Showing 12001 words to 15000 words out of 56183 words
Chapter 5 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf
(Jan. 2017)
*_In dedication to Aunty Sdy Jegalí ½í¸˜_*
{~51-60~}
A lokacin mun zama 'yan mata cikakku masu jini a jika,
Ba yabon kai ba ni kyakkyawa ce koda yake ba saina fad'a miki ba saboda kema kin gani da
idonki,
Sai a wannan lokacin diri na ya sake fitowa sosai,
Samari suka fara kawo min hari amma ni duk basa gabana,
Babban burina bai wuce inyi zurfi a karatuna ba, inaso in zama wata mai matsayi a b'angaren
education, hakan yasa ko a jamb d'ita na cike Bsc ed. Biology a Talent University Jalingo,
Itama Gentle shi ta cike dukda ba shine burinta ba, amma kuma saboda taga hakan nakeso
yasa itama tacewa mamanta lallai irin karatu d'aya take son muyi.
A duk family d'inmu babu waada baisan Gentle ba, haka itama kag family'nta kowa ya sanni,
Maganarta d'aya dai Aisha Abubakar, kullum Ummimah, har wasu daga cikin danginsu itama
suke kiranta da Ummimah sabida yawan fad'ar sunan da takeyi.
Afrah da Amrah kuwa an girma, yanzu sune suka shiga SS3, mu kuma muna jiran
sakamakonmu na jamb ya fito.
Bayan sati biyu kuwa ya fito, Alhamdulillah sakamako yayi kyau sabida samu 216, Gentle
kuwa 190 ta samu, amma dai lafiya lau babu matsala, saboda 180 akeso ko wane d'alibi ya
kawo,
Murna a wurinmu ba'a magana, har sadaka nayi saboda wannan sa'ar dana samu,
Babana kuwa Alhamdulillah! Yanzu company'n da yake ya d'an tashi, saboda har albashinsu
akan lokaci ake basu, dan haka mun saau warwawa sosai.
Amrah ta samu sauk'i sosai kamar bata tab'a yin ciwon ba, dan haka muka kasance happy
family bamuda matsalar komai duk da talaucinmu bai hanamu sakewa da walwala ba.
Cikin mun fara shirye shiryen fara registration ne kwatsam ciwon Amrah ya fara dawowa,
Iya tashin hankali mun shigeshi, saboda yanzu ya canja salo ma, harda jini take zubarwa
sosai babu cobtrol, ga wannan yawan shan ruwan nata, sannan kuma saurin mantuwa, yanzu
za'ayi abu yanzu zata mantashi,
Ta zama tamkar tab'ab'b'iya.
Hankalim baba ya tashi sosai, hakan yasa ya kama hanyar asibiti ya nufi wurin likitan daya
saba kula da Amrah,
Bayan ua shaida mashi halin da ake ciki ya dafe kanshi,
"Lallai yanzu ina ganin dole sai anyi aikin nan, saboda cutar ta fara zama chronic a jikinta, ina
mai shawartarku indai kunada damar fitar da yarinyar nan waje to ku fitar da ita tun wuri ayi nata
aiki, saboda inhar kuka zauna a haka da ita tofa zaku iya rasata".
Hankalin Baba ya tashi sosai, haka ya kamo hanya ya dawo gida babu nasarah,
Cike da tausayin Amrah yayi mana bayanin yanda sukayi da likita, kuma gashi yanzu ma wai
kud'in aikin sun k'aru, sun tashi daga miliyan biyu da rabi sun koma miliyan hud'u saboda kud'in
jirgi da suka k'aru.
"Allahumma ajirnaa fi musibati, wakhlifnaa khairin minha" kawai ke fita daga bakina, da muna
murnar Amrah ta samu sauk'i, sai gashi kuma ciwo ya dawo mata.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya kowace rana sai na karanta mata suratul Yaasiin a ruwa
tasha, hakan yasa ta ringa samun sauk'i sosai, amma kuma duk da haka bata daina zubar da
jini ba, duk bayan sati biyu sai anyi nata k'arin jini.
Da daru da komai na tafi makaranta, da nace bazanje ba saidai inyi asarar admission d'in,
nayi niyyar sama in kula da 'yar uwata,
Saida Baba ya kirani yace
"Bai kamata kiyi hakaba Aisha, wannan karatu da kika samu wata damace wadda bai kamata
ki bari ta kufce miki ba, idan kuma kika bari ta kufce miki tofa samun dawowarta ba abune mai
sauk'i ba,
Kinga da yanda nayi na had'a kud'in registration d'inki,
Sannan kuma zamanki a gida ba shine zai warkar da Amrah ba, kiyi hak'uri ki tafi makaranta,
ki ajiye hankalinki kiyi karatu, insha Allahu Amrah zata samu lafiya, ki cire duk wata damuwa a
ranki, na siyo miki komai da zaki buk'ata suna d'akin mamanku na ajiye jiya dana dawo na samu
duk kunyi bacci".
Wani irin hawayene ya k'wace min, bana komai bane face na tausayin Babana, ya gwammaci
ya rasa komai ya kyautata mana, ya gwammaci ya kwana da yunwa mu kuma ya ciyar damu,
ya gwammaci ya k'ask'antar da kanshi ga mutane duk dan ya samu abunda zai rufa mana asiri,
lallai iyayenmu abun muji k'ansu ne, bai kamata muna wulak'anta iyayenmu ba, wai har sai
kaga yaro babanshi yana magana shima yana magana.
Hak'uri Baba ya ringa bani har saida yaga nayi shiru, da yake mutum ne mai barkwanci saida
ya sakani dariya sannan yabar d'akin.
Bayan kwana uku kuwa na kama haramar shiri,
Su Gentle sukazo saboda munyi da ita tare za'a kaimu a motar gidansu,
Dan haka da sauri ta shigo tace in fito ana jiranmu.
Hak'uri na bata akan tayi min uzuri in jira dawowar Baba, saboda yace in jirashi akwai sak'on
da zai kawo min bazai dad'e ba.
Ba tare da nuna gajiyawarta ba ta zauna har baba ya dawo,
Bawan Alkah ashe waya ce 'yar baby nokia yayo min fafutukarta harda sim card na MTN,
Wani hawayen na sakeji amma ban barshi ya fito ba,
Har k'ifar gida suka fito rakiyarmu, ciki kuwa harda Amrah dake kukan tafiyata.
Shiga motar mukayi gidan baya nida Gentle, kasantuwar driver d'in gidansu ne yasa babu
wanda ya zauna a gaba,
Suna d'aga min hannu har motarmu ta fita daga kwana.
Sai a lokacin kuka ya fito min,
Sosai Gentle ke rarrasata amma nak'i uin shiru har sai lokacin dana gaji dan kaina sannan
nayi shiru.
Kusan awa shida muka d'auka sai gamu a cikin Jigawa, sosai garin ya burgeni saboda
yanada kyan tsari sosai,
Har cikin makarantar aka kaimu, dama mun kama room dan haka wurin securities na
hostel mukaje, number'n room d'in muka fad'a sannan aka bamu key aka shaida mana akwai
katifa da gado a ciki.
Gentle ta umurci driver d'insu daya tafi kawai, mu kuma muka kwashi kayakinmu muka ringa
nufar block B dasu, babban haushin ma wai 3rd floor muke, na tsani hawan bene a rayuwata,
Saida mukayi zarya uku sannan muka gama kwasar kayanmu,
Salloli na fara gabatarwa, nan ma saida nacema Gentle ta tashi tayi sallah sannan tayi.
Aunty Sultana wallahi ban zaton Gentke zata saka min da abunda tamin ba, ashe babu
alkhairi a zuwana wannan jami'ar" Ummimah ta fashe da kuka,
Koda ta farga ashe Barrister Sultana ma ta dad'e da fara kukan, tun lokacin da Ummimah ke
fad'a mata ciwon Amrah ta fara kuka.
Da k'yar ta samu ta share hawayen tace "ina jinki kici gaba".
"Bayan mun huta na saka wayata a chaji, tana jikin chajin na kunnata, koda na saka layina
ashe harda katin dari biyu baba ya saka min, dan haka lambarsa kawai na saka dan inada ita a
kaina,
Ringing d'aya tayi kuwa ya d'auka, cike da farin ciki yace "'yata Aisha",
Murmushi nayi nace "sannu baba, ya gida yasu mama?",
"Lafiya k'alau kun sauka lafiya?",
"Alhamdulillah baba, mun dad'e da sauka harma mun huta",
"To masha Allah, ki gaishe min da Salmah d'in",
"To zataji baba, ya jikin Amrah",
"Amrah taji sauk'i sosai, gobe ma zamuje a k'ara mata jini",
"To baba Allah ya k'ara mata lafiya, a gaishesu duka" nayi hanging up na wayar, na fad'a ma
Gentle sak'on Baba na gaisuwa.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya mana, muna karatu sosai har first semester ta k'are muka
koma gida, kasantuwar hutun bashida yawa nan da nan muka koma School,
Wannan komawar ce baki d'aya Gentle ta canja halinta, ta xama mace maras kamun kai, duk
mazan course mates d'inmu babu wanda bata huld'a dashi musamman ma irin 'yan iskan nan
masu sauke wando k'asa.
Har ni d'inma ta fara canja min fuska, kuma da zarar na mata magana sai ta nunar da babu
ruwana da halinta, inyi irin ruyuwar da nake so itama in barta tayi wadda take so,
Wannan canjin da tayi yasa wani lokaci in zauna in yita kuka,
Saboda har k'awancen ma ta daina yinshi dani,
Ta samu wasu 'yan iska sune abokananta.
Wata rana mun tashi lecture 2pm,
Tun fitata daga theater nake jiran Gentle ta fito mu tafi amma shiru batazo ba, gashi kuma ina
azumi saboda ranar Monday ne, ga rana kuma anayi.
Jinta shiru yasa na koma Theater d'in, a tsakiyar maza na sameta sai kashewa suke suna ihu,
Jiki ba k'wari na matsa inda suke nace "ke bake jira Salmah kin san azumu nake",
Bud'ar bakinta tace "toni ina ruwana da azumin da kikeyi? Nace ki rakani ne iye? Ko kuma
bansan hanyar hostel d'in ba?".
Da tsawa tayi maganar, tunda nake da ita bata tab'a yimin magana irin haka ba,
"Ki tafi ai nima nasan hanya, wannan ma ai kilbibi ne ace wai dole sai tare dani za'a tafi",
Shewa abokan nata maza da mata suka saka, bansan lokacinda naji hawaye suna fita daga
idona ba,
Ban kuma fad'ar komai ba na fita na nufi hanyar hostel ni kad'ai ina mamakin sauyin hali da
Salmah ta samu lokaci d'aya.
Bayan kwana biyar muka fara second semester exam, sam Gentle bata miyar da hankalinta,
karatun ma bata sama barin tayishi.
Wata ranar alhamis wadda bazan tab'a mantawa da ita a rayuwata ba, ta zame min bak'ar
rana abun gudu ga kowane mutum.
Zaune nake ina karatu kasantuwar wata chemistry exam da zamuyi gobe jumu'ah,
Course d'in yanada matuk'ar wahala kuma gashi 4 unit ne, amma sam ni bana jin wahalarsa
saboda na iya kuma bana missing lecture d'in,
Gentle kuwa ban tab'a ganinta ta zauna lecture d'inshi ba, ko magana na mata saidai ta bini
da bak'ar magana.
Ji nayi bazan iya zama ba ita kuma bata iya ba dan bana son ta fad'i a course d'in.
Block A na tafi nemanta wurin wata k'awarta amma k'awar ta bini da kallon banza,
Saida ta gama sannan tace "ta tafi wurin saurayinta AK" ta fad'a tak'aice.
D'aukar hanyar fita daga hostel d'in nayi na nufi inda naga masu samari suna tsayawa fira.
*_ina miki murnar kammala novel d'inki mai suna DAWA ZANYI KUKA?, tabbas kin cancanci
a yaba miki saboda novek d'in yayi ma'ana sosai, Allah ya k'ara miki baseerah Aunty'nmu (Sdy
Jegal)_*
°•°AKA°•°Princess Amrahí ½í¸˜
NWA
[2:25pm, 18/01/2017] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: *WATA SHARI'AH* í ½í¸ª
í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“
í ½í¸ª
Na Amrah A Mshí ½í²“
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)
*_In dedication to Aunty Sdy Jegalí ½í¸˜_*
_Da gudu na taho har ina cin tuntub'e saboda makarar da nayi wurin mik'a jinjina tare da yabon
gwanata kuma namesyna *Futhatul-Khair* akan daddad'an littafinta mai taken *k'awata
kishiyata,* da jin sunan ma ba sai an fad'awa mutum kalar ma'anarsa ba, dan haka na tayaki
murna, sannan kuma na miki fatan Allah ya k'ara miki baseerah da kaifin ido #onelove#_
{~61~}
Fitilar hannuna na ringa haska motocin gaban gate d'in, amma kuma duk wadda na duba
babu Gentle a cikinta,
Dan haka na k'ara matsawa daga gaba ina hahhaskawa still dai babu ita,
Cike da tashin hankali na kashe fitilar wayar tawa, na latsa kiranta saidai kuma naji ana
shaida min da babu kud'i kona flashing a wayar,
Hankalina ya k'ara tashi, kamar zautacciya na ringa k'wala mata kira amma shiru ne.
Har kusan Faculty of Humanities naje da yake shine daga gate d'in hostel babu nisa saishi
amma babu ita,
Motoci biyu na hanga daga can nesa aikuwa babu shamakin komai na doshi wurinsu,
Dalle fitilar nayi ata farkon amma sai samari matasa na gani cike da motar, zasu kai kimanin
mutum takwas zuwa goma, harma mamakun yanda motar ta d'aukesu nayi,
Hak'uri na basu sabida naga kamar basuji dad'in haskewar ba.
"Ke ubanme yasa kika haskemu da fitila? Ko mu sa'anninki ne?" Wani daga cikinsu ya
tambayeni cike da muryar maye, alamar yasha ya bugu sosai.
"Kuyi hak'uri 'yar uwata na fito nema ne, nayi zaton ko itace anan" na fad'a cike da tsoronsu
bayan na doshi inda d'ayar motar take.
Basu kuma cemin komai ba har na isa wurin d'ayar motar,
Haske cikinta nayi saidai kuma banyi sa'ar kallo ba,
Saboda mace da namiji ne a bayan motar sunata aikata alfasha gasu tsirara haihuwar
uwarsu,
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" Kawai na fad'a cike da tashin hankali, saboda sam basa
cikin hayyacinsu sun lula can wata duniyar.
Har nayi shirin juyawa zan tafi naci tuntub'e da takalmi,
Haskawa nayi saboda harda shirin kadani yayi,
Cike da mamaki na kalli takalmin na k'ara kallonshi,
"Wannan ai takalmin Gentle ne" na fad'a a fili bayan na tsuguna k'asa ina k'are mashi kallo,
Daga cam gefe na hangi gyalenta da d'ankwalinta,
"Ya Salam" na sake furtawa saboda sam ganin abun nake kamar a mafarki.
Tamkar bana cikin hayyacina na koma jikin gilashin motar na ringa bubbugashi da k'arfi,
saboda ni a tunanina kota k'arfi da yaji ne aka turata cikin motar.
Duk bubbugawar da nakeyi shirune sabida har yanzu basu dawo hayyacinsu ba,
K'afar takalmin nata d'aya na fara bubbuga gilashin dashi take kuwa suka zabura su duka
biyun a tare,
Da sauri mazan dake cikin waccan motar sukayi wurina,
"Waike wace irin sakaryar yarinya ce? Ubanme kike a wurin nan? Ina ruwanki dasu?" Wani
daga cikinsu ya fad'a kamar zai fad'o min,
Saurin matsawa nayi gefe hannuna aka ina tsala ihu ina fad'in "jama'a ku taimaka mana, sun
tura 'yar uwata a cikin mota",
Kasantuwar babu giccin kowa yasa babu wanda yajimu,
Da hanzari cike da kunya macen ta miyar da kayan jikinta bayan namijin ya sauka daga
gareta,
Fitowa daga motar sukayi su duka biyun suna tambayar abunda ya faru.
Gaba d'aya wutar kaina ta d'auke lokacin dana d'ora idona akan Gentle sai rarraba ido take
tana fad'in "wai miye haka kukeyi Khalifx? Muna tsaka da jin dad'inmu zamu nemi tsayar damu"
har a lokacin bata kula dani dake gefe ba ina binta da kallon mamaki.
Cike da tashin hankali nace "Salmah! Kenan da saninki kika shiga motar nan ake aikata
alfasha dake?",
K'are min kallo tayi ta tabbatar da nice sannan cikin halin ko in kula tace
"Ehh da sanina ne sai kuma me? Ke Aisha bari kiji in fad'a miki, tun wuri ki fita daga sabgata
idan ba haka ba kuma wallahi ni kad'ai nasan matakinda zan d'aukar miki".
Kallonta nayi cikin ido saboda an kunna security light na cikin makarantar,
"Kiji tsoron Allah Salmah, ki sani iyayenki da suka kawoki makarantar nan fa sun damk'a miki
amanar kanki, idan kikaci amana kuwa sai amana ta kamaki, zina Salmah? Wal'iyadhu billah!
Da idona na ganki kina aikatata, sam banyi tsammanin halin naki har yakai