Showing 15001 words to 18000 words out of 47460 words

Chapter 6 - In Da Rai Book 2 Complete By Garkuwa.pdf

Advertisement

06 Jul 2025

6550

fiskarta ganin su manya-manyan aranta tace ya akayi Taj
yasan har size ɗin Pant ɗina ahankali ta zaro Pant da Brassier duka farare ta ajiye kana ta
ɗauki Skin tied ta sanya ta kimtsa kanta tare da komawa cikin Weldrop ta dauki turaruka masu
daɗin ƙamshi kana ta fito.

Akan dining ta same sa already yayi serving abinci.
Ganinta yasa ya mike tare da jan hannunta ya zaunar da ita akujeran dake facing dinsa kafin
shima ya koma ya zauna.
Yana zama ya miƙa mata fork ɗin abincin.
Ajiyar zuciya ta sauke kana ta karɓa ganin acikin abinci akwai cheaps yasa ta sauke numfashi
tasan ko bata iya cin saura ba zata iya cin cheaps ganin ya zuba mata idanu yasa ta lumshe
Idanunta cikin langwaɓar da kai mai sanyi gami da rauni tace.
“Toh kaima Kaci mana”.
Cikin sanyi yace.
“Nafi bukatar naga ke kinci shine babban matsalata inga kin daina zubda hawaye sannan kina
cin abinci shine abinda zai iya samin farin ciki arayuwata”.
Numfashi ta fesar muryanta cike da sanyi da kuma rauni tace.
“Toh yanzu ina yin hawayene?”.
A hankali ya ɗan daura rafin hannunshi kan sajensa yana ɗan shafawa tare da cewa.
“Ko ba kiyi yanzu ba kinyi daren jiya kuma har yanzu ga idanuki akumbure alamun yau da safe
ma kafin kishiga wanka kinyi”.
Ya ida maganar yana kallon yanda Idanunta sukayi luhu-luhu dasu .
Shiru tayi batare da tace komai ba.
Muryar can kasan maƙoshi yace.
“Kinyi ko?”.
Kanta ta girgiza alamar batayi ba,
langwaɓar da kai yayi tare da cewa.
“Kinyi mana faɗa min gaskiya?”.
Idanunta ta lumshe tare da buɗewa tace.
“Toh ai ɗazune da nayi waya da Hamisu gaba ɗaya yasa Naji nayi kewan gida yana cewa gidan
mu ba daɗi ”.
Murmushi yayi kana yace.

“Ina ga zan hanaki yin waya da Hamisu ”.
Da sauri tace.
“Kayi haƙuri”.

Cikin ɗan murmushi da langwaɓar da kai yace.
“Toh ai yana samun ke kuka.
Ni kuma bana son abinda zai saki kuka ”.
Baki ta ɗan tura cikin shagwaɓa da rauni tace.
“Toh Kaci abinci mana”.
Kai ya girgiza mata alamun bazaici ba.
Cikin kwaɓe fuska tare da ɗan ture plate ɗin gabanshi tace.
“Nima bana son cin sannan kuma nima Taj”.
Sai kuma tayi shiru Idanu ya tsira mata yace.
“Kema me?”.
Kallonsa tayi sai kuma ta sunkuyar da kai.
Ahankali ya sake motsa laɓɓansa yace.
“Kuma me ki faɗa min”.
Batare data kallesa ba tace.
“Kuma mai ya hanaka bacci da daddare?”.
Kansa ya sunkuyar cikin rauni da sanyi yace.
“Bana jin bacci.
Bacci ya ƙauracewa idanu na Ma'eeshah na rasa yanda akayi bacci ya ƙini bansan ya za'a yi in
samu inyi bacci ba”.
Cikin sauƙe numfashi da tarin tausayinsa tace.
“Baka da lafiya ne?”.
Kai ya girgiza mata zazzafan Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa.
“Ka faɗa min mana”.
Araunane yace.
“Nima ban sani ba Ma'eeshah”.
“Toh Ni dai Kaci abinci”.
Ta ida maganar tana miƙa masa fork kusan tare suka ci abinci.

Jim kaɗan da gama cin abincin su,
su kaji ana knowking miƙewa yayi ya buɗe kofar ganin Dr Amdaz ne yasashi ɗan sakin fuska
tare da mishi sannu da zuwa.
Cikin alamun sabo da shaƙuwa da alamun yawan magana Dr Amdaz yace.
“Barka da safiya Dr”.
Anutse Taj ya amsa tare da bashi hanya.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Ishmah tare da cewa.
“Ma'eeshah tashi ki shiga ciki”.
Kai ta gyada tare da mikewa Akuma dai-dai lokacin Dr Amdaz ke cewa.
“Barka da safiya Amarya”.
“Barka dai Dr”.

Ta faɗa tare da shiga bedroom...

Dr Amdaz kuwa kallon Taj yayi kana yace.
“Dr naxo da duk Doctors ɗin fa ”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Ba matsala ka shigo dasu ai zama zamuyi dasu gaba ɗaya ne za muyi meeting ɗin”.

Fita yayi jim kadan ya sake shigowa mutum tara na biye dashi shida daga ciki maza ne sai mata
uku. shine cikon na goma suna shiga suka zauna a Falon.
Dr Amdaz kuwa gefe sa ya zauna tare da cewa.
“Wa'annan sune manyan Doctors ɗin mu ko wanne da fanni daya karanta akwai Brain Dr, Skin
Dr, Eyes Dr, Teeth Dr, heart Dr, ko wanne problems muna da Dr'nsa da kuma magungunansu
maganinsa.
Kai Taj ya jinjina cikin gamsuwa yace.
“Masha Allah”.
Dr Amdaz kuwa zamansa ya gyara tare da faɗin.
“Dama nace yau kayi zama da Dictors gobe kuma Norse's.
Sai Jibi kuma in Allah ya kaimu kayi zama da Cleaners da sai sauransu”.
Cikin gamsuwa Taj ya jinjina kansa kana yace
“Eh hakan ne yayi abi komai step by step”
Daga nan suka Cigaba da tautauna sauran abubuwa daga bisani ya ɗauki key ɗin office da
muhallin ko wani Dr ya basu tare da tsaida ranakun zuwansu da lokaci da kuma dakarun su
daya kasance mai gwaɓi, ya ƙara da faɗin satin firko da zasu fara aiki komai kyautane zasuyi
duk nauyin ciwo da maganin da zaici. Sosai sukaji daɗin haka mussaman da suka kasance duk musulmaine sai biyu daga cikine ɗaya
ba India ne da addinin hindu ɗaya kuma ahlul kitab ne, wanda da kyar Amdaz yasashi ɗaukarsu
sabodo kwarewar su da kuma nuna mishi ai zasuyi fatan su kasance tare dasu su zama
sanadin musuluntarsu. Cike da jin daɗi sukayi godiya kana suka ci gaba da tattaunawa da yadda zasu tallata asbitin..

Acan gidan Addawa kuwa da yammaci suna zaune Garkuwa ce da Aunty Nana suka kalli
Addawa jin tana cewa.
Zulaihat tashiga kitchen tayi musu girki.
Murmushi garkuwa tayi tare da cewa.
“Addawa bari mu shiga mu taya ta girkin ai abin ya mata yawa ita kaɗai take ta fama”.
Addawa na gyara zama tace.
“Zata iya ai Zulaihat nada ƙoƙarin”
Zulaihat na gab da shiga kitchen tace.
“Allah Aunty Ku huta”.
Khadija na miƙewa tace.
“A muje dai na tayaki”.
Aranta tace gwara dai muje mu ga abinda za'a mana Kada ayi mana abincin Larabawa ko na
Amharic wanda ba lallai mu iya ciba.

Daga nan suka shiga kitchen kana su kuma suka ci-gaba da hiransu.

Aunty Nana dake ƙoƙarin kunna gas tace.
“Wai ni har yanzu ba wanda yayi waya da Ishmah?,”.
Khadijah na ɗauraye tukunyar tace.
“Wai ke me matsalar ki da sai kinyi magana da ita na rasa mene matsalar ki yanzu fa da da ba
ɗaya bane da in kina tunanin cewa Ƙanwar mijinkine tana zaune agida yanzu fa matar Aurece
kuma gurin mijinta take”.
Adai-dai lokacin kiran Ishmah ya shigo wayar Aunty Nana murmushi tayi tace.
“Ƴar halak kinƙi ambato”.
Ta kai karshen maganar tana amsa kiran tana ɗauka tace.
“Ohhh Ikon Allah yanzu dan Allah dan Annabi Ishmah ina kika shiga tunda muka zo ba amo ba
labarinki.
Kinje kin rungumi mijinki kunyi shiru wannan abu har ina daga ke har Taj ɗin kun bani kunya".
Cikin sanyi Ishmah tace.
“Wallahi nikam ba ruwana dan ko yatsana bai riƙe ba har da cewa wai na rungumi miji ance Miki
ni irinki ne!?”.
Dariya Aunty Nana tayi tare da faɗin.
“Ai dake irina ne da tare zamu zauna kawai sai naga mutum ya canza hanya da ban toh yanzu
ina kuke?”.
Cikin sauƙe numfashi ta faɗa mata sunan hotel ɗin da suke.
Aunty Nana na dariya ta juya ta kalli Garkuwa tare da cewa.
“Kin gani ko Garkuwa wai fa a Hotel suka sauka yanzu yaushe zaki dawo?”.
Ahankali Ishmah ta girgiza kai tare da faɗin.
“ Nima ban sani ba Aunty Nana anma anjima idan ya shigo zan baki ki tambayeshi”.
Dariya Garkuwa ta sanya kana tace.
“Madallah kinyi min naganinta”.
Kana ta karbi wayar suka ci-gaba da hira...

Aranar dai haka Taj ya yini tattaunawa da Likitocinsa koda suka gama ranar ma haka ya kwana
kamar jiya baiyi bacci ba Ishmah kam bacci take shi kuma yana zaune bakin gadon yana karatu
idan ya ɗan gaji da zaman yayi nafila haka nan zuciyarsa ta gaza amsar hukuncin Yah Abana ji
yake yi ya rabashi da dukkan farin cikinsa a hankali ya ɗan juyo ya kalli Ishmah da ta ɗanyi juyi
tare da matsowa gab da bakin gadon murya cike da bacci tace
“Tajj kayi bacci”. Sai kuma ta ƙare maganar tare da kife kanta alamun cikin bacci tayi mgnar
kuma baccin ya kuma danneta, sassayan numfashi ya fesar tare da gyara zamansa ganin
fuskantar a kusa dashi a matsayin matar sa kaɗai ne ke sawa yaji zuciyarsa ta ɗan samu
sassaucin tarin damuwarsa da ta kauda dukkan shauƙin jiki da zuciyarsa gami da ruhinsa....
Washe gari da safe Ethiopia.
Meymer ce zaune gaban Momynta.
Cikin tsuke fuska Momyn Meymer tace.
“Toh Meymer kin dai yi abinda kike so”.

Cikin matsanancin kuka da zubda hawaye tace.
“Momy me nayi?,dan Allah ki daina cewa nayi abinda nake so”.
Cikin takaici tace.
“Meymey kin sani na sani kinyi abinda kike so Afif ya sake ki ko?”.
Kai ta gyada cikin gamsuwa da jin daɗi tace.
“Eh”.
Cikin rashin walwala tace.
“Shawar da zan baki ki fara Istigfari kafin Sakayya yazo ko Ubangiji zai kawo Miki Sakayyan da
sauƙi”.
Da sauri tace.
“Wallahi Allah Momy ba abinda nayi mishi Momy abinda ya aikata fa aka faɗa banyi masa ƙazafi
ba”.
Cikin tarin takaici Momy tace.
“Ni dai ban nemi ƙarin bayani ba, abinda zan faɗa Miki ki kama kanki ki riƙe kanki da Dr
Zakariyya duk abinda zakuyi sai ki bari sai kin gama Iddah kafin ku fara maganar Aure”.
Cikin sauri tace.
“Momy nifa babu Iddah akaina tunda mu kayi Aure da Yah Afif ko hannuna bai taɓa riƙe wa ba”.
Wani kallon takaici Momy ta watsa mata kana tace.
“Ni dai ban nemi wani bayani ba kawai kiyi zaman Iddah kafin kuyi aure da Dr Zakariyya dan
nasan shine aranki”.
Ta ƙare maganar tana mai jin takaicin rabuwar Auren Afif da ƴarta...

Acan gidansu Adaya kuwa Ummi ce da Aminullah tsaye a falo bisa alamu aike ta yiwa
Aminullah yanzu ya kawo mata cikin mamaki ta buɗe ido ganin Adaya ta fito tana tafe cikin
rausayawa bisa duk kan alamu zata tafi Reharzal ne cikin tarin takaici da bakin ciki ya kalli
Ummi itama Ummi kallonsa tayi . Cikin jujjuya kafada da jijjiga ƙirji tace
“Toh Ummi na tafi ”.
Cikin tarin takaici da Mamaki tace
“Ina zakije Adaya?”.
Ɗan wara idanunta tayi tare da faɗin.
“Ummi kin manta kwana biyun nan ƙuguna da yake ciwone yasa ban samu na naje Reharzal ba
yanzu fa wata biyu ne fa kacal ya rage mu tafi India gasar rawa Ummi ki tayamu da addu'a”.
Cikin tashin hankali Ummi tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un dama har yanzu Adaya wannan gasar rawar yana ranki”.
“Eh mana Ummi ”.
Ta faɗa tare da ficewa a falon.
Cikin kunci da tarin damuwa Aminullah yace.
“Badan ciwo ba daɗi ba da nace ciwon daya. dami Aunty Adaya ya dawwama ajikinta har
Abada saboda ta nutsu ta daina abinda takeyi”.
Cikin sanyin jiki da karaya da lamarin Adaya Ummi ta zauna kan kujerar tare da dafe kanta da
hannunta duka biyu.

Adaya kam tuni ta fita tana isa hall ɗin da suke Reharzal ɗin duk suka miƙe tsaye saboda jin an
saki wani irin....
*Kunsha typing errors dan banyi editing wannan page ɗin ba*



*BY*
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286:

*INDA RAI*

*BOOK 2 PAGE 3*
*AYASHA ALIYU GARKUWA*






*Lockpage*


Ido suka zuba mata cike da farin ciki Aunty Nana ta juyo ta kalli Garkuwa dake murmushi sai
kuma ta kalli Ishmah dake raɓa gefenta, kai a sunkuye tana tafiya ne cike da sanyin jiki da
kaɗuwa da dukan ba zata da kalmar aurenta ya saki mata, gami da raunin da ganin Taj a cikin
yanayin da yasa har yanzu hawayenta basu tsagaita zubar da sukeyi ba. Cikin sanyi Aunty Nana ta ɗan jujjuya kai, tare da ɗan juyawa ta nufi hanyar fita saboda haka
nan taji rauni yana diro mata.

Ita kuwa Ishmah tana shiga bisa gadonta ta faɗa tare da sakin sassayan kukan da yaƙi
dannuwa.

Da sauri Garkuwa ta biyo bayanta.
A gefen ta ta zauna tare da kamo hannunta ta tada ita zaune, cikin sanyi da tausasa zuciya
tace.
“Haba dai Ishmah, wannan shine irin godiyar da zakiyiwa Allah? Hakan bai cancanci
nagartaciyar mace irinki ba, ki sani fa ɗan adam baya tsallake ƙaddararsa, kuma duk
managarcin musulmin da ya cika mumuni na gaske, amsar ƙaddara yakeyi a duk san da tazo
mishi, a kuma duk yanayin da yazo mishi.” Sai kuma ta ƙare maganar tare dasa hannunta ta jawota tsaye.
“Shiga kiyi al'wala kizo kiyi salla, ki godewa Allah da ni'imar da yayi Miki, na mallaka Miki miji
mafi daraja da tsada a cikin mazaje, miji irin wanda ko wanne uba yakewa ɗiyarsa fata da

addu'ar sumu.
Ishmah ki sani fa cewa Allah yayi Miki ni'imar mafi ƙololuwar ɗaukaka, ni’imar samun mallakar
Sheykh Afif Muhammad Taj a matsayin mijin aurenki, Kin fini sanin waye Taj domin kece mace
mafi kusanci dashi a duniya, harma da mahaifiyarsa tunda yanzu zaki rayu a ƙarƙashin inuwar
aurenshi, zaki zame mishi sutura, zai zame miki sutura, kana garkuwanki”
Wasu irin tafassasun hawayene masu tafe da tsananin tsoron Allah da girgiza da girman ikonsa
da ƙudurarsa, wai yau itace Aisha Ishmah ake kira a matsayin matar Taj ya Salam.
Shine kaɗai abinda ta iya cewa.
Dai-dai lokacin kuma Aunty Amina wacce take ƙanwa ga Daddy, ta ɗan juyo ta kallesu lokacin
da ta fito daga bathroom bisa alamu al'wala tayi.
A hankali ta matso kusa dasu tare da tallafe habar Ishmah tana faɗin.
“Mu yau duk faɗin family d’in mu, cike muke da tsananin farin ciki da bazai misaltu ba, saboda
haka dan Allah kada ki raunata mana zuciya shiga kiyo al'wala”.
Kai ta jinjina tare da juyawa ta nufi Bathroom ɗin.
Bayan tayi al'walan ta fitone itama Garkuwa ta shiga tayi.

Bayan sun idar da sallan isha’i zaune suke a tsakiyar Parlour kowa da abinda ke gabanshi.

Cikin kulawa Garkuwa ta ƙara turo mata plate ɗin da ta zuba mata dungulen zabuwar.
“Dan Allah ki cinyeta, dan so nake inga kin cinyeta kafin Oga yazo, dan yace yau da kansa
zai-zo ɗaukata dan yana son yayi wa Abba murnar auren Boɗɗinsa”.
A hankali ta ɗan kalli plate ɗin wanda ta ci kusan rabin zabuwar, fork ɗin hannunta tasa, tare da
ɗan sabulo tattausaar tsokar da magunguna suka sa tayi baƙi, ido ta rufe lokacin da ta kai
tsokar cikin bakinta.
“Ai nima yau bazan tafi ba, sai ta cinyeshi”.
Cewar Aunty Hauwa.
Fuska ta ƙwaɓe cike da rauni tace.
“Cikina ya cika fa”.
Kai Aunty Amina ta gyaɗa tare da cewa.
“Ba matsala Garkuwa bata damun tasha, anjima kan mu tafi zata ƙarasa zabuwar”.
Ta ƙare maganar tana kai cup ɗin ruwa bakinta.

Aunty Maryam da yanzu ta shigo ne tace.
“Ai kada ku damu a barmin wannan aikin, ni daɗi nake ji inga na tisa mutun a gaba yasha
magani”.
Cikin sanyi da ya gaza barin ruhi da jinkinta tasa hannunta ta amshi kwanon Ƙasaitacciyar
mace da yake ɗauke da damun.
Lumshe idanunta tayi domin sosai damun yayi mata daɗi a bakinta sai dai, ina cikinta ya cika
rabi tasha kana ta ajiyeshi.
Tana hamdala domin tun safe bataci komai ba.

Ƙarfe tara dai-dai duk ummomin ta suka tafi, bayan sun jaddada wa Garkuwa ta bata ta cinye

sauran.

Ƙarfe goma dai-dai, Oga ne, zaune da Abba a falonshi tare kuma da Taj.

Sosai sukayi hira daga bisani.
Sheykh ya kira Bobbuga rumbun Abboi ɗinsa ta fito su tafi.

A hankali ta sauƙe numfashi tare da cewa.
“Yauwa yanzu dai hankali ya kwanta tunda kin ƙarasa kazar, kin shanye damun kuma”.
Cikin sanyi Ishmah ta ɗan shafa cikinta da bazakace a ciki zabuwar nan da damun nan sunka
samu muhallin zamaba.
Sai kuma ta ɗan kwaɓe fuska jin Garkuwa na cewa Maryam.
“Akwai kuma haɗin jan Nama dama na dafa mata, yana cikin fridge da safe ki ɗumashi sai ki
bata ta cinye, garukan nan kuma dasu tsumi, sau uku zata rinƙa sha safe da yamma, da rana”.
Da sauri tace.
“Toh wannan kam sune zasu zama abincina ko yaya, zasuyi min yawafa Aunty Garkuwa”.
Murmushin tayi tare da ɗaukar mayafinta tana yafawa tace.
“Ai haka nakeso suyi miki yawan, Sheykh Afif ya banbance tsakanin aya da tsakuwa.”
Tana gyara mayafin jikin ta, ta fara binta a baya ganin ta nufi hanyar fita tana faɗin.
“Toh Maryam na barku, da aiki.
In sha Allah zuwa jibi kuma zan turo mata dahuwar zuciyar farin rago.”
Suna fita Maryam tace.
“Kada ki damu, mun gode sosai a gaida gida”.

A hankali suka iso harabar gidan.
Tsaye suka samu Oga da Taj.
A hankali suka ƙaraso kusa adasu dai-dai lokacin da Sheiykh ke cewa.
“Wannan ba matsala in sha Allah, zanyiwa Capting Sadik sale mgna akan visa ɗin, masu
rakiyar tunda nasan na ango da amarya kam can ne zasuji daku”.
Cikin sanyi Taj ɗin ya bashi hannun tare da cewa.
“Amman dai za'a bamu aron Garkuwa ko, tayi mana rakiya”.
Da sauri duk suka kalleshi jin yana faɗin.
“Kai kuyi haƙuri bazan iyaba”.
Cikin sanyi Taj ɗin yace.
“Haƙuri zakayi”.
Yana ɗan murmushi yace, .
“To yanzu dai bari muji ta bakin Sadik ɗin muji ko zaku samu visa ɗin, duk yadda mukayi dashi
zakaji ni”.
Ya ƙare maganar tare da bawa Taj ɗin hannunsa sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login