Showing 21001 words to 24000 words out of 56183 words

Chapter 8 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf

Advertisement

bak'i mai b'arka doguwa daga gabanshi, sanye
take da riga 'yar k'arama orange bakin hannu da kwalar rigar anyi ado da burberry bak'i, sai
tad'an yafa d'an kwalin after dress k'arami,
Babu wanda zaice ita bahaushiyace sai idan dama ya santa,
Dariya had'e da shewa ta d'auka a lokacinda taga ina kallonsu,
Cike da b'acin rai na kawar da kaina daga garesu itada saurayinta.

A cikin hakane su Zarah suka iso, kallo sukabi Gentle dashi Rabiatu ta watsa mata harara,
Wata dariyar ta saka bayan sun matso inda muke ita da saurayin nata.
"Tunda an koreki ai saiki tattara tsimmokaranki kibar makarantar saboda ba anan aka haifi
uwarki da ubanki ba, sai a koma aci gaba da cin k'anzo da tuwon dawa,
Ai dama na fad'a miki nafi k'arfinki, wanda ya fikima nafi k'arfinsa,
Talent University tamuce mu keda ita, saboda malaman cikinta namune kaf mun gama dasu,
tun daga junior har senior lecturers d'in, ke har senate mun gama da 'yan cikinta saboda damu
suke damawa".

D'aga hannu nayi na d'auketa da kyakkyawan nari saboda maganganun da sukemin sun isa
haka,
Kanta ta d'ago ta kalleni cike da mamaki tace

"Ni kika mara Ummimah?",
"An mareki d'in wacece ke da ba za'a marekiba? Ki sani yanzu ni ba d'aliba bace a
makarantar nan, inada damar yi miki komai ba tare da naji haufin wani abuba, idan kikaci gaba
da fad'a min magana kuma in k'ara miki wani".

Saurayin natane ya d'aga hannu da nufin rama mata,
Dakatar dashi tayi tareda fad'in
"K'yaleta Bash, nasan maganinta",
Ta juyo gareni
"Ke kuma sai kinyi regreting d'in marina da kikayi, ba gida zakije ba? Ki tafi" tana gama fad'in
haka ta wuce cikun School abunta, shima saurayin nata yabi bayanta.
"Karki damu k'awata, babu abunda zaki gani a gida sai alkhairi, kar kiji komai ki rabu da ita
Allah ya fisu" Zarah ta fad'a cikin sigar rarrashi.
Hak'uri sukaci gaba da bani har lokacinda keke napep tazo ta sauke wasu, tsayarmin da ita
Rabiatu tayi,
Da kuka muka rabu dasu, har mukabar wurin suna d'aga min hannu,
Saida sukaga tafiyarmu sannan na hangesu sun shiga cikin makaranta.

Wani sabon kukan ne naji yana saukomin,
Mai napep d'in yace
"Baiwar Allah kiyi hak'uri ki daina kukan nan, tunda na d'aukoki kike kuka kar wani ciwon ya
kamaki",
"Karka damu bawan Allah, kaidai kayi aikinka" na fad'a cikin muryar kuka.
Tashar mota ya kaini babu b'ata lokaci kuwa na samu motar Katsina,
Mun jima bata cikaba kasantuwar yamma tayi babu matafiya sosai,
Sai wurin k'arfe biyar sannan motar ta tashi.
K'arfe tara da rabi na dare muka shiga Katsina,
Nice banje gidaba sai kusan goma da rabi kasantuwar abun hawa da yake wahala idan dare
yayi,
A bakin gidanmu napep ta saukeni,
Saidai kuma mutane dana gani mak'il k'ofar gidan,
Har shiga kanta da k'yar na sameta,
Duk wanda ya kalleni saiya gyad'a kai wasu suna hawaye.




_Alhamdulillah! Nagode sosai da addu'o'inku masoyana, yanzu kam nagode Allah na samu
sauk'i, idona ya fara warkewa, da wanda suka kirani a waya da wanda suka min addu'ah ta
chart duk ina godiya musamman aminiyata *ZARAH BB,* nagode once again._

°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[5:33pm, 23/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*


{~65~}


Ganin kallonda ake bina dashi yasa duk na tsargu, nayu tsaye a k'ofae gida kasantuwar
babu hanyar shiga,
Ganin nayi tsaye yasa wanda ke baki k'ofar duk suka daddare kowa yana kallona,
Saurin shigewa gidan nayi gabana sai fad'uwa yake hankalina ya matuk'ar tashi,
Da sauri na shige naci karo da Baba yana kuka sosai kamar k'aramin yaro,
Hakan ya k'ara tasar min da hankali matuk'a,
Wurin Baba na isa tare da gurfanawa k'asa ina kuka,
"Baba mefaru? mesa k'ofar gidanmu yake a cike? Mesa kake kuka?" Duka a tare na jefa
masa wannan tambayoyin.

Bakinshi na rawa yace
"Aishatu 'yan fashine sun..." ya kasa k'arisa maganar kasantuwar kuka da yaci k'arfinsa.

"Baba me 'yan fashi sukayi? Dan Allah kamin bayani ka daina kukan nan" na fad'a hankalina
a tashe.

Hannunshi ya d'aga ya gwada min inda aka harbeshi, sai kuma raunuka dake bisa kanshi
wanda ban kula dasuba tun shigowata tsabar tashin hankali sai yanzu.
"Na rasa mesa sukazo wurinmu, ni nayi zaton ko saa masu kud'i 'yan fashi ke zuwa inda
suke, sai gasu nan gidan sunzo mana" Baba ya fad'a bayan ya dafe kanshi saboda wani irin
sara masa da yayi,
"Sannu Baba, inma a haka abun ya tsaya ai angode Allah" na fad'a cike da tausayin Babana.

"Ba anan ya tsayaba Aishatu, akwai matsala babba, sun d'aure Afrah da Amrah sun tafi

dasu..." tun bai rufe bakiba na mik'e tsaye ina kallon Baba,
"Sun tafi dasu Baba? Wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffaraba wannan cinne ne, turo
manasu akayi wallahi Baba" na k'ara fashewa da wani kukan ina tunanin furucin Gentle na
k'arshe,
"Lallai babu wanda zayyi wannan aikin sai ita, ko tantama babu itace" na fad'a a bayyane
dukda a zuci naso maganar ta tsaya.

"Wacece ita? Me kike fad'a ne waima?" Baba ya tambayeni a rikice,
Samun kaina nayi da kasa fad'a masa sai wani irin kuka da nakeyi zuciyata sai tafarfasa take.

"Ki fad'a min abunda yake ranki Aishatu, bai kamata kiyi shiru ba, waima meya dawo dake
daga makaranta bayan kuma jiya kika tafi? Ko kin samu labarin abunda ya faru yau d'in ne?".

Shiru nayi k'irjina saa dukan uku uku kawai yake,
Hankalina ya k'ara tashi,
"Baba zan maku bayani amma ka bari sai mutanen nan sun lafa, sirrine tsakanina daku
iyayena".

Da gudu na k'arisa d'akin mama, na samu d'akin cike da mata sai jaje ake masu, hakan
yasa na j'ara fashew ada kuka bayan na rungumeta ina sauke ajiyar zuciya,
Itakam babu abunda ya sameta alamar basu tab'ata ba kenan,
A kid'ime ta janyo fuskata ta kalleni dan a tunaninta ko Amrah ce, saboda bata tab'a zaton
zata ganni a wannan lokacin ba.

"Mama ashe abunda aka mana kenan, sun tafi mana da Amrah da Afrah, shikenan mama
sun gama damu" na sake fashewa da wani kukan.

Sosai mutanen d'akin suka tausaya mana, wasu na hawaye wasu kuwa tagumi sukayi kowa
da kalar tunaninsa, babban abun mamakin bai wuce yanda kowa yasanmu mabuk'atane amma
kuma wai bama b'arayi masu yawi da sanda ba, 'yan fashi masu amfani da binduga sune
sukazo gidanmu.
Sau wuraren sha biyun dare sannan mutane suka gama watsewa, hakan yasa Baba ya dawo
d'akin mama ya samemu kowa da abunda yake sak'awa, kuka kuwa babu mai rarrasar wani.

Inda muke ya zauna ya dafa min kafad'ata,
"Komai yayi zafi maganinshi Allah, sannan kuma dukkanin tsanani yana tare da sauk'i haka
Allah mad'aukakin sarki ya fad'a a cikin littafinsa mai tsarki, dan haka dan Allah ku daina kukan
nan, bana son wata cuta ta sameku a dalilin haka, insha Allahu Afrah da Amrah zasu dawo
garemu".
"To muna fatan haka Babansu, Allah ya tabbatar" mama ta fad'a tare da share hawayenta.

Jikina na rawa na fara labarta masu duk abunda ya faru tun daga farko har k'arshe babu
abunda na b'oye masu,
Hankalinsu ya k'ara tashi sosai, sun tausaya min kuma suma sun tabbatarda Gentle ce tayi
wannan aiken,
Babbar matsalar yanda take d'iyar masu kud'i, mun tabbatarda ko munkai maganar ga
hukuma babu abunda za'ayi masu.

Yanda mukaga rana haka mukaga dare, ko rintsawa babu wanda yayi a cikinmu, sai koke
koke dake tashi wanda har Baba kukan yake yana k'ara tausayawa rayuwata, saboda yanzu
shikenan an rabani da martabata.

Washe gari da sassafe Baba yaje yayi reporting maganar ga 'yan sanda,
A tak'aice dai saida akayi sati biyu babu ko labarin su Amrah, gashi kuma yanzu har
indiyawanda zasu duba Amrah sunzo, likitanta yayi waya yace a kaita za'a nata aiki dan yayi
masu bayanin komai, hakan ya k'ara tayar da hankalinmu, muka rasa duk wata natsuwarmu,
Gashi kuma hukuma ta kas ayin komai akai,
Har tadin maganarma basu sakeyi ba dukda cikakken bayani da Baba ya masu tun daga
abunda Gentle tasa akamin har 'yan fashinda suka tafi da k'annena biyu.

A ranarda suka cike sati biyun ne aka tsinci gawar Afrah a daidai kwanarda zata shigarda
mutum layinmu,
Mutanenda suka tsinci gawar natane suka kawota nad'e cikin buhu jina jina,
Bayan sunyi sallamah da Baba ya fitane suka shaida masa avunda suka gani,
Amma kuma basu tabbatarda cikin 'ya'yan Baba bane kawai dai sunyi hasashen hakan ne,
kasantuwar fuskar duk jinice kallo d'aya ba za'a iya gane ko waye ba.

A rikice Baba ya k'wala mana kira nida Mama,
Koda jin kiran muka tabbatarda ba lafiya ba,
Dan haka muka fito k'ofar gida hankalinmu tashe ko d'an kwali ban nema ba.

Bayan ya bud'e buhun ne ya janye yalwataccen gashin Afrah da duk ya b'aci da jini daga bisa
fuskarta,
Baki d'aya fuskar tayi dameji,
Kayan jikintane ya k'ara tabbatar mana da d'aya daga cikinsu ne, *Afrah ko Amrah* saboda
mun kasa banbancesu,
Jiki na rawa Mama tace
"Ko tantama babu Afrah ce, wallahi Afrahta ce wannan, saboda wannan kayan sune a jikinta,
Amrah kuma blue shaddace ta saka ba wannan atamfarba".

Bansan lokacinda na fasa wani irin ihu mai k'arfi ba, inda buhun yake na tsuguna ina kuka
sosai ina k'ara kallon yanda fuskar Afrah ta koma,
Tam! Na rik'e buhun ina sauke ajiyar zuciya bayan na nemi hawayenda nake na rasa,
Duk abunda ke faruwa har yanzu Baba ya kasa furta komai,

Saidai kuma kallo d'aya za'a masa aga tashin hankali k'arara a fuskarshi.

Muna cikin haka ne wani mutumi yazo, a biye dashi wasu gardawa ne majiya k'arfi,
Cike da izgili mutumin yace
"Na gaji da hak'uri nikam hak'urina ya k'are,
Dan haka yauyau d'in nan zaku barmin gidana,
Shekara biyu kenan ana kan ta uku rabonka da biyan kud'in haya,
Dan haka dole ku nemi wurin zama kubarmin nawa yanzu",
Kallon gardawan yayi yace
"Hame ku shiga ku firfito masu da kayakinsu".

Da hanzari kuwa suka shiga, mu kuwa kallon mamaki kawaa muka bisu dashi,
Rashin imaninsu ya matuk'ar d'aure mana kai,
Basu ko dubi halinda muke ciki ba amma suka ringa jifa da kayanmu,
Hakan ya tabbatar min da cewa wannan ma aikene daga Gentle.

K'ara mukaji da k'arfi Baba ya fad'i k'asa,
Da sauri Mama ta matsa inda ya fad'i d'in tana kiran sunanshi,
"Abubakar, Abu dan Allah ka tashi, karka tafi ka barmu a daidai lokacinda muke buk'atar
taimakonka, dan Allah ka tashi.." kuka yaci k'arfinta.




°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[3:36pm, 24/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*


{~66~}


Duk kukan da mukeyi baisa mutanen sunji tausayinmu ko d'aya ba,
Cike da rashin imani suka ringa watsi da baki d'aya kayakinmu,

Ga gawar Afrah cikin buhu ga kuma Baba da yake kwance baya ko alamar numfashi,
Kukanma nemanshi nayi na rasa, sai mama daketa ambatar sunan baba amma har yanzu ko
alamar motsi bayayi.

"Ku tashuwa min daga k'ofar gida bana son ganinku, idan ba haka ba kuma a wulak'antaku
cikin unguwar nan" mutumin mai gidan hayar ya fad'a cike da izgili da gadara.

Mutanen da suka kawo gawar Afrah d'aya daga cikinsu yace
"Kai kuwa bawan Allah ka tausaya masu mana, bakaga hakinda suke ciki ba? Ka barsu suji
da d'aya mana, tunda dai kasa an fitar masu da kaya ai sai ka shafa masu lafiya haka, tunda
mai gidan nasu ma gashi nan kwance bama asan halin da yake ciki ba".

A wulak'ance yace
"Babu ruwana da halinda suke ciki, gidana kawai na sani kuma na basu minti goma subar
harabar nan, idan kuma basu bari ba duk abunda na masu su suka ja".

Cikin rashin tsoro na tashi tsaye,
Ko alamar kuka babu a idona na dubeshi ido cikin ido nace
"Kaga malam ka kama kanka, na kula kai baka da tunani kuma baka san darajar d'an adam
ba,
Munfi k'arfin ka wulak'antamu wallahi,
Sannan kuma duk halinda ka tayar damu daga Allah ne, bawai dan Allah baya sonmu bane
kaga ya barmu a haka,
Jarabtace kuma babu wanda yafi k'arfinta,
Kaima bakafi k'arfin Allah ya jarabceka ba".

Dariya ya k'yalk'yale da ita tare da fad'in
"'Yan mata Kenan, dama an bani labarinki tun kafin inzo, wallahi kinji na rantse, idan na tafi
na dawo na sameku anan zakiyi mamakin abunda zan maku, ni nafi k'arfin ki fad'a min wannan
maganganun marasa dad'i" yana gama fad'in haka ya juya ya tafi,
Gardawansa ma suka mara masa baya.

Sai a lokacin na sake jin wani irin kuka maras control yazo min,
Wannan mutanen su suka ringa rarrashinmu tare da kwashe mana kaya suna kaiwa gidan
d'aya daga cikinsu,
A gidanshi aka sallaci Afrah, a lokacin har ankai Baba asibiti domin duba lafiyarsa.

Bayan ankai Afrah ne muka tafi asibiti,
Mukayi sa'a kuwa Baba ya farfad'o,
Farin ciki mukayi sosai Mama ta matsa kan gadon ta rik'e hannunshi,
Da k'yar yake iya bud'e idonshi sai hawaye ke fita daga idonshi,
A hankali ya iya bud'e bakinshi tare da furta
"Ku yafemin nasan tawa ta k'are,

Wanda suka zalunceku ku barsu da Allah shi zai maku sakayya,
Ku rik'e addu'ah a ranku kamar yanda Baffa da Hassu suka rik'i addu'ah kuma tayi masu
jagora a cikin *Dodon Jatau,* duk wanda ya rik'i addu'ah baya tab'ewa,
Sannan duk wanda yazo neman aurenki Aishatu karki b'oye masa abunda aka miki, bana son
zalunci ya shigo ciki,
Idan kika fad'a masa yaji zai iya aurenki shikenan, idan ba zai iyaba kuma sai kici gaba da
neman zab'in na gari".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login