Showing 54001 words to 56183 words out of 56183 words

Chapter 19 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf

Advertisement

Tabbatarwar da alk'ali yayi cewa ita ce Amrah yasa ya gyara alk'alaminshi ya d'anyi rubutu
kad'an sannan ya fara bayani...



_ku biyoni gobe insha Allahu zaku samu k'arshen labarin *wata shari'ah,* nagode sosai ga
masoyana masu kirana a waya da masu bina ta private chart suna min fatan alkhairi. ILYSM._






°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[9:57am, 13/02/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*


{~83~}

*K'ARSHE*



"A bisa shaidu da hujjoji da suka gabata, kowa yaji yanda mai laifi ta amsa laifinta da bakinta,
sannan kuma..." shiru alk'ali yayi kasantuwar tari da yaci k'arfin YB,
Sosai yake tarin harda jini ke fita daga bakinshi,
Cike sa tausayi kowa ke kallonshi,
Baifi minti goma a wannan halin ba rai yayi halinshi,
Da k'arfi iyayenshi suka d'auki salati had'e da kuka, dama sun san haka na zuwa saboda
yanayin ciwonshi babu alamar zai tashi ko kad'an.

An d'auki kusan awa d'aya da mutuwar YB harma an tafi da gawarshi Jalingo sannan kotu ta
sake zama.

"Kotu ta tabbatar da cewa Salmah ita ce ta saka akayima Aishatu fyad'e, bayan nan kuma
tasa an kashe mata 'yar uwa wadda a dalilin haka babanta ya yanki jiki ya fad'i ya mutu,
Indiyawa sunzo zasu duba lafiyar d'umbin al'ummah wanda a cikinsu harda Amrah k'anwar
Aishatu, dalilin saceta da Salmah tasa akayi yasa har likitocin suka k'araci zamansu suka koma
k'asarsu,
Salmah tasa an sakawa gidansu Aishatu wuta har ya k'one k'urmus, tayi hakan ne da nufin
Aisha da mamanta su k'one dan bata san basu ciki ba.
Dan haka kotu ta yankewa Salmah Abubakar hukuncin d'aurin rai da rai a gidan yari,
Sannan kuma iyayen Salmah wato Alhaji Abu Abu da mahaifiyarta zasu bada tarar naira
miliyan goma, wanda a cikin miliyan goma d'in za'a ware kud'in da za'a fitar da Amrah zuwa
k'asar Indiya, za'a fidda wanda Aishatu zata koma makaranta saboda Salmah ita tayi silar da
aka koreta, sannan kuma za'a fitar dana gidansu da Salmah tasa aka k'ona. Abdul k'adir kuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda shi da kanshi ya
furta cewa da hannunshi ya kashe Afrah, sannan kuma a gaban kowa yazo ya watsawa Salmah
acid a fuska wanda fuskarta tayi dameji harma abun ya shafi idanuwanta.
Sauran matasan nan kuwa wanda suka kasance kisa itace aikinsu kamar yanda kotu ta
tabbatar,
An yanke masu hukuncin kisa ta hanyar harbi da bindiga su dukansu.
Sarki manu kuwa bashida laifi saboda kotu bata sameshi da laifi ko d'aya ba saima taimako
da yayi, dan haka kotu ta wankeshi daga laifi.
Idan Alhaji Abu Abu bayada kud'in tarar da aka yanka masa, kotu zata d'aureshi na tsawon
shekaru uku, ko kuma za'aci gaba da tsaronshi har sai lokacin daya kawo kud'in.
A k'arshe kotu na bama Aishatu Abubakar hak'uri akan abubuwa da dama, mahaifinta da
'yar uwarta da suka mutu Allah yaji k'ansu, 'yar uwarta maras lafiya kuma Allah ya bata lafiya
yasa ayi aiki cikin nasarah".

Kabbara kotun aka d'auka baki d'aya mutanen dake ciki,
Kuka Gentle ta sake b'arkewa dashi da taji hukuncin da aka yanke mata,

Ta tabbatar da zata fuskanci tsangwama sosai a kurkuku saboda damejin da fuskarta tayi, ta
zama abun tsoro kamar *dodon Jatau.*

"Zan biya, ko miliyan d'ari ne Allah na amince zan bayar akan a d'aureni" Alhaji Abu Abu ne
yayi wannan maganar had'e da share guminsa.

Murmushin dattako alk'ali yayi dan dama abunda yake jira kenan, da gangan yayi maganar
yasan Alhaji Abu Abu ba zai yarda a d'aureshi ba saboda shi d'an siyasa ne, sannan kuma
yanada mak'udan kud'in da ko fin haka aka nema sai ya bayar.

Ummimah, Amrah, mama, Zarah da Rabiatu kukan farin ciki kawai suke,
Barr. Sultana da Barr. Umar kuwa sai farin ciki baki har kunne,
Har inda Barr. Sa'eed yake zaune yana had'a gumi Umar yaje,
Bayan ya mik'a masa hannu yace
"Kamar yanda kayi fatan Allah ya had'amu a *WATA SHARI'AH* gashi kuwa ya had'amu,
Yau gashi d'an k'aramin Barr. Ya kayar da babban Barr."
Murmushin k'arfin hali Barr. Sa'eed yayi tare da fad'in
"Bana fatan Allah ya sake had'amu a *WATA SHARI'AH.* A yau kam na tabbatar da kai ba
k'aramin Barr. Bane kai babba ne, dan zan iya cewa kama fini girma daga kai har matarka, tashi
tsaye ma mu gwada tsawo inga ni da kai wa yafi wani girma?." Ya kwashe da dariya tare da
mik'awa Umar hannunshi sukayi musabaha. Haka suka rabu Barr. Sa'eed na k'ara girmama
Umar da Sultana dan ya tabbatar da su ba k'anana bane.

Godiya Ummimah tayima Sarki Manu Akan irin halarcin da yayi mata,
"Karki damu dama na jima ina neman ta hanyar da zan taimakeki, sai daga baya na samu
labarin ke 'yar katsina ce, shine na dage har na samu inda kike, na kuma samu labarin halayen
Barr. Umar da matarshi, shine na samu lambarsu na fara tura masu sak'una akan su taimakeki,
na kuma k'i bayyanar masu da kaina dan bana so wani abu ya biyo baya , nasan halin lawyers
sosai saisa na b'oye masu kaina, sanin zan iya masu amfani yasa dana had'u dasu na fara
mayen k'arya wanda duk a lokacin cikin hankalina nake, na basu complimentry card d'ina
sannan muka shiga ciki ni da abokina, hatta had'uwar da mukayi da ku a traffic duk tsari ne,
saida na fahimci komai zai faru sannan nabi bayanku da mashin d'ina".
Godiya ta sake yi masa sannan tabar wurin cikin mamaki.

Gidajen television sai faman d'auke d'auken hotuna da videos suke,
Har inda su Ummimah suke saida wani d'an jarida yaje da nufin yayi mata tambayoyi,
Har tayi niyyar bashi amsa Dr. Rafiq fuska murtuke ya k'ariso inda suke yace
"Kai dillah malam ja can, matar auren kake so ka d'auka ka yad'awa duniya?"
Kallon mamaki Ummimah ta bishi dashi,
'Taya akayi ta zama matar aure da har ake hak'ilo kanta?' Ta tambayi kanta.

Barin wurin d'an jaridan yayi dan yaga Dr. Rafiq da gaske yake ba wasa ba.

"Kike kallona koke ba matar auren bace?" Ya tambayi Ummimah had'e da d'an guntun
murmushi.

"Taya akayi wadda ko saurayi batada shi ta zama matar aure?",
"Wadda ko saurayi batada shi? Dan Allah kice Allah kin tuba, ya budurwa kamarki zatace
batada saurayi? Gaskiya wasa kike",
"Sam babu wasa a maganata, ka yarda dani wallahi da gaske nake".
Murmushi yayi dan dama abunda yake so kenan yaji daga bakinta.

"Tun kafin in ganki, sunanki da labarinki kawai naji hankalina ya kwanta dake, ki daure ki cije
kiso Rafiqu, wallahi zai rik'eki da amana, na jima ina fatan Allah ya kawo min ranar da Rafiq zai
kawo min wadda yake so ya aura sai yau, ina fatan zaki karb'i wannan tayin Ummimah" Umman
Rafiq ce ta jefo wannan maganar a daidai isowarta inda suke.
Shiru Ummimah tayi na tsawon lokaci batace komai ba,
Kallon Umman Rafiq tayi sannan ta miyar da kallonta ga Rafiq d'in,
Murmushi ta saki wanda har saida hak'oranta suka bayyana,
Haka kawia ta sameta cikin nishad'i wanda rabonta dashi an d'auki tsawon lokaci, tun kafin
komai ya faru da ita.
Wannan murmushin da tayi shi ya tabbatar da amincewarta,
Cikin murna k'anwar Rafiq ta rungumeta tana fad'in
"Mungode da kika amince da soyayyar yayanmu, insha Allahu zamu kula dake tamkar 'yar
uwarmu ta jini",
Batace komai ba saidai fuskarta kawai za'a kalla a tabbatar da tsantsar farin cikin da take ciki.

Suna nan tsaye sai ga nurses d'in makarantarsun nan su hud'u sunzo kowace tana kuka
hannunta rik'e da takarda,
D'aya daga cikinsu tana fad'in
"Wai yanzu dan wulak'anci tun anan za'a bamu takardar sallamah? Shegen son kud'inmu ya
kaimu ya baromu, yau gashi gwamnati ta d'auki nata hukuncin a kanmu tun kafin ayi nisa". Da
wannan surutan har suka bar wurin. Ummimah kuwa cikin motar su Rafiq ta bisu suka rankaya
sai gidansu Sultana cike da farin ciki dan dama kowa ya koma su kawai ake jira.


*Alhamdulillah! Nima kuma anan sai na d'igawa wannan labarin aya, wata shari'ah labari ne
wanda zan iya cewa fiye da rabinshi ya faru da gaske. Saidai kuma wadda abun ya sama har
yanzu gaskiya tak'i ta bayyana, rayuwarta ta wulak'anta kamar yanda ta Ummimah ta
wulak'anta, an koreta a makaranta an nuna anfi k'arfinta ta hanyar dukiya, 'yan uwa musulmai
mu taru mu saka wannan baiwar Allah'r a addu'ah ko Allah zai kawo k'arshen mawuyancin halin
da take ciki.*

Godiya ga masoyana maza da mata, na nesa dana kusa, masu kirana, masu yimin text

messages, masu bina ta pchart suna min fatan alkhairi harma da wanda Allah bai basu daman
yimin magana ba nagode sosai da kulawarku. Amrah na k'ara jaddada yanda kuke a zuciyarta.

A duk inda kaji an ambaci hanta dole a ambaci jini, *RAZ* daku nake tink'aho, da bazaraku
nake taka rawa, ban san ya rayuwata zata kasance idan babuku a cikinta ba, fatana a kullum
Allah ya kareku daga sharrin mahassada da mak'iya, Allah ya k'ara maku baseerah da
d'aukaka. Amrah na masifar sonku. (@Rerbee'art sk and Zarah bb).

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* k'ungiya mai albarka da had'in kai, Allah ya taimakeku
ya kareku daga sharrin masu sharri.

Wannan littafin sadaukarwa ne Ga Sadiya Labaran Jega (Aunty Sdy Jegal) nagode sosai da
kulawarki a gareni.

Tukuici ne ga k'awata Aisha Abubakar Gege (Ummimah) sunanki ne a cikin labarin. ILYSVM.


Ina fatan wa'azin dake cikin littafin nan zai amfanar da d'umbin al'ummah, mu daure mu turawa
wanda basu karanta ba domin su karanta su k'aru da babban darasin dake cikin *wata shari'ah.*



*_FASAHAR AMRAH_*

"Kiyi hak'uri *KHAULAT,* Nasan irin *YAUDARA* da *DR. RAFIQ* yayi miki, kiyi hak'uri kiyi
amfani da karin maganar da hausawa sukace *MAHAK'URCHI* mawadaci. Ina so kiyi koyi da
rayuwar *UMMU HAYDAR,* Duk da irin *SO DA SHAK'UWA* dake tsakaninta da mijinta saida
ta zama *MAI BAK'IN JINI* a wurinsa. Ya nuna mata *TSANTSAR ZALUNCHI* amma daga
baya ta samu *D'AUKAKA DAGA ALLAH* tama Usman *RAMUWAR GAYYA,* ta nuna masa
cewa *BABU MARAYA* sai rago. Nasan ba zaki rasa karanta labarin *YARIMA SAIFULLAH* ba
kinga irin wahalar da yasha a rayuwarsa. Amrah ma tayi fama da *ZAFIN SO* na wadda
batama san tanayi ba, a koda yaushe ta zauna maganarta d'aya ce *'INA ZANGA KDEEY?'*
saida ta zama kamar wadda *JINNUL-ASHIQ* ya aura, amma daga baya da tayi hak'uri saida
burinta ya cika na ganin Kdeey. Ina so ki nemi labarin *WATA SHARI'AH* ki karanta, nasan zaki
k'aru da abubuwa da dama a cikinsa. Idan kin gama kuma sai ki rakani mu d'auko labarin
*DAFIN SO,* Inda zakiga yanda soyayya ta miyar dashi kamar zautacce ko kuma ince kamar
mahaukaci.

Littattafan Amrah kenan, labarin *DAFIN SO* na nan zuwa maku insha Allah. DOle in
ambaceku kafin in rufe wannan littafin:
Asma'u Umar, Ummi Saddam and Ashnur Pyar, kunfi kowa son wannan labarin.

www.princessamrahh.blogspot.com

@instagram: miss_amrahmashi.

07037603276 for any correction or comment.

Amrah A msh, Also known as Princess Amrah kema kowa fatan alkhairi, Allah ya had'a
fuskokinmu a aljannah amin.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login