Showing 24001 words to 27000 words out of 34531 words
Chapter 9 - SIGN MARRIED 2 BOOK OUM HAIRAN.pdf
mahaifiyar Daddynta
itama Sudanese ce kuma kince Ma'eesh da mahaifiyarsa yake kama Kinga kenan maybe ko
sun haɗa wata alaƙa ta jini ta nesa ma bata kusa ba, wannan dai ƙanin angonki me jiran gado
ne nan da 10 days Kinga kenan bashida alaƙa da Ex-husb ɗinki a cewarki"
Komawa tayi ta zauna tana sake dage kanta tace “Idan ko ya zama haka maganar gaskiya zan
sanar da Deen banason wannan ƙanin nasa a sashina saboda zai rinƙa firgitani Samha Ni kaɗai
nasan me nake gani a tare da yaron nan kuma na fahimci ya gane yanda na ruɗe da ganinsa
har wani zolayata yake yi" dariya Samha tayi tace “Wannan ango yana ganin rayuwa tun yanzu
za'a fara kafa masa dokar wanda zaizo da wanda bazai zoba" bayi ta shiga ta sakarwa kanta
ruwa tana wankan taji shigowar Janah fitowa tayi suka rungume juna tace “Kaga manyan mata
ke batool kiji tsoron Allah wannan uwar ƙiba da kikayi me kikeci ne a Turain"
Murmushi tayi taci gaba da shafa manta tana gamawa ta zura riga Janah tace “Ba kwanciya
zakiyi ba kitse Sarkin bacci tashi zakiyi muje ga motarki can ta rigaki zuwa ki jamu ki kaimu inda
angon namu ya ce zamuje gyaran jiki na kwana takwas" kallonta tayi tace “Wai ina kikasan
Deen ne Janah?" Dariya tayi sosai tace “Taya bazan san Deen ba bayan kusan koyaushe yana
gidannan"
Taɓe baki tayi ta ɗauki wata kanannaɗaɗiyar hula ta ɗora saman sumarta data baje saman
bayanta ta yafa mayafin a kafaɗa ta zura takalmi suka fito sai yanzu ta gaisa da danginta da
suka cika gidan yan uwan Inna da ƙannen mahaifinta Inna tace “motoci ne guda biyu aka
kawosu jiya yace saboda zirga zirgar da zakuyi yanzu key ɗin wacce za'a baki?" Murmushi tayi
tace “ki bani na tawa Inna girgiza kai tayi tace “Aa bazaayi haka dani ba Ta Manzo yaba kyauta
ai tukuici ki hau tasa don Allah"
Cikin zaƙuwa tace “Shikenan bani key ɗin" remote ɗin Inna ta miƙo mata duka ukun ta fita
compound na gidan ta latsa na farko wata hamshaƙiyar mota ta amsa mata ta nufeta gabanta
yana faɗuwa ta shiga ta zauna Janah da Samha suka fara baza mata hoto suna mata kirari
Janah tace “Wannan amaryar tafi kowacce amarya a shekarar nan Capacity" dariya tayi data
sanya kyawawan haƙoranta suka bayyana yar siririyar wushiryarta ta bayyana Janah tayi maza
ta baza mata hoto ta shiga motar suka tafi.
Wani katafaren gurin kwalliya da gyaran jikin amare ne me suna MB Bridal Beauty nan Janah
tace su tsaya suka tsaya Batul ta tsaya tana ƙarewa wajen kallo iyakar haɗuwa tun daga haraba
gurin ya haɗu ta sauke ajiyar zuciya wani sihirtaccen ƙamshi na tashi a gurin, suka taka suka
hau saman kamar yanda Janah tace musu, suna shiga taga ma'aikatan suna zubewa suna
gaisheta tare da wata irin girmamawa ita dai bata fahimci komai ba ta ɗauka dabi'arsu ce
girmama customer.
Wata kyakkyawar mace ce ta fito da ganinta kasan ba tamu bace cikin hausarta da bata fita
tace “Barka da zuwa Hajiya mu shiga daga ciki" babu musu sukabi bayanta a parlour tace su
Janah su zauna ita kuma suka shiga ciki matar tace “Ranki ya daɗe sunana Nuriyyah Surukarki
ita ta bani damar yi Miki gyaran da ba'a taɓa yiwa wata amarya irinsa tace keɗin ta musamman
ce" ƙasa tayi da kanta batare da tace komai ba, tun daga wannan lokaci suka fara gyaran jikin
wannan amarya taga masifa yanda ake durzar jikinta da haɗin dilka saida tayi kamar tace ta
shiga uku ta lalace" iya gyaran na rana ɗaya tayi wani fitinannen kyau da haske, sai yamma
Hajiya Nuriyyah take sanar da ita gidanta zasu wucce akwai abubuwan da bazasu yiwu a
shagon ba da tayi tunanin zuwa gidansu to kuma aikin baya buƙatar hayaniy.
Saida su Samha suka shiga maganar sannan ta yarda suka tafi can ɗin Jany kam da Jalal a
Inna suka barsu a takaice Saida aka ɗauki sati guda ana wannan gyaran jiki ita kanta Batool
bata gajiya da kallon kanta tayi wani fitinannen kyau ga wani zaunannen ƙsmshi daya zauna
daram a jikinta ko wuccewa tayi sai guri ya haura sama da 1 hour yana ƙamshinta duk wannan
abinda akeyi tsakaninta da Deen sai test ko kuma Muhsin yazo ya kawo mata saƙo baya ɗaga
wayarta sosai abin yake ƙular da ita amma ya zatayi da tayi masa complain ma cewa yayi da ita
haka al'adarsu take idan biki ya rage saura sati biyu amarya da ango basu ƙara magana sai a
gidansu, sannan yace mata tayi haƙuri da duk wani Event susa ayi musu saukar Kur'ani suyi
sadaka su taimaki marasa ƙarfi da miskinai yafi su kashe kuɗaɗe a Event. Matuƙa ta shiga mamaki da wannan sauyin lokaci ɗaya da take fuskanta gurin angon nata Duk
yanda taso fahimtar dashi tanada mutane da zasuzo mata waɗanda sukayi zama dasu a
Austaralia ya barta tayi Event ko ɗaya ne fir ya nuna rashin amincewarsa yace shi albarkar
aurensa yake nema da samun dawamamme zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba ranar taci kuka
tasha takaici gashi duk wanda ta nemi shawararsa sai yace to ta haƙura mana ai yafita gaskiya.
Haka ta haƙura ranar Event ta zama Ƙur'ani day haka suka shirya cikin wasu manyan hijjabai
harda niƙaf sukaje gurin, tabbas Zuciyarta ta gasƙata ba babu bace ta sashi soke mata Event
da gaske albarkar aurensa yake nema domin duk wanda yazo sai an haɗa masa complete tea
basket madara Milo Nescafe Lipton da Envelope me ɗauke da Dala ɗari da hamsin bayan
kyautar ƙur'ani da sallaya da casbaha da hisnul Muslim da kowa yake samu, anci ansha an
ƙarya kasusuwan kaji an tauna tsokar raguna, karfe tara taro ya tashi wanda ya zama na farko
daya kafa tarihin bam mamaki a birnin Kano.
Suna komawa suka tarar an kawo kayan lefen da ya tashi kan kowa, goma saura amma dangin
amarya da dukkan yan unguwa kowa a tsaye yake cirko cirko saboda al'ajabin wannan lafe iya
akwatuna guda ɗari biyu ne banda iyayen akwatunan kaba suma guda hamsin Wasu kalar
akwatunan ma tunda Allah ya halicce ta ko a film bata taɓa ganin irinsu ba saboda girmansu da
ƙawatuwarsu, Itadai amarya tsoro ne ya kamata na wannan abu me kama da saida rayuwa,
zuwa yanzu ta fara dasa ayar tambaya akan Deen ta fara tantama akansa, shi ɗin waye ina
yake samun kuɗi in kuma yi masa ake shin iyayen nasa su waye da basajin asarar barnar da
kuɗi haka?.........
*Paid book 500 VIP 1k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay.*
*Contact me*
*09013718241*
[7/11, 11:42 AM] Oum Hairan: *SIGNED MARRIAGE*
*_(Kalma ɗaya)_*
*Oum Hairan*
*____________________________________*
*Book 2 page 23-24*
*____________________________________*
Washegari ta kama ranar juma'a a tsarin bikin ranar yini ce washegari asabar a ɗaura aure
hakan ce ta faru sunyi yininsu ba ƙarya ankar uwar kuɗi a kuma ranar ne akayi kamun amarya,
ranar amarya taga al'ada su irin nasu kamun ma na masu hannu da shuni daban yake dana
yaku bayi a iya dangi ma da sukazo kamu sun haɗa kuɗi bana wasa ba wai kuɗin Lipton nasu
na buzaye, suka rinƙa hotuna da amarya wata baturiyar tsohuwa tazo ta rungumeta aka rinƙa
kafta musu hoto matasan dangin suna tsokanar tsohuwar suna cewa “Granny ta rungumi
kishiyarta Granny tayi mubaya'a" yanda kowa ke nuna mata ƙauna da kulawa a wannan ahli ya
tashi kanta batasan sanda ta kama hawaye ba, gsky ta aminta Deen ɗan gata ne babu ƙarya,
kowa murna yake tayashi na samunta matsayin iyalinsa duk da cewa kuwa ta samu naƙasu
amma babu kyara babu tsangwama haka suke nuna mata soyayya, sunata carafke da Jany da
kamar sune suka raɗa mata sunan suna cewa da Granny ga Namesake ɗinta dama sunanta
yace zaisa indai aka haifa masa baby girl to gashi ya cika alƙawari, da suka tashi komawa ne
Granny tace yace a tafi da Jany ta fara shiga danginta kafin Mom ɗinta ta biyo baya.
Haka aka tafi da Jany yarinyar tanata yima mamanta baybay itadai don anfi ƙarfinta ne but
tafison tilon ɗiyarta a jikinta ko yaushe, bayan sun gama bidi'arsu sun tafi ne suma suka fara
shirin kwanciya kasancewar dare ya shiga a lokacin ma 11:30pm zare kayan jikinta ta rinƙayi
ɗaya bayan ɗaya tana ajiyewa faɗuwar gabanta na nunkuwa ninkin wanda take fuskanta kusan
sati biyu kenan, kwanciya tayi a gadon kanta yana kallon sama Zuciyarta na ƙara hargitsewa,
tayi nisa sosai a cikin tunani taji wayarta tayi ƙara alamar shigowar saƙo ta ɗauka da sauri zuwa
yanzu ta matsu taji daga gareshi.
Ilai kuwa wata baƙuwar number ce ta Turo mata sakon, _"Aysha ta girma Wife ina fatan kin
shirya karɓar wani babyn soon ko?"_ Murmushi tayi ta rubuta masa _“Yeah Inason sama mata
me ɗaibe mata kewa banso ta taso da kaɗaici kamar Ni"_ Sake turo mata yayi da cewa _"Na
matsu naga wannan lokaci Fateemah wlh ji nake kamar ba zan kai goben ba, idan na tuna
saura 10 hours ki zama mallakina halal wadda bazan fuskanci ƙalubalen komai a sanda nake
gabatar da komai ba ji nake farin ciki yana neman kai numfashina ƙarshe, don Allah ki kula dani
Bea....."_ zabura tayi ta tashi zaune ƙirjinta na bada wani dam! dam! Ta sake kallon saƙon tare
da maimaita “Bea! Bea fah?" Maza tayi ta kira layin amma babu amsa tayi kira yakai uku
sannan akayi rejected saƙo ya shigo da cewa.
_“Ki daina gaggawa duk abinda kikeson sani zaki sanshi nan da 24 hours kinji_ da haka ya
kashe wayar ta koma kiran layin Deen still shima saƙon ne yace mata _“Don Allah Zumata ki
kwanta Saida safe banso ki makara wajen tashi da asuba kiyi mana addu'ar shiga rayuwar aure
cikin nasara kinji, so nake mu fara da twins Idan mata ne mu samu Fateemah da Sukaina idan
maza ne musa musu Nuraddeen da Taheer"_
Komawa tayi ta kwanta tana murmushi tare da yin addu'a ta shafa ta ja duvet ta rufe jikinta
Samha dake chat ta kalleta ta kawar da kai, wannan dare baccin Batool rabi da rabi ne iya
daɗin bacci idan ta tuna gobe iyanzu tana gidan Deen matsayin matarsa sai tashi tana me
riskar kanta da faɗuwar gaba a haka aka cinye daren asubayi tayi sukayi sallah gidan ya
kacame da hargowar yan biki wannan ya sasu sulalewa suka tafi gidan maƙota acan sukayi
nasu yinin kasancewar ba'a Kano za'a ɗaura auren ba a Ƴar kuka ne yasa basusan meye ya
wakana ba ƙarfe biyu na rana ta idar da sallah kenan saƙo ya isheta a waya ta ɗauki wayar da
sauri cike da faɗuwar gaba hannunta da dukkannin jikinta yana ɓari, so take ta buɗe saƙon
saidai tsoron me zata gani a jiki takeyi itadai tasan yau ita ne ranar ƙarshe kuma tana cikin
awanta na ƙarshe matsayin mallakar kanta da mahaifiyarta cikin ƙasa da yan mintina daƙiƙu ko
awa take shirin zama mallakar waninta kuma ikonsa lumshe idanunta tayi lokacin da Janah ta
karɓi wayar ta buɗe saƙon ta fara karantawa a bayyane _“Alhmdllh! Alhmdllh!! Alhmdllh!!!
Fateemah bayan kawo result na gwajin jini da kwayoyin hallitarki da bayyana nawa yau dai
burina ya cika na amsa sunan mijinki na sunnah Alhamdulillahi ya rabbil azeezul mannah!
Fateemah nayi alƙawarin kare mutumcinki da ƙimarki har fitar numfashina na ƙarshe, na gode
Fateemah"_
Zabura tayi ta miƙe jikinta yana ci gaba da rawa hankalinta na ƙara tashi wani irin yanayi na
shigarta jiri na ɗibanta abinda ya sabbaba mata zamewa ta zauna tanajin wani baƙon al'amari
yana shigarta wanda tunda take bata taɓa fuskanta ba a rayuwarta.
Wani irin zazzaɓi taji ya fara sauko mata ta kwantar da kanta bisa kujera tana furta
"hasbunallahu wa ni'imal wakil" daidai lokacin wayarta ta fara Ring ta kai idanunta ga sensor ɗin
tare da tura hannunta kamar wadda jijiyoyinta suka daina aiki ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta
suka sauke ajiyar zuciya tare ta kuwa rushe da kukan da ita kanta batasan ba meye ba,
numfashi ya sake saukewa yace “Me kikewa kuka Fateemah?" Cikin sarƙewar murya tace
“Shikenan yanzu Nuraddeen Shikenan?" Ajiyar zuciya yayi yace “Hakane Fateemah Shikenan
iya Shikenan ɗin ita zan iya faɗa Miki Ina tayaki murnar samun farin cikin da ya sallama farin
cikinsa danke, nayi alƙawarin bazan barki a duhun da kike ciki ba Insha Allahu a yau zaki san
komai game dani kuma zaki fahimci komai game dani!"
Numfasawa ya kuma yi sannan yace “Motocin da zasu ɗaukeku zuwa airport suna hanya ku
zama cikin shiri Amaryarmu bani Samha Inason magana da ita"
Miƙawa Samha wayar tayi Samha tace “Ango kasha ƙamshi yau kam baki ya buɗe kenan"
ajiyar zuciya yayi yace “Samha don Allah karku ɓata lokaci mu daga Niger Sudan muka dawo
kuma yau zaku taho yanzu haka motocin ɗaukar amarya sun taho Muhsin shine jagora kamar
yanda yayi alƙawari" daga haka ya kashe wayar Samha ta saki baki tana bin wayar da kallo,
yanda taji Muryarsa babu walwala babu wani cikakken farin ciki ya sanyata tafiya tunanin to
meye yake faruwa musamman a gaɓar furucinsa na ƙarshe da taji Muryar ta kama rawa, to
dake ba huruminta bane haka ta miƙawa Batool wayar tana cewa “Wannan sauye sauye sunyi
yawa Janah kinji fah yanzu Bama Abujan zasu zauna ba Sudan za'a tafi da amarya kuma a yau
ɗinnan" itadai Batul banda kuka babu abinda takeyi wanda ta kasa gane na meyene, itadai
bazatace kukan rabuwa da Inna take yi ba domin dama ba tare suke ba sannan bazatace kukan
tunanin haɗuwa da Namiji takeyi ba domin tasan namijin da take tunanin samun samansa a
naci abune me wahala sannan ba kukan ƙiyayyar Deen takeyi domin kuwa ita ta zaɓeshi cikin
tarin manemanta tace shine gwarzonta domin ya cancanta, sannan Jany ta ma rigata samun
gurin zama a gidansa, to kukan me take yi ne ita?.
Tambayar da tayiwa kanta kenan bata da amsa, batasan tsayin lokacin data ɗauka ba ita dai taji
ana cewa “Inna ga amaryar anan" Shigowa Inna tayi ita da Baffa Khamilu da Baffa Maigari suka
zauna a saman kujera Suka sauke ajiyar zuciya Baffa Khamilu yayi gyaran murya tare da
salatin Annabi yace “Faɗimatu haka Allah yake ikonsa, tabbas wannan lamarin yin Ubangiji ne
bana mutum ba don Allah kiyi haƙuri da abinda zakiji ko kuma gani dukkanmu munsan zaki
shiga mamaki amma ya za'ayi da tsarin Ubangiji shi komai nasa tun kan ya halicci duniya ya
gama tsara shi kiyi haƙuri Faɗimatu kuma kiyi biyayya da mijin da Allah ya zaɓa miki Insha
Allahu zakiyi alfahari dashi wlh bazan yaudareki ba mijinki Innanki ne kawai befi sonki ba itama
don kar na shiga hurumin Ubangiji ne yasa na faɗi haka, Yaya in kana da abin faɗa ka faɗa sun
jima suna jira kuma tafiyar da tsayi donma jirgin gidane" Nan Baffa Maigari yayi mata nasiha me
ratsa jiki kafin daga bisani Inna tayi mata tata ta rungume Inna tana wani irin kuka me ratsa ruhi
daƙyar su baffa suka rabasu aka sanyata a mota Inna Tabi'ah ƙanwar mahaifin amarya da suka
ciki ɗaya sai Inna Saude da suke uba ɗaya sannan Inna Jamila matar Yayan Inna Laure sai
ƙawayen amarya guda biyu Samha da Janah su sai maƙociyarsu Aunty Jamila sune zasu raka
amarya, motoci suka lula bisa titi babu abinda yake tashi a motar da amarya ke ciki sai sautin
ajiyar Zuciyarta inda Muhsin dake zaune a gefe ya kirawo yayan nasa a waya ya kara a
kunnensa yace “Muhsin kace ta daina kuka nayi mata Alƙawarin duk yanda taso haka zamu
rayu Muhsin Don Allah wlh banason kukanta"
Murmushi yayi yace “Kana karɓar aikin zata daina Big Bro" kashe wayar yayi sukaci gaba da
tafiya, suna zuwa airport suka shiga jirgi aka basu izinin tashi suka ɗaga zuwa birnin Khartoum,
shigar dare sukayiwa Sudan amma duk da haka parke suka tarar masu ɗauke da tutocin ƙasar
sun jeru reras gwanin sha'awa, fitowa sukayi kasancewar motocin guda goma sha biyu ne biyun
tsakiya aka sanya amarya da mutum biyu ɗayar kuma sauran mutane suka shiga suka ɗauki
titin masaukin amarya.
Ba wata doguwar tafiya akayi ba daga airport ɗin suka shiga wata unguwa da Mazajen sojoji
suke gadi nan ɗinma layi na biyu suka parker jerin wasu manyan gidaje cikin wanda yafi
kowanne girma suka shiga zubin gidan zubin ginin manyan attajiran duniya a cikin gidanma
sunyi tafiya me ɗan tsayi sannan suka parker suna fakawa wani sassanyan kiɗan tarɓar amarya
ya soma tashi, aka buɗe mata motar kowacce kusurwa soji ne ke gadinta Inna Saude ta kamo
hannunta Samha ta kamo ɗayan hannun suka fito da ita ji kake ana sakin harbi ta ko ina sosai
suka tsorata Saida wata matashiyar budurwa tace “Ba yaƙi bane sanarwar zuwan amaryarmu
ne" ajiyar zuciya suka sauke suka fara tattaki zuwa wani ɓangare da yafi kowanne ɓangare
haɗuwa da ƙawatuwa suna riƙe da hannunta anata zubansu kuɗaɗe da turare gabaɗaya gidan
wani ƙamshi yake me sanya kasala.
Step suka taka suka haura Wannan budurwar ta buɗe ƙofar parlour da ya girmi hasashena
wajen haɗuwa Saida suka wucce parlour uku kowanne in ka shiga sai kaga kaidai iyakar
ganinka baka taɓa ganin wanda ya kaisa haɗuwa ba hatta Samha a wannan rana Saida ta
zama ƴar ƙauye Zuciyarta tana raya mata to sukuwa waye Deen ne a duniya ɗan waye shi?" Muryar wannan matashiyar kyakkyawar budurwa ce ta katse mata tunani da cewa “Alhmdllh
mun gama namu Amaryarmu yanzu nasan tunanin haɗuwa da angonki bazai baki damar
fahimtar komai ba saboda haka gobe Insha Allahu in Kin dawo cikin nutsuwarki na gabatar Miki
da kaina" Juyawa tayi wajen baƙin tace “Yawwa kuma muje na kaiku masaukin ku kuyi wanka
kuci abinci ku kwanta