Showing 21001 words to 24000 words out of 34531 words
Chapter 8 - SIGN MARRIED 2 BOOK OUM HAIRAN.pdf
yi domin fatan
duk masifar da zata shigo rayuwar masoyiyar da ɗiyarsa tazo musu da sauƙi umarni ya bayar
na cewa yau duk wanda yaci abinci a gidajen abincin nasa kar a karɓi kuɗinsa sannan ya nufi
babban Companynsu na drinks ya zauna a office ɗin ba tare da iya hassala komi ba, ganin
hakan bai masa bane ya kuma fita ya nufi asibitin da yake aiki, haka yake yini yawo tsakanin
masa'antun nasu ba tare da ya iya taɓuka komi ba"...........
*Paid book 500 VIP 1k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay.*
*Contact me*
*09013718241*
*OUM HAIRAN*
[7/9, 8:31 PM] Oum Hairan: *SIGNED MARRIAGE*
*_(Kalma ɗaya)_*
*Oum Hairan*
*___________________________________*
*Book 2 page 19-20*
_________________________*__________*
Fasalta irin tashin hankalin da Batul ta shiga lokacin da labarin irin wulaƙancin da su Baffa
Maigari sukayiwa iyayen Deen wannan ma ɓata baki ne tayi kuka kamar ranta zai fita a ƙarshe
taja bakinta tayi shiru iya Samha ce tasan shirinsu, haka ake ta shirye shiryen biki bata cewa
kowa komai Samha ce ta sanar da Inna Laure zataje Niamey akwai ƙanwar babarta zata kai
mata katin biki kuma zata iya kwana biyu a can, ba tare da tunanin komai ba tace “Ai kuwa
badan kar na ɗora Miki nauyi ba da na baki wasu yan kuɗaɗe kinyo mana siyayya kinga babu
abinda aka siyo har yanzu" satar kallon Batul Samha tayi tace “To Inna mu tafi tare mana dama
Nima nayi tunanin hakan in yaso saita zaɓo irin abubuwan da take so Kinga lokaci sai ƙurewa
yake yi saura kwana takwas fah ɗaurin aure"
Ba tare da tunanin komai ba Inna ta zuge jaka ta zaro kuɗi zata basu Samha tace Inna kibar
kuɗin nan idan Batul ta tafi ɗakinta sai kija jari mu muna da kuɗin da idan dukka auren zamu
ɗauki nauyi na bazamu girgiza ba"
Yarda Inna tayi suka shirya Samha tace “Inna bari mu tafi da yaran nan saboda kar su dameki
da ƙiriniya suma mayi musu siyayyar kayan fitar biki" cewa tayi “Eh fah Waɗannan koɗaɗɗun
ƴaƴan naku sai ku ai kuje da abinku inba haka ba magana ma ta isheni a garin nan" sudai suna
samu suka fice kai tsaye daga Damagaran motar Katsina suka shiga basu suka shiga Katsina
ba sai dare suka nemi hotel suka kama bayan sun shiga ɗakin hotel ɗin ne suka kalli juna
Samha tayi dariya tace “In sun san wata ai basusan wata ba kulle wayarki tun a nan bamu sake
kunna MTN line sai mun keta hazo yanda duk nacin me naci bazai iya biyomu ba"
Zama Batul tayi dafe da kai tace “Allah sarki Inna yanzu nasan kanta zatayi wabi cewa zasuyi
ita ce tasani na gudu Ni kuwa wlh dana auri Anwar gara na kare rayuwata a ɗebe kwanukan MB
kitchen's dariya sosai Samha tayi tace “Kedai kawai kina son rayuwa da Deen kinga haɗaɗɗen
Guy ɗan ƙwalisa ana shirin manna Miki wani garan ƙauye koda yake Anwar bashida laifi kawai
dai wayewarmu ce ta girmi tunaninsa, sai wani ihu suke a France yake yo inda France tana
cikin wayayyun ƙasashe meyesa su basu waye ba, nifa wlh na matsu naga lifestyle naku da
Deen nasan za'a ɗauki darasi"
Murmushi tayi tace “Hmmm bakiga lifestyle ba tunda bakiga rayuwarmu da Ma'eesh ba Samha
Bama gajiya da cinye juna fah gashi da zaƙi nifa badan kar nayi ƙarya ba zan iya cewa Yafi
zuma daɗi"
“Ma'eesh! Ma'eesh!! Nikam kamar nasan wannan sunan Batul? Ohhhh Manager na MB
kitchen's sunansa kenan yanzu daganan ina mukayi?" Taɓe baki tayi tace “Muje Kano muga
gidan da aka siya daganan mu koma Abuja idan so mu ɗaga ko me kikace?" Jinjina kai tayi tace
“shikenan hakan za'ayi" wanka sukayi sukayiwa ƴaƴansu sukayi sallah suka kwanta bacci. Kiran Deen ne ya shigo tana ɗagawa tace masa “Ka koma ne? Murmushi yayi yace “Jiya naji
damar jikina yau na sauka a Austaralia course Yayana bashida lfy shima but ya fara jin sauƙi, ya
shirye shiryen biki?"
Murmushi tayi tace “Nima ina hanya cikin satin nan" zaro ido yayi yace “Ya batun bikin naki?"
Murmushi ta sakeyi tace masa “Bazan cuci kaina bane Noor tunda sun hanamu aure to Nima
wlh bazan auri wanda sukeso ba su barni na rayu da ƙaddarata" ajiyar zuciya yayi yace “Idan
kikazo sai musan abinda ya dace kawai muje Embassy a ɗaura mana aure tunda parents ɗinki
sunƙi ɗaura mana" dariya sosai abin ya bata yace “Haba Deen abin na kaɗo ai ba hauka bane
nayi Sign married sannan yanzu nazo nayi Embassy married ai kayimin faɗan nabi komai a
hankali, tunda dai komai lokaci ne"
Kwantar da kai yayi yana kallon Ma'eesh dake gefensa yace “Nace da Bro Wife ɗina a ɗaya
cikin Restaurants nasa take aiki idan kin dawo zamuje mu gaisheshi yasa mana albarka, ko na
haɗaku ku gaisa?" Saurin girgiza kai tayi tace “Aa ka bari dai nazo sai muje mu gaisheshi ai
yayanmu ne bai kamata ayi masa gaisuwar miƙe ba" Murmushi yayi yace “Hakane kinyi gsky
yanzu yaushe zaku taho?" Haka sukayita hirarsu tare dayi musu alƙawarin zai sama musu visa
urgent, haka kuwa akayi kwana biyun da sukayi a Kano sunga gidan da Batul ta siyawa inna
gidane me kyau ya ƙawatu duk da ba wani babba bane Saida ta zubanta komai na amfani hatta
kayan abinci sannan ta bawa Janah kuɗi masu yawa tace taje ta ɗaukota ta dawo da ita nan"
washegari kuwa Zakara ya basu Sa'a sai Cairns shigar dare sukayi shigar dare sukayi sosai
domin Saida suka yada zango a Canada sannan suka ɗauki hanyar Austaralia.
Dake Turai ba Africa bace a daren suka dangana da gida domin kuwa a airport ɗin suka ishe
Deen yana jiransu kallo daya tayi masa ta tabbatar da ramarsa sosai ya bata tausayi ta kwantar
da kanta a jikinsa tace “My Noor ka rame da yawa don Allah kar ka sanya damuwa a ranka
komai yanada lokaci" shafa kuncinta yayi yace “Bazasu gane bane Fateemah inashan wahala
fah ina buƙatar abokiyar rayuwa wlh" murmushi tayi a ranta tace “Gara ma kai baka ɗanɗana ba
but a zahiri ce masa tayi lokaci zai zo soon Insha Allahu.
Saukesu yayi bayan sun biya ta Restaurant nasu sun karɓi abinci a ƙaramin office ya tadda
Ma'eesh yana zaune ya zuba uban tagumi ya taɓashi yace “Har yanzu bazaka rage damuwar
nan ba Bro no condition is permanent please ka rage damuwa ko dan lfyrka" kifa wayar yayi a
ƙirjinsa tare da danna sweetch ɗinta ya zubawa ƙaninsa nasa idanu yayi yace “Ka ɗaukosu
ne?" Jinjina kai yayi yace “Abinci ma muka biyo su karɓa sai su wucce gida Bro na mutu akan
Babyn nan Teemah ta haɗu sosai rayuwa ta ce?" Murmushi yayi yace “Allah yasa rabonka ce
Deen Kaje ka kaisu gida dare yayi Ba zamu haɗu a wannan karon ba Ni gobe zan koma Sudan
banason mutuwa a garin nan gara naje na mutu a gaban Mom ta dafa kaina tayimin addu'a
Inason bata duk wani abu dana mallaka idan na mutu ta nemi Batul ta batashi ita da babynmu
su rayu rayuwa me inganci"
Miƙewa yayi ya fice in da sabo ya saba da Waɗannan kalaman na yayan nasa kullum abinda
yake cewa kenan matarsa da ɗiyarsa shi ya fara sarewa yanda ya baza ma'aikata ake neman
yarinyar nan inda tana raye da tuni an ganota" jan motar yayi ya kaisu gida sukayi masa godiya
suka shiga ɗakinsu kawai suka gyara sukayi sallolinsu suka kwanta baccin gajiya sun fara
mantawa da sanyin Austaralia gashi sun dawo lokacin saukar Snow abin ba sauƙi haka suka sa
shirga shirgan kayan sanyi suka kwanta bacci kuwa ya sacesu cikin dare ta farka a firgice tana
furta “Innanillahi wa innah ilaihirraji'un!" Abinda ya tashi Samha tace “Ya akayi?" Ajiyar zuciya
tayi tace “Na godewa Allah daya zama mafarki Samha kwanan nan Ma'eesh ne ya dawo a
mafarki na, na fara cire shi a raina har ina jin a raina fah ko bayyana yayi gareni bazan iya sake
rayuwa dashi ba saboda hankalina bazai kwanta ba zama da matsafi" tsaki Samha tayi tace
“Wlh da kayan haushi kike yanzu yaushe zaki koma aiki yanzu nake gani gobe Shugaba yana
neman dukkan ma'aikata zai yi taro dasu zai koma ƙasarsa shan magani" taɓe baki tayi tace
“Gsky gobe ba zanje ba zan huta shi kuma Allah ya bashi lfy"
Komawa sukayi suka kwanta da safe Samha ta tafi aiki ita kam zamanta tayi a gida da yamma
Deen yazo yake ce mata Bro yakai airport nan suka shantake da hirarsu ta masoya.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya ta kowanne ɓangare babu daɗi Inna ta fuskanci ƙalubale daga
ƙarshe ne Alh Khamilu yazo ta zayyane masa komai Aikuwa ya rufe yan uwan nasa da faɗa
yace sunci amanar maraici Meyesa yarinya zata kawo wanda takeso suƙi bashi su haɗata da
wanda bataso, yanzu in a baya sunce laifin uwarta ne yanzu kuma na waye? Waye yake da
alhakin sake fantsamarta duniya?" Dake yanada citta a hannunsa take sukayi nadama suka
bashi haƙuri duk kuwa da cewa shi ce masa sukayi batada manemi ne shiyasa sukeson haɗata
da ɗan uwanta, da kansa yaje ya bawa Inna Laure haƙuri yayi mata jagora har Kano inda suka
samu lambar Batul gurin Janah bai bar sabon gidan Inna ba Saida ya kira Batul lokacin tana
gurin aiki ta ɗaga suka gaisa yace “Batula baki ganeni ba ko? To ubanki ne Khamilu" cike da
kunya tace “Lahhh Baffa ina yini ya gida da mutan gidan?" Dariya yayi yace “Kinci uwaki ƴar
ƙaniya to ki turomin number surukin nawa sai jiya nake sanin abinda ya faru wlh banga laifinki
ba Batula Ni daɗi ma naji da kika nuna musu kin san kanki ke kam yanzu idan ba'a rarrasheki
ba ai ba'ayi Miki dole ba"
Cikin kunya tace “To Baffa na gode" tana aje wayar ta tura masa number Deen tayi wani tsalle
ta rungume Samha tace “Ke burinmu ya kusa cika yanzu baban Anwar ya kirani yace na tura
masa number Deen nasan maganar aurenmu za'ayi wlh na gaji da haɗiyar ƙwayar kashe
sha'awa nima Gara naje na warwasa na baje masa ya lasa ya tsotsa yaci ya ƙoshi" dariya
sukayi tare da tafawa suka kama rawarsu ta yan Iskan gari, ranar basu bari sun tashi ba gida
suka koma harda haɗa ƙwaryan party Suda ƙawayensu tun basusan me ke faruwa ba.
Da dare kuwa kiran Inna ya isheta ta ɗaga suka gaisa tace “Yanzu sai yaushe zaki dawo a yau
ɗinnan Ƙanin Mamar saurayinki yazo sun kawo dukiyar aure da sadaki Miliyan biyar an tsayar
da ranar aure wata guda me zuwa".......
*Paid book 500 VIP 1k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay*
*Contact me*
*09013718241*
*OUM HAIRAN*
[7/10, 11:18 AM] Oum Hairan: SIGNED MARRIAGE
*_(Kalma ɗaya)_*
*Oum Hairan*
*____________________________________*
*Book 2 page 21-22*
*____________________________________*
Wata alkafura tayi ta tashi a gadon tace “Inna 5Ml saidani zaki kumayi?" Dariya abin yaba Inna
Laure tace “Ba saidaki zanyi ba Batool abinda suka kawo kenan sunce saboda yanayin faɗuwar
Naira abubuwa sunyi tsada kuma irin wannan auren ba shiryawa akayi ba dole sai jin ƙai ya
shiga, yanzu dai yaushe zaki dawo Kano?" Ajiyar zuciya tayi Samha ta karɓe wayar tace “Inna
mu bari sai bikin ya rage saura sati biyu inaga Zaifi" a haka suka bar abin sukaci gaba da
shirye-shiryensu sabon babi na soyayya ya buɗe tsakanin Batul da Deen ko yaushe suna
manne a waya ko suna chat kasancewar tun kwana biyu da sa ranar bikin ya tafi Nigeria da
yake anan yake ra'ayin zama a Abuja yanata gyare-gyaren gidan da zasu zauna ranar da zasu
tafi ne wani abu me kama da almara ya faru suna zaune a reception suna jiran cikar lokaci wani
ƙamshin turare da bazai taɓa ɓacewa a ƙwaƙwalwarta ba ya ziyarceta abinda ya katse mata
numfashi na tsayin daƙiƙu ta miƙe zumbur tare da fara dube² ajiyar zuciya tayi ta koma ta zauna
tare da dafe kanta.
Samha dake kallonta ta dafa kafaɗarta tace “Me kike nema?" Ajiyar zuciya tayi tace “Babu
komai" janye hannunta tayi tunda tace babu komi tasan bazata mata bane, da wannan aka fara
kiran matafiya suka tashi suka shiga jirgi bayan kowa ya gama zama jirgi ya tashi bakin Batool
ɗauke da addu'ar neman kariyar Ubangiji, har yanzu kuma hancinta bai daina jiyo mata ƙamshin
daddaɗan turaren da ta gaza jinsa a gurin kowa sai a gurinsa shi kaɗai wato Ma'eesh inda
taketa satar kallon gefe da gefenta amma bataga wata alama da take nuna akwaishi a gurin ba.
Ba su so tafiyar tazo musu a karkatse ba but dole haka suka haƙura ashe jirgin yawo suka biyo
Saida suka tsaya a Japan suka kwana biyu abinda yake ƙara bata mamaki kuma ya koma
tsoratata yanda wannan ƙamshin turaren yake bibiyarta idan ta duba kuma taga babu kowa.
Daganan suka tashi sai Canada daga Canada suka dira a birnin tarayya suka kwana ɗaya
abinda ya bata mamaki duk kiran da takewa Deen wayarsa bata shiga daga ƙarshe aka turo
mata saƙo.
“Kiyi haƙuri na turo Muhsin zai ɗaukeku zuwa Kano Nima zan biyo bayanku Fateemah ina ɗakin
taro ne" Jinjina kai tayi babu ɓata lokaci batare da tambayar address ba saiga wani saƙon ya
kuma cewa “Zai kiraki ƙaninmu ne zama kiga kama" tana gama karanta daƙon kira ya shigo
wayarta ta ɗaga “Sosai gabanta ya faɗi jin Muryar tasa, yace “Auntyna ina jiran ku" saurin sauke
wayar tayi a kunnenta tace “Nikam na shiga uku Samha komai nashi yake zamemin, meye
haɗin ƙanin Deen da Muryar Daddyn Jany?" Murmushi Samha tayi tace “Wannan mayen
mutumin zai kashe Miki aure idan bakiyi da gaske ba, yoni na taɓa ganin wannan masifa kin
damu da mutumin da neman sanin yanda kike da lafiyar ɗiyarsa dake hannunki ma ya
gagareshi"
Iska ta furzar tace “Inashan wahala da Zuciyata akansa Samha kema kin kasa fahimta ta wlh na
faɗa Miki a yanzu ko bayyanarmin yayi bazan ɗaukeshi nabar Deen ba but kinsan meye yanzu
yake zuwa raina? Shin daga shekara biyun yarjejeniyar ta ƙare kenan?" Tsaki Samha taja tace
“Wai yarjejeniya toke ubanwa yace Miki aure kukayi kawai kunyi iskancinku ne amma ko a
kafirci aure a curch ake ɗaurashi bare a musulunci da sai anyi siga waliyyay sun haɗu an bada
sadaki shaidu sun shaida sannan aure ya ɗauru"
Bata kuma cewa komai ba suka isa jikin motar ta Zubawa Muhsin ido da yayi caraf ya cafe Jany
yana cillata yana dariya dimple ɗinsa na lotsawa hatta dariyarsa irin ta Ma'eesh ce hasken
tsananin kamar har ta zarce misali hasken fatar sa ne kawai ba irin na Ma'eesh ba shi nasa da
sirkin duhu a ciki saɓanin Ma'eesh da yake tar irin hasken Turawa har wani ɗaukar idanu
yakeyi. Juyowa yayi yana kama hannun Jalal ya rusuna yace “Gaisuwar ban girma matar
Babban Yaya Uwar sha lelen Mom!" Zuba masa idanu tayi ya buɗe musu motar suka shiga ya
lura da kallon ƙurullar da take yi masa but yasan dalilinta domin kaf gidansu babu wanda suke
kama ta Kwabo da Kwabo irin shi da Mijinta duk kuwa da cewa Uwa suka haɗa koda yake
dukka da Mommy suke kama dama Deen da Aunty Nuwairah ne suke basuyi kama dasu sak ba
su sunfi kama da Abbuh Hakeem amma a hakan akwai wasu yanayiyyika da suma ake cewa
suna kama da Mom, jan motar yayi a guje kiɗansu na Sudanies na tashi a motar ita kanta motar
ƙamshin turaren da yake rikita mata lissafi takeyi, Samha sai magana takeyi mata ita kuwa
kanta ya kulle sai juya mata yake yi musamman da take jiyo hirarsu da Jany, yarinyar tana
masa surutu shima ya dage sai tayata yakeyi yana ce mata “Babyna yau taga Dad ɗinta, kina
cikin alkhairi yarinya"
Nisa na tsakanin Kano da Abuja ita dai Batool sai ji tayi yana cewa da ita “Matar Big bro ko baki
gaji bane mu juya?" Firgigit tayi ta dawo hayyaci ta dauki jakarta ta fito ta nufi gidan ya ɗaga
murya yace “Am Matar Big bro sai nazo ɗaukar amaryata" cije lips ɗinta tayi ta nufi cikin gidan
tana ayyana ya fahimci halin da ta shiga da ganinsa ma shine yasa yake neman zautata.
Duk yawan mutanen dake tsakar gidan na Inna bata iya kula kowa ba ta shige ɗaki ta fincike
mayafin kanta ta wullar tare da zubewa kan gadon tana furta “Innanillahi wa innah ilaihirraji'un
Allahumma ajirni fi musibati wa'akalifni khairin Minha!" Jin yanda lazumin "hasbunallahu wa
ni'imal wakil" ne yasa Samha zubanta ido tace “Na lura da rikicewarki tun fitowarmu da kikayi
arba da wannan kyakkyawan guy ɗin, ya hayyu ya ƙayyumu Teemah An ƙure kyau a wajen nan
nifa Saida nace to wai samarin aljanna sun fara kawo mana ziyara duniya ne?"
Miƙewa tayi tace “Kinsan me ya bani mamaki? Samha bayan Muryarsa da yanayin dariyarsa da
kuma kama ta zahiri dana gani hatta tsayinsa da faɗinsa irin nasa ne, Jany bata kama dani but
daya ɗauke kasa bambamce bambancin tsakaninsu nayi, kince Jany tana ɗiban kama da Deen
shi kuma wannan me Jany takeyi dashi?" Kama hannunta Samha tayi tace “Ba kama bace
gaurayar jini ce, wallahi azza wa jallah badon nasan komai game da Jany ba babu yanda zaayi
naga mutumin nan ɗauke da Jany naki bada shaidar shine ubanta, saidai karki manta duniya
tanada faɗi kuma dukkanmu Allah ɗaya ne ya haliccemu sannan inaso ki rinƙa tuna abu guda
ɗaya nasabar gari ɗaya ma tana bin jini, Batool kince Kakar Jany ammana