Showing 18001 words to 21000 words out of 56183 words

Chapter 7 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf

Advertisement


asibitin,
Ni na fad'a masu sunanki nayi signing a wata takarda sannan likitan daya fita d'in nan shida
wani guda suka hau dubaki,
Kullum sai munzo amma mu tayar baki farfad'o ba, saidai kuma likitan yana k'ok'arin kwantar
mana da hankali ganin yanayin halinda muke cikinsa,
Mun sanar da Gentle abunda ya sameki amma tsaki kawai tayi ko a jikinta,
Yanzu haka fitowarmu kenan daga exam d'in Bio1203, kuma munma HOD na Biology
complain cewa bakida lafiya, yace idan kinji sauk'i ki sameshi za'asan yanda akayi ayi miki".

Nannauyar ajiyar zuciya na sauke bayan Zarah ta gama bani labari, na j'ara tsanar Gentle
sosai a raina,
Sai yanu nake dana sanin amince mata ta dama k'awata, ga irin muguntar data bini da ita,
Na k'ara tuna nasihar da Babana yayi min akan in guji abotaka da yaran masu kud'i, bawai
duka aka taru aka zama d'aya ba, amma kuma wasu daga cikinsu basu da tarbiyya.
Gashi kuwa na gani da idona, naga kalar k'etar da babbar k'awata ko ince aminiyata tayi min,

To ba anan kad'ai abun ya tsayaba Aunty Sultana, duk ta wannan ma mai sauk'i ne akan
wasu abubuwan.





°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[3:22pm, 20/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*


{~63~}


Bayan sati d'aya na fara jin sauk'i, har zama na farayi sab'anin da da ko zaman ma bana
iyawa,
Sosai Dr. Rafiq yake bani kulawa, komai shi yakeyi min, hatta da magani da kanshi yake
siyamin ya bani ruwa insha,
K'awayena Zarah da Rabuatu kuwa tamkar 'yan uwana na jini, duk wani abu daya dace suna
yiminshi,
Abun haushi kuwa har yanzu Gentle batazo da dubani ba.

Kwatsam ina zaune Rabiatu da Zarah na gefena, labari muke sosai suna bani dariya, hakan
yasa hankalina yad'an kwanta, a gidanmu kuwa har yanzu basu sani ba, saboda Dr. Rafiq yace
kar in fad'a masu abunda ya sameni harsai idan na koma gida dan kar in tayar masu da
hankali.
Securities ne suka shigo roon d'in har mutum hud'u, bayansu kuwa wani babban mutum ne
sanye da babbar riga,
Bayan shigowarshi saiga wasu securities d'in guda hud'u a bayanshi.

Cike da girmamawa muka gaishesu,
Mutumin kawai ya amsa sallamar, tun bai rufe baki ba saiga wasu manyan mutanen sun shigo

masu yawan gaske, har room d'inma bai iya d'aukarsu ba wasunsu a bakin k'ifa suka tsaya.

Hankalina ya tashi sosai ganin manya manyan lecturers d'inmu ne,
Kallo suka bini dashi baki d'aya kafin sukayi min ya jiki,
Wancan mutumin wanda ya fara shigowa ya gyara zamansa a plastic chair d'inda yake zaune
yace
"Aisha Abubakar ko?"

Cike da mamaki na d'aga kaina alamar ehh,
"Good" ya fad'a tare da zaro wata 'yar takarda daga aljihunshi na gaba.

D'an rubutu yayi sannan ya mik'ata ga wani yace
"PA a ajiye min wannan" sannan ya juyo gareni yace
"Ya jikinki?"
Alhamdulillah na furta cike da alamar tambaya.

"Karki damu ba wata matsaka bace kinji, sunana Khalil MA Khalil" ya furta tare da mik'ewa
tsaye yabar d'akin,
Securities d'inshi ne suka nara masa baya sannan sauran malamn ma suka fita.

"Ya Salam" na fad'a sabida jin sunanshi,
Da fitarsu Zarah tayi ajiyar zuciya tace
"VC nefa da kanshi yazo dubaki Ummimah, lallai kin ciri tuta, wata k'ila sun samu labarin
abunda aka mikine sukazo dubaki",
Rabiatu tace
"To a ina zasuji labarin? Ke VC fa, wa zai fad'a masa? Kiga gayyar da sukayi fa".

Nidai saurarensu kawai nake amma fa sam hankalina bai kwanta da zuwansu ba.
Bayan kwana biyu aka gama exam aka rufe School baki d'aya,
A ranar nima na nemi sallamah, saboda Zarah da Rabiatu bana son na shiga hakkinsu, sunce
wai ba zasy tafi su barni ba.

Babu yanda Dr. Rafiq bayyiba akan inyi hak'uri in k'ara samun sauk'i amma kuma na nace sai
ya sallameni, hakan yasa ya bani takardar sallamah tare da kud'i masu yawa yace inyi kud'in
mota.

*****

K'arfe hud'u na rana na sauka Katsina,
Akwatina naja tare da tsayar da mai napep nace ya kaini Saulawa,
Babu b'ata lokaci kuwa muka isa gida.

Cike da farin ciki Afrah ta tareni, jakata ta karb'a tare da kaita d'aki,

"Afrah ina sauran 'yan gidan ne?" Na tambayeta bayan ta zauna tana min saanu da zuwa.

"Sun tafi sukai Amrah asibiti, booking zasuyi mata, insan ance wai nanda wata biyu ko uku
indiyawan nan zasy dawo".

Harda tsalle nayi dan murna, hakan yasa na fama ciwona sabida har yanzu raunukana basu
gama warkewa ba.

Saurin duk'ewa nayi ina matse matse,
Da tausayi Afrah tace min
"Bakida lafiya ne Aunty?"
Kai kawai na d'aga mata alamar ehh,
"Ayyah! Sannu gashi kuma kun gaji, kiyi wanka kafin nan na kawo miki abinci, nasan su Baba
ma yanzu suna hanya saboda tun safe suka tafi".

Haka na tashi jiki babu k'wari na nufi toilet,
Har ga Allah naji dad'in bayanin Afrah,
Bayan nayi wanka na jiyo muryar su Mama,
Aikuwa da sauri na saka kayana na nufi parlor ko mai ban shafa ba.

Har k'asa na gaishe dasu Baba,
Sunji dad'in ganina sosai Baba yace
"Wannan zuwa na bazata, baku fad'a mana zaki dawo ba ai",
"Ehh Baba, nafison nayi surprising nakune dama",
"Gashi kuwa kinyi ai hankalinki ya kwanta" mama ta fad'a tana kallona.
Baba ya k'ara yimin bayanin komai,
Naji dad'i sosai na matsa inda Amrah take,
"Sannu k'anwata, ya jikin naki?",
"Jiki da sauk'i Aunty Ummimah, ya karatu?",
"Alhamdulillah, Allah ya baki lafiya".

Bayan naci abinci nayi tunanin in fad'a masu abunda ya sameni amma kuma na fasa,
Da zarar nayi k'ok'arin fad'i sai wata zuciyar ta haneni,
Hakan yasa nayi shiru nabar maganar a cikina dukda cimin rai da takeyi.

Idan ma zaune nake na tuno da wannan abu sai hankalina ya tashi, kuka sosai nakeyi ni
kad'ai ba tare da kowa ya sani ba,
Wata rana ina cikin yin kukan Mama ta shigi ta sameni a haka,
Sallamah uku tayi amma duk bansan tayi ba,
K'arisowa ciki tayi ta ganni inata sharar kuka,
Hankalinta tashe ta tsuguna kusa dani tace
"Ummimah lafiya? Me sameki kike kuka?".

Zabura nayi tare da share hawaye ina fad'in
"Babu komai mama",
"Kamarya babu komai? Babu komai shine kike kuka?"
Gyara zama tayi sannan tace
"Nasan babbar matsakarki itace ciwon 'yar uwarki, dan Allah ki cire wannan damuwar, insha
Allahu k'arshen cutarta ya kusa zuwa, saboda muna sa ran nanda wata uku indiyawan nan zasu
dawo, kuma wannan karen ance zasu iya tafiya da marasa lafiya a k'asarsu, kinga kuwa insha
Allahu Amrah ta kusa rabuwa da cutarta har abada".
Goge hawaye nayi nace
"Shikenan Mama, Allah ya bata lafiya" na fad'a kamar da gaske abunda ya sakani kukan
kenan.

Murmushi tamin nima na miyar mata dana k'arfin hali,
"Kizo Afrah ta gama girki, nasan kina jin yunwa",
Tashi nayi nabi bayan Mama har parlor.

Satina biyu a gida Mama tamin maganar Gentle, gar saida gabana ya fad'i data ambata min
sunanta,
"Naji Salmah shiru kema kuma bakije inda takeba, Allah yasa dai lafiya",
Gabana ya fad'i na rasa abunda zan fad'a mata, sai daga baya nace
"Ta fad'a min cewa ba'a garin nan zatayi hutu ba, wai Kaduna zata tafi" nama Mama k'arya,
"Ahh to babu komai ai, Allah ya dawo da ita lafiya"
"Ameen" na amsa mata dashi cikin raina kuwa wata irin k'unar rai nakeji, saboda yanzu babu
wadda na tsana a doron k'asa kamar Salmah".

Sannu sannu har hutunmu ya k'are na fara haramar yin registration,
Da k'yar da wahala Baba ya samo min kud'inda zanyi,
Koda naje banki zan saka kud'in abun mamaki da zarar an saka password d'ina baya
bud'uwa,
An gwada kusan so biyar amma portal d'ina yak'i ya bud'u,
Zarah na kira a waya na fad'a mata abunda ke faruwa,
"Wannan ba matsaka bace, akwai sauran lokaci kuma kinsan akwai table payment, ki bari a
koma School sannan kawai ki biya acan, kinsan dama bank payment d'in nan matsalace dashi".

"Hakane k'awata, to nagode sosai".

Da haka na kashe wayata tare da ajiyeta k'asa.

Sati d'aya daya zagayo na fara shirin komawa,
Su Mama sunyi mamaki da sukaji nace masu ni kad'ai zan tafi,
Sallamah nayi dasu na nufu tashar mota,
Babu b'ata lokaci muka sauka cikin garin Jalingo.

Wurin biyan kud'in naje,
Abun mamaki ki acan d'inma babu sunana,
Abu wasa ba wasa ba har maganar taje sama,
Anan ne aka tabbatar mun da anyi expeling d'ina from the University, saboda kamani da akayi
da zubar da cikin shege,
An samu takardar asibiti wadda ta tabbatar da hakan, sannan kuma likitan daya dubani da
kanshi shi ya tabbatar daa hakan.

Take jikina ya d'auki rawa, bakina ya kasa furta komai, kaina ya ringa jujjuya min,
lummm na fad'i k'asa sumammiya.


_ayi hak'uri da wannan, ina fama da ciwon idone fitinanne, ina buk'atar addu'arku._




°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[11:40pm, 22/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*


{~64~}


_Na tayaki murnar kammala wannan littafin naki wanda ya ilimantar gamida fad'akarwa, lallai
littafin *HARAMTACCEN ZAMA* ya kawo darussa da dama, fatana a kullum Allah ya k'ara miki
baseera 'yar uwata ko ince aminiyata *(Rabiatu sk msh AKA Babymsh)* #onelove#_


*****

Tun daga nan ban k'ara sanin abunda yake faruwa ba, sai farkawa nayi na ganni kwance

kan gadon asibiti, gefena Zarah da Rabiatu ne sunyi tagumi suna jiran tsammani.

Kallo d'aya na masu suka bala'in bani tausayi, domin kuwa na k'ara tabbatarda sune
k'awayena na gaskiya wanda suke k'aunata.

Basu ankara da farkawata ba saidai shesshek'ar kukana sukaji,
Da hanzari kuwa suka mik'e tsaye, Rabuatu ta furta
"Alhamdulillah tunda kun tashi, sannu Aisha",
Kai kawai na d'aga mata ina hawaye sosai saboda k'ara tunowar da nayi wai yau nice aka
kora daga makaranta, an cuceni kuma an hanani kuka.

Zarah ta zaro d'an kwalinta daga kanta dake cikin hijabi ta mik'o min
"Bana son kina kukan nan Aisha, ya kamata ki d'auki k'addara saboda *KOWA DA
K'ADDARARSA,* ba wai Allah baya sonki bane yayi miki hakan, kawai dai *JARRABTARKI
KENAN* kuma ina fatan zakiyi k'ok'arin ki cinye wannan jarabawar,
Wanda suka cuceki kuma ki barsu da Allah shi zai miki sakayya, kiyi fatan Allah yasa hakan
shine mafi alkhairi a gareki, ungo wannan ki share hawaye" ta mik'o min d'an kwalin nata.

K'arba nayi na fara share hawaye saidai kuma da zarar na share sai wani ya fito,
Da k'yar na iya furta
"Babu komai k'awayena, na yarda na kuma d'auka cewa *K'ADDARATA CE* banida hanyar
maganceta, na barwa Allah komai saboda shine zai saka min, dan Allah wace asibiti nake?"
Zarah tace "inda aka kawoki ne last time, munje School clinic ank'i karb'arki sunce saboda wai
ke yanzu ba student bace".

Saurin mik'ewa nayi dukda ciwonda duk gab'ob'in jikina suke min,
"Na gwammaci in mutu akan in zauna a asibitin nan, Zarah mesa kuka kawoni nan? Kunsan
kuma irin sharrinda suka k'ullamin, su da kansu suka rubuta takardar k'arya cewa an zubarmin
da ciki, basu fidda takardar gaskiya ta cewa fyad'e akamin ba" na k'ara fashewa da kuka bayan
Rabiatu ta rungumeni a jikinta itama kukan take sosai tana k'ara jin tsanar Gentle a ranta,
saboda tasan duk sharrintane da makircinta.

Duk maganganunda mukeyi ashe a kunnen Dr. Rafiq ne, shigowa yayi jiki babu k'wari ya
nufo inda muke tsaye har yanzu ban saki Rabiatu ba,
"Ka fita daga nan bana son ganinka, kai mugune kuma munafuki, ka munafurceni ka
gwadamin kai mutumin kirkine ashe ba haka bane sai naga sab'anin haka, ka fita kafin in fasa
maka kai da kwalbarcan" na nuna kwalbar malt dasu Zarah suka kawo min.

"Nasan zayyi wahala ki yarda dani, amma dan Allah inaso ki ajiye hankalinki ki saurari
bayaninda zan miki" ya fad'a bayan ya k'ariso inda muke,
"Ki koma ki zauna har yanzu jikinki bayyi k'wari ba".
Cikin zafin rai na saki Rabiatu, a tsiwace nace
"Bazan saurarekaba Dr. Saboda bakada abunda zaka fad'a min in yarda dakai, wallahi ka

bani kunya, ka shirya k'arya kanaji kana gani bayan kuma ga gaskiya, to an koreni kun samu
abunda kuke so, sai kuji dad'inku da kyau kaida wanda suka sakaka" ina gama fad'in haka na
jawo hijabina na saka,
Hanyar fita na kama ina kallon yanda Dr. Rafiq yayi shiru alamar yaso in saurareshi amma
sam nak'i bashi damar yin magana saboda babu abunda zai fad'a min in yarda dashi.

Bin bayana Zarah da Rabiatu sukayi,
Purse d'ita Rabiatu ta bani tace
"Anata kiranki daga gida, ban d'aukaba saboda bansan abunda zan fad'a masu ba, bana son
tayar masu da hankali".

Karb'a nayi na zaro wayar daga ciki na danna kiran Baba,
Bugu d'aya ya d'auka hankalinshi tashe yace
"Aishatu ince dai lafiya kike, tun jiya nake kiranki inji ko kin sauka lafiya",
Gabana ya fad'i sosai na k'irk'iro murmushi,
"Na sauka lafiya Babana, wayar na jefa a cikin jakata can k'asa, sai yanzu na ganota",
"To masha Allahu, dama sauka lafiyar ake fata ai, ina Salmah kun had'u ko?",
Har wayar da Baba ma ji nayi bana so, tsinke wayar nayi kawaa naci gaba da kukana tare da
kashe wayar baki d'aya.

Bayan mun bar asibitin kai tsaye makaranta muka wuce,
A bakin gate na tsaya su kuma suka shiga ciki domin su kwaso min kayakina,
Ina nan tsaye saiga wata mota tayi parking a daidai bakin gate d'in kasantuwar ba'a barin
mota mai tint shiga cikin harabar makaranta,
Gentle ce ta fito sanye da irin skirt d'in nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login