Showing 18001 words to 21000 words out of 34531 words
Chapter 7 - SIGN MARRIED 2 BOOK OUM HAIRAN.pdf
bai ci na kirki ba yanayi
yana duba agogo.
Sukuwa suna fita suka nemi abin hawa ya fitar dasu cikin garin Damagaran tare da kiran Deen
sukaji inda yake suka karasa suka gaisa sun jima tare dashi sannan ya shirya suka fita kasuwar
sukayi siyayyar Samha ce tayi musu siyayyar suko guri suka samu suka tsaya ya dubeta sosai
yace “Wani abu ya kuma faruwa ne My Zumata?" Ajiyar zuciya ta sauke tace “Yaushe zaka
tafi?" Murmushi yayi yace “Munyi magana da Dad yace na zauna gobe zai shigo Niger zasu
taho da yayansa sai suje garinku su nemamin aurenki" ajiyar zuciya ta sauke tace “Naji daɗin
hakan saidai Allah yasa su amince" nan ta sanar dashi abinda suka yanke, yayi ajiyar zuciya
yace “Basu canza hukuncin Ubangiji Fateemah mu barwa Allah shi yasan me yake rubuce a
allon ƙudura" da wannan sukayi sallama suka nufi gida shi kuma ya koma masauki.
Tunda suka koma ko a ido taƙi yarda Anwar ya sanyata in ya kirayi wayarta ma bata ɗagawa
haka suka cinye kwana biyun da rana kuwa Noor ya kirata yace ta faɗawa su Baffa Maigari ga
baƙinsu nan, haka ta sanar da Bana Haladu shine ya sanar dasu zuwan baƙin suka shigo garin
da jiniyarsu suka parker tarɓa sosai suka samu gurin su Baffa Maigari sannan suka zayyana
musu abinda ke tafe dasu sukayi shiru na tsayin lokaci kafin daga bisani Baffa Maigari yace.
Munyi tunanin zai sanar daku gskyr abinda muka sanar dashi da bai wahalar daku ba Alh wato
wannan yarinyar mun riga munyi mata miji yanzu haka bikin ma saura sati biyu da yan ɗoriyar
kwanaki kuma kunsani bisa ga al'ada in ba dole ba yarinya ta rasa masoyi cikin dangi mu Bama
kai iri waje gonar gida bata shuku ba saboda haka muke baku haƙuri wahalar daku da wannan
yaro yayi yarane na zamani kai haifesu baka haifi halinsu ba, itama haka muke fama da ita
shiyasa ma mukaga Gara mu bada ita a gida a rinƙa kwaɓarta ana mata tsawa"
Duk yanda Abbuh da ɗan uwansa zasuyi sunyi abin yaci tura haka suka tashi jiki babu ƙwari
sukayi musu sallama suka tafi basu sanar da Deen abinda ke faruwa ba Saida suka haɗu a
Sudan suka zaunar dashi sukayi masa nasiha tare da nuna masa ya haƙura ya nemi wata
tunda sunce bazasu bawa bare ba inda shi kuma yakejin duk kalmarsa ta ya haƙura kamar
suna watsa masa dalma a zuciyarsa haka ya tashi jikinsa a mace ya shige ɗakinsa yaja bargo
ya ƙudundune zazzaɓi ya sauko masa wannan lamari yayi kama da neman rayuwarsa
waɗancan bauɗaɗun buzayen sukeyi, shiru har dare har wayewar gari bai fito ba har rana ta
kuma ɗagawa hankalin Mom yaƙi kwanciya ta tashi ta nufi ɗakin nasa ta buɗe ta shiga tare da
isa gadon da sauri tace “Nuraddeen kashe kanka zakayi akan mace haba Deen Meye yake
damunka da zaka kwanta a ɗaki kayita rawar sanyi" cikin ciccijewar murya yace “Mom.....
Mutuwa zanyi...." Da sauri ta haura gadon tana danna masa ƙirji tace “Ka rufamin asiri Deen wlh
bazaka mutu akan mace ba ka kwantar da hankalinka nayi maka alƙawarin indai nice
mahaifiyarka sai sama maka wadda tafita" cikin azabar ciwo yace “bazan samuba Mom please"
Yanda jikinsa yake rawa yasata kiran likita yayi treatment ɗinsa Dad ya shigo ɗakin ya miƙa
mata waya yace “Tun ɗazu Junior yake kiran wayarki" karawa tayi a kunnenta tace “Babana ya
Austaralian?" Cikin mutuwar jiki yace “Not Lucky Mom still banganta ba ance tana Cairns duk
inda nake tunanin zan iya samunta naje babu wani bayani Mom inajin tsoron wani abu ya faru
da ita" Hamm ta sauke ajiyar zuciya itakam tana ganin jarabawa duk akan mata ƴaƴanta suke
neman zaucewa.
Ƙwallar idanunta ta share tace “Indai ana nema za'a dace Junior ƙaddararku ce nidai banji a
raina Batul ta mutu ba ta ɓuya ne saboda tsoron sake maimaituwar abinda ya faru a baya Insha
Allahu soon zata bayyana gareka" lumshe idanunsa yayi tare da kwantar da kansa saman
pillow yace “Kuma zata soni Mom tun kusan sati ɗaya gabana yake faɗuwa" murmushi tayi tace
“Bazata taɓa daina sonka ba" ajiyar zuciya yayi yace “Yaushe Bobbo zai dawo?" Kallon Deen
tayi tace “Shima yana kwance ciwon soyayya ne yake damunsa yanason wata buzuwar yarinya
da suka haɗu anan Austaralian Su Dad ɗinku da Shaikh Muhammad Saleem sunje nema masa
aurenta iyayenta sun wulaƙantasu sunce bazasu bawa bare aurenta ba, shine yake kwance tun
jiya babu ci babu sha gashi ma suna shirin auradda ita.
Murmushi yayi ajiye wayar tare da shafa sumarsa ya zubawa ƙaton hoton Batul idanu dake
ajiye a duk wani guri da yake zama hatta office na ma'aikatun da yake jagoranta kowanne sai
ya saƙala wannan hoto.
Juyawa yayi ya kafama hoton idanu yana mayar mata da martanin Murmushinta yace “Nayi
mafarkin kina rayuwa dani a zuciyarki Bea ki dawo mu gyara rayuwarmu muyiwa Jany gata
nasan yanzu tanason ganin Dad ɗinta Batul ke rayuwata ce"
Tashi yayi ya fara goge hoton tare da kissing lips ɗinta yace “Bakisan komai game da mijinki ba
nasan zaki karemin kanki ki adanamin daɗina ko?" Dariya yayiwa kansa tare da shafa
kwantacciyar sumarsa yace “Soon zan baki ƙanin Jany naga kina tashi daƙyar na tsokaneki
muyita zagaya compound na gidanmu kinaso ko?"...............
*Paid book 500 VIP 1k via 9031307566 Fauziyya Tasiu Umar Opay*
*Contact me*
*09013718241*
[7/9, 11:02 AM] Oum Hairan: *SIGNED MARRIAGE*
*_(Kalma ɗaya)_*
*Oum Hairan*
*____________________________________*
*Book 2 page 17-18*
*____________________________________*
Komawa yayi ya kwanta tare da buɗe wani hotonsu da yayi musu ranar darensu na farko bayan
komai ya kammala lokacin da Dad ya kirasa yake masa hannunka me sanda akanta ashe
shima rayuwar farin cikinsa yake nema, sosai yayiwa Allah gdy lokacin da ya samu labarin
abinda ya faru a ƙungiya lokacin da Daddynsa yayi ƙoƙarin haikewa daɗinsa ashe zata iya kare
kanta itama? Murmushi yayi tare da ɗaukar cup ɗin Wine ɗin dake samen bedset ya kurɓa ya
ajiye tare da yamutsa sumarsa cikin shekaru biyun abubuwa da yawa sun faru shi kansa karfin
addu'ar mahaifiyarsa ce da kuma nisan kwana ya kawosa wannan lokacin.
Sake zubawa hoton idanu yayi as emerging ace yanzu ne suke cikin wannan rayuwar yasan
zasu rayu cikin kwanciyar hankali, babu wani tarnaƙi da zai shigo rayuwarsu bare ya hana musu
farin ciki.
Lumshe idanunsa yayi tare da ɗaukar wayarsa ya fara kiran layin Batul na Nigeria ya kira sau
ba adadi baya shiga kamar ko yaushe sake yamutsa sumarsa yayi ya tashi zuciyarsa nayi masa
zafi ya zubawa ƙasan gidan nasa idanu yana kallon ɗaiɗaikun mutanen da suke kai kawo ya
busar da iska me zafi tsayin lokaci zuciyarsa har nauyi takeyi masa kullum tsammani yakeyi na
ganinta bai rabo da Melbourne a tunaninsa ko nan ta koma da zama shine har Sydney but
kullum amsar tasa shiru ce ya gaji da yawo tsakanin ƙasashe zuciyarsa kullum tana faɗa masa
Bea ɗinsa tana kusa dashi to amma mene yasa ta kasa nemansa?
Lumshe idanunsa yayi ya kwantar saman garun yace “Dole zata nemeni to ta ina?" Buɗe
idanunsa ya sakeyi, lokacin da yace mata gashinan zuwa Australia Bayan ya shigo Austaralia a
hanyarsa ta zuwa gidan da yake tunanin Lateef zai yi camping nata komai ya faru da ya zamo
silar ɓacewa junansu gashi yanzu komai ya wucce ya zama tarihi babyn da suke burin
hallakawa wadda ta dalilinsa suke son su jefata a ƙungiyar asiri, yau tanada shekara kusan biyu
a duniya.
Yanajin duk wani motsin gudan jininsa a cikin nasa jinin yana rayuwa da kewarsu kullum da
wannan damuwar yake kwana a mafi yawan darare takan hanashi bacci, yana tsoron halin da
zai riske Batul a ciki duk da cewa baya zargin faruwar wani abu domin kuwa masifar da aka
ɗora mata ta feeling kafin mutuwar Lateef ya sanar dashi ya karyata wannan ma shine dalilin da
yasa ƙungiya tayi Allah wadarai dashi tare da janye masa tallafi a ƙarshe suka bayar da jininsa
ga dodon tsafi wannan ya faru ne ranar da Batul ta haifi Jany ranar ne duk wani ƙulli da aka
shafe shekara sama da 30 ana kullawa ya rushe, ranar ne alƙaluman tsafi suka ƙwacewa
dukkan wani wanda ya dogara da kungiyar Emenisty ranar ne kuma ruhika suka rabu da gangar
jiki da yawa, still dai a ranar ne asirin ɓoye ya fito fili haka dai a ranar ne jinin wasu manyan
hadiman ƙungiya ya halarta ga dodon tsafi ciki harda Daddy da Lateef da shi kansa Ma'eesh
ɗin, a wannan rana ne a gaban idanunsa akayiwa Amininsa a farko maƙiyinsa a ƙarshe Lateef
dandatse aka cire gabansa da marainansa aka gasawa wasu manyan jakadun ƙunguya a
cewarsu saboda jin daɗin kansa da burarsa ya rusa musu shirinsu na shekara sama da 30 shi
kuwa Dad tik sukayi masa suka jorner masa wani abunsu na tsafi ya rinƙa zuƙe jini da ruwan
jikinsa Saida ya ƙafar dashi ƙaf sannan ya faɗi matacce.
A lokacin da suka juyo gareshi ne suka nemeshi suka rasa gashi shi kuma a gurin yana
kallonsu duk yanda sukaso ganinshi ta cikin madubin tsafinsu ya gaza nuna masu shi and end
ma idan suka cika binciken madubin tarwatsewa yakeyi ko kuma wanda ya dage wajen gano
shi ta cikin madubin kawai aji ya saki ƙara ya faɗi matacce, a wannan halin Saida ya kwana uku
babu ci babu sha gashi a ɗaure shidai baisan ya akayi ba kawai ya wayi gari ya ganshi a
kwance a wani ɗaki ya buɗe idanunsa yana ƙarewa ɗakin kallo can yaga wani mutum ɗaure da
wani abu me kama da ganye a gabansa irin dai shigar nan ta arnan daji shidai daga haka ya
kuma fita daga hayyaci ya kuma farkawa ne ya gansa a gefen titi a tashe mutane sun zagayeshi
daƙyar cikin tambayoyin da ake ta yi masa ya iya amsar wayar wani yasa number Mijin
mahaifiyarsa, daganan Saida ya shafe wata shida baisan komai dake faruwa dashi ba a duniya
yake a lahira yake oho.
Bayan watanni shida ne ya farka cikin wani gigitaccen yanayi Allah yasa ƙaninsa Bobbo da Mijin
mahaifiyarsa Alh Hakeem suna tare dashi suka rirriƙeshi tare da fara tofa masa duk addu'ar da
suka san zata zama waraka gareshi kusan awa guda sannan ya dawo hayyaci ya sauke
idanunsa kan Mahaifiyarsa yace “Kin ganta can tana kallo na nace tazo taƙi zuwa Mom ki faɗa
mata ba raayina ne yasani zama cikin matsafa ba gadarmin kukayi Mom ki faɗa mata itan
haske ce ga rayuwata itan itace ƙaddarata kar ta gujeni Ni ɗim don ita kaɗai aka halicceni Mom
Batul tanason rabani da Ƴata idan ita ta gujeni ta bani ƴata....."
Rufe masa baki tayi ta kalle Abbuh Hakeem tace “Har yanzu yaron nan bai dawo hayyaci aci
gaba da basa kulawa" jinjina kai yayi Bobbo yace “Mom a ƙara sauke masa Kur'ani zai samu
relief sosai sun rikita masa ƙwaƙwalwa ne ta yanda bazai iya tuna komai ba but anyi nasara
tunda ya farka da hoton Budurwarsa da ɗiyarsa akwai yiwuwar komai ma zai dawo masa a
ƙwaƙwalwa saidai kuma dole ne sai an saka tsaro akansa fah kinsan bai saba zaman guri ɗaya
ba, nasan zuwa yanzu sunsan bai mutu ba kuma zasuci gaba da bibiyar sa don ganin bayansa
kamar yanda sukaga bayan Lateef da Daddyn Junior"
Jinjina kai tayi tana share hawaye duk ita ta jawa ɗanta shiga wannan masifar daga bijirewa
maganar iyaye taje ta jefa kanta a masifa shima ta jefashi gashi ya cinye rabin rayuwarsa bai
amfana da komai ba sai kaico da kaucewa tafarkin addinin Muslunci kullum kokawa suke ita da
mahaifinsa akan ganin yabi addinin kowanne ita tayi nasarar jansa zuwa musulunci amma
kuma Daddy ya juya mata tunanin yaro da tsari na addininsu na yahudanci yanzu ita ina zasu
fara neman Batul tana tsoron kar taje tayi aure kan aure, koda yake abin zai zama me sauƙi
tunda a cikin Musulunci suke dukkansu to amma shima auren yarjejeniyar da sukayi ita da
Ma'eesh ɗin yanada asali a Addinin yahudanci tunda shidai ta fahimci addini biyu yake bi abinda
yayi masa daɗi a Addinin Musulunci shi yakeyi addinin Ubansa ma yahudanci zaɓa yake daga
ciki ya ɗauki wanda yayi masa daɗi.
Sosai aka dage masa da magungunan Islama ƙarshe ma gidan Shaikh Muhammad Saleem ya
koma da zama inda basu barshi ya ƙara fita daga ƙasar ba Saida suka tabbatar da samun
lafiyarsa, tashin farko Kano yaje inda ya samu mugun labarin Inna ta Saida gidanta ta koma
Lagos koda ya koma Lagos ya gama bulayinsa bai ganta ba haka ya ɗauki hanyar Austaralia
inda kai tsaye Melbourne ya sauka ya nufi gidan Daddy wanda akayi camping na Batul a ciki
abun mamaki dukkan komai na gidan ya daskare ya zama gunki hatta mutanen dake hidima a
gidan dukkansu sun zama kwarangwal domin an tsafacesu ne ta yanda bazasu iya guduwa ba.
Shidai zuciyarsa na rawa haka ya shiga gidan ya fara Ratsa faluka da ɗakuna har ya kai ɗakin
ƙarshe na gidan inda anan aka ajiye Batul ya shiga ya fara bincikensa abu biyu ya samu a ɗakin
daga wayarta sai zoben diamond daya sanya mata daren da zai tafi South Africa ɗauka yayi
yana juya zoben a hannunsa kafin ya ɗauki wata takarda da ya gani a yashe a ƙasa cikin wani
bushasshen jini sai yanzu ya lura da tarin Glass ɗin dake ɗakin da kuma kwarangwal ɗin dake
kwance cikin ƙura da jini bushasshe, haskawa yayi sosai tsutsa duk ta gama cinye mutumin
dake kwance mace ce ko namiji bai sani ba daƙyar cikin tashin hankali ya ɗauki takardar
rubutune akayisa da rashanci da jini.
“Zaka Sameta a duniya ne bayan ruhina ya mutu soon Matarka tana Cairns ta kashe gangar
jikina amma ruhina zaici gaba da bibiyarta har sai na cika burina, nasan zakazo bayan ta haihu
an kashe gangar jikina ta biyu a gabanka......"
A tsorace ya rinƙa kallon kwarangwal ɗin tare da ja da baya ganin yana wani irin motsi tare da
wata irin curewa waje guda wannan bushasshen jinin ya zama ɗanye ya rinƙa haɗewa yana
curewa ƙarshe ya zama kamar ƙwai wannan kwarangwal ɗin ya ɗauka ya maƙala a zuciyarsa
take saiga wata hallita ta tashi tana ƙyalƙyala dariya ta cafki wuyansa tana ƙoƙarin kashe shi
cikin wata murya wannan dodon ya fara cewa “Ma'eesh jiran zuwanka mukeyi dama munsan
dole zaka biyo Matarka da ɗiyarka hahaha dole mu shanye jininka tunda ka hanamu na Matarka
da ƴarka sai mun kasheka! Hhhhhh sai mun kasheka..... Jini.....zansha jini..... Hhhhhh jinin ɗana
zansha....."
Cikin fitar hayyaci ya rintse idanunsa ya fara karanto wata addu'a da Muhammad Saleem ya
bashi yace saboda tsaro domin har yanzu ana biyar rayuwarsa waɗancan matsafan da aka
sadaukarwa dashi tun yana cikin uwarsa sunanan sun sake shiri a kansa, addu'a yakeyi sosai
yana riƙe maƙogwaronsa inda daga baya yaji an saki wata ƙara an sakeshi wuta ta kama ɗakin
ganga ganga take yaji wani hucin zafi yana neman narkar dashi haka ya fita a guje daga gidan
da ashe gabaɗayansa ne ya kama da wuta yana fita ya nufi tashar jirgin ƙasa ya shiga na
Sydney Saida yayi sati biyu yana karɓar magani sannan ya fara fita inda a sati na uku ya nufi
Garin da yafi rayuwa inda ya baza kasuwancinsa da duk wasu halattatun kuɗaɗe dake
hannunsa wato Cairns garinsa na haihuwa kenan nan ne state origin nasa domin shi ba
haifaffen Rasha bane kuma ba haifaffen Sudan bane, lokacin da dangin Mom suka koreta
bayan tsira daga kaidin Dad da yayi masu ƙaryar musulunci ya nemi aurenta iyayen sukaƙi ita
kuma ta kafe saishi ƙarshe sukaje aka ɗaura musu aure batare da amincewar iyayenta ba ya
ɗauketa ya tafi da ita Rasha.
To bayan iyayenta sun koreta sunce bazasu raini ɗanta na shege ba Shine ta yanke shawarar
barin yankin gabaɗaya nan zuciya ta raya mata ta tafi Austaralia, acan ta samu wani gidan
abinci ta fara da wanke wanke da shara bayan ta haihu ne kuma ta samu miji ɗan kasarta ne ta
Sudan mazaunin Austaralian ɗan kasuwa sukayi aure dashi anan ne kuma ta haifi Nuraddeen
sannan Nuwairah da Muhsin ta haɗa kan yaranta huɗu harda Ma'eesh wanda yanada shekara
biyar ne Mahaifinsa ya gano inda take yaje ya sace ɗansa a lokacin mijinta ya gina mata
katafaren gurin cin abinci na yan Africa a ƙasar Austaralia, a haka suka raineshi idan Nazhan
ya sace shi sai ya ɗauki shekaru baya tare da ita, haka itama idan ta samu dama ta sace shi sai
ta ɓatar dashi ta tura shi Nigeria gidan yayanta Muhammad Saleem don ya samu ilimin addini,
shidai a haka ya girma tsakanin ƙarya da gaskiya.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kai idanunsa ga agogon da yake maƙale jikin bangon wajen
hutawar 2:30am ya sake sauke ajiyar zuciya ya nufi dakin baccinsa ya sake wanka yayi alwala
ya tayar da sallar nafila zuwa yanzu so yake ya koyi miƙa Komansa ga Allah tare da neman
mafita a gareshi kamar yanda Mom take sanar dashi kullum ya jima yana kaiwa Allah kokensa
kamar yanda kullum Mom Abbuh da Shaikh Saleem suke faɗa masa da ɗan uwansa
Nuraddeen, bai koma ya kwanta ba Saida yayi sallar asuba kasancewar unguwar tasu babu
musulmi sosai a gida yake Sallah bayan ya idar ne ya kwanta bacci ya ɗaukeshi kamar kullum
dai mafarkinsa na Abar ƙaunarsa ne saidai yau yanayin damuwa ya riƙeta a ciki abinda ya
sanya shi yana tashi ya fita ya nufi ɗaya cikin gidajen abincinsa sadaka yakeson