Showing 33001 words to 34531 words out of 34531 words
Chapter 12 - SIGN MARRIED 2 BOOK OUM HAIRAN.pdf
jijiya ta fito ya damƙi jijiyar yasa cellular a
jiki ya fara matsa mata allurar a hankali yanajin kamar jikinsa take shiga, baiso taɓata ba amma
bazai iya jure zamanta cikin wannan sumar ba shine kawai dalilinsa nayi mata allurar bayan ya
gama ya zare drip ɗin ya ɗaura wani ɗan ƙarami bayan ya zuba wasu magunguna a cikinsa ya
jona mata wata Na'ura ya haske mata fuskarta da ita, ita dai Mom tana gefe tana kallon ikon
Allah duk yazo ya hargitsa ɗakin, koda likitocin ma suka shigo basu iya ce masa komai ba to
masu abu da abinsu ai saidai suja baya suyi kallon ikon Allah.
Cikin ƙasa da awa ɗaya suna tsaye suna kallonta sukaga ta fara motsa ƙafarta can ta saki wata
ajiyar zuciya me ƙarfi ta fara ƙoƙarin daga hannunta tare da matse idanunta tana motsa bakinta
alamar magana zatayi, matsawa yayi ya janye wannan fitilar ya kasheta ya zauna a gefenta ya
kamo hannunta ya buɗe bakinsa cikin nauyin furuci yace “Sorry Bea" da wata muguwar azama
ta janye hannunta ta fara ƙoƙarin tashi yayi saurin riƙeta ya tsugunna daidai kunnenta yace
“Bakida lfy ba'a buƙatar motsi me ƙarfi Bea me kike buƙata?" Saurin buɗe idanunta tayi ta
saukesu akansa ta kuwa ƙwalla ƙara tana cewa “Ka fita Ni ka fita ka fita nace mugu mara
tausayi....."
Duk da cewa baya cikin yanayi me daɗi yanda take acting taji maza role Saida abin ya bashi
nishaɗi ya sunkuya daidai kunnenta yace “Au haba! Ashe mijinki bashida tausayi" ayyah so sad
sorry Na tausayawa matar mara tausayi, raguwa dake sai kauɗin bala'i daga ihu ɗaya har
murya ta dashe Miki"..... Dundu yaji Mom ta sakar masa a baya yayi ƙasa tare da sakin yar
siririyar ƙara yace “Ohhhh Mom! Cewa fah tayi banida tausayi...." Watsa masa ruwa tayi tace
“Idan baka ficemin anan ba zanci ubanka Ma'eesh jeka bana buƙatarka" sosai kai yayi yace “Ok
na gama nawa dake na dawo Miki da wannan raguwar Inlow ɗin taki hayyaci is good zamu sake
jamewa yarinya sai anyi miki ɗinki har a baki"
Duka Mom takai masa ya fice yana dariya tace “Zanyi maganinka ne Ma'eesh dani kake
zancen" shidai mota ya shiga ya nufi gida yana shiga suka haɗu da Deen suka gaisa yace
masa “Ya me jikin?" Shafa sumarsa yayi yanajin kunyar ƙanin nasa yace “Ta fa ji sauƙi dama
raki ne kawai irin nata" murmushi yayi yace “Ai ka fita raki Ni wlh ba ƙaramin tsoratani kayi ba
jiya da dare" murmushi yayi suka shiga ciki a dinning suka zauna suka fara breakfast ya kira
Nuwairah yace ta shirya masa nasu Mom yana rufe baki suka shigo Batool na kwance jikin
Mom idanunta ya sauka kan Deen da yayi saurin yin ƙasa da nasa idanun saboda wata faɗuwar
gaba daya riski kansa a ciki nandanan duk wata walwalarsa ta gudu, kowa yana musu sannu da
zuwa banda shi da kamar ma ya tafi wata duniyar daban.
Miƙewa Ma'eesh yayi da nufin taimakawa Mom ta kaita ciki ta tureshi tare da sakawa Mom kuka
tace “Ni ka tafi ka barmin nan banason ganinka" dariya sosai abin yake bashi yace “ok na tafi
Bea sai nazo ɗaukanki anjima" yana faɗin haka ya kalli Deen daya miƙe ya fice shima ya fice
kowanne ya nufi part ɗinsa. Kwanciya yayi sosai yakejin bacci bashi ya farka ba Saida yaji ana taɓa ƙofar ya tashi yasa
rigarsa ya fito tare da buɗewa, Samha ce ta gaisheshi ya amsa tare da cewa “Tana part ɗin
Mom" juyawa yayi ita kuma ta nufi part na Mom ta ishesu a parlour har yanzu akwai ragowar
yan biki a part ɗin na Mom suka gaisa Mom ta kalli wata dake gefenta tace rakata ɗakina baƙin
Matar MB ne"
Rakasu tayi suka taddata kwance ƙudundune cikin duvet saman lafiyayyen gadon suka zauna
Tare Da buga pillown da kanta ke kai, ta sauke ajiyar zuciya tare da wani zabura zata tashi
Samha tace “Haba amarya yada tsorata haka?" Ajiyar zuciya ta sauke tana gyara kwanciyarta
ta zubawa Samha ido can tace “Allah ya isa wlh duk ke kika jamin masifar nan Saida nace Miki
bazan auri Deen ba kika matsa har Saida kikaga na yarda ashe shima makasata zai kawoni,
jiya na saddaƙar ma na mutu na gama wai sai ɗazu Nuwairah take faɗamin ashe Farkeni
wancan mugun mutumin yayi zai haɗemin gindi da takashi daƙyar Allah ya cetoni bayan nasha
ɗinki kamar ƙwarya wannan bala'i har ina nikam wlh ƙafarku ƙafata.
Dariya sosai Samha tayi tace “Waini ya kuka ƙare ne har bis ta ɗaurin sin haka da wuri banyi
zato ba fah, koda yake ai dama yafi zuma zaƙi nasan ko bezo ba ke kyaje" yunƙurawa tayi ta
tashi tace “Ni wai meye yake faruwa Samha har yanzu a duhu nake kuma naga ɗazun da muka
dawo daga asibiti Deen ko kallona baiyi ba shikam wancan mugun Saida Mom ta koreshi
sannan ya haƙura ya tafi"
Murmushi Nuwairah dake gefen Batool a zaune tayi tace “Dama fah dashi aka ɗaura aure bada
Akheey Deeny ba kinsan yanda abin ya faru?
Tun ranar da Baffanki yace ki tura mai number Deen zasuyi magana ranar ne komai ya faru ya
faru a wannan ranar bayan sunyi waya da Deen shima ya tura masa number Shaikh
Muhammad Saleem ne suka yanke washegari zasu kawo kuɗin aure da sadaki domin dama a
lokacin suna Abuja su duka. Haka kuwa akayi ranar suka kai komai aka tsai da biki wata guda, Aikuwa take Deen ya haɗa
hotonki da nasa ya fara bazawa a media tare da turawa makusantansa don neman addu'arsu a
wannan aure da zaiyi, kinsan meye ya faru? Kawai Muhsin yana kwance a cinyar Mom yana
zuba mata taɓararsa kawai yaji ta zabura tace “Innanillahi wa Innah ilaihirraji'un" abinda ya
janyo kowa dake parlourn har Nuwairah dake shigowa suka nufeta da sauri ganin yanda jikinta
ke rawa, da sauri ta nufi Abbuh ta nuna masa hoton tace Abbuh wannan ba matar Ma'eesh
bace wadda ta ɓata yaketa nemanta tsayin shekaru kusan uku?" Duban hoton abbuh yayi sosai
tare ɗagowa yace “Anya kuwa Sukhaina kinsan fah buzuwa ce wannan ita kuma waccan ba
ance bakanuwa bace Ni kinsan dake bansanta ba" daidai nan kira ya shigo wayar Abbuh
number Shaikh Muhammad Saleem ne don haka ya ɗaga da sauri Saleem yace “me nake gani
ne Hakeem yarinyar nan da Deen zai aura matar ɗan uwansa ce Batool wadda ta ɓata ɗinnan
fah" Nan Abbuh ya sauke waya tare da zama yana furta “Innanillahi wa innah ilaihirraji'un"
dukkansu zama sukayi zugum cikin rashin abinyi daidai lokacin Ma'eesh ya faɗo parlourn a
hargitse alamar da take nuna yaga abinda ke faruwa zama yayi a ƙasa jikinsa na rawa yana
dafe ƙirjinsa take ya fice daga hayyacinsa abinda ya ƙara tashin hankalin kowa suka
cukuikuyeshi sai asibiti a nan ake faɗawa Deen maza ya dawo Ma'eesh babu lafiya, washegari
kuwa sai gashi dama dake ya shirya tahowar nan fah aka koma kallon kallo kowa yaƙi faɗa
masa musabbabin ciwon na Ma'eesh domin kuwa shima alama ta nuna idan yasan dalilin ciwon
zai iya shiga hakan tunda anyi lokacin da akace bazaa basa aurenki ba angani.
Saida Ma'eesh ya kwana uku a wannan hali sannan ya dawo cikin hankalinsa yana tashi kuwa
yasa Deen dake kula dashi ya kira masa Mom, dawowa sukayi tare ya sake dubansa yace ina
Abbuh?" Shima kiransa akayi suka zauna ya sauke ajiyar zuciya ya buɗe baki a wahale yace
“Don Allah ko zai zama ajalina kar kuce zaku hanashi auren Batool Mom na haƙura na bar
masa ita ba rabona bace"....... Rufe masa baki yayi yace “Aa Bro bazai taɓa zama haka ba indai
Fateemah itace yarinyar da kake ciwon nan a kanta to ka ƙaddara taka ce Ni na haƙura domin
ka fini sonta kuma ka fini buƙatarta sannan itama kai takeso kullum burinta Daddyn Jany a
rashinka ne ta karɓeni ko yanzu ta sameka bazata kalleni ba, nasan zakayi mamakin yanda
akayi na sani, Jiya da yamma Abbuh Saleem ya kirani yake faɗamin abinda ke faruwa sai a
lokacin ne na gano dalilin da yasa a farkon neman aure na da Fateemah danginta sukace
bazasu bani ba har suke cewa nine mahaifin Jany ashe da gaske Ni ɗin ne, ƴar ɗan uwana ce"
Murmushinsa ya faɗaɗa yace “Wlh duk yanda nakejin Fatimah a raina Ni nasan tafi dacewa
dakai sannan ko ba kai bane sanyi wannan sadaukarwar Bro kayimin alfama kar kace min a'a
sannan Inason a ɓoye mata kai so nake na baka ita as surprised nasan zatayi farin ciki da
hakan" da wannan ya zari layinsa da kika sani ya bawa Mom yace duk maganar da zakuyi da
Ma'eesh kuyita da layin a zuwan shine, tun daga wannan lokacin ne kuma komai ya canza
shirin biki ya koma na Ma'eesh akeyi bana Deen ba har kawo yanzu da kika tabbatar da waye
mijinki a cikinsu".............
*Promo price 300 VIP 600 today only, via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay*
*Contact of evidence*
*09031307566*
*OUM HAIRAN*