Showing 9001 words to 12000 words out of 34531 words

Chapter 4 - SIGN MARRIED 2 BOOK OUM HAIRAN.pdf

keda Jany, tayi nufin shirya tafiya don zuwa ta gano meye yake faruwa saidai
tuna turakunan da rayuwarta ta tsallake har Allah ya kawota yanzu yana kashe mata gwiwa
karshe ta sanar da Samha sosai ta fusata tace “idan shi bai nemeki ba Mom Jany bai kamata
ke ki zubar da yanci ki nemeshi ba ai shine yake da abun nema a gurinki kinga kuwa shi
nemanki ya kama" haka ta haƙura ta sallama.
Yau dake asabar ce basu da aiki suna zaune a parlour Jany ta miƙe ta fara tafiyarta sosai
shekara ɗaya da rabi Batul ta dubi Samha tace “Kinsan me yake zuwa raina?" Girgiza mata kai
tayi ta sauke ajiyar zuciya tace “Inason zuwa Nigeria Mahaifiyata nakeson naje na gani" jinjina
kai tayi tace “Nima ina shirin yi Miki maganar kika rigani duk da cewa babu abinda na bari a
TChad Inason zuwa naga kawaye da yan'uwana da suka wofintar dani kinga daganan sai muyi
Nigeria yanzu mu shirya tafiya yaushe kike ganin zamu tafi?"
Murmushi tayi tace “Ƙarshen wata ko? Kinga ko 1 month sai muyi mu dawo amma ke me kika
gani?" Jinjina mata tayi tace “Hakan yayi zamu tafi da yaran ne ko zamu barsu gidan raino?"
Zaro idanu Batul tayi tace “Ni shegiya inji ɗan daudu ai ƙafata ƙafar Jany na bazan iya kwana
batare da ita ba ke nifa yanda nakejin Jany a raina banajin kaina" dariya sukayi suka tashi suka
fice suka nufi beach yauma kamar kullum a inda suka saba zama suka zauna aka kawo musu

kofin coffee kowacce na danna wayarta suna hira sama sama, sallama sukaji a bayansu abinda
yasa Samha juyawa tare da kallon me sallamar wanda idanunsa ke kan Batul da ko arziƙin ta
É—ago ta kalleshi bai samu ba"
Numfasawa yayi yace “Ko zan iya zama?" Jinjina masa kai Samha tayi tare da gyara masa
wajen zama ya zauna yana kama hannun Jany yace “Ƴar uwar taki kurma ce halan?" Sai yanzu
ta ɗago ta watsa masa wani mugun kallo tare da miƙewa taja hannun Jany suka bar gurin, ya
bita da kallo cike da mamaki yace “Ni sunana Nuraddeen ana kirana da Deen ɗan Nigeria ne ni
Kano shine garin iyaye na amma mazaunan Abuja ne Ni kuma ina aiki anan kuma ina
kasuwanci, am ƙawarki ta daɗe tana burgeni saidai yanda naga bata bawa Kowa dama yasa
nima jikina yayi sanyi duk da ƙarin abinda yasa naƙi zuwa gareku da ƙoƙon barata saboda a
farko na zaci matar aure ce sai daga baya nake samun labarin bata da aure"
Zamewa yayi daga kan kujerar yace “Don Allah in da hali ki shigar da ƙoƙon barata gareta wlh
ba da wasa nake ba idan ta amince ko ina iyayenta suke a duniya zan tura nawa ayi magana
nidai burina ta karɓeni ta yarda da buƙatata" jinjina kai Samha tayi tace “To Deen saidai a
gwada wannan kawar tawa dakon son gaibu takeyi taƙi kallon kowa bare ta bashi dama amma
zanyi maka bakin ƙoƙari" godiya sosai yayi sukayi musayar number tare da bashi ta Batul
sukayi sallama ya tafi itama ta tashi ta isa motarsu ta tarar da Batul ta cika ta batse tace “Tuba
nake Allah ya taimakeki kinsan Allah ya karrama É—an adam musamman wannan bawan
kammalalle Ni tunda nake zuwa gurin nan bantaɓa ganin yayiwa wata mace magana ba sai yau
yawanci a gefe zaki sameshi yana yan aikace aikacensa" cikin hassala tace “to aku me
magana kizo ki kaimu gida ko ki bamu mukullin mu tafi".........



*_Assalamu alaikum everyone_*

*Sunana Fauziyya Tasiu Umar (OUM HAIRAN)*


Yau muna birthday Hairan da Widad dole muyi promo 300 Nrml group VIP 600 please iya yau
ne kaÉ—ai

Kar kuyi ƙasa a gwiwa kuzo ku runguntsuma ku tattaru muji chakwalkwalin chakwakiyar nan me
rikita tunani da sanya shauƙi, shin ya rayuwar zata kasance bayan kowa yayi baram baram da
hanyar Allah? Akwai sauran damar tuna ko lokaci ya ƙure?




And please adult contact ne wannan labarin don Allah in Baki iyawa ki haƙura don wlh sai na
zubar da Abin a wannan book É—in.

Via 300 Normal group VIP 600 only
9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay Evidence 09031307566.

please Ku daina turamin Evidence ta wannan number 09013718241 course saƙonni suna yawa
a kanta.




*In kun shirya🤗 Nima na shirya👌🏽*


*Oum Hairan*
[7/7, 4:51 PM] Oum Hairan: *SIGNED MARRIAGE*
*_(Kalma É—aya)_*


*Oum Hairan*
*______________________________________*
Book 2 page 9-10
*______________________________________*


Dariya Samha tayi tace nidai zanga inda inda zakikai wannan kayan da kiketa tsumawa saidai
ki wanke kisa masa pant, Please Teemah tunda dai kinƙi ki bada na haram aci aji daɗi a
raƙashe a hole yanzu ga zancen gsky yazo Allah kar kiyi sake da damarki Wannan guy ɗin ya
haÉ—u sosai" banza tayi da ita har sukaje gida ta shigewarta É—akinta ta cire kayanta tayi wanka
tayiwa ɗiyarta ta sanya mata kayan sanyi itama tasa domin yau alamun ya nuna dusar ƙanƙara
za'a kwana zubar musu.
Room hitter ta kunna ta kulle ko ina kasancewa bata sallah taja Æ´arta suka kwanta cike da
kewar ɓangarorin rayuwarta kamar yanda ta saba ta ɗauki wayarta ta fara kiraye kirayen
numbers cikin numbers biyar data kira É—aya ce ta shiga ta Laminu me shayi ta daÉ—e tana ring
ba'a ɗaga ba Saida ta kira so uku sannan aka daga tace “Assalamu Alaikum Laminu Batula ce"
ajiyar zuciya ya sauke yace “Hajiya Batulu ta Manzo kwana biyu" murmushin yaƙe tayi tace
“Don Allah ko zan iya magana da Innata?" “Toh Batulu Ni yanzu ina zan samu Inna Laure ai
tunda kikayi aure itama ta tashi ta koma gidan benen da mijinki ya siya mata ta rangaÉ—a
aurenta da Idi dillali ban kuma ganinta ba sai watanni biyar da suka wucce da na haÉ—u da
ƙawarki Murjanatu nake tambayarta labarin Inna Laure take faɗamin ai tasai da gidan da mijinki
ya bata ta Idi dillali Lagos yanzu haka suna can"
Tashin hankali sosai ta shiga tace “yanzu ya akayi duk haka ta faru Bansani ba Meyesa kullum
wayoyinku basa shiga yanzu ina zaka nemonin Murjah?" Cewa yayi “ah ita wannan tana
gidansu bata samu promotion irin naki ba duniya tayi mata attishawar tsaki tananan tana fama

da ciwon nan na zamani in ta fara gudawa har ƙofar gida" cikin tashin hankali tace “Eh
Murjanatun? Yaushe ta gamu da wannan ciwon Innanillahi wa innah ilaihirraji'un don Allah
Laminu ka haɗani da ita ka turomin account ɗinka xansa maka kuɗi kaima ka ƙara jari"



************


Sosai ya rinƙa mata Godiya ya kashe wayar ya kalli mutanen kusa dashi yace “Waye zai iya
kaiwa Murja Waya zasuyi magana da Batulu" Isah ɗan garuwa ne yace “Ah zan iya amma nawa
zaka bani?" Cikin masifa yace “Kaidai kwai maye to kaje ka kai mana sai mu tura acct ɗin muga
nawa za'a Turo mana" karɓa yayi ya tafi ya kaiwa Murja tana zaune a zauren gidansu duk ta
kwarjale ga ciwo babu kuɗin shan magani, daga bakin ƙofa yace mata “Batula ce tace a kawo
Miki waya" cike da zumuɗi ta karɓi wayar, tana karɓa kuwa tana kira tace “Batulu kin samu
duniya kin barmu a wahala ko nemanmu bakyayi" numfasawa tayi tace “ta ina zan nemeki
Janah sama da shekara guda nake kiranki wayarki bata shiga idan na kira ta Laminu me shayi
shima bata tafiya daƙyar yau Allah ya bani Sa'a na sameshi Janah meye yake faruwa ne ance
Inna ta tabar Kano ta koma Lagos ina zan samu lambar da zan sameta?"
Girgiza kai tayi cike da tausayawa kai tace “Ki bari kawai Batulu babu yanda bamuyi ba nida
Mamanmu kan Inna karta yarda da zugar mugun mutumin nan ta siyar da gidanta amma ta
fitittike taci mutumcinmu har tana cewa baƙin ciki mukeyi mata likkafarta zata ƙara ci gaba zata
tashi daga cikin talakawa taka koma cikin danginta masu kuÉ—i haka munaji muna gani ta siyar
da gidan da Yake mallakinki wanda Ma'eesh ya baki matsayin Fansar budurcinki Naira Miliyan
É—ari uku da hamsin, wlh Batul ko la'ada Duk kyauta ta Inna Laure Idi dillali bai barta ta bamu ba
cikin dare ya kawo mota suka É—ebi tsirarin kayansu tunda dama furniture duk a suna cikin ciniki,
suka tafi suka bar unguwar nan babu sallama yanzu haka dai zancen da nake Miki wata rana
na haÉ—u da Inna ga tsohon ciki a jikinta ga bara tanayi a Lagos na tambayeta ya haka tana kuka
tacemin ko kuÉ—in motar dawowa arewa bai bar mata ba ita yanzu Damagaran takeson komawa
cikin danginta haka na É—auketa na kaita tasha na biya mata kuÉ—in mota tare da guziri ta tafi
Damagaran yanzu haka dai tana Damagaran" cikin tashin hankali tace.






“Amma ciki fah kikace Janah?" Murmushi tayi tace “kuma ƙarin baƙin cikin ma tace bana Idi
dillalin bane wai Wasu ne suka ganta a wahale shine sukace tazo gidansu ta rinƙa karɓar abinci
kullum suna bata abinci harda ruwan wanka tayi wanka kinsan Inna idan taji gyara kyakkyawar
mace ce gata jajir iya wuya bantaɓa ganinta tayi baƙi ba, a hakan ne ɗaya cikin mazaunan
gidan ya ritsata wata rana yayi mata fyaÉ—e shine ta samu cikin kuma yace idan ta danganta shi
da cikin sai ya kasheta ita kuma gudun kar su nemi rabata da rayuwarta kawai ta yanke

shawarar barin gidan shine ta fito tana bara tana kwana a ƙasan gada har Allah ya haɗata Dani
watarana a kasuwa" Tashin hankalin da Batul ta shiga fasalta yawansa ma ɓata baki ne haka ta
aje wayar Zuciyarta a jagule ta tashi tana zaga É—akin, cikin shekara biyu abubuwa sun rikicewa
rayuwarta tana ganin kamar ta samu sauƙi ashe akwai wata ƙurar a ƙasa, shigowar Samha ne
ya sata tsayawa tare da zuba mata idanu, Samha ta tako gareta tace “Mene kuma yake
faruwa?" Nufar wardrobe tayi ta buɗe tace “Dole ya zamemin neman visa don komawa Afrika
cikin satin nan Samha idan kin shirya mu tafi tare in kina da abinda zaki ƙarasa na tafi Ni kaɗai"
fahimtar yanda take a dame ne yasa batayi mata mgnr abinda ya kawota ba itama ta fara taya
ta shirya kayan tace “Amma bamu sanar da gurin aiki zamuyi tafiya ba gashi kinsa mana tafiyar
a ƙurarren lokaci" bata iya bata amsa ba haka suka gama suma kwanta washegari suka fita aiki
kamar yanda ake ta shirye shiryen zuwan mamallakin rukunin gidajen abincin Na MB Kitchen's
haka akaci gaba da gabatarwa cike da annashuwa ita kam batada walwala haka suka tashin
washegari juma'a ta kama ranar da shugaban nasu zai shigo bata wani bawa zuwan nasa
muhimmanci ba duk da cewa an sanar da ita idan ya shigo taron ma'aikatansa gabaÉ—aya yake
haÉ—awa haka idan zai tafi.





Taje wajen aiki tayi abinda zata yi gaf da fara taron ta tafi ambassy domin gama shirye shiryen
tafiyara Afrika daya rage saura kwanaki biyu ta tashi daga ambassy gida ta wucce saboda
ciwon kai da faɗuwar gaban daga sarƙeta washegari asabar ce bata da aiki Samha ce ta fita ita
kam a gida ta yini sai yamma ne wayarta ta fara rurin neman agaji tayi tsaki tare da danna
gefenta cikin kwanakin nan kaÉ—aici yafi mata komai daÉ—i da wannan ko wayarta batason taji tayi
rurin neman agajinta.
Bata dawo daga duniyar tunanin datayi nisa a ciki ba wayar ta ƙara ɗaukan ruri ta ɗauka a
fusace ganin number ƙasar ce ya sanyata karawa a kunneta, sallama aka fara mata da ita ta
amsa tare da Nutsuwa don tuna inda tasan Muryar, maimakon haka sai taji an sauke numfashi
anci gaba da cewa “Ranki ya daɗe gani a harabar gidanku a taimakeni a zo a ji da menazo"
sosai mamaki ya cika ta tasan wannan dukka sharrin Samha ne haka dai ta daure ta gyarawa
Jany dake bacci kwanciya ta ɗauki ɗan ƙaramin hijjab ɗinta ta sanya ta nufi inda ake neman
nata.
Tunda ta fito idanun Deen ke kanta har ta ƙaraso inda yake tsaye fuskarta a ɗaure tayi masa
sallama ya amsa tare da zubanta idanu tana ci gaba da latsa wayarta, dama baiyi tsammanin
wata tarɓa me kyau a gare ta ba domin tunani yakan fidda kamanni bisa dukkan alamu yarinyar
tsoron maza takeyi koda yake ga yanda Samha ta basa labarinta ya halatta na tayi tantamar
sake yarda da wani namiji a duniya to amma ai ba'a cire tsammani kuma banda abinda shi
dama farin banza ai a farau faraun banza yake ƙarewa, ita me take tsammani da mutumin da
sukayi wannan rayuwar dashi, yafi mata sha'awar taimakon kanta ta gyara gobenta saidai ya
fahimci kamar hankalinta baya zuwar mata da haka, but me nema baya ƙasa a gwiwa zai dage
bakin rai bakin fama don ganin ya mallaketa halalinsa.

Ajiyar zuciya suka sauke a tare ta juya da nufin bar masa wajen domin ta tsargu sosai da kallon
da yake yi mata, da sauri ya riƙo hannunta tare da janyota jikinsa ta faɗa ƙirjinsa yayi saurin riƙe
ƙugunta yaja ajiyar zuciya me ƙarfi tare da ɗora bakinsa daidai kunnenta yace “Kyakkyawar
fuska tana ƙara Armashi tare da murmushi gimbiyata don Allah ki daina hukuntani da laifin
ƙaddarar da Allah ya jefoni cikinta a ƙarshe Fateemah koma mene Ni a haka nakeson ki zama
sirrina kuma uwar ƴaƴana ki yarda ki bawa wannan ƙasƙantaccen bawan dama yaje dake ga
iyayensa matsayin Sarauniyar data yarda ta rayu ƙarƙashin mulkinsa Fateemah nayi alƙawarin
kare miki mutumcinki da ƙimarki har fitar numfashina na ƙarshe"
Zamewa yayi ƙasa ya riƙe Ƙafarta yace “Don Allah Mom Jany ki taimaki Deen ki damƙar
rayuwarki data Jany amana a wajensa wlh bazanci amanarki ba, zan rayu ne yanda kikeso"
Tunda ya fara maganar ta zubansa idanu kyakkyawan saurayi Masha Allah son kowa yanayinsa
yana fidda wata kala da akafi samunta a halpcase wato ruwa biyu yanada ƙirar ƙarfafa yanada
suma kwantacciya wadda alama ta nuna rashin barinta ta taru sosai shine ya hanata zama irin
ta larabawa, da gaske Deen ya haÉ—u. Cikin kwanakin daya shigo rayuwarta babu abinda yake bata mamaki irin sanyin halinsa, duk
wulaƙancin da take yi masa bai taɓa nuna ya damu ba abu ɗaya yake faɗa mata kullum Mom
Jany (Walaƙad karramana bani adam) wannan cewar Allah S.W.T ce don Allah ki bani dama
nasan bazan taɓa samun matsala da ke ba kiyimin alfarmar so Fateemah"




Rikita mata lissafi yake yi da kalamansa sannu a hankali ya fara cusawa Zuciyarta tausan sa
wasu ɓangarori na ranta yana bata shawarar to ita me take jira da rayuwa ne? Da bazata
nemawa kanta makoma ba kafin ita duniyar da kanta ta nema mata, idan tace Ma'eesh take jira
har sai yaushe ne zai waiwayesu meye ya hanashi nemansu tabbas bata taɓajin a ranta
Ma'eesh baya duniya ba ita dai tafi zargin duk abinda yake buƙata a gurinta ya gama samu ne
shiyasa ya wofintar da rayuwarsu" da wannan tunanin taji ya sake riƙe hannunta yace “Damar
farko kuma ta ƙarshe Fateemah don Allah...." Wani kuka ne me ƙarfi ya ƙwace mata da ya
sanyata ture hannunsa ta nufi cikin gidan da gudu ta faÉ—a gado ta rushe da kuka me sauti tana
yage hularta da Hijjab É—inta, daidai lokacin da Samha ta shigo da uwar leda a hannunta ta aje
tana cewa “Ananan ana sana'ar kenan? To Allah yabada Sa'a yayi miki tsari da makantar
ƙuruciya domin tabbas baki daina kuka akan wannan Guy ɗin da alama ta nuna babu shi a
wannan duniyar ba"

Sake fashewa tayi da kuka tace “Ya zanyi ne Samha so nake na saba da rashinsa so nake na
cire shi a raina saidai na kasa ta ina zan fara ne?" Murmushi Samha tayi ta zauna a kusa da ita
tace “Abinda nakeso ki tambaya kenan kika kasa Teemah matakin cire matacciyar soyayya a rai
shine ɗaukan me rai kisa a samanta kiyi ƙoƙarin barin matacciya matsayinta Na mara amfani ki
bawa rayayyiya power ta hanyar kallon masoyin gsky da idanun rahama Teemah tunda nake
dake Deen shine mutum na biyu da ya nuna yana miki so irin na aure dama Hameed bai kai ba
domin bashida nagartar zama abokin rayuwa but meye matsalar Deen ne idan kyau kike nema
shima ya samu rabonsa Asalin ta inda kyau yake ya ɓullo mahaifinsa Balaraben Sudan ne Kano
ne amma mahaifiyarsa Balarabiyar Labanon ce É—an babban gida ne gidan addini gidan dattako
gidan kamala kuma gidan arziƙi sannan shima ya tara nasa, gashi da sanyin hali da ɗabi'a wlh
ranar da na sanar dashi wacece ke banyi tunanin zai dawo gareki ba sai gashi washegari ya
dawo kuma yake faÉ—amin ya shiryawa aurenki har ya sanar da Abbunsa ya samu matar aure
Abbunsa yace ya nema koda kaifin takobi ne indai kin masa suma kin musu duk kuwa da ya
sanar da Abbunsa ƙaddarar data faɗa Miki shin Fateemah zakiyi wasa da wannan damar ki saki
reshe ki kama ganye, bayan kinsan cewa yanzu duniya ta daÉ—e da tashi daga bacci mata sun
daina damuwa da soyayya mafitar rayuwarsu kawai suke dubawa a aure ba soyayyar banza ba
da so tari tafi tafiya a dararen farko na cin amarci Teemah ba sonki Nuraddeen yakeyi ƙaunarki
yakeyi wadda ƙauna ita ke ɗorar da haƙuri da juriya a zamantakewar aure ba soyayya ba"





Sosai yau take fahimtar Samha hakanne ya sata ɗagowa tace “Ni kaina zuwa yanzu juriya ta ta
fara gazawa Samha idan naƙi bawa Deen dama a kaina banyiwa kaina adalci ba domin dama
bata cika maimaituwa ba saidai ina jin kamar naci amanar kaina da Zuciyata Samha har gobe
Daddyn Jany shine kaɗai nakewa kallon namiji" share mata hawayen Samha tayi tace “Shi
kika sani ne Teemah but shima akwai maza a gabansa fah wannan Guy É—in daga yanayinsa in
samu dama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login