Showing 15001 words to 18000 words out of 34531 words

Chapter 6 - SIGN MARRIED 2 BOOK OUM HAIRAN.pdf

jiƙamin aiki ji nake dama abani
dama yau ɗin nan!"





Cike da kunya ta zame hannunta ta zauna tana sunne kai kamar wata muminar gaske tace
“Noor kasha hanya, ya gajiya" lumshe idanunsa yayi yace “Bangaji ba sai yanzu dai kike gajiyar
Dani" Sosai sukayi masa sauka me kyau shayinsu na buzaye shine yafi komai burgeshi yasha
shayi babu ƙarya a ƙarshe yake faɗa mata Sudan zai wucce ya dawo ya tarar Mom da Dad
duka suna can daga can kuma zasuyi waya da ita a basu lokacin da zasuzo ayi komai a gama a
tsayar musu da lokacin bikin.
Itadai batace masa komai ba haka Inna tace ta rakashi ya gaisa da uwayenta suna tafe cikin
garin cike da shauƙin juna zuwa yanzu da gaske zuciyar Batul ta fara buɗewa a hankali ta fara
koyawa kanta soyayyar Deen, yanda hadari ya lulluɓe sararin samaniya ya ƙarawa yinin
masoyan armashi suna tafe suna hirarsu ta ƙauna har suka isa gidan me gari sukayi Sa'a yana
zaune a faɗa shida yan uwansa suna ganinta suka washe baki Baffa Lame yace “Aa ta Manzo
yanzu muke tamtamnawa akanki sai gaki dama ɗiyan halak yaƙi ambato kice baƙo kikayi daga
birni" zama tayi cike da kunyar iyayen nata suka gaisa da Deen tayi ƙasa da kai sunason tayi
masu bayani ita kuma kunya ta hanata.
Sai shine yayi ƙarfin halin gabatar da kansa sukayi shiru na lokaci kafin daga bisani Mal me gari
yace “Ta Manzo bamu guri ko?" Cike da girmamawa da kunya ta tashi ta fice tana fita Suka
haɗu da Almustapha a ƙofar fada yace “Yawwa amaryata dama yanzu nake shirin zakkuwa
gareki ance kinyi baƙo daga Nigeria cikin ɗiyan iskan da sunka ɓata mani rayuwarki ko? To
maza ki dakatar dashi zowa gareki ki hwaɗi masa niya ammijinki yanzu haka taɗi yaje gaba ga
manya kinjiya"




Wani mugun kallo ta watsa masa tayi gaba abinta Zuciyarta na rawa ita kam bata yarda da
wannan zama da akace Deen yayi ba to me zasu hwaɗi mashi da sai batta gurin?" Ji tayi an
damƙi hannunta ta juya taga Mustapha ne yake mata wani kallo yana washe mata baki takaicin
yanda yake mata kallon ne yasa batasan sanda da zuba masa wani mari ba, ta ja da baya da
sauri tana huci idanunta ya kawo ruwa tace “Mustapha tun ranar da na shigo garin nan nasan
akwai irinku da yawa marasa tarbiyya marasa ɗa'a kuma marasa manner ta furuci, don Allah
kar mu ƙara gauraya dakai a gonata zan keta alfarmarka....."
Cikin bala'i yayo kanta Anwar dake tsaye nesa dasu yayi saurin janyeta hakan ya kara fusata

Mustapha yace “Har kece zaki cewa wani bashida tarbiyya shin ke waye ya baki tarbiyyar
Sallamamen Uban naki da shima bai isa ba gurin gyatumarki ko kuwa ita Laure idon Naira ɗin
ce ta baki tarbiyyar da saboda kin kwankwaɗi ta har kikayo ɗiyan dakan kuka a gantalin barikin
naki yo bandama anason taimakonki mi zaayi dake Ni aggareki balle ki bani guri duk an
rarakeshi......"
Wani marin Anwarr ya zabga masa daya sanyashi zubewa a ƙasa yana tashi kuwa ya zare
takobin dake rataye a jikinsa yayi kan Anwar ya ɗaga zai buga masa tayi kukan kura ta shiga
gabansa Aikuwa Allah ne ya kiyaye ya sauke mata ita a allon kafada a Anwar ɗin yayi mata
daukar jaririya ya kauce da ita daga gurin shima ya zare tashi takobin yayi kan Mustapha yana
huci abinda ya sanyata fasa ƙarar data sanya uwayen nasu fitowa daga zauren Mal me gari
daƙyar suka raba rigimar suna muzurai suna cin ƙwafa kowa aka janye shi inda ita kuma Deen
yazo ya kama hannunta suka bar gurin duk jikinta yana rawa.




Inda motar data kawo shi take nan suka nufa har yanzu kuka takeyi wannan shine karo na uku
a zamanta na sati ɗaya a garin nasu da akayi mata gori akan ƙaddarar da bata zaɓeta da kanta
ba sosai ranta yayi kunci takejin bazata yafewa duk wanda yayi silar ɓata mata Future ta
rayuwa ba, durƙushewa tayi ta saki wani marayan kuka daya ƙara tashin hankalin Deen daɗi da
wanda yake ciki ya tsugunna gabanta yace “Sunce bazasu bani aure ba Ni bare ne, sunce
sunada samari a wannan dangi da yawa marasa aure ciki ma akwai biyu da suka nuna suna
son aurenki Fateemah na fito da wannan raɗaɗin tashin hankalin me maimakon ki kwantar min
da hankali sai ki ƙara jefani a tashin hankali meye yasa zasu hanani ke bayan na riga na gama
lissafa rayuwata dake Fateemah don Allah kar su rabani dake kome sukeso xanyi musu in
sunaso na dawo rayuwa a cikinsu ne ma na yarda a nemamin fili xanyi gini zansai raƙuma zanyi
naɗi Wlh Fateemah har yawon tallan kanwa in sunaso zanyi inda akanki ne"
Sake rushewa tayi da kuka tace “Meyesa ƙaddarata ta zama mummuna Deen ban zaɓi
rayuwata ta zama a haka ba, ban shiryawa ƙaddara me muni ba amma ya zanyi an gina
rayuwata da tubalin toka yayi kyau amma daga ƙarshe bai ƙarko ba Nuraddeen bantaɓa riskar
rayuwa me ƙunci irin rayuwar da nayi da Daddyn Jany ba duk kuwa da na soshi bantaɓa
tunanin gujewa muradansa ba duk kuwa da nasan gaba zasu ƙalubalanceni, Nuraddeen
Meyesa bazasu barni nayi nesa dasu ba zasuce a cikinsu zasuyimin aure bayan duniya bata
taɓa yimin goron ƙaddarata ba Saida na dawo cikin dangina, ƙaryane Nuraddeen bazan iya
aure a wannan ahlin ba ko kowa bazai fahimceni ba ni zan fahimci kaina so nake Jany ta rayu
kamar kowa taya zan yarda da rayuwa cikin mutane masu ƙabilanci irin DANGINA"........



Idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur ya ɗago yace “Yaushe zaki koma Austaralia?" Girgiza
masa kai tayi tace “Bana burin sake barin ƙasata batare da aure ba ina gudun ƙaddarar da tafi
wacce ta gabata muni ta faɗo rayuwata don Allah Nuraddeen don Allah ka yarda duk wuya kace
saini nima zance sai kai bayan iya karɓar ɗayan waɗanda suke shirin zaɓamin ba"

Share mata hawaye yayi yace “Ba gudu ba ja da baya sai sun bani rabona da ya ratso ta
hannunsu ko suna so ko sunaƙi Fateemah ke ɗin tawa ce" haɗe bakinsu yayi guri ɗaya Saida
numfashinta ya ɗauke saboda wani sinadari da ɗanɗano da bazai taɓa gushewa a
ƙwaƙwalwarta ba ta janye da sauri tana gwama numfashi yayi mata murmushi yace “Special gift
ne My Zumata yau sai nayi wanka idan naje masauki na ko zaki rakani ki ƙarasa ladanki!?" Ya
ƙarashe maganar yana narkar da murya ta rufe idonta da hannunta tana masa dariya ya
shammaceta ya ɗagata cak ya azata saman motar ya sake ɗora bakinsa saman dokin wuyanta
yasa harshensa yana lasar wuyanta yana sakin wani numfashi me tada mata hankali.
Wani irin rikicewar ƙwaƙwalwa take samu lokacin da yake mata komai sai takejin salon Ma'eesh
hatta ɗumin harshensa bai saɓa dana Ma'eesh ba da sauri ta sake tureshi ta rintse idanunta
tace “Wayyoh ka bari don Allah Noor!" Cikin sarƙewar murya yace “Sai yaushe?" Da sauri ta
buɗe idanun ta tar a kansa tana masa kallon tsaf brand ɗinta na yamutsawa tana ƙara shiga
bala'i hatta sautin nasa na yanzu sautin Ma'eesh ne, hannun da yasa yana zagaya idanunta
shine ya dawo da ita hayyaci yi firgigit tace “Kaine Noor?" Da rashin fahimta yake kallonta yace
“Nine mana Fateemah na canza ne?" Dirowa tayi daga saman motar tace “Zamuyi waya Noor"





Tana faɗin haka ta shige gida ya bita da kallo yana murmushi tare da addu'ar Allah ya nuna
masa ranar da zata tabbata tashi forever, tana shiga gida ta fara watsi da kayanta tun daga kan
mayafi har zuwa dankwali zuwa awarwaro da komai ta zube a saman simintin ta fasa ƙarar data
fito da Samha da Inna da yaran daga ɗaki da gudu suka nufota ta faɗa jikin Samha tace “Waini
Samha anya Ma'eesh ba aljani bane Meyesa duk sanda nake tare da Deen yakemin gizo"
Sake rushewa tayi da kuka tace “Wlh har ɗanɗanon yawun bakinsu iri ɗaya ne hatta ɗumin
jikinsu Samha kodai bazai bayyana kansa bane yake zuwar min a siffar Noor?" Dariya sosai
abin ya bawa Samha Inna kam ficewa tayi domin maganar ba Tata nace, Samha tace “Mutum
ne kamar ke kawai kin ƙwallafashi a ranki ne shiyasa Deen yake Miki kama dashi a wannan
fannin but ai har yanzu baku kai ƙarshen wasan ba da Deen sai anan ne zaki bambance" wani
kallo takewa Samha tace “Kina ɗaukar kamar wasa ko wlh tallahi da gaske nakeyi Deen
Komansa yanamin kamar na Ma'eesh ne" cikin fusata tace “to wai meye ne inma yayi Miki ɗin ai
dama abinda kike nema kenan kuma kin samu kuma naga shima Ma'eesh ɗin kince mamansa
Yar Sudan ce to kika sani ko sunada relation ta wani fannin ko kuma haɗin country yaja musu
gamayyar Yanayin halitta"
Ganin Samha bata fahimceta ba yaɗata tashi ta nufi bayi tayi fitsari tayi alwala iya ɗan taɓatan
da yayi har ta jiƙe itakam ta rasa irinta ko ya namiji ya raɓeta sai yaji shauƙin son kusanci ya
kamata duk kuwa da kokarin dannewa da take yi da kuma hana abin tasirantuwa ga yanayinta,
sallah tayi sannan ta kwanta yunwa yakeji amma ta kasa cin komai sai bayan komai ya lafa ne
take bawa Samha labarin abinda ya faru tsakaninta da Mustapha da kuma hukuncin dasu baba
me Gari suka yankewa Deen but yace babu gudu babu ja da baya zai Turo manyansa Azo ayi
magana ɗaya ko su bayan ko kuma su faɗi me sukeso ayi musu ya amince zai yi".............

*Paid book 500 VIP 1k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay*



*Contact me*
*09013718241*



*OUM HAIRAN*
[7/8, 8:12 PM] Oum Hairan: *SIGNED MARRIAGE*
*_(Kalma ɗaya)_*


*Oum Hairan*


*___________________________________*
*Book 2 page 15-16*
*___________________________________*


Washegari da safe suna kwance a ɗaki Mal me gari yazo gidan da kansa yasa akayi masa iso
Inna tace ya iso ciki haka ya iso Inna ta shimfiɗa masa taburma ya zauna suka gaisa yace “Ina
ta Manzon ko basu tashi ba" fitowa Batul tayi tace “Gani Baffa na tashi tun subahi ban koma ba"
amsawa yayi da cewa “To to ta Manzo hakan yana da kyau dama komawa baccin safe Na mara
rabone ai" gaisawa sukayi ta nufi bakin mafitar ruwa ta tsugunna tana brush.
Mayar da hankalinsa ga Inna yace “Dama duba da cewa kinada haƙƙi akan ɗiyarki ta Manzo
yasa nace zanzo da kaina na sanar dake hukuncin damu waliyyanta munka yanke game da
amrenta Duba da abinda ya faru tsakaninta da yaron nan Mustapha ɗan wajen Lame yasa
muka fahimci idan anka amra mata shi ma bassu zaman lafiya shiyasa mukaga tunda dama
wannan yaron Anwarr ya nuna shima yana da soyuwa gareta a massashe da amren kansa, to
Alhmdllh mun kira Alh Khamilun mun gumtsa masa kuma shima yayi fatan alkhairi yanzu dai an
tsayar da lokaci ɗai da amren su Ladiyo da Jumme sai ki fara shiri kema"
Batul da tunda ya fara maganar tayi zaman dirshan a gurin ta ɗago da sauri tace “Amma Baffa
saboda kar hakan ta faru nikkawo maku zaɓina jiya kuma yace zai turo uwayensa cikin satin
nan...." Daƙuwa Inna tayi mata tace “Ungo nan ta Manzo ince dai Maigari shine madadin ubanki
dukkuwa duniyar nan shine ya faɗa kike maida masa?" Durƙushewa tayi gaban Inna tace “Wlh
Inna bana fatan wannan dalilin yasa na ƙara maki nisa ban iya auren kowa a duniyarga inba
Deen ba, Meyesa zaku yimin dole, bayan baku sabarmin da hakan ba ɗai wollah bani amren

Anwar saidai kowa ya haƙura wahala tau ce bata shuɗe ba"





Gwaɓe bakinta Inna tayi tace “Bakiyin shiru ke nan" cikin fusata Baffa Maigari yace “Yo in batayi
haka ba ya za'ayi mu gane Ita wacece Laure ai hakan shine yake tabbatar mana da irin nonon
da ta tsotsa da irin tarbiyyar da ta samu to dama barewa tayi gudu ɗiyanta yayi sassarhwa ai
Idan batayimin haka ba bazan tabbatar da itan jinin Ɗahirun Inna Yaure da Lauren Buban
Bugaje bace mutanen da suka zaɓi fita daga danginsu don su rayu babu me sanya musu
idanun su tsula tsiyarsu son ransu, Laure sai Ta Manzo tayimin hakan zan tabbatar da ita ce
yarinyar nan da aka cire mana Zakka a dangi ta shiga duniya har ta kawo mana ɗiyan shege
cikin ahlinmu ba, banji haushi ba ko kaɗan Laure irin tarbiyyar data samu kenan saidai kuma
ihun kurwa baya hana ruhi motsi tunda na riga na zartar sai an aiwatar in ba haka ba to saidai
ta koma inda babu ƙwaɓar taci gaba da rayuwar da shi farkan nata data kawo mana wai har
yana ce mana shi amrenta zaiyi yo wanne aure ne bayan gashi har ɗiya sun haifa dashi
gashinan yarinyar haske ne kawai tayo na uwarta amma kama da komi daka ganshi kasan
shine yayi cikinta da rana ma domin in dare ne da an samu cuɗin kamanni"





Kuka sosai Batul takeyi haka ya tsallaketa ya bar gidan yana jaddadawa Inna sati Uku saura
bikin don haka su fara shiri Niamey za'a kai amarya Anwar ya riga ya gama gininsa daganan
zasu wucce France tunda acan yake zaune" Samha ce ta kama hannunta suka koma ciki ta
zube a katifar tana wani irin kuka me gunji tace “Anwar fah Samha wlh bazan aureshi ba saidai
su kasheki"
Murmushi Samha tayi tace “Mukam zuwa cikin waɗannan bauɗaɗun mutane baiyi mana rana
ba munyi gudun Gara mun haikewa zago wai dama duk dangin uba haka suke ne Teemah ko
namu ne a haka? Shin ɗiyansu Ladiyo da Jumme suma amren dolen za'ayi musu ko kuwa sai
ke da bakida gata?" Cikin kuka tace “Samha mubar garin nan" da sauri tace “ina zamu Batul da
ranar auren wani a kanki?" Ta miƙe ta fara haɗa kayanta tace “Ban shirya zama ajalinsa ba ban
kuma shirya ɗaura kambun mutuwa ba shiyasa nace Miki mu bar musu garinsu sai suyiwa wata
amren dolin but wlh duk duniya namiji ɗaya ne zaɓina da ban sameshi ba na riga na haƙura a
barni na rayu da wanda raita ta karɓa take fatan ya zama madadinsa"
Murmushi tayi tace “Kar muyi gaggawa Batul mu jira zuwan Uwayen Deen muga irin karɓar da
zasuyi masu daganan kuma sai muyi abinda ya dace" bata kuma cewa komai ba ta zauna tana
yamutsa sumarta tace “Oh God! Samha Meye laifin Deen ne da zasu ɗora masa abinda babu
ruwansa Samha wlh shima ba sonsa nakeyi ba na zaɓeshi ne da fara koyawa Zuciyata sonsa
don mafitar rayuwar Jany kamar yanda kika bani shawara, taya ma wai zan yarda nayi aure a
wannan bauɗaɗen dangin? Waini ko bazanyi farin cikin bane na haƙura"

Cikinsu babu wanda ya kuma magana sun ɗauki lokaci a zaune ko break sun kasa daga ƙarshe
suka shirya samun shiga gari suyi shopping suna fita suka haɗu da Anwar daga kallon da yaga
Batul nayi masa yasashi sanin lallai saƙo ya isheta yayi murmushi yakai hannu zai ɗauki Jany ta
janye ɗiyarta ta ɗagata tayi gaba sai Samha ce sukayi magana yace su jirashi yazo ya kaisu
amma fir Batul taƙi haka dole ya ƙyalesu ransa babu daɗi shikam baisan meye yasa Batul taƙi
karɓarsa ba, duk kyansa duk gatansa ace a cikin danginsa ne mace take nuna masa tsana
bayan duk matan da ke bibiyarsa.
Komawa yayi gidansu ya shige ɗakinsa ya kwanta yini sur bai fito ba shirun Inna Hari taji tayi
yawa ko abincin rana bai fito yaci ba, hakan ya sanyata shiga ɗakin ta iskeshi kwance a ƙasa ya
zubawa selling idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur ta zauna a gefensa yace “Anwar Kai baka
iya sanya abu a ranka ba kaima irin ubanka ne Ni wlh banga abinda zaisa ka damu ba bayan
dai gata nan ta kusa zama taka" zuba idanunsa yayi kan Inna Hari ya miƙe zaune yace “Da
gaske takeson Guy ɗin tunda na fahimci ba don farin cikinta sukeson rabata da zaɓinta ba don
wata manufa ne sai naji Gara na haƙura na barta ta zaɓeni da kanta nasan nafisa cancanta"
Numfasawa yayi yaci gaba da cewa “saidai kuma bakin alƙalami ya bushe Mamee sun ƙara
rura wutar ƙiyayyata a zuciyar Batul bantaɓa son abinda nakejin zan iya ɗaukar kowacce
kasada akansa ba sai akan Batul amma Mamee hakan zai faru ne idan bata ɗaukeni a yanda ta
ɗaukeni yanzu ba Inason na rayu da ita ne rayuwa me daɗi saidai ita tanamin kallon takobin
dayake shirin sare farin cikinta garata Mamee inajin kamar na haƙura banson amsa sunan
azzalumi tun a neman amre zataci gaba da kallo na a haka ne har cikin amren"


Shafa kwantacciyar sumarta tayi tace “Meye kuma Azzalumi Anwaru bakai ne azzalumi ba
uwayenta ne kuma kasan Hwaɗuwar gaba asarar namiji ka dake idan ka ɗauka zata sauko itan
ɗiya mace ce Anwaru (Hal jaza'ul ihsanu illal Ihsan) sakamakon me kyautatawa a kyautata
masa inada tabbacin idan da irin mu'amalarka zaka mu'amalanci Ta Manzo wlh sai tasoka fiye
da son da takewa wannan Sudanies ɗin kaidai ka wasa zuciyarka ka ƙarfafa ƙaddararka Ni wlh
tamsayi kaka bani wannan bazaurar ɗiya duk ta susuta mana samarinmu Ni har yanzu banga
irinta ba......"
A Hassale yace “Zaki fara ko Mamee bazan ɗauki taɓa martabar Batul ba, ko mece inasonta a
haka haba don Allah Bama dole taƙini ba tunda tazo wannan garin kujera jifanta da munanan
kalamai wai mutum yakan iya canza ƙaddara tai ne?" Murmushi tayi tace “Aa Anwaru ayi haƙuri
Ni banƙin Ta Manzo kawai dai yanda ka susuce ne yake bani mamaki cikin kyawawan buzayen
ɗiyoyin dake wannan gari an baka kaƙi yau kuma gaka kwance kakai kanka inda baka da gurbi"
bathroom ya shige itama ta miƙe ta fice daga ɗakin ta kawo masa abinci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login