Showing 9001 words to 12000 words out of 56183 words

Chapter 4 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf

Advertisement

dan kinsanta
ita tsoron bulala gareta".
"Mama bazan iya tafiya in bar Amrah a haka ba, na fasa zuwa kawai",
"To shikenan ai, kekam wannan soyayyar da take tsakaninki da yarinyar nan tayi yawa,
zanga ranar da zaku rabu da junanku, ko kuma ranar da mutuwa ta d'auki waninku tabbas
zakusha wahala".

Wani irin hawaye naji yana bi min kumatu a lokacin da Mama ke wannan maganar, cike da
tashin hankali nace "dan Allah mama kibar wannan maganar, muyi mata fatan Allah ya bata

lafiya".

Da haka har dare yayi, bayan sallar isha Baba ya dawo daga masallaci,
Lokacin kuma Amrah ta d'an samu relief dan har ta fito palor amma dai duk da haka batada
wata walwala.

Bayan Baba ya gama cin abinci ne na masa maganar rashin lafiyar Amrah,
"Baba dan Allah idan ka samu kud'i ayi k'ok'ari ko chemist ne a kaita ayi mata awon jini dan a
gane ciwonta".

"Hakane Ummimah, insha Allahu gobe zan tafi da ita wurin aikina, zan kaita wurin wani uban
d'akina wanda a k'ark'ashinshi nake aiki, zan gwada mishi ita insha Allahu indai ya ganta nasan
zai tausaya mata, sai ya taimakemu da kud'in da zan kaita asibitin saboda yana da matuk'ar
taausayi, ko kud'in dana baki jiya kika biya maku kud'in islamiya na wata biyu da ake binku
shine ya bani su ".

"To shikenan Baba, Allah ya kaimu goben, Allah kuma ya bata lafiya" na fad'a cike da
tausayin mahaifina, saboda nasan duk wata wahala da yakesha duk saboda mune, babban
burinshi shine yaga ya sakamu cikin farin ciki, baya so ya gammu muna buk'atar wani abu shi
kuma bayada halin yi mana abun". Ummimah ta fashe da kuka bayan tayi wannan maganar.

Barrister Sultana ta kalleta sosai sannan tace "bazan hanaki kuka ba Ummimah, saboda
bansan abunda aka miki ba, ban kuma san dalilin kukan ba, amma dan Allah ki daure kici gaba
da yimin bayani ko zan samu bayanin da nazo nema a wurinku".

Bayan ta share k'wallarta taci gaba da,
"washe gari kuwa da sassafe baba ya tafi da Amrah wurin aikinshi, duk da jarabawar da
gareta a ranar da safe,
Mun yanke shawara akan ni zanje in rubuta mata jarabawar saboda ba lallai bane a iya
banbancemu, duk da kamar da Afrah da Amrah keyi amma nafi kamada Amrah, tsaf wanda bai
sani ba zai iya cewa nice twin sister d'inta ba Afrah ba, musamman ma yanda na shak'u da ita,
duk wata shawara ko matsala da gareni ita nake sanarwa kafin kowa ya sani. Hakan kuwa ta kasance, ni na rubuta mata jarabawar kuma ba'a ganeba har aka gama muka
koma gida,
Nikam nama manta da maganar Gentle, kwata kwata ban tab'i mama da maganar ba saboda
nikam rashin lafiyar 'yar uwata shine damuwata a halin yanzu.

Da yamma lik'is Baba ya dawo, kallo d'aya za'a masa asan baya tare da walwala, da k'yar
Amrah ta iya sauka daga kan tsohon mashin d'in baba,
A hankali take tafiya har suka shigo cikin d'aki,
Da sauri na tashi na nufi inda take na rirrik'eta na zaunar da ita akan kujerar dana sauka, ni
kuma na zauna k'asa ina kallonta cike da tausayi,

"Sannu Amrah, ya jikin naki?",
"Alhamdulillah" ta fad'a bayan ta kwanta ta duk'unk'une jikinta akan kujerar.
"To Allah ya baki lafiya, sannu kinji? Na rubuta miki jarabawar yau kuma lafiya lau ba'a samu
matsala ba",
D'aga min kai kawai tayi ba tare data fad'i komai ba, jikinya sai rawa yake, jijiyoyin kanta duk
sun tashi, idonta sun k'ara girma sosai dama abunka ga mai manyan idanuwa.

"Babansu ya ake ciki ne?" Mama ta fad'a tare da zama kusa dashi, saboda a yanayin data
ganshi ciki tasan akwai matsala, amma ita a tunaninta ko kud'in da zai kai Amrah'n asibiti ne bai
samu ba.
"To lafiya lau zance" ya fad'a bayan ya sunkuyar da kanshi k'asa.
Da jin haka gabana ya fad'i, dan nasan tunda baba ya fad'i haka to akwai matsala.

"Wanda nake fad'a maku zai taimakeni d'in ya taimaka mana, ya kaimu asibiti kuma asibitin
ma ta kud'i, ya biya kud'in duk wasu test da akayi mata,
Amma kuma bayan sakamakon ya fito ne hankalina ya tashi,
Saboda Amrah tana d'auke da wata cuta a cikin k'wak'walwarta wadda ake kira da *brain
tumor,* likitan yamin bayani sosai akan cutar tare da illolinta.
Yace min cutace wadda take uncontrolling na cell division na mutum,
Cutar bata tsananta ba sosai a jikinta, dan haka yasa mukaga iya alamar hakan a tattare da
ita,
Idan tayi tsanani sosai tana saka mutum shan ruwa sosai babu control, ya gwada min wani
bokiti plastic yace min zata iya shanye baki d'ayanshi ba tare da taji ya isheta ba, sannan kuma
fitsari ma babu control zata ringa yinshi, komai dai zai koma mata babu control tamkar
mahaukaci, sannan kuma yana hana haihuwa, yayi mamakin yanda cutar ta kama Amrah 'yar
shekara goma sha uku, saboda sai manyan mutane take kamawa, yace shi tunda yake ma bai
tab'a ganin ta kama mai k'ananan shekaru kamarta ba.
Amma da sauk'i tunda abun baikai haka ba, yace min hanya d'ayace wadda za'abi dan ganin
cutar batai tsawo kamar haka ba,
Saidai idan za'a fitar da ita k'asar waje a fidda mata ita, idan aka fitar da ita kuma akwai wani
magani wanda za'a d'orata a kanshi,
Duk bayan sati biyu maganin yake k'arewa, kuma an sameshi da sauk'i to dubu talatin da
biyar idan ma an samu a k'asar nan kenan saboda maganin Indiya ne ba'a cika kawoshi Nigeria
ba, kati biyu ne a cikin wani kwali, duk sati d'aya ake shanye kati d'aya.
Wannan maganin shi zata ringa sha har k'arshen rayuwarta saboda ko an cireshi idan ba'a
shan maganin to cutar tana iya sake yib dashe a cikin k'walwa, idan ba haka ba kuwa to komai
zai iya samunta idan cutar ta tsananta a jikinta".

Tunda Baba ya fara wannan maganar nake kallonshi,
Ji jake tamkar a mafarki ne da nafi kowa farin ciki.
"Yaa Salaam" Mama ta fad'a hannunta dafe a k'irjinta.
"Allah gamu gareka, Allah ka fitar damu daga wannan jarabawar" ta fashe da kuka mai cike
da tsananin ban tausayi.

Mutuwar zaune kawai nayi, kukan baizo ba and i was totally speechless,
K'ara kallon Amrah nayi cike da tausayinta,
Yarinya k'arama 'yar shekara sha uku ce a cikin wannan hali,
Sai a lokacin naji wani irin kuka maras control yazo min,
Na d'ora hannuna bisa kai inata sharar kukana, Afrah ma kukan take, Mama kuwa dama tun
sanda baba yake maganar ta fara kuka.
Shi kanshi Baban hawaye ke zarya a bisa kumatunshi, ya kasa ko rarrashinmu ma,
Babban tashin hankalinshi bai wuce inda zai samu har miliyan biyu da rabin da za'ayiwa
Amrah aiki ba, kuma ma idan ya samesu ina zai samu kud'inda duk bayan sati biyu za'a ringa
siyama Amrah magani?.

Ita kuwa Amrah baccinta take batama san abunda ake ciki ba, sai wannan zafin jikin wanda
baya yin sauk'i, idan tasha pain reliever ne yake d'an kwanciya na awa d'aya kuma sai ya dawo,
ga yawan yin amai da takeyi, wani irin kuka na sake fashewa dashi had'e da rungumarta na
mak'alk'aleta har saida ta tashi daga bacci.



°•°AKA°•° Princess Amrah😘
NWA
[3:54pm, 16/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪


Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)



*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*


{~41-50~}


A gigice ta farka cike da azabtuwar ciwo, ganin ina kuka yasata k'ara k'ank'ameni itama tana
kukan,
"Aunty Ummimah ki daina kuka ai naji sauk'i, tunda Baba ya saimin panadol nasha zazzab'in
ya sauka, ki kwantar da hankalinki, idan kuna kuka nima sai kisani in ringayi".

Wani kukan maras control ya sake fito min da k'arfi, kenan Amrah bata san cutar da take tare
da ita ba? Allah sarki baiwar Allah, Allah ya bata lafiya. Fatan da nayi mata a raina kenan bayan
na saketa nace,
"Barin kawo miki abinci nasan bakici komai ba".
Da hanzari Baba ya share hawayensa dan baya so mu fahimci cewa shima kukan yayi,
"Ki duba booth d'in mashin d'ina akwai yoghurt na nan ki kawo mata, nasan zata fi buk'atar
abu mai ruwa ruwa".

Tashi nayi kuwa na nufi inda mashin d'in yake,
Bayan na bud'e booth d'in na fiddo yoghurt kai tsaye na wuce palor,
Bud'eshi nayi na juye a kofi na fara bama Amrah,
Saida tasha kamar rabin kofin sannan na sauke shi k'asa,
Kamar tana jirana kuwa sai amai ta fara kwarawa babu sassauci, saida ta harar da komai
dake cikinta sannan cike da azabar ciwo ta koma ta kwanta,
Hawaye naji sosai suna fita daga idona,
Cikin natsuwa na dangwali ruwa a hanky na goge mata bakinta sannan na fara gyara jikina,
Har a lokacin Mama da Afrah basu daina kuka ba, kowansu tana tausayin halinda muka tsinci
kanmu a wannan yanayi.

Bayan na gama gyaran wurin duka na koma kan kujerar na d'ira fuskar Amrah akan cinyata,
baki d'aya zazzab'i mai zafi ya taso mata,
Kuka nake sosai amma maras k'ara, hawayena ne ya sauka bisa kumatun Amrah,
K'ok'arin tashi zaune tayi amma ta kasa,
Ganin haka yasa na tasar da ita zaunen ta fuskance ni,
"Dan Allah ki daina kuka Aunty Ummimah, na fad'a miki naji sauk'i fa, yanzu ma aman da
nayi ne yasa zazzab'in ya sake dawowa".
Goge hawayen nayi tare da yi mata murmushin yak'e, itama murmushin tayi sannan ta koma
ta kwanta a bisa cinyata,
Mama da Afrah kuwa barin d'akin sukayi dan basa so ta fahimci kuka sukeyi.

Bayan sati biyu.

Zaune muke ina bama Amrah abinci a baki,
Kwatsam naji sallamah da muryar mace babba sai kuma d'ayar muryar kamar ta budurwa,
A lokacin Afrah ta tafi islamiya Baba kuma bai dawo daga wurin aiki ba,
Mama kuma tana d'akinta tana fitar da kayan wanki.

Amsa sallamar nayi tare da ajiye abincin a k'asa,
"Maraba daku, ku shigo daga ciki".

Babbar macen ta fara yi gaba sannan budurwaw ta shigo,
Murmushi na saki a lokacin dana Gentle, itama murmushin ta miyar min dashi,

Kamarsu d'aya ita da babbar matar hakan ya tabbatar min da mahaifiyarta ce,
Sauke Amrah nayi daga bisa jikina na gaishe da matar,
"Ahh Salmah kune a gidan namu?,
"Wallahi kuwa mune Aisha, na jiki kwana biyu bakizo School ba, shine naje har Principal's
Office ya duba min address d'inki,
Nayima Momy na bayaninki sai tace zata biyoni mu duba ko lafiya kike, shine fa kika gammu
da yammacin nan".

Murmushi na mata sannan nace "Amrah baki iya gaisuwa bane?",
Jiki babu k'wari ta duk'a har k:asa ta gaishesu,
Bayan sun amsa ne Mama ta shigo saboda muryoyin da taji,
Fuskarta d'auke da fara'a suka gaisa da Momy,
Nayi ma Mama bayaninsu da kuma dalilin zuwansu,
Sannan kuma nayima su Gentle d'in bayanin rashin zuwana makaranta,
Sun tausaya mana sosai sun kuma tausayawa Amrah,
Sai yamma lik'is sannan Momy ta bama Amrah 10k cike da tausayi suka bar gidan.

Sosai Momy ta yaba da kirkinsu, hakan yasa ta amince min da yin k'awance da Gentle, koba
komai tanada hankali, sannan kuma tanada kula itada mahaifiyarta.

Tun daga wannan lokacin kusan kullum sai Gentle ta ziyarce mu, hakan ba k'aramin dad'i
yake min ba,
Wannan kular da take mana ita ta siye min zuciya baki d'aya, naji Gentle ta kwanta min a rai.

Saida mukayi wata d'aya a haka, lokacin har na gama rubutama Amrah jarabawa, hakan
yasa na koma makarantata, ammafa rabin karatun da nakeyi hankalina yana gida, ina matuk'ar
tausayin 'yar uwata, saboda yanzu ciwon k'ara yawaita kawai yake, kuma gashi babu ko
maganar *kud'in aiki* (Raheem and Basmah err lele) barin kud'in magani, saisa a kullum na
zauna banida aiki sai kuka.

Wata rana cike da murna Baba ya dawo daga wurin aiki, kallo d'aya na masa na gano farin
ciki a tattare dashi,
Da sauri na karb'i ledar hannunshi,
"Balango ne na gani a hanya na siyowa maras lafiya, idan taci sai ta baku sauran",
Murmushi nayi na fara bata a baki,
Bayan Mama ta shigo d'akin tayima Baba sannu da zuwa,
"Nazo maku da albishir mai girma, amma fa sai kun bani goron albishir",
Murmushi d'auke a fuskata nace "ka fad'a mana koma menene Baba, zan baka goro babba".

"Yanzu na dawo daga wurin likitan da yake duba Amrah, ya tabbatar min da cewa gwamnati
ta kawo manya manyan likitoci daga India, wanda zasu duba narasa lafiya wanda suke d'auke
da ko wace irin cuta kuma kyauta bada ko sisi ba, zasuyi wata uku sannan su koma k'asarsu,
Dan haka ya bani form d'aya na cike da sunan Amrah, nan da sati d'aya zasu fara aiki".

Hamdaka muka saki mu duka dake d'akin, harda Afrah da yanzu ta shigo ta tsinci zance,
Amrah kam dama bata san ciwon da yake damunya ba, tayi zaton zasu dubata ne kawai akan
yawan ciwon da takeyi.

Shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanina da Gentle, ta kaiga bani b'oye mata ko wace irin
damuwa haka itama bata b'oye min tata damuwar,
Saidai a iya zamana da ita na fahimci sam ibada bata dameta ba, amma dai ina k'ok'arin
nunar mata da muhimmancin ibada,
Saidai kuma a duk lokacin da zan mata maganar ibada sai ta b'ata rai, wani lokacin ma ba
zata sake min magana ba har a tashi daga makarantar.
Sam hakan baya sa indaina fad'a mata gaskiya.

Yanzu kam mun d'an samu kwanciyar hankali har sati ya zagawo,
Baba da Mama da kansu suka kaita FMCK saboda acan ne za'a gudanar da taron likitocin.

Likitici biyar suka hau kan Amrah, da manya manyan na'urori suke amfani wanda suke
haska mata baki d'ayan k'walwarta,
Sun tabbatar da brain tumor ce take d'auke da ita, saidai kuma bata tsananta ba,
Dan haka akwai wani gashi da za'a ringa kaita na tsawon wata uku, duk bayan sati za'a ringa
gasa mata k'walwarta sannan kuma akwai wani ruwan allura da za'a ringa duba mata a hanci
shima dai duk satin ne,
Sannan kuma sunma baba bayanin ba lallai bane idan akayi haka cutar ta rabu da ita har
abada, amma kuma zata samu sauk'intana wasu shekaru.

Duk da hakan Baba yaji dad'i yayi masu godiya sannan suka kama hanyar dawowa gida,
Lokacin da Baba yaimana bayani ba k'aramin dad'i mukaji ba, har da sadaka saida Baba yayi
duk da shima mabuk'aci ne.


Bayan shekara uku

*******
Pls kuyi hak'uri da wannan page d'in yayu gajerta, bana jin dad'in jikina ne, luv you all.





°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[1:20pm, 17/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓

😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login