Showing 12001 words to 15000 words out of 34531 words
Chapter 5 - SIGN MARRIED 2 BOOK OUM HAIRAN.pdf
zai iya bai dake pri nursery a karatun namiji Yanada manyan halittu ga ƙirar ƙarfi ga
kyau ga hatimin nasara"
Kasa sake cewa komai tayi ta koma ta kwanta Jany da Jalal da Samha keta buɗa kayan da
Deen ya kawowa yaran itadai tayi nisa a duniyar tunani Saida Jany ta haura samanta tana cewa
“Mom, Dad she's call you"
Numfashi ta sauke me tsayi kafin takai dubanta ga wayar still dai shine batason ɗagawa amma
kafin ta gama yanke hukunci Jany ta kara mata a kunne suka sauke numfashi tare shiru ya
ratsa tsakani kafin yayi ƙarfin halin cewa “Yaushe ne tafiyar taku?" A gajarce yace “Jibi" shiru
yayi sannan yace “Naso tafiyar yazo ɗaya da tawa amma babu komai Nima cikin satin nan zan
taho in yaso sai ayi komai a gama idan kika bani dama ma har bikin sai ayi mu dawo matsayin
ma'aurata mu buɗewa rayuwarmu sabon babi ko?" Murmushi tayi ta ƙuta tace “Wai kai baka
zuciya ne?" Dariya tambayar ta bashi ko babu komai yau yanada Sa'a tunda har tayi masa
magana, yace.
“Bamani da ita akanki Fateemah na matsu naga na mallakeki kinsan me? Tunda na haɗu dake
bantaɓa cewa Allah ya zaɓamin alkhairi tsakanina dake ba abu ɗaya da nake faɗa masa ya
gajarce mana wannan zaman yasa da wuri ki zama matata na baki baby ki haifamin twins"
Dariya sosai ya bata tace "Shikenan and Ni nace Allah ya tabbatar maka da alkhairin dake tare
dani Deen komai na rayuwa alkhairansa yafi ai" narkewa yayi kamar yana gabanta yace “Amma
dai kin daina wahalar Dani yanzu zaki aureni ko?" Murmushi tayi tace “Idan Allah ya aura
makani ya zanyi, Ni zaɓinsa nake nema" sunyi hira sosai shi kansa mamaki yakeyi tare da jin
daɗin yanda masoyiyar tasa ta saki jiki dashi aje wayar sukayi tare da yi mata alƙawarin gobe
zai zo yanason ya ganta matsayin wadda ta bashi damar ya zama jagoran rayuwarta.
Alwala tayi tasa kayan bacci ta kwanta Zuciyarta cike da tunani barkatai so take ta kawar da
tunanin Ma'eesh kamar yanda kowa ke bata shawara saidai ta kasa duk kuwa da cewa itama
batajin zata iya yafe masa wofintar dasu da yayi indai yana raye kuma lafiyarsa ƙalau cikin
duniya, ta haƙura koda son sa zai zama ajalinta ta amince saboda abinda ta fahimta da rayuwa
kawai ka rayu inda ake buƙatar rayuwarka" Washegari kuma da wuri yazo ya kawo mata uwar
siyayyar da yayo musu ita da Jany da Jalal idan yayi wani abin har tausayi yake bata gashi da
kara bai taɓa siyawa Jany abu bai haɗa da Jalal ba wannan ya ƙara masa ƙima a idanun
Samha taketa kafa masa gwamnatinsa, ranar Litinin kuwa zakara ya basu Sa'a a Nigeria suka
sauka garin Kano suka kwana biyu tare da bawa Janah manya kyautuka da kaita asibiti aka
ɗorata akan magani ashe ma ba HIV ɗin bace sanyi ne yaci jikinta fiye da tunani, washegari
sannan suka ɗauki hanyar Niger cike da zullumin abinda zasu tarar.........
_Am so sorry yau naje asibiti na gaji kuyimin haƙurin gobe_
*Paid book 500 VIP 1k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay Evidence of payment
09031307566.*
*Oum Hairan*
[7/8, 7:43 AM] Oum Hairan: SIGNED MARRIAGE
*_(Kalma ɗaya)_*
*Oum Hairan*
*____________________________________*
*Book 2 page 11-12*
*____________________________________*
Sun isa Niger da dare a babban birnin ƙasar suka sauka suka kwana wani katafaren hotel da
safe suka shirya suka fito domin nufar Damagaran tun fitowarsu wata hamshaƙiyar mota take
musu horn basu kula ba domin basu ma kawo dasu ɗin ake ba har Saida matashin buzun ya
fito a motar cikin shigarsa ta buzaye ya iso garesu yayi musu sallama Samha ce ta amsa tare
da kallonsa ya zame ƙallen daya rufe fuskarsa dashi saboda yanayin hunturun da akeyi ya
kama hannun Jany yana mata wasa yace “Da alama ku ɗin baƙine ko zan iya sanin
masaukinku?" Da farasanci yayi maganar Samha tace.
“Eh zamu karasa Damagaran ne can ammasaukin mu" ba tare da tunanin komi ba yace “Sara
kan gaɓa Nima can nayi muna iya tafiya tare?" Da sauri Samha tace “Ah haba ai Bama ɗora
maka nauyi ba kaje kawai muma muna tahowa" waya ya zaro yace da drivensa yaja motar ya
tafi zai taho da baƙinsa" da sauri Samha tace “Aa kar ayi haka muje" Batul da batasan me suke
tattaunawa ba Samha ta kalla tace “Muje Hajiya mun samu lipt zuwa Damagaran ɗin" bata ja ba
duk da bata bada fuska ba saboda ta lura hankalinsa a kanta yake.
Address ɗin gidan ta rinƙa basu suna bi cike da mamaki Ansar zai yi magana Anwarr ya
hanashi sunyi tafiya me ɗan tsayi sannan suka isa ƙauyen Ƴar kuka inda sukayi parking gaban
gidan me unguwa suka fiffito suna kallon garin cikin shekara bakwai da tayi batazo garin ba
matuƙa ƙauyen ya canza ga raƙumansu nan turke gaban gidajensu. Wasu matasan buzaye sukaga sun nufosu ita dai bata iya gane wani cikinsu ba suna ƙarasowa
suka fara gaisawa dasu Anwar ya tambaye su me garin yananan, nan suka sanar dasu yaje
gona amma bashi jimawa yaka zakkuwa itadai Batul kallonsu tayi tayi musu Godiya ta nufi cikin
gidan gabanta na faɗuwa Zuciyarta fal da tunanin irin kallon da zasuyiwa juna ita da Inna Laure,
sallama tayi daidai lokacin da Inna ta fito daga makewayi, tana ganin tilon ɗiyar Tata ta saki
butar ta nufi Batul da gudu tana cewa "ga Batula ga Batula" nandanan dukkan matan dake
ɗakunansu suka firfito domin ganin ɗiyar data sallamu duniya yau a gidansu kowa kallonta
yakeyi da mamaki suna kallon Jany da tsoron mutane yasata kanƙame mamanta tana kuka
tana cewa a ɗauketa, Samha dake shigowa itane ta ɗauki Jany tana cewa da ita “Ke kin cika
rigima Jany meye kuma na kukan?" Jansu Inna Laure tayi har ɗakinta itadai Batul kallonta
takeyi cike da tsoro badan Inna haihuwarta tayi ba da bazata gane ta ba saboda muguwar
ramar da tayi tunda take bata taɓa ganin Inna tayi baƙi ba sai wannan karon, haka suka shiga
dakin da aka shimfiɗawa ledar buhu a ƙasansa da ɗan karamin gadon ƙarfe Inna ta kuma
shimfiɗa musu darduma sunata kallon kallo da Batul bayan dukkan matan gidan sunzo sun
gaggaisa yaran ma sunata zuwa ganinsu suna cewa wai baƙin Turawa ne sukazo, to jiki yaci
kuɗi sun saje da masu jajayen kunnen.
Kallon Nutsuwa Inna tayiwa Batul tace “Yanzu Batul akwai daɗin da zaisa ki manta Dani a
duniya inanan abin duniya yayimin zafi nadama ta baibayeni inata tunanin ta inda zanjiki ko na
ganki ke kuwa kina can kin samu guri kin manta dani" girgiza kai tayi wato har yanzu Inna
tananan da ɓirɓushin halinta wai ta samu duniya ma take cewa ba tambayarta zatayi halin da
rayuwarta ta shiga ba, murmushi kawai tayi ta share hawaye tace “Inna wannan ƙawata ce
Kuma uwar ɗakina Samha a lokacin da aka saceni daga Nigeria aka kaini Austaralia bayan kin
siyar dani a hannun matsafa sun ɗaukeni sun kaini can da zummar idan na haifi wannan
yarinyar dake jikinki wadda kuka siyarwa da ubanta Ni na shekara biyu, su kasheni su kashe
yaron da na haifa don cika burinsu na tsafi.
Nan ta kwashe labarin komai ta labartawa Inna Laure Aikuwa ta shiga tashin hankali da ɗimuwa
tayi kuka kamar ranta zai fita ta rinƙa yiwa Samha godiya data gatanta mata ɗiyar tana.
Suna tsaka da wannan tattaunawa ne Mal Garbu da yake matsayin uba a gurin Inna Laure ya
shigo, kasancewar shi ƙanine ga baban Inna Laure ya kalli Batul yace “Ke ar baƙauyiyar kawai
kizo da baƙi ki barsu a waje badan ƴan gari bane Wagga ɗiya da tabawa mutane kunya Laure
ɗiyan Alh Khamilu ƙanin me unguwa dake zaune a Niamey ne ya kawosu yaron nan mazaunin
France Anwarr yake kamar ko?"
Dafe kai tayi tace “Kai tsohon nan har yanzu kananan da azarɓaɓinka to naga bani suka biyo ba
wannan sarkin kwashe²n ce ta ɗebosu" tashi yayi ya fita ya shigo dasu aka shimfiɗa musu wata
dardumar suka gaisa da mutanen gidan har suna zolayar Anwarr yaushe zai yi aure ko sai ya
gama cin bokon?" Murmushi yayi yana kallon Jumaire matar Mal Garbu yace. “Inna Jumre Ni ai na samu mata a gidanki gani sai ki ƙwaɗani ki cinye dama rabonta ne ya
hanani ganin kowa sai gashi yau nayi gamon Katar gashi cikin ikon Allah tuwonku manku ko
ƙanwata?" Wata harara ta watsa mashi da ta sanya hantar cikinsa kaɗawa yayi ƙasa da kai
Jumre tace “Kai kuwa Anwaru ina zaka kai Ta Manzo Wagga ɗiya da shaiɗan yayima fitsari a
ƙafa ta zama karuwar ƙasa da ƙasa ita zakace zaka ɗiba to kuwa kasan kaima uwayenka basu
barinka saboda haka ka ruha mamu asiri ka barmu mu ƙarasa da ƙwarinmu"
Koda bashi aka faɗawa maganar ba Saida ta girgiza shi kuma ta ɓata masa rai ya kuwa haɗe
rai yayi shiru itama ganin kallon da Mal Garbu yake yi mata yasata lallaɓa tsufanta tayi gaba
abinta.
Tashi Anwar da Ansar sukayi sukai masu sallama da cewar zasu dawo zuwa dare dai lokacin
ne suka samu hutawa sukayi wanka sukayi sallolinsu duk da cewa duk basu nutsu da gidan ba
da alama Inna ba zaman lafiya sukeyi da mutanen gidan ba sai zubar musu da maganganu
sukeyi suna yan waƙensu na mutanen ƙauye na habaici, itadai Inna tsumu a ɗaki bata cewa
ƙala ganin abin nasu bana daraja bane ya sanya Samha samun Batul tace mata “Nifa ba komi
raina yake ɗauka ba Teemah duk da cewa Innanki tayi kuskure amma bai kamata zuwanki yasa
waɗannan ƙauyawan matan suyita yi mata ɗan bikin nan ba magana ta Allah zan kira Anwar
yazo su nema mana hotel mu kama idan kuma da wani abu da za'ayi to ayi amma idan naci
gaba da zama a wannan gidan tsaf zanmusu duka" share hawayen daya zubo mata tayi tace
“Nima bazan iya zama a nan ba kinji fah yanda suketa ƙyararmin Jany duk taƙi sakewa sai kuka
take yi" kiran Inna sukayi Samha ta sanar da ita sufa zasu shiga gari su nemi masauki “Nan
Inna take faɗa masu suyi haƙuri Haladu ƙaninta yazo ta karɓi mukullin gidan Mahaifin Batul ɗin
da tasa aka kwaskware zata koma ciki da zama itama zaman gidan ya isheta kullum sai sun
sata kuka akan rashin Batul ɗin yanzu kuma ta dawo da yarinya tasan abin ƙaruwa zai yi" haka
akayi Halliru yana zuwa ya rakasu ba laifi gidan yafi wanda suka baro kyau domin ginin zamani
ne ya gama ginawa kenan zasu dawo Yar kuka da zama Allah yayi masa rasuwa dake sunyi
canjin kuɗi sosai a Kano haka suka cire kuɗi aka siyo musu katifu guda biyu manya six by six
sai ƙarama guda ɗaya ta yara suka sanya ɗaya a ɗakinsu ɗaya a ɗakin Inna gefe suka saka
ƙarama ta yara suka saka glub aka simunte bayin cikin kwana ɗaya suka mai da gidan yanda
sukeson ya kasance kafin su tafi domin kuwa tuni Batul tasa a nema mata gida a Kano kuɗaɗen
da suke account ɗinta da Ma'eesh ya zuba mata sunada nauyi sosai sannan ga na wajen Lateef
suma batayi komai dasu ba Gara ta nema musu gida inda babu wanda ya sansu su zauna su
nutsu su nemi mafitar rayuwarsu.
Da safe sukaje gidan me unguwa inda nan ne aka haifi Mal Daheer mahaifin Batul sosai sukayi
murnar ganinta Musamman kakarta mahaifiyar babanta da mugun halin Inna Laure yasa basa
ga maciji dake tun jiya sun san da zuwanta gurin Anwar da yake matsayin abokin wasa gareta
domin da Mal Ɗaheer da Alh Halliru yan turaka suke ma'ana ubansu ɗaya zumunci ne dake
bayinsa sukeyi ba domin shi Mal Ɗaheer da baƙin halin Inna Laure ya ishi danginsa sukace sai
ya sake ta ne shi kuma yace yanason matarsa bazai rabu da ita ba ta wannan sukaji haushi
suka sallamawa Inna shi shine dalilin da yasa ko sun shigo ƙauyen Ƴar kuka Inna bata bari
Batul taje ta gaida dangin mahaifinta kwatsam kuma sai gashi lokaci guda Inna ta sauko.
Tunda sukazo kullum suna maƙale da Deen a waya nan yake gaya mata shima nan da kwana
huɗu zai taho, a ɓangare ɗaya kuwa Anwarr daya taho Damagaran da niyyar kwana ɗaya sai
gashi ya nemi gurin zama duk da cewa Batul taƙi bashi fuskar yace mata komai amma
matsayinsa na ɗan uwanta yasa bata wulaƙantashi.
Kwanansu biyar da zuwa Deen ya kiratd yake cewa da ita yana Damagaran ta bashi address,
sosai suka cika da mamaki matuƙa nan take bashi kwantancen inda za'a kawo shi ta tashi ya
shiga wanka ta fito ta sheƙa kwalliyarta cikin shigarsu ta buzaye.
Tana tsaka da shiryawa Anwar ya shigo ya tsaya yana kallonta ta ɗago tayi masa murmushi
tace “Yada kallo haka Yaya Anwar?" Ajiyar zuciya yayi yace “Aa babu komai wankan ne ga kin
karɓeshi Masha Allah"
*Contact me*
*09013718241*
*OUM HAIRAN*
[7/8, 10:29 AM] Oum Hairan: *SIGNED MARRIAGE*
*_(Kalma ɗaya)_*
*Oum Hairan*
*____________________________________*
*Book 2 page 13-14*
*____________________________________*
Ajiyar zuciya tayi tace “Allah da gaske nayi kyau da shigar gado na, wow! Hammah Anwarr
kace zanja magana...." Numfashinta taji yana barazanar ɗaukewa tayi maza ta dawo hayyacinta
ta sauke idanunta kan Anwar daya ƙure mata guri numfashinsu na dukan juna ya sanya hannu
yana zagaye lips ɗinta tare da janyota ya shigar da ita jikinsa ya ɗaga kanta sama yace “Kalli
waɗancan tsuntsayen Batul basu burgeki gani ba?" Ɗaga kanta tayi ta zubasu kan wasu
kyawawan tsuntsaye da ko a Turai bata taɓa katarin ganin ƙananun tsuntsaye masu kyawunsu
ba bakinsu yana cikin na juna ɗayan yana rerawa ɗaya kukansa me jan hankali, sosai
tsuntsayen suka sanyata a shauƙi sosai ta kamu da sha'awarsu da kewar abinda sukeyiwa
juna, ta kuwa lafe a jikin Anwar me fitar da wani sihirtaccen ƙamshi me kashe jiki.
Bata fahimci abinda take aikatawa ba Saida taji saukar Muryarsa a dodon kunnenta yace
“Kamar haka ya kasance Ni dake ne ƙanwata cikin wannan shauƙin da begen rayuwar da zanji
daɗi zanji kamar nafi kowa Sa'a, saidai baƙin cikina nasan kin fahimci me nake nufi amma kinƙi
nunamin ganewarki bari nasa ran zaki juyo ki dubeni, Batul Ni ba yaro bane shekaru na sun fara
nauyi fah inada shekaru talatin da biyar na kusa alba'in kinga dole ina buƙatar abokiyar rayuwa,
wlh ban fahimci haka ba Saida idanuna ya sauka a kanki, dama zaki bani dama tabbas da na
nunawa duniya irin saarki da kika sameni matsayin abokin rayuwa"......
Tureshi tayi ta nufi ƙofa zata fice ya sake cafkar hannunta yace “Laifi ne don na buɗe maki
Zuciyata Batul meye ne kikeso na baki shi wlh Ni ke kaɗai nakeso ki bani dama kinsani komai
son da wani zai nuna Miki bayakai yani da jininmu yake gudana iri ɗaya don Allah ki bani dama
Batul"...... Ficewa tayi daga ɗakin ta nufi ɗakin Inna inda suke hirarsu ita da Samha tanawa
Jany kitso tana cewa “Yo ace a barwa yarinya kai ba'a kumbushe matashi Wagga wannan suma
mu a nan ai baki lalata zaiyi"....... Faɗowarta cikin ɗakin ne yasa Su Inna miƙewa suna
tambayarta “menene?" Tsayawa yayi jikin ƙofar “Bafa wani abu bane Inna kawai don na roƙeta
alfarma ne shine take wannan abin Wlh Inna Inason Batul kuma ina raye bazata tafi dangin
wasu ba"
Murmushi Inna tayi tace “Anwaru kenan ba laifi bane don kaso ƴar uwarka amma kasan ƙura
zaka tayar idan maganar nan ta fita sanin kankane uwayenku basasona bare su so halwata, ta
yaya kake tunanin zasu yarje maka auren ta Manzo?" Sosai zuffa take keto masa amma dake
Buzun gaske ne sau cewa yayi “Nifa Inna zata soni to kowama ya barni bana neman tallafin
kowa wajen kula da iyali na" daƙyar Inna ta lallaɓashi ya tafi sannan itama ta fito suka dubi juna
da Samha, Samha tace “Ke kiji wata lukutar masifa Teemah wannan Anwar ɗin da gaske gaɓo
ne daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi kuma fah akwai ƙura wlh don jiya da mukaje gaida
Inna Yaure Tayi wata magana dana kasa gane me take nufi lokacin da take cewa “Tunda Allah
yasa kin dawo cikinsu basu kuma bari kiyi nisa dasu zasu sama Miki Samrayi cikin Samarinsu
buzaye su amra miki kin tuna lokacin kuma kinsan lokacin Anwar da Mustapha suna wajen
suma har sun kalli juna kallon dana kasa gane wanne iri ne inda Mustapha yayi saurin cewa
“Inna Inaso nikam in za'a bani shi kuma Anwar yayi ƙwafa ya fice kin tuna?"
Numfashi ta sauke tace “Ina sane Samha duk wannan abinda sukeyi ai babu wanda ya Isa
goge zanen ƙaddara Ni har yanzu fa banjin akwai mijina a cikinsu kawai dai suna abinsu ne in
banda haka Ni yanzu yama za'ayi ace za'a min aure a zaunar dani a ƴar kuka suma sun san
bazai yiwu ba, ke nifa gabaɗaya Niger ma ba taƙamarsu Niamey ba to Ni batamun a zama ba" Wayarta ne ya shiga ruri tana dubawa taga number Deen ta kalli Samha tace “Deen ne kije
gareshi ki shigo dashi" fita tayi iya kuma ta koma ɗakin Inna ta ɗauki awarwaronta ta saka tana
fitowa suna shigowa idanunsa a kanta tayi saurin janye nata tana murmushi, ya sauke ajiyar
zuciya ya shiga inda aka saukeshi bayan sun gaisa da Inna ya zauna itama ta shigo da
sallamarta ya amsa idanunsa na kanta tana shirin zama ya riƙo hannunta tare da zaunar da ita
a gabansa ya saki wata ajiyar zuciya me ƙarfi yace “Alhmdllh Fateemah ranar da za'a kaiki
gidana irin wannan dressing ɗin zakiyimin wlh kin tashi kaina kin