba jin abinda
yake faɗane kuma yasata fahimtar cewa ya shiga cikin jarraba mai tsanani.
Shi kuwa Taj a hankali ya motsa lips inshi tare daci gaba da faɗin.
“Akasi kuma yasa mutumin da yafi kowa sona a duniya ya nesanta kanshi dani, ya barrantani
da yaransa yace, ya barwa duniya ni, kinga gwara ke zaman aurene sunnar Manzon Allah ne
yasa na rabaki da Abba, Ma'eeshah dani dake bamu da banbanci, nima tamkar maraya nake,
bani da kowa duniya sai ke da Addawa da Laylah, Ma'eesha kece kaɗai sauran hope d’ina, in
bake a kusa dani ba amfanin rayuwata gwara kawai in mutu in hut”.
Shiru yayi ba tare da ya ƙarasa mgnar ba jin yadda take jijjiga mishi kai.
Aunty Amina ce ta ɗanyi murmushi tare da nunawa Garkuwa inda suke da idanu.
Itama Garkuwa murmushin tayi tare da cire idonta.
Khadijah kuwa tuni tayi baccinta mai daɗi.
Adam kuwa kurui yayi da idanu yana kallon yadda suke keta hazo da gajumare, suna fesa
gudu.
Ita kuwa Ishmah a hankali ta fara jin bacci saboda.
Yadda yake ɗan jijjiga ƙafafunshi a hankali hankali wanda wannan halittarce in dai yana zaune
sai yayi ta haɗa guiwowinshi yana ɗan rabawa.
Fahimtar tayi bacci ne kuma yasashi gyara mata jingina.
Kana shi kuma ya faɗa duniyar nazarin rayuwar da zai fuskanta.
“Zan rayu dake tamkar abokiyar da kika kasance min Ma'eeshah bazan taɓa kusantar ki a
matsayin matar aurena ba, har sai ran da naga sona a matsayin mijin aure ba aboki ba a cikin
kwayar idanunki, kuma harshenki ya furta min, dole in fara sauya matsayin soyayya ta a
zuciyarki kafin sauya matsayin abota zuwa miji”.
A haka sukayi ta keta hazo har karfe huɗu.
A hankali ta ɗan yunƙura zaune.
Sai kuma ta ɗan kalleshi jin yana cewa.
“Je kiyi al'wala kizo muyi sallan la'asar, ki gayawa su Adam ma duk suyi al'wala suyi niya suyi
sallah.
Kai ta jinjina kana ta miƙe tare da nufar wurinda taga yana nuna mata.
Bayan ta fitone duk suka sabunta al'wala bandashi dan yasan al'walarsa na nan.
Koda suka idar da sallan, hannunshi ya ɗago tare da jera musu addu'a.
Daga nan suka ci gaba da tafiya.
Hakama sukayi Magrib da isha.
Koda aka kawo musu ɗan abin taɓawa kowa yaci abinda aka bashi, amma ita babu yadda baiyi
da itaba tak’i ci shima kuma baici ba.
Ƙarfe takwas ne ta ɗanyi hamma tare da ɗan lumshe idanunta kana a hankali tace.
“Mun kusa isa? Saura awa nawa?”.
Yana ɗan jawo hannunta yace.
“Saura mana 2 Hours and 35 minutes, bacci kikeji ko?”.
Ya ƙare maganar cike da kulawa, kai ta gyaɗa mishi, ganin haka ne yasa ya jawota jikinsa tare
da cewa.
“Zo kiyi baccinki”.
Da sauri Goggo Dijan tayi sauri cire idonta daga kansu.
Ita kuwa yana jawota ya manna kanta a damtsen hannunshi lokaci d’aya bacci yayi awon gaba
da ita.
Ƙarfe 9 da minti 35 dai-dai jirginsu yayi landing a Qatar Airways tower.
Bayan duk sun shiga motocin.
A hankali ya kamo hannun Ishmah tare da nufar ɗaya daga cikin motar suna shiga.
Akaja motar tare da bin bayan sauran.
Tafiya mai tsawo sukayi.
Yayinda gaba ɗayansu suka ware idanunsu suna kallon tsari da shaharar ƙasar Qatar da da ta
wuce tunanin mai tunani.
Cikin buɗe ido Adam ya kalli Khadijah tare da cewa.
“Yah Sallam Anty Khadi Kinga duniyar da Allah ya kawo mu”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Ai ni nama rasa abin faɗa, wannan abu kamar aljanna!”.
Garkuwa kuwa a motar da suke sassayan numfashi ta fesar tare da baza ido tana ƙarewa Qatar
kallo tare da ƙudurtawa a ranta in sha Allah sai tayi littafin a Qatar.
Su Garkuwa ɗiɗɗiri sai baza na mujiya ake ana kallon kauyenci to ba fulatanar daji a tsakiyar
birni Doha.
Aunty Amina kuwa cikin sanyi tace.
“Allah ɗaya gari bambam”.
A motarsu Ishmah kuwa a hankali ta kalleshi cikin sanyi tace.
“Ya naga sunyi can mu munyi nan”.
Cikin kulawa yace.
“Su gida zasu wuce!”.
Cike da gajiya tace.
“To mufa?”.
Yana ɗan matsota yace.
“Zaki gani”.
Dai-dai lokacin kuma taga driver ya ɗan karya kwana ya fuskanci wani ƙaton gada daya yake
gicciye a tsakiyar tekun dake zagaye da ƙasar, da sauri ta rumtse idanunta saboda iya ganinta
ruwane a kwance bila haddin.
Tafiya mai tsawo sukayi kana taji an buɗe musu Gate.
Yah Salam shine abinda tace dai-dai lokacin da idanunta suka sauƙa kan wani Mashahurin
Hotel Rixos Gulf Hotel Doha, wani irin hotel ne na alfarmar kai da gani ma kasan bana yara
bane.
Wanda ke jan motar ne ya fito, tare da ɗaukar trollybag d’in Ishmah, kana suka fito suka bishi a
baya.
Sassayan numfashi mai nauyi ta fesar a hankali da ta kutsa kanta cikin Parlour.
Ya ilahi ya mujibat da'awati, sune kalaman da ta faɗa saboda wani irin ni'imtaccen ƙanshin gami
da sanyi mai kashe jiki da zuciyar ɗan Adam.
Jujjuya kwayar idanunta tayi tana ƙarewa Parlorn kallo a saman lips inta tace.
“Wannan a duniya ne haka? Ya Allah ka bamu aljanna”.
Sai kuma ta ɗan kalleshi jin ya kamo hannunta tare da amsar trolly bag din.
Shi kuwa driver’n juyawa yayi ya fita.
A hankali suke takawa har suka shiga cikin bedroom ɗin, a hankali ya sauƙe numfashi kana
yace.
“Shiga kiyi wonka, kafin a kawo miki abinci!”.
Yess tana son yin wanka Amman jin ni'imomin cikin ɗakin yasa taji wani irin sassayan bacci na
diro mata.
Shi kuwa Taj drawer’n dake kafe daga dungu har dungu ya ɗan buɗe mata side ɗaya tare da
cewa.
“Ga sleeping dress a nan in kin fito.
Ya ƙare maganar tare da sa hannunsa ya zaro wata tattausan jallabiya Black blue mai sheƙi,
kana ya fita Parlour.
Bayan tayi wanka ta fitone kuma ta kimtsa kanta cikin wasu soft sleeping dress na companyn
Gucci riga da wondo ne masu kyau da shek’i had’i da ɗan kaurin da zasu kareta daga tsananin
sanyin AC’n dake d’akin, rigar pink and white color ce, sai kuma white headband me kyau da
tasa a kanta tare da tubke gashin kanta, idanunta ta d’an lumshe alokacin da ta d’au d’aya daga
cikin unisex perfumes d’in da ta gani akan tsararren dressing mirror d’in dake d’akin, turaren me
suna Symphony na companyn Louis Vuitton ta fesa ajikinta, sosai kuwa kamshin yayi mata
dadi.
Cike da gajiya ta zauna a bakin gadon,
Da sauri kuma ta lumshe idanunta saboda jin kamar anayi mata lilone sunkuyar da kanta tayi
tana shunshunan kanta da kanta saboda jin yadda take baza ni'imtaccen ƙamshi.
Lokaci d’aya kuma sai ta kalli wayarta jin alamun an turo mata saƙo a WhatsApp.
“tana buɗewa kuwa taga Hamisu ne, sai kuma ta ɗan kalli saman profile picture d’inshi ganin
alamun yasa abu a status ɗinsa.
A hankali ta danna kanshi.
Cikin wani sanyi mai cike da gajiya kasala, ta zame ta kwanta a bakin gadon tana fuskantar
ƙofar shiga.
Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara silalo mata.
Dai-dai lokacin kuma Taj ɗin ya shigo sanye da jallabiya sai faman baza fitinannen ƙamshi mai
kashe jiki da zuciya yake.
Ido ya ɗan zuba mata ganin alamun bata ma san ya shigo ba, da fari yayi zaton tayi bacci ne,
sai da ya ɗan matso kusa kuma yaga idanunta na zubda hawaye.
Cikin sanyi ya fara takawa yana matsowa bakin gadon.
Tare da yawo da kwayar idanunsa akan dukka sassan jikinta.
Ahankali ya zauna a ƙasan gadon dai-dai inda kanta yake, cikin nutsuwa ya daidai ta fuskarsa
da tata fuskar.
Kana asanyaye cikin wani irin fitinannen yanayi mai hana zuciya sukuni ya kusan to da fuskarsa
tare da zira....
********************** ? **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************? **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko
kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI
HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ? **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ? **************************
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286:
*INDA RAI*
*AYASHA ALIYU GARKUWA*
*BOOK 2 PAGE 7*
“Bazan iya zama a gaban ka ba, kana suffanta min kanka da waɗanan mugaye, ƙazaman,
lalatattun, halayyar da nasan ba naka bane, kuma bazaka aikata ba, Wallahi tallahi bazan taɓa
yarda da kaiba koda zaka kwana dubu kana faɗa min waɗanan kalaman ne.
Please dan Allah Tajj kace min wasa kake min, kace min ƙarya Addawa tayi min, kasan na sani
cewa kai maitsarki ne kuma tsarkakken da zuciyata tasashi a sahun masu cikar imani kuma
nagartataccen da bani da haufi kan nagartarka Please dan Allah kada ka faɗa min kalaman da
zasu fasa min zuciyata”. Taƙere mgnr cikin Muryar kuka tare ysyyarfa hannu ɗaya, ɗaya kuma na bisa ƙirjinta.
Shi kuwa Tajj da sauri ya tashi tsaye tare dasa hannunsa ya kamo hannunta da take ta yarfawa
tamkar wacce ta ƙone.
Wani irin nannauyan numfashi ya fesar mai zafi tare da sakin ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya dake nuni
da kaso 50 na cikin dari na damuwar dake nuƙurƙusar rayuwarsa ya bar zuciyarsa.
Addawa kuwa tun sanda yacewa Ishmah yayiwa Laylah fyaɗe ta shigo da sallamar da basu
jitaba bare su amsa mata, gefensu ta tsaya a duk da basu gantaba.
Shi kuwa Taj cikin sanyi ya jawota jikinsa tare da yi mata amintaccen ruƙuma murya can ƙasan
maƙoshinsa yace.
“Babe haka akace wai ni nayiwa Laylah fyaɗe, kuma har Ummeey na da Yah Abana sunyi fushi
dani”.
Cikin jujjuya mishi kai da zubda hawaye tace.
“Karya ne Tajj wlh ƙazafi akayi maka! Ban yarda ba, baka aikata hakaba waye ce kai kayiwa
Laylah...”.
Sau kuma ta gaza ƙarasa kalmar.
Shi kuwa cikin sanyi kamar a narke mgnar ta fito.
“Meymey ce tacewa Yah Abana ni nayiwa Laylah fyaɗe, kuma Laylah ta tabbatar gashi tsorona
takeji”.
Da sauri ta ɗan janye jinkinta daga gareshi tare da jujjuya kanta tana faɗin.
“Allah ya isana ban yafe mataba, tayi ma ƙazafi mafi muni, ta rabaka da mutani mafi soyuwa a
gareka, tayi maka illar da har abada zuciyata bazan taɓa iya yafe mata ba”.
Sassayan numfashi Addawa ta fesar domin itama da fari taji tsoron ƙarshen kalaman Ishmah
kar tace bazata zauna da Tajuddeen ɗin ba”.
Ita kuwa Ishmah a hankali ta zame ƙasa ta zauna, wanda haka yasa shima ya zame ya zauna.
Suna fuskantar juna, guiwowinta na manne da guiwowinsa cikin sanyi da alamun ta fara
dawowa gayyacinta, tunda yace mata ance ne bawai shi da kansa bane yake jaddada mata
cewa yayi fyaɗen ba.
Murya a sanyaye tace.
“Allah ya isana bazan taɓa yafewa duk wanda yayi maka wannan ƙazafinba, Saboda an sawa
Al-AHLI AFISHA tabo mai wuyar mancewa, zan ƙare ragowar rayuwata dayi maka addu'o'in
neman sakkayar duk wanda yayima ƙazafin nan, da yi mishi addu'o'in tonon asirinsa da rashin
samun duk kwanciyar hankali a cikin burinsa kai harda addu'o'in ganin azab...” A hankali ta lumshe idanunta hawaye masu zafi na kwaranyo mata saboda jin yasa tattausan
tafin hannunsa ya rufe mata bakinta.
“A'a Babey banda addu'o'in azaba domin Bama fatan ko wanne musulmi ya faɗa cikin azabar
Allah”.
A tare suka kalli Addawa jin tana cewa.
“Alhamdulillah Ishmah kin kasance yadda muka zata, kin ƙarfafa yaƙini da Amincin Tajuddeen a
kanki, ko duniya duk zasu gaza fahimtarsa ke zaki fahimceshi.”
Shi ma Taj a hankali yace.
“Mar'atussaliha”.
Da sauri Addawa ta miƙe ta fita.
Ita kuwa Ishmah cikin sanyi tace.
“Tajj wannan ƙazafin ne yasa duk rayuwarka ta ƙuntata?”.
Kanshi kawai yake jijjiga mata dan baya jin zai iya mata cikekken bayanin a yanzu saboda yafi
son sai ƴan uwanta sun tafi baya kuma jin zai iya faɗa mata hukuncin Yah Abana na cewa in ya
sake yiwa Ummeeyshi mgn ko suka haɗu a kan auren iyayen nasa.
Shigowar Addawa da trayn abincin da ta shirya musune yasasu ɗan gyara zama a plate ɗaya ta
zuba musu tare, da ajiye musu spoon guda biyu kana ta tace.
“Bismillah kuci abinci shine abinda zai sama min nutsuwa, bari inje in kawo muku tea.”
Jim kaɗan da fitan ta dawo ga mamakinta ko taɓa spoon ɗin