Showing 45001 words to 48000 words out of 56183 words
Chapter 16 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf
tace
"Ba za'a tab'a siye Rafiqu da kud'i ba d'an nan, shari'ar nan tana ransa kawai dai an nuna anfi
k'arfinsa ne..." Umman Rafiq ta kwashe duk abunda ya faru ta fad'awa Umar,
Sultana ma tana tsaye tana saurarensu wani irin dad'i taji a ranta,
Itakam dama tayi mamakin rashin zuwansa kotun, ta tabbatar da akwai wani babban dalili
daya hanashi zuwa lokacin da ake buk'atar ganinshi.
Har k'asa ta duk'a ta gaishe da Umman Rafiq sannan ta gaishe da Rafiq d'in ma,
Motarsu suka koma Sultana ma ta koma ta shiga tata wadda su Ummimah ke ciki suna
hangen duk abunda yake faruwa amma kuma basu san kome ake fad'i ba.
Bayan ta shiga ta labarta masu duk abunda ya faru, hamdala Mama tayi sannan tace
"Allah majik'an bawa, dama shaidarshi ake nema kuma gashi Allah ya kawoshi, Allah dai ya
kawo mana k'arshen wannan shari'ah ya bawa mai gaskiya nasarah",
"Ameen" su duka suka amsa dashi sannan Sultana ta tayar da motar,
Umar ne gaba sai Dr. Rafiq a bayanshi,
Sultana kuma a bayan Rafiq, a hankali suke tafiya har suka isa court of apeal.
Sun samu motoci da yawan gaske a pake, hakan ya tabbatar ma Umar da cewa su kad'ai
ake jira,
Savoda tun k'arfe takwas akace suzo za'a fara shari'ar yanzu kuma gashi har takwas da rabi
ta wuce.
A hanzarce suka zira rigunansu sannan suka shiga,
Wuri d'aya su Sultana suka zauna da Umman Rafiq da k'annenshi biyu,
Sultana da Umar kuma suka tafi inda aka tanada domin zaman lauyoyi.
Bayan sun zauna baifi da minti biyar ba alk'ali ya iso,
Mazauninsa ya zauna sannan mai gabatar da k'ara ya tashi ya gabatar.
"Kotu tana son ganin Aishatu Abubakar wadda ta kawo k'ara da kuma Salmah Abubakar
wadda ake k'ara" alk'ali ya fad'a tare da yin d'an rubutu a takarda.
A hankali Ummimah ta taso ta tsaya cikin akwatin tuhuma,
Salmah ma tasowar tayi ta tsaya itama a cikin akwatin tuhuma wanda ke kusa dana
Ummimah.
"ba sai an tsaya wani dogon bayani ba, kamar yanda kowa ya sani cewa wannan k'ara ce
aka d'aukaka, dan haka zamu so wanda suka kawo k'arar su tashi suyi bayanin dalilinsu na
d'aukaka k'arar sannan su bamu hujjarsu ta farko".
Cike da natsuwa da kamun kai Sultana ta tashi tsaye,
"Sunana Barr. Sultana Saddam Bakori, a tare dani akwai Barr. Umar Mohd Bashir, mune
wanda muka d'aukaka k'ara,
Dalilinmu na d'aukaka k'ara kuwa shine; an yanke hukunci a zamanmu na kotun daya gabata
wanda kuma hukuncin bai mana ba,
Shine muka d'aukaka k'ara a wannan kotu mai adalci tare da hujjojinmu wanda muke fatan
kotu zatayi masu duba ta yanke hukunci ga mai laifi".
"Kotu ta gamsu da dalilinku na d'aukaka k'ara, tana jiran hujjarku ta farko" alk'alin mai cike da
dattako ya fad'a yana kallon Barr. Sultana.
A kotun data gabata, akwai likita wanda yake shine ya duba Ummimah a lokacin da aka
kaita, shine ya tabbatar da fyad'e aka mata,
Munyi dashi cewa zaije ya bayarda shaida, sai kuma mukajishi shiru baizo ba, kasantuwar
dama dashi kad'ai muka dogara yasa aka yanke hukunci bamuda wata hujja,
To yanzu dai yana kusa kuma ya halarci kotun nan,
Zanso kotu mai adalci data bani dama domin gabatar dashi dan aji ta bakinshi".
Kai alk'alin ya jinjina kafin yace
"Kotu ta baki dama Barr. Sultana".
Tasowa Dr. Rafiq yayi ya iso inda aka tanadar dominshi,
Tunda ya taso Gentle ke binshi da kallon mamaki, itakam sam batayi tunanin zaizo ba,
Hankalinta kuwa ya matuk'ar tashi dan tasan zayyi bayanin duk abunda ya faru.
Qur'ani aka bashi ya dafa tare da fad'in
"Nayi alk'awarin zan fad'i gaskiya tsakanina da Allah".
Sultana ta matsa inda yake tace
"Dr. Rafiq inaso kayiwa kotu bayanin tun dawowarka daga Lagos ina kaji? Sannan kuma me
ya hanaka zuwa kotu domin bayarda shaida?",
"Ranar dana dawo daga Lagos shine ranar jumu'ah, ko a ranar munyi waya da Barr. Umar
kuma na k'ara tabbatar masa da zanzo,
Kwatsam ina shirin tahowa da rana tsaka wasu mutane suka shigo mana manya manya abun
tsoro,
Cike da fargaba na tambayesu 'me sukazo yi?',
Basu bani amsa ba saa d'aukeni da mari da babban cikinsu yayi,
Fitowa sukayi dani daga d'akina, a parlor na tayar sun nannad'e Ummana da igiya sannan
sun nad'e mata bakinta da selotape,
A lokacin k'annena basu nan,
Tafiya sukayi damu bayan sun nad'e mana fuskoki dan kar musan inda zasuje damu,
A wani d'aki suka jefa Ummah ni kuma suka barni a tsakar gida,
Saida muka kwana biyu a haka sannan suka min bayanin dalilin kamomu da sukayi,
Sukace 'inhar na kuskura na sake ko waiwayarku barin har inyi tunani bayar da shaida sai sun
kashe Ummana',
Na masu alk'awarin ba zanyi ba, bayan mun dawo gida shine Ummah tace 'kome zai faru
saidai ya faru amma sai na bayar da shaida ta amince, tun a ranar mukayi niyyar tafiya amma
saboda mun san ana bibiyarmu yasa muka jinkirta vamu taho ba sai jiya,
Tun jiyan muke neman gidan Bar Umar muka rasa,
Sai daga baya bayan mun sauka hotel muka tambayi wani mutum shine ya mana bayanin
gidan,
Da safen nan myka nufi gidan shine Allah ya had'amu dasu a hanyarsu ta zuwa nan kotu".
Cike da gamsuwa alk'ali ya d'aga kanshi.
Sultana tace
"Kotu zata so ka fad"a mata duk yanda abun ya faru bayan an kai Ummimah clinic d'inka,
Sannan kuma abokin aikinka Dr. Khalid ya tabbatarwa kotu a baya cewa clinic d'insa ce kawai
dai ya d'aukeka aiki ne, shin ya abun yake?"
Cikin mamaki Dr. Rafiq ya kalli Barr. Sultana yace
"Ba gaskiya Dr. Khalid ya fad'awa kotu ba,
Asibiti dai tamu ce ni da shi muka had'a k'arfi da k'arfi muka bud'eta,
Ya zuba dukiyarshi nima kuma na zuba tawa, a lokacin ma ni kad'ai nayi niyyar bud'eshi sai
ya rok'eni akan yana so mu bud'e tare,
Saida Ummana ta musa hakan amma daga baya ta amince saboda taga yanda muka shak'u
dashi,
Na amince masa muka bud'e asibin saisa muka saka mata *'KADRAQ CLINIC'* inada hujjar
hakan saboda ina tafe da takardun asibitin baki d'aya, wanda shima kuma Dr. Khalid d'in yana
dasu, idan ya musa wannan bayanin da nayi sai ya kawo nashi wanda suka tabbatar da cewa
clinic d'inshi ce shi kad'ai" ya duk'a k'asa ya d'auko 'yar jakarsa, A hankali yake d'aga takardu har yakaiga ta asibitin,
Mai gabatar da k'ara ya karb'i takardar tare da isar da ita ga alk'ali.
Bayan ya karb'a ya dudduba yayi rubutu a takardarsa sannan ya dawo da ita ga Sultana,
"Wannan bayanin da hujja da Dr. Rafiq ya kawo kad'ai ya isa ya tabbatarwa kotu da cewa Dr.
Khalid mak'aryaci ne, idan kuwa shi mai gaiskiya ne nasan yana kusa, zai iya kawowa kotu
takardar da zata tabbatar da asibitinsa ce ita kad'ai".
"Objection my lord!" Barr. Sa'eed ya fad'a,
"Barr. Sultana tana k'ok'arin ta canja salon shari'ar nan, bayan kuma ba akanta muke ba, tana
k'ok'arin tozarta Dr. Khalid ta hanyar k'aryatashi".
"K'orafi bai karb'u ba, savoda Barr. Sultana k'ok'ari take dan tabbatarwa kotu da gaskiya ne
Dr. Rafiq ya fad'a wanda ta wannan hanyar ce kotu zata san ganskiyar wannna lamari, Barr.
Sultana kici gaba" ya miyar da kallonshi ga Sultana dake murmushin jin dad'i.
"Ko zan iya ganin Dr. Khalid da takardarshi wadda sata tabbatar da cewa asibitinsa ce?".
Cikin raba ido Dr. Khalid ya taso har ya iso kusa da Dr. Rafiq,
"Kotu tana buk'atar ganin takardar kamar yanda na fad'a a baya" Sultana ta fad'a tana kallon
Dr. Khalid.
Cikin in ina yace
"Nn.nn...banzo da ita ba, sssaboda banyi zaton za'a tambayeni ba",
"Ka kwantar da hankalinka ka daina wannan in inar Dr. Khalid,
A ina rakardar take yanzu?",
"Tttttana can gida banzo da ita ba" ya bata amsa,
"Kotu zata so ganin wannan takarda kuwa" ta jiya ga alk'ali tace
"Ya mai girma mai shari'ah, ina neman alfarma da kotu ta d'aga wannan shari'ah zuwa goma
ga watan biyu shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, a wannan ranar muke buk'atar Dr.
Khalid ya kawo mana wannan takarda, nagode ya mai shari'ah".
Rubutu alk'alin yayi mai d'an tsawo kafin ya d'ago kanshi yace
"Kotu ta yarda da alfarmar da Barr. Sultana take nema,
Ta d'aga wannan shari'ar har saa gima ga watan biyu shekara ta dubi biyu da goma sha
bakwai, koooootu!" Ya buga guduma tare da mik'ewa ya fice.
_gaisuwa gareki *Basman mai sanyinta,* nagode da kulawa sosai, Allahu yabar zaman tare.
ILYSM._
°•°AKA°•°Princess Amrahí ½í¸˜
NWA
[10:03am, 9/02/2017] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: *WATA SHARI'AH* í ½í¸ª
í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“
í ½í¸ª
Na Amrah A Mshí ½í²“
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)
*_In dedication to Aunty Sdy Jegalí ½í¸˜_*
{~79~}
Tunda suka bar kotun su Brr. Sa'eed ke cuku cukun yanda zasuyi su buga takardar da zata
tabbatarwa kotu cewa asibitin Dr. Khalid ce shi kad'ai,
Da sa'a kuwa suka samu aka bugata yanda babu wanda zaiga takardar yace ta k'arya ce, ni
kaima Amrah nayi,matuk'ar mamakin wannan takardar, saboda tama fi ta kirkin tsaruwa, babu
wanda zai ganta yace ta k'arya ce sai ni da nasan kan zancen.
Ana sauran kwana uku su koma kotu ne Sultana suka fita ita da Ummimah da Umar zasu
koma police station maganar b'atar Safiyya,
Sun tsaya a daidai roundabout suna jiran traffic light ya basu hanya, wani irin hold up ne sosai
wanda basuyi mamakinshi ba saboda duk ranar Friday ana samun irin hold up d'in a duk fad'in
garin Katsina.
Wasu matasa ne su biyu akan mashin suna tuk'insu cike da natsuwa har suka kutso ta daidai
inda su Sultana suke,
Kallon mamaki ta bisu dashi kafin tace
"Wai nikam honey ka gane wancan masu mashin d'in?",
D'aga kanshi yayi tare da sauke gilashi ya kashe AC, ya kallesu sosai yace
"Ya bazan ganesu ba, basu bane mashayan nan wanda muka tab'a had'uwa dasu har
wancan na gaban ya bani complimentry card d'insa?",
Murmushi ta masa tare da fad'in
"Ehh lallai ka ganesu, tunda suka k'ariso nake kallonsu sai daga baya na tuna ashe sune",
"Aikuwa dai kinga sune, haka fa rayuwar d'an shaye shaye take, baya da wani galihu a
rayuwarsa, kullum a tozarce yake saboda baisan me zai aikata ba a cikin halin mayen da yake",
"Wallahi kuwa, vatada wata amfani rayuwar, hatta da matar aure ba lallai ya samu ta kirki
ba, to ina dalilin wannan rayuwar kuwa".
Suna cikin surutunsu basu san an basu hanya su wuce ba, matasan dake kan mashin d'in
kuma basu da hanyar da Asu wuce saboda daga d'ayan gefensu daf ce babba,
Hakan yasa suka k'ara kutsowa daidai gilashin da Umar ya sauke na gaban mashin d'in yace
"Haba malam ya zaku ringa fira kuma ku kasa bamu hanya mu wuce?".
Caraf Ummimah taji muryar da ba zata tab'a mantata ba a rayuwarta,
Shiru tayi tare da fad'awa a kogin tunani,
Har suka bar wurin bata saa lokacin da suka rabu da masu mashin d'in ba,
A bakin police station d'in suka isa duk suka fita a mota amma Ummimah tunani take,
Hankalin Sultana ya tashi har ta bud'e motar saitin Ummimah amma duk bata san anyi ba,
Zama tayi daga gefenta tace
"Ummimah" amma bata san tayi ba,
D'an bubbugata tayu firgigit ta dawi hayyacinta tana fad'in
"Ina yake? Wallahi yana cikinsu, amma shi bayyi ba, nasan muryarsa bazan tab'a mantawa
da ita ba, shine wallahi" ta fashe da kuka sosai tare da duk'ar da kanta bisa cinyoyinta.
"Me kike fad'a ne Ummimah? Lafiyanki kuwa? Waye kike magana?" Duka a had'e Sultana
ta jefo mata da wannan tambayoyin,
Umar na tsaye abunku da Barr. Har ya fara fahimtar wani abu,
"Muje kawai mu fito, idan mun koma gida kafin nan ta dawo hayyacinta sai mu mata ko wace
irin tambaya",
Tashi Sultana tayi tana k'ok'arin tayar da Ummimah,
"Ki barta anan kawai ai ba dad'ewa zamuyi ba" ya fad'a bayan ya kama hanyar shiga station
d'in, itama Sultana bin bayanshi tayi amma fa kanta d'aure yake, ta mastu taji inda maganar
Ummimah ta dosa.
Koda suka shiga basu wani dad'e ba, inspector ya shaida masu cewa tsaye suke ana
bincike sosai kuma suna sa ran insha Allahu zasu samu nasarah, ya tabbatar masu da cewa
yanzu haka akwai 'yan sandansu hud'u da kwanansu biyar basu nan, suna cikin gari banda
aikin bincike babu abunda sukeyi.
Cikin farin cikin wannan maganar Umar da Sultana suka koma mota, a yanda suka bar
Ummimah haka suka sameta, saboda ji take tamkar waai tsohon tabo ne aka fama mata,
"Ki daure ki daina kukan nan dukda bansan dalilinki na yinshi ba, kar ki tadowa kanki ciwo
kinsan kinada hawan jini".
D'ago rinannun idanuwanta tayi ta share hawayenta, amma kuma idan ta share sai wani ya
ringa fitowa,
A haka har suka isa gida bata daina kukan ba,
A parlor suka samu su Mama zaune suna firar kotu ita dasu Zarah,
Sallamah Sultana tayi ita dake gaba sannan suka shiga,
Koda Mama ta kalli fuskar Ummimah ta tabbatar da ba lafiya ba, saboda idonta yayi jajur
sannan har ya fara kumbura,
Da gudu ta iso inda take tare da d'ora kanta bisa cinyar mama taci gaba da rizgar kukanta
sosai kamar yanzu ne komai ya faru,
Itama mama kukam take tana tambayarta abunda ya faru amma ta kasa fad'i.
"Haba Ummimah? Ya zaki tayarwa mama da hankali bayan kuma kinsan ku duka biyun ba
isasshiyar lafiya ne daku ba? Dan Allah ki daina mana, ki mana bayani tunda dai harmu da
muka fita tare d'in bamu san dalilinki na yin kukan nan ba, ki mana bayani idan akwai abunda
zamu iya yi miki sai muyi" Sultana ta fad'a cike da tausayi, Umar ma zama yayi daga can gefe
yana sauraren abunda Ummimah zata fad'a.
Da k'yar tayi shiru ta sauka k'asa, cikin rawar murya tace
"Wallahi ko tantama babu muryar sarki Manu ce naji, wanda a cikin mutum tara shine kawai
baimin fyad'e ba" ta sake fashewa da kuka.
Su duka kallon mamaki suka bita dashi, kowansu ya kasa furta komai sai kallo, Zarah ce tayi
k'arfin halin cewa
"Ummimah kodai muryarsu tayi kama ne kawai? Naga Sarki Manu a Jalingo suke me zai
kawosu Katsina?",
"Kamarya me zai kawosu Katsina Zarah? Kinsani ko dama d'an katsina ne? Wallahi ba zanyi
kaffara ba muryarsa ce naji, shine kawai yake da imani a cikinsu, shi kad'ai ne yasan ko su
waye sukamin fyad'e, ku taimaka ku tayani nemanshi domin ya tabbatarda