Showing 6001 words to 9000 words out of 34531 words

Chapter 3 - SIGN MARRIED 2 BOOK OUM HAIRAN.pdf

baƙar gajiya da
yunwa da takeji cikinta me watanni bakwai da sati biyu sai dunƙulewa yakeyi dake shiga tayi irin
ta Muslim hijjab ɗinta jalbab kwata² Samha bata lura da halin da take ciki ba.
Kitchen ta wucce domin samawa baƙuwar Tata abinci indomie ta dafa fara ta zuba Stew a gefe
sai kwai guda huɗu da soyayyen nama ta ɗauka ta kaiwa Batul dake zaune Zuciyarta babu daɗi
har yanzu tsoro takeji kada dukan da tayiwa wannan mutumin ya mutu ita kanta bazata iya tuna
ya akayi ta samu Zarrah iya haike masa har ta illatashi haka ba kawai da tasan Allah ne ya
kareta daga mugun nufinsa, ta sani duk inda suke yanzu sunanan suna nemanta.

Ajiyar zuciya tayi ta godewa Allah da yasa ko waya batada ita bare ayi tracking a gano inda
take, firgigit tayi ta ɗago ta kalli Samha dake zaune a gefenta tace “Tun ɗazu na kawo Miki
abinci kici kiyi sallah ki kwanta ki huta sai mu tattauna Ni zanyi wani aiki a system" jinjina kai tayi
tare da yi mata Godiya ta fara cin abincin zuwa yanzu ba daɗin komai takeji ba saidai kawai
tanaci ne don tasan da wanda yake jiran taci shima yaci a jikinta.
Taci abincin sosai Samha ta kaita ɗaki ta nuna mata toilet tare da fito mata da wata doguwar
riga sabuwa cikin kayanta dake tsayinsu kusan ɗaya saidai Batul ta ɗan fita kauri kaɗan dake
ita tayi buɗewar ciki, bathroom ɗin ta shiga tayi wanka tayo alwala ta fito tana tsaye ta bata rigar
tana me binta da kallo sai yanzu ta lura da cikin dake jikinta batayi mata magana ba ta nuna
mata wajen sallah tayi sallar daƙyar tana idarwa wani zazzaɓi ya sauko mata ɗan gado ita dai
tunda Allah yasa ta haɗu da Ma'eesh har yau bata zauna lafiya ba, a jikinta a Zuciyarta da kuma
ruhinta kullum cikin zullumi take.
Abinda yake bata mamaki zuwa yanzu wani irin so take yiwa Ma'eesh da takejin zata iya fansar
da duk wani farin ciki nata akansa saidai kuma Zuciyarta tana samun rauni da sarewar gwiwa
ganin ko sanda tana gidan Lateef tunda yace mata yana zuwa Australia har rana me kamar ta
yau bai kuma nemanta ko a waya ba still ko ta nemeshi bata samunsa, ajiyar zuciya tayi tana
gyara kwanciya tare da dafe cikinta da bai wucce six weeks yazo duniya ba.





Share siririn hawayenta tayi cikin sanyin muryarta tace “Bani na zaɓi hakan ba na ɗauki wannan
matsayin ƙaddara Allah kai kasan yanda zakayi dani da abinda ke ciki na Allah ko zai karɓa?"
Gabanta ne ya faɗi tana tuna to wai shi cikin ma taƙamaimai na waye? Lateef ko Ma'eesh?
Tasha jin Lateef yana danganta cikin da kansa sannan daren da zai satota daga gidan Ma'eesh
tana tuna lokacin da Ma'eesh yake faɗa mata duk da yanason baby dole ya haƙura da wannan
na jikinta domin ya gurɓata kenan nashi ne?
Da waɗannan bad thinking ɗin bacci ya ɗauketa kamar kullum dai Ma'eesh ɗin ne cikin baccinta
tanata murmushi yanayi me daɗi yanata tsumata da salon ƙaunarsa, zuba mata idanu Samha
tayi yanda take murmushi da kiran Ma'eesh da gani kasan tana cike da kewarsa, ajiyar zuciya
ta sauke ta gyara mata rufa ta fita ta koma wani ɗakin ta kwanta, washegari da asuba Samha ta
tasheta sukayi sallah Samha tace zataje islamiyya a nan masallacin gaban gidan da take kamar
tace zata bita sai kuma ta share ta fita ita kuma ta gyara kwanciyarta.
Bacci tayi sosai dake ranar ta kama asabar sai wajen 10:30am Samha ta tasheta tace “Wannan
bacci haka Teemah" murmushi tayi tace “bansan meye yasa bacci na ya karu ba bana gajiya da
bacci" abin kari ta nuna mata tace “Oya tashi kiyo brush muyi break mu zauna mu tattauna"
bata gardame ba tayo brush da sabon brush ɗin da Samha ta bata ta dawo Saida tayi walaha
sannan suka zauna cin abincin Samha ta tambayeta wacece ita sannan ina mijinta meye ya
rabata dashi har ta fito batasan inda zata ba a ƙasar da bata da kowa?" Taso yiwa Samha
tsallake a labarinta saidai tasan mutum yana ƙara ƙima ne da gaskiyarsa saboda haka ta sanar

da ita gskyr labarinta sosai Samha ta kaɗu da jin wannan cukurkuɗaɗɗen lamari ta dubeta tana
share hawaye tace.






Koda nafito bariki Teemah maraici ne yajamin da iyayena suna raye bazanyi bariki ba koda wani
abun zanen ƙaddara ne amma ke mahaifiyarki ce ta yarda kije kiyi sign married kawai saboda
soyayyarta da kuɗi yanzu ga abinda hakan ya janyo ke baki rayu da wanda ya zaɓi rayuwa
dake ba kin ɓige da zagaya duniya Teemah rayuwarki darasi ce ga mutane ba duk abinda kake
tsarawa rayuwarka ne yake zama zanen ƙadɗararka ba tabbas na tausaya Miki kuma na
tausayawa masoyinki na gaske Ma'eesh ki daina zarginsa da watsar sake bana tunanin a cikin
Nutsuwa yake abu daya da zakiyi addu'a a kai Allah yasa maƙiyansa basu samu nasarar ganin
bayansa ba"
Da sauri ta ɗago tace “Sai ya mutu ya barni Samha? Me zance da abinda ke cikina bayan yazo
duniya ya buƙaci sanin mahaifinsa a lokacin da bansan wani da zan kama a duniya na nuna
masa ba?" Murmushi Samha tayi tace “Ai cewa nayi ayi addu'a Teemah ki saki ranki Insha
Allahu zamu cinye jarabawarmu Ni yanzu zan fita munyi da saurayina zamu haɗu a beach
banason ya jima yana jirana duk abinda kike buƙata akwai a kitchen" fatan alkhairi tayi mata ta
shirya ta fice ita kuma ta kwanta tana lazumi har azahar tayi sallah ta shiga kitchen tayi musu
girki ta jera a dinning ta gyara gidan ta kunna kallo tanayi tana duba agogo gajiya tayi da zama
ta koma ɗaki ta fara duba kuɗin dake cikin jakar data ɗauko a gidan Lateef Saida tsoro ya
shigeta kuɗin ba ƙananu bane kuma dukkansu Dollars ne ta mayar ta zuge ta kwanta.





Sai yamma Samha ta dawo sukaci abinci tana bata labarin beach ɗin da irin nishaɗin da ake
samu a kallon ruwa ita dai murmushi kawai takeyi, Samha tace “ki shirya gobe muje dake zakiji
daɗin gurin" ɗagowa tayi tace “ni yanzu ina zan iya wannan yinin da kikayi a beach bayan haka
ma Ni yanzu nasan nemana akeyi dole sai na ɓoye kaina na dogon lokaci abubuwa sun lafa
kinga kuwa zuwana beach kamar nace gani kuzo ne" jinjina kai tayi tace “Kuma hakane gskyrki
yanzu yaushe zamuje asibiti ayi mana scanning muga me zamu samu mu fara siyayya"
harararta tayi tace “Saikace wani ɗa me ƴanci zan tafi yin scanning da wata siyayya haɗe rai
Samha tayi tace “Banaso Teemah ki rinƙa jin Babyn nan kamar a ɗakin aure kika samoshi karki
cire masa karsashin rayuwa me daɗi tun yana yaro mu zama gatansa don Allah mu jiɓanci
lamuransa Insha Allahu sai ya rayu rayuwa me inganci Teemah wahala nawa da tarko kika
tsallake kuma duk akan abinda ke cikinki da ke kanki iya wannan ya isa ki gane akwai abinda
Allah yake nufi da kasantar dashi a haka"
Bata kuma cewa komai ba suka kwanta Samha na wayarta ita kuma tana karanta wasiƙar jaki

har bacci ya kwasheta. Haka rayuwa tayita tafiya cike da kalubale kala² sun samu wata
shaƙuwa da aminci tsakaninta da Samha komai tare sukeyi but ita bata fita ko ina hatta likitan
da yake dubata gida Samha ta kirashi suka sakar masa kuɗi.
Wani dare cikin ranakun rayuwarta tana kwance baccinta me daɗi tana mafarkin Ma'eesh wai
suna kwance yana shafa cikinta yana cewa da ita "Wanne suna zamu sawa babynmu Bea Allah
yasa yayi kalanki yayi kama dake....."







Ai bata gama idasa mafarkin ba ta buɗe idanu tana rarraba shi saboda wata nutsattsiyar azaba
da taji ta ratsa mararta ta kuwa zabura ta mike tana furta Innanillahi wa innah ilaihirraji'un
Allahumma ajirni fi musibati wa'akalifni khairin Minha la'haula wala ƙuwwata illah billahil
aliyul'azeem....." Sunan Allah babu irin wanda bata kira ba a wannan lokaci, can saitaji ciwon ya
lafa ta miƙe da nufin zuwa bayi ai bata idasa miƙewa ba baya ya ƙamar da ita mara ta riƙe taji
wani ɗumi yana bin ƙafarta daidai lokacin da Samha ta buɗe ƙofar ta shigo domin tunda EDD
ɗinta ya ƙarato bata yarda tayi bacci me tsayi tanayi tana leƙota wani lokacin ma tare suke
kwana.
Ganinta a durƙushe ya tabbatar mata giji tazo ta ƙaraso da sauri tace “Teemah haihuwar ce bari
na kira Dr Maleesha tazo ta dubaki" cikin few minutes saiga Dr Maleesha tana dubawa ta dago
tace “Haihuwa ce but dole muje asibiti Babyn yanada girma sai an taimaka mata" babu musu
dake taji damƙar Ubangiji suka tafi asibiti aka jorner mata wasu ƙarafa aka taketa aka saita wata
fitila gabanta Dr Maleesha da Dr Rudah suka duƙufa aikinsu cikin ikon Allah bayan tasha ƙari
aka ciro mata ƙatuwar babynta mace zam baturiya zance ma ko balarabiya oho, don babu ta
inda tayi kama da akwai jinin Bakar fata a jikinta.
Zuwan wannan yarinya a wannan yanayi ya tashi hankalin masu jiran zuwanta duniya a duk
inda take a faɗin duniyar da suka kasa ganosu sunga haihuwar yarinyar amma bayan haka
komai ya ɓace musu cikin hikima ta Ubangiji da suka takura ma sai alƙaluman tsafi suka fara
ƙwace musu. Ita kuwa Batul ana ciro yarinyar tace a bata a barta tun kafin a cireta daga jinin haihuwa ta fara
tofe abarta a ayoyin Ubangiji na tsari da manyan addu'o'in data sani na kariya daga kaidi da
sharrin maƙiya koda ta gama duk abinda suke mata har ɗinki da akayi mata tana maƙale da
yarta da bata tsaya ta ƙare mata kallo ba amma wani baƙon yanayi ne yake shigarta na tausayi
da ƙaunar gudan jinin nata...........
[7/5, 3:40 PM] Oum Hairan: *SIGNED MARRIAGE*
*_(Kalma ɗaya)_*


*OUM HAIRAN*

*_______________________________________*
*Book 2 Bonus page 7-8*
*_______________________________________*


Ɗinki tasha ciki da waje domin dama ko bata ƙaru ba Samha tace idan ta haihu sai an ɗinketa
to bare ga ƙari anyi mata aka basu wasu magunguna da zata rinƙa zubawa a ruwa me dalam²
tana tsarki dashi sannan bayan sun huta aka sallamesu, saurayin Samha Faruq shine yazo ya
ɗaukesu ya kaisu gida suka shiga ɗakin da ta sauka tun zuwanta nan suka rakata ta zauna sai
yanzu ta samu damar buɗe fuskar yarinyar ta zuba mata idanu tare da sauke ajiyar zuciya,
wannan shine Madara mai kama da nono zam Babyn da ubanta take kama hatta lips ɗinta da
yatsun ta komai dai, wasu hawaye ne suka zubo mata ta share tare da rungume yarinyar
soyayyarta ga Ma'eesh a hankali ta rinƙa kwaranyewa tana komawa kan yarinyar sosai ta rinƙa
jin tausayi da ƙaunar Babyn na zaga ruhinta a hankali ta furta “Alhmdllh ala kullu Hal!" Hawaye
ne yake sintiri ta fuskarta wanda batasan na mene ba farin ciki ko baƙin ciki, batajin ƴarta a
matsayin wata mara galuhu duk da tasan ba aure akayi irin na sunnar Annabi Muhammad
(S.A.W) ba amma dai da sauƙi tunda ba gantali tayi ta sameta ba da yarjejeniya aka samar da
ita.
Samha ce ta shigo dauke da cup na tea da soyayyan dankali da ƙwai ta ajiye a gefe tace
“Matsalarki kenan Teemah yau muna cikin farin ciki inacan inata status da Jany ke kuma kina
nan kina kuka saboda ke me wahala ce nifa yau jina nake kamar a filin Arfah nima na zama
Mom don Allah ki ware meye ne a ciki duka fah a duniya ne Nima inada Jalal ɗina yana gurin
babansa ne yaje Hutu but anytime zai dawo saboda na kira Dad ɗinsa nace ya kawomin shi
munyi baby yazo yaga ƙanwa"





Kallonta tayi tace “Ke naki halalltacce ne ko Samha?" Murmushi tayi ta share hawayen daya
kawo a idanunta tace “Kamar yanda Janny take haka shima yake, lokacin da Chadi tayimin zafi
na rasa tudun da zan hau na zauna mafita ta kullemin hatta kuɗin abinci ya gagareni bare na
zuwa makaranta sai na yanke shawarar haƙura da komai na tafi Algeriya domin neman kuɗi,
Teemah haka naje wajen wani mutum a unguwarmu da yake fitar da matasa ƙasashe don
neman abin dogaro da Kai na sanar dashi ƙudiri na na tafiya Algeriya ya tsaya ya gama sauraro
na sai yace zai min hoto banja ba na amince ya ɗaukeni hoto ya bani kuɗi me yawa tare da
waya me layi yace naje gobe zai kirani.
Haka akayi Teemah washegari ina kwance a BQ na gidanmu da Ƙanin babana ya karɓe ya
koreni daga cikin gidan kuma ya kafamin dokar karna ƙara shigar masa gida domin bazan
shafawa matarsa da yaransa HIV ba kasancewar ita ne ajalin mahaifana, wayar da Abdullahi
ya bani tayi Ring yace nazo na taho da shirina tare da tambayata inada passport nace masa eh
amma Zuciyata tayi mamakin yanda za'a tambayeni passport nida zanyi tafiyar mota.

Haka cike da ɗoki na tafi bayan ya sallami bakinsa ya dubeni yace “Samha na daɗe ina
tausayin rayuwar da kikeyi tun bayan rasuwar Mahaifanki saboda haka na yanke Miki wani
hukunci domin ki samu damar data dace dake akwai wani mutum a Cairo Egypt kenan yana
neman wadda zata zauna tare dashi ta kula masa da gidansa tsayin shekara guda zai baki 2.5
millions Dollars a. Cikin shekara ɗaya kinga kuwa ai kin haye"




Yawan kuɗin bai bani damar tunanin irin aikin da zanyi ba haka na amsa nidai haka muka fita da
Abdullahi yayi mana Urgent booking zuwa uku na yamma muka tashi sai Birnin Cairo mota aka
Turo ta ɗaukemu aka kai mu wani katafaren gida anan wajen Tara na dare ne wasu motoci
sukazo suka ɗaukeni tun anan na fara raina kaina da jinjinawa haukana Teemah wani gida ne
me zubin gidan sarakai aka kaini aka tafi aka barni na rayu tsayin sati biyu Ni kaɗai kafin
Khazeem yazo gareni ranar da yazo ranar ya samin kuɗina a acct ɗina da aka buɗemin kuma a
ranar ne ya bayyana min aikina, na raina kaina nayi kukan da banida mafita a ƙarshe dai na
bashi dama kinsan damar dana bashi? Zai yi mu'amala Dani har na samu ciki idan nayi ciki na
haifa masa baby zai sallameni na tafi na bar masa Babyn, na amince ne saboda bani da mafita
haka muka fara rayuwa dashi cikin ikon Allah a watan kuwa na samu ciki Teemah naga gata har
cikina ya isa haihuwa akayi min C.S aka cire min Yarona namiji Balarabe me kama da ubansa,
idan na kalli yaron nakanyi kuka matuƙa da tuna cewa bazan rayu tare dashi ba, bansan meye
yazo ran Khazeem ba bayan naji sauƙi wata rana ina zaune a ɗaki ina feeding Jalal ina kuka, ya
shigo ya sameni ya tsugunna a gabana yacemin.
"Samha" ɗagowa nayi na kalleshi ya sanya hannu ya sharemin hawaye yace “Kinsan dalilin da
yasa na zaɓi nayi Miki ciki ki haifamin babyn nan" bai bani damar bashi amsa ba yace.





Tun ina ƙarami a dokar masarautarmu aka haramta min aure saboda dalilin da har yau bansan
wanne bane, shekaruna sunyi nauyi gashi na jarabtu da son samun ɗan kaina duk abokaina
sunada yara meye yasa Ni zan kasa samarwa kaina ɗan da zanke kallo ina jin daɗi, banida
kowa sai shi kaɗai mahaifina ya rasu tun ina ƙarami Mahaifiyata ma bayan rasuwar mahaifina
tanada cikin ƙanina aka kasheta na tsira ne saboda bana tare da Masarauta tunda aka yayeni.
Nayi tunanin riƙe Jalal a gurina saidai na fahimci idan na riƙeshi za'a farauci rayuwarsa saboda
haka zan canza Miki Ƙasa zan ki raineshi cikin kulawa da gata ya rayu kamar Basarake"
wannan shine dalilin zuwana Austaralia ya bani wannan gidan da motar hawa ya zubamin
mazajen kuɗaɗe a acct ɗina tun daga wannan lokacin bai kuma neman wani abu a gurina ba
muna rayuwa dani da ɗansa cikin gatansa da kulawarsa Teemah Inason nayi aure saboda na
riga na saba da maza bana iya tsare kaina saidai kuma duk duniya uban ɗana shine namijin da
nakeso shi kuma har yanzu Emirates ɗinsu taki bashi damar aure"

Jinjina kai Batul tayi cikin tausayin kansu tace “Duk da haka gara ke Samha maybe society
ɗinku bazasu kyamaceki da ɗanki ba nikuwa ƴata zata zama abar tsangwama idan na koma
ƙasata da wannan na fara tunanin ya zanyi don hanata shiga taskun rayuwa" ɗaukan yarinyar
tayi tace “Ita dai babu abinda ya dameta bacci takeyi hankali kwance" Ranar sati guda yarinyar
tace suna Aisha suke kiranta da Jany duk da batasan ma'anar sunan ba zaɓin Ma'eesh ne a
mafarki haka kwana uku da suna Jalal ya dawo yaro kyakkyawa Masha Allah, kulawa sosai
Batul ke samu ita da Jany, cikin watanni shidan da suka biyo baya ne a hankali yau da gobe da
kuma yanayin mutanen da take rayuwa a cikinsu itama ta fara sakewa sukan fita beach suyi
nishaɗinsu, abu ɗaya da yake neman hana Batul kwanciyar hankali yanda idanun maza ke
kanta duk wani motsinta sai ta samu me tankawa duk kuwa da cewa taƙi bada dama.
Cikin hakan ne Samha ta sama mata aiki a babban rastuarent ɗin da take aiki taji daɗi sosai
course kaɗaici na damunta idan Samha ta fita ta barta, suka sanya Jany makarantar da Jalal ke
zuwa kullum zasu kaisu idan sun dawo su ɗaukosu haka suke gudanar da rayuwarsu, ko a
restaurant ɗin haka take fama da mutane maza da mata Allah yayi mata baiwar mutane ita kam
abu ɗaya da yake dakatar da ita da kula kowa duk kuwa da yanda me masaukinta take bata
shawarar sakin jiki tayi rayuwarta da yanci, shine tsoron sake afkawa matsala.





Zuwa wannan lokaci har ta gaji da kiran wayar Ma'eesh ta haƙura ta sallama tanajin cewa ita
kaɗai ce kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login