Showing 33001 words to 36000 words out of 56183 words

Chapter 12 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf

Advertisement

"Lauya mai kare wadda ake k'ara, ko kanada hujja?".

Tashi Umar yayi ya fuskanci alk'ali yace
"Ehh inada ita ya mai shari'ah",
"Kotu tana son gani" ya fad'a bayan ya zare gilashinshi.

"Zan iya ganin Salmah Abubakar?" Barr. Umar ya tambaya bayan ya miyar da kallonshi ga
sauran mutane.

Cikin daburcewa Gentle ta mik'e a susuce take taku har ta iso inda aka tanadar domin
tsayuwar wanda ake tuhuma.

Kusa da ita Umar ya matsa ya kalleta cikin ido yace
"Kotu zataso jin cikakken sunanki daga bakinki?",
"Sunana Salmah Abubakar" ta bashi amsa a tak'aice.

"Salmah kad'ai? Babu wani lak'ani da ake miki?".

Cikin in-ina tace
"Ana...ana cemin Gentle",
"Good malama Gentle, ko zaki fad'awa kotu alak'arki da Aisha Abubkar? Ina nufin wadda tayi
k'ararki",
"Ehh Aisha k'awata ce sosai tun a Secondary School, mun shak'u sosai da ita hakab yasa
har jami'a muka cik'e d'aya a JAMB d'inmu kuma course iri d'aya, tare muke karatu kwatsam
naji ance wai an koreta daga makaranta saboda an kamata da case d'in ta zubar da ciki".

Har cikin ran Ummimah taji wannan maganar, jin hawaye tayi suna zarya a kumatunta.

"Wane irin yanayi kika sjiga a lokacin da kikaji wannan maganar? Ina nufin kin yarda da
maganar ko kuwa kin musa?" Ya tambayeta.

"Nayi mamaki sosai, amma kuma daga baya sai na cire mamakin saboda mutanen yanzu
abun tsoro ne" Gentle ta bashi amsa.

"To duk yanda kike k'awance da ita har baki san tana yawon banza ba? Kuna rabuwa
kenan?",

"Ehh a'a, da dai bamu rabuwa da ita, amma kuma lokaci d'aya ta canja halinta, batada aiki
sai yawon banza, idan na mata magana tace babu ruwana da ita, kowa yaji da kansa".

"kina nufin bakiji damuwa ko kad'an ba a lokacin da akace an koreta daga makaranta?
Amma a yanda kuke da ita ya kamata ace ko yaya kinyi mamaki saboda ace babbar k'awarki
wannan al'amarin ya faru da ita abun mamaki ne".

Cike da gadara Gentle tace
"Nikam banji komai ba gaskiya, saboda dama ta dad'e da canja halinta, kuma ta nuna tafi
k'arfina",
"malama Gentle kuma bakya tunanin ko wasu k'awayen ne ta canja yasa ta rabu dake?
Saboda kinsan zaman da kuke zaku iya gundurar juna, sannan kuma kina nufin ke kullum kina
zaune cikin d'aki daga can sai School area kawai kike zuwa? Kenan bakya zuwa wurin kowa?".

"Objection my lord!" Barr. Sa'eed ya fad'a a fusace,
"Wannan kuma rayuwarta ce bai shafi shari'armu ba, bai kamata barr. Umar yana yima
Salmah irin wannan tambayar ba".

"Barr. Umar a kiyaye" Alk'ali ya fad'a bayan yayi rubutu a takarda.

"Malama Gentle ko kinsan wasu k'awayen Aishatu masu suna Zarah BB da Rabiatu Sk?
Sannan kuma bakya tunanin ko wurinsu ne take zuwa wani lokacin saisa bakya ganinta?",
"Ehh nasan tana dasu, amma ni bansan ko wurinsu take zuwa ba, saboda suma d'in wani
lokaci suna zuwa wurina nemanta idan ta tafi yawon darenta",
Murmushi kawai Umar yayi saboda a yanayin kalaman dake fita daga bakinta ma kad'ai ya
isa ya tabbatarwa mutum da rashin gaskiyarta.

"Zaki iya komawa ki zauna har sai na sake nemeki nan gaba" Umar ya fad'a tare da
komawa mazauninsa ya zauna.

"Kafin ta koma ta zauna, ko Barr. Sa'eed yanada tambayar da zayyima Salmah Abubkar
wacce yake karewa a wannan shari'ar?" Alk'ali ya tambaya.

Bayan ya sunkuya k'asa yace
"Ehh inada ita ya mai shari'ah" ya matso inda take yace
"Salmah inaso ki fad'a mana yanayin alak'arki da Aishatu a tak'aice",
"Alak'ata da ita mai k'arfi ce, saboda gidansu talakawa ne ni kuma gidanmu munada hali
sosai,
So wani lokacinma ni nake taimaka masu da abunda zasuci a gidama barin a School idan
tayi broke, komai nata nice kuma tana nuna min jin dad'in hakan,
Amma kuma lokacin data fara canja hali na fahimci har abinci idan na dafa bata ci, bama ta
zama barin taci, wani lokaci idan tayi dare zatazo da abincin restaurant mai rai da lafiya taci ko
kallon inda nake batayi" Gentle ta sharara k'arya hankalinta kwance.

"Barin d'an miyar dake baya, naji kincema Barr. Umar suma k'awayen nata wani lokaci suna
zuwa nemanta, hakan ya tabbatar da cewa ba kowane lokaci take tare dasu ba kenan, to kina
nufin bataje wurinsu ba kenan suma?",
"Ehh lallai bataje wurinsu ba kam, tunda inda ace taje wurinsu ai ba zasu zo nemanta inda
nake ba".

"Objection my lord!" Barr. Sultana ta fad'a bayan ta buga teburi,
"Yanayin yanda suke magana bai kamata ace suna yinta ba ya mai shari'ah! Wannan zai iya
zama cin fuska ga wadda take k'ara".

Jinjina kanshi alk'alin yayi yace
"Barr. Sa'eed ka tausasa kalamanka".

"Iyakacin tambayar da zan mata kenan ya mai shari'ah, ina neman kotu ta bani dama domin
kiran Aishatu Abubakar, wato wadda take k'ara domin akwai tambayoyin da nake so na mata"
Barr. Sa'eed ya fad'a had'e da sunkuyawa k'asa yana kallon alk'ali.

"Kotu tana son ganin Aishatu Abubakar" alk'alin ya fad'a yana kallon ta inda zata fito.

A hankali cike da natsuwa ta taso kanta sadde a k'asa ta tsaya inda Gentle ta fita.






°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[6:44pm, 29/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*


{~72~}

Cikin izzah da tak'ama Barr. Sa'eed yace
"Aishatu shin a cikin kalaman da Salmah tayi ko akwai maganar data fad'a wadda kike da ja
akanta?",
Da hannunta ta share hawaye jikinta ya fara rawa saboda yanda taga an tsura mata ido,
"Ehh...ehh a..akwai" ta fad'a cikin rawar murya.

Murmushi Barr. Sa'eed yayi yace
"Ki kwantar da hankalinki ki daina rawae murya indai da gaske kinada gaskiya ba k'arya zaki
fad'a ba".

"Objection my lord!" Barr. Sultana ta fad'a k'ufule,
"Bai kamata Barr. Sa'eed yana fad'in wannan kalaman ga Aishatu ba, ya kamata yayi la'akari
da yanayin yawan mutanen wurin nan ne yasa take rawar jiki da rawar murya",
"Barr. Sa'eed a kiyaye" alk'ali ya fad'a yaci gaba da kallonsu.

"uhm, kr nake sauraro" ya fad'a a hankali.

"Kusan duk maganganun data fad'a k'arya ne, nasan dai tana yimin wasu abubuwan idan
taga inada buk'ata, amma maganar da tace ita ke d'aukar nauyinmu wallahi k'aryane, babana
bai rageni da komai ba, kusan duk wata ko baya da kud'i sai ya ranta ya turo min, sannan kuma
da tace na canja hali wannan duk halayenta ne, babu inda nake zuwa, idan ma na fita daga
room d'inmu to bazan wuce room na kusa da namu ba inda k'awayena Zarag da Rabiatu suke
ba".

"Ina su k'awayen naki suke a halin yanzu? In da gaskene ai ya kamata ace sunzo nam
kodan su bada wannan shaidar ga k'awarsu".
Jikin Ummimah ya hau rawa saboda rashin halartar su Rabiatu kotun, tasan ba lallai bane a
yarda da maganarta.

"Gamu" Zarah da Rabiatu suke fad'a daidai lokacin da suka shigo cikin kotun.

Ajiyar zuciya ta sauke farin ciki bayyane a fuskarta, hamdala tayi ga Allah a lokacin da suka
iso inda ake son ganinsu.

Qur'ani aka basu sukayi rantsuwa da zasu fad'i gaskiya sannan cikin rashin jin dad'in
zuwansu Barr. Sa'eed yace
"Kune k'awayen nata?",
"Ehh mune" suka had'a baki wurin fad'i.

Baki d'aya yama rasa tambayar da zayyi masu, saboda sam bayyi tunanin zasuzo ba, dan
saida ya tabbatar da babu su a cikin kotun sannan ya nemi yana son ganinsu.
Sai daga baya wata fasaha ta fad'o masa yace

"Wai da gaske wurinku Aishatu take zuwa wani lokaci?",
"Ehh da gaske wurinmu take zuwa duk lokacin da Gentle ta fita tayi dare, wani lokacin ma a
d'akinmu take kwana saboda tace ba zata iya kwana ita kad'ai ba" Rabiatu ta bashi amsa.

Shiru ya d'anyi kafin yace
"To idan da gaske ne mesa wani lokacin idan bata d'akinku kuke zuwa ku tambayi Salmah
inda Aishatu taje? Kenan hakan ya tabbatarda ba kowane lokaci kuma d'in kuka san inda take
ba".

Zarah tayi caraf tace
"So d'aya ne tak hakan ta kasance, kuma ranar ma ta fita neman Gentle ne akan tazo suyo
karatu dan exam d'in da zamuyia washe gari mai wahala ce, tun fitar da tayi shine vata dawo ba
har mukaje nemanta room d'insu".

Kallonshi ya miyar ga alk'ali yace
"Ya mai girma mai shari'ah, da wannan bayanin da k'awayenta sukayi ya isa ya tabbatarwa
kotu da cewa ba kowane lokaci ne take tare da k'awayentan da take cewa suna tare always ba,
kenan akwai gyara a maganar Aishatu saboda gashi k'awayenta sun fad'a da bakinsu, ta masu
k'aryar zataje ta nemi Salmah domin suyi karatu, amma kuma Salmah ta dawo tace ita batama
ga Aishatun ba, wannan ya tabbatar da cewa ta tafi yawo kenan"
Ya juya gasu Zarah yace
"Zaku iya tafiya ku zauna".

"Amm kafin su tafi su zauna, ko lauyoyi masu kare wadda take k'ara sunada tambayar da
zasuyi masu?" Alk'ali ya tambaya.

"Ehh akwai ya mai shari'ah" barr. Sultana ta fad'a tare da tasowa cike da natsuwa ta iso inda
suke.

"Bayan kun tambayi Salmah inda Aishatu take, zaku iya tuna amsar data baku?",
"Ehh zan iya tunawa,
Saida ta bimu da kallon banza sannan tace 'idan har bamu k'yaleta da tambayar inda Aisha
take ba wallahi sai ta saka an mana abunda tasa akaima Aisha', duk da vamu san ko menene
ba amma hankalinmu ya tashi, babu yanda muka iya dole muka bar mata d'akin baki d'aya
ranmi a dagule yake".
"Well" Sultana ta fad'a,
"To daga nan ku kuma wane irin mataki kuka d'auka?".

Rabiatu tace
"Babu yanda muka iya duk da tashin hankalin da muka shiga, mun nemeta a duk blocks d'in
hostel amma bamu sameta ba, hakan yasa muka koma room d'inmu amma babu wadda ta iya
yin bacci a cikinmu,

Washe gari tun gari bai gama wayeba muka fita waje nemanta,
Acan muka tsinceta cikin jini nesa da hostel,
Hankalinmi ya tashi muka d'auketa muka kaita school clinic,
Bayan sun dubata sukace suma ciwonta yafi k'arfinsu saidai si kaida wata asibiti,
Tare muka tafi da ita ta dad'e bata farfad'o ba,
Likitan daya dubata ya tabbatar mana da fyad'e ne aka mata kuma an illatata sosai, yace
mana ya rubuta a takarda zai bamu mu tafi da ita idan ta samu sauk'i,
Amma kuma sai muka shafa'a, shi bai bamu ba muma kuma mun manta bamu karb'a ba,
Saida aka dawo hutu ne akace wai an koreta, kuma harda gwada mana takardar asibitin anyi
amma kuma sab'anin waccan ta farkon wadda bamu san dalilin canzata ba".

Barr. Sultana zata sake magana kenan alk'ali yace
"Kotu zata so ganin likitocin da suka dubata a asbitinsu,
Sannan kuma zataso taga ma'aikatan School clinic d'insu domin su fad'a mana 'mesa sukace
ciwonta yafi k'arfisu?' Saboda ta yiwu su abunda suka gani daban, zamuso jin komai daga
bakinsu idan suna kusa".

Cike da ladabi Sultana tace
"Likitan da yayi mata aikin mun buk'aceshi da yazo amma kuma yayi tafiya zuwa Lagos, ga
wannan takardar" ta mik'awa wanda ya gabatar da k'ara domin ya isar da ita ga alk'ali,
"Takarda ce wadda ta tabbatar da likitan baya nan, yaje wani course ne amma ya tabbatar da
yau saura kwana hud'u ya dawo, ranar Friday kenan,
Sannan kuma bamuyi magana da ma'aikatan School clinic d'inba,
Muna rok'on kotu mai albarka data d'aga wannan shari'ar har sai zuwa next week, wanda
insha Allahu a ranar ma'aikatan zasuzo, shima kuma likitan kafin nan ya dawo".

Shiru alk'ali yayi bayan yayi 'yan rubuce rubuce sannan ya d'ago kanshi yace
"Kotu ta d'aga sauraron wannan shari'ar har sai ranar litinin, bakwai ga watan d'aya shekara
ta dubu biyu da goma sha bakwai",
Ya buga tuburonshi da guduma tare da fad'in
"Kooootu!" Yana mik'ewa kowa ma ya mik'e


***

Bayan sun fita daga kotu ne Gentle ta ringa watsawa Ummimah harara cike da tsana,
Zarah da Rabiatu sukayi tsaki tare da fad'in
"Ta Allah bata mutum ba, kuma insha Allahu sai munyi nasarah, Allah baya goyon bayan
azzalumi".

K'ara k'ufule Gentle sukayi,
Momy'nta taja hannunta da sauri suka tafi dan tasan halin Gentle tsaf zata iya yin dambe
dasu a wurin, kuma idan har tayi to mutane zasu tabbatar da cewa da gaske tasa anyima

Ummimah fyad'e duk da yanzu ma wasu sun fara gasgatawa.

Kallon Rabiatu Ummimah tayi tace
"k'awayen kun rufa min asiri sosai da kukazo, inda ace bakuzo ba da bansan yanda zanyi ba,
banyi tunanin zakuzo ba gaskiya".

Zarah tace
"Ai dole ne a garemu muzo Ummimah, an cuceki kuma aka nemi a hanaki kuka,
Jiya muna Hostel mukaga text d'in lawyer d'inki, ta mana bayanin komai kuma ta nemi in da
hali anada buk'atarmu a kotu,
Kinsan akwai nisa daga Jalingo zuwa Katsina, tun da sassafe muka taso amma bamu iso da
wuri ba har akayi nisa da shari'ar, Allah yasa daidai muna zuwa muna ji ana nemanmu".

Ummimah tace
"Kuma fa haka kawai na bata number d'inki, saboda kin san yanzu banda waya,
A wata takardata ce dana tab'a ajiye number'n sanda zan miki call me back,
Lokacin da zamu baro gida na had'ata cikin jikarmu,
Ashe da rabon zatayi amfani".

"Aikuwa dai kin gani".
Da wannan firar Sultana ta samesu,
Takardar dubu d'aya ta zaro a jakarta Ta mik'awa Mama tace
"Mama ku hau napep da wannan ku tafi gida, ni inada aiki da yawa a Office".

Karb'a mama tayi tace
"To mungode sosai Allah yayi albarka,
Sai kun dawo d'in" suka tafi yayinda Sultana kuma ta koma Office d'inta.



_ina cigiyar *Sadiya Afka* nikam, ko ina ta shige oho? Gashi ba'a samun lambarta idan an
kira, Allah dai yasa lafiya inji Amrah._






°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[11:41pm, 31/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login