Showing 51001 words to 54000 words out of 56183 words

Chapter 18 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf

Advertisement

forcing d'in Dr. Khalid akan ya amsa abunda
bashi yayi ba, ya fad'a mata cewa wannan sugning d'in ba nashi bane amma kuma ita tayi
insisting akan nashi ne bayan kuma batada wata hujjar data tabbatar fa hakan" Barr. Sa'eed ya
fad'a jin ana neman k'ure Dr. Khalid.

"Barr. Sultana a kiyaye" alk'alin ya fad'a tare da miyar da kallonshi ga Sultana.

"Iyakar tambayar da zan masa kenan ya mai shari'ah" ta furta had'e da komawa mazauninta
ta zauna.

"Ko akwai mai magana a cikin sauran lawyers d'in" alk'ali ya tambaya.

Tasowa Umar yayi ya gyara zama hularsa yace
"Sulaiman Usman Saraki, Yusuf Bilal Mohd, kotu zata so ganinsu idan suna kusa".

Daga k'ofar shigowa sarki Manu ya shigo, a bayanshi kuma gado ne irin wanda ake d'ora
marasa lafiya d'in nan,
YB ne kwance cikin gadon duk yabi ya lalace kamar bashi ba.

Ido bud'e Gentle ke kallonsu,
Ko a mafarki bata tab'a tunanin wannan rana ba,
Shikenan yau tasu ta k'are, asirinta zai tonu kenan,
Gabanta sai dukan uku uku yake ta kasa rufe bakinta,
Tunani take waima ya akayi hakan ta kasance?,
D'an marin kanta take wai idan ma barci takeyi ta farka.

A k'asa aka ajiye gadon kusa da Ummimah, Gentke kuwa tasha mamkin halin da taga YB
ciki,
K'yafta masa ido kawai take tare da d'an murmushin yak'e wanda da k'yar take fiddoshi.

Gyaran murya Umar yayi yace
"Sarki Manu kotu zata so jin cikakken sunanka, garin daka tashi, sannan kuam menene
alak'arka da Salmah Gentle?".

Tuni Gentle ciki ya d'uri ruwa, zawayi take ji amma babu halin tace zatayi,
Sai raba ido take tana kallon mahaifinta sannan kuma ta juya ta kalli lawyer'nta.

"Sunana Sulaiman Usman Saraki, zan iya cewa na d'an tab'a rashin ji a baya kafin Allah ya
shiryeni yanzu, alak'ata da ita kuwa ita budurwar wani abokinmu ne Abdul K'adir amma duk da
AK muke kiransa".
"Ko zaka iya yima kotu bayanin yanayin tarayyar Gentle da saurayin nata AK?",
"ehh zan iya mana, yana sonta tana sonshi sosai, harma son da take masa yafi wanda yake
mata yawa, hakan yasa ya rainata sosai saboda yaji tana yawan fad'in ba zata iya rayuwa idan
babushi ba,
Babu abunda zai nema a wurinta ya rasa, zina kuwa sun miyar da ita tamkar abincinsu, sun
zama kamar miji da mata, abun nasu har a cikin makaranta yinshi suke kuma kusan kowa ya
san da hakan,
Wata rana...." ya basu labarin avunda ya faru ranar da akayima Ummimah fyad'e.

Salati duka mutanen dake cikin kotun suka d'auka,
Alhaji Abu Abu kuwa sai cire hula yayi, dukda sanyin da akeyi amma shi zufa yakeyi tsabar
kunya da yaji, gashi d'an siyasa sananne kuma a gaban jama'a wannan abun yana neman ya
kasance.

"K'arya kakeyi wallahi ni banma sanka ba? A gidan uwarwa ka sanni? Kaji min mutum da
sharri, ko tab'a ganinka banyi ba amma kake fad'in haka, ya mai shari'ah karka yarda dashi
wallahi k'arya yake".

Daka mata tsawa alk'ali yayi had'e da buga teburinshi,
"Karki manta nan kotu ce ba wurin shirme ba, ki nemi izinin magana idan kina son kiyi ba wai
ki sakota haka ba".

Shiru tayi gabanta sai fad'uwa yake,
Ji take tamkar k'afarta ba sata iya d'aukar gangar jikinta ba.

Ga YB umar ya koma yace
"Me zaka iya fad'i game da maganganun da Sarki Manu yayi?"
Cikin muryar ciwo YB yace
"Babu k'ari ko kad'an a bayananshi,
Ina d'aya daga cikin wanda sukama Aishatu fyad'e kuma Gentle ce ta sakamu,
Duk sauran wanda mukayi abun tare babu wanda ya sake samun kwanciyar hankali tun daga
ranar da muka mata fyad'en,
Kwatsam kwanakin baya munyi shayr shayenmu muka had'u da tsautsayin accident, baki
d'aya mutanen motar suka rasu nine kawai Allah ya kub'utar dani,
Tun daga wannan lokacin nake rok'on Allah ya had'ani da koda kad'an ne daga mutanen
dana zalunta in nemi yafiyarsu,
Kuma case d'in Aishatu yana d'aya daga cikin abubuwan da nayi wanda suke yawan fad'o
min a rai,
Tun daga wannan lokacin nake fatan Allah ya gwada mib ranar da san had'u da ita dan
neman gafararta amma Allah bayyi ba sai yanzu,
Ko tantama babu Gentle itace ta saka muka mata fyad'e,
Bayan nan kuma akwai abubuwa da dama wanda ta saka aka mata,
Itace ta tura 'yan daba suka sace k'annen Aishatu 'yan biyu,
Tasa an kashe d'aya daga cikinsu aka kai gawarta kan layinsu aka yar,
Itace ta had'a baki da manyan makaranta aka kori Aishatu akan laifin wai ta zubar da cikin
shege harda fad'in wai ba wannan ne na farko ba,
Itace tasa aka k'ona gidansu Aishatu wanda da bakinta ta bamu labari saboda ni nayi zaton
ma bata raye, dan yanda muka mata fyad'e mu kusan takwas sauk'inta ma duk bamu da wani
k'arfi sosai a lokacin saboda yanda muka bugu,
Ban tab'a zaton ma tana raye ba saida ita Gentle d'in ta bamu wannan labaran,
Ina rok'on wannan kotu mai adalci datayi gaggawar yanke mana hukunci tare da k'watarwa

Aishatu hakk'inta" ya k'arisa maganar cikin rawar murya had'e da fashewa da kuka.

Duk mutanen kotun babu wanda bayyi mamaki ba,
Hamdala kawai ke tashi a ciki banda b'angaren iyayen Gentle da har yanzu suke ganin
k'age ne aka mata.

"Yanzu haka d'aya daga cikin k'annen Aishatu tana wurin Gentle a b'oye, banda azaba babu
abunda ake mata" YB ya fad'a a hankali.

Har Sarki Manu saida yayi mamaki sosai, saboda shi duk baima san da wannan mugayen
abubuwan da Gentle tasa akama Ummimah ba.

Kuka Gentle ta fasa da k'arfin gaske wanda duk fad'in kotun babu wanda baiji ba,
"Na shiga uku ni Salmah, na cuci kaina, kai co na ni Salmah, dama hausawa sunce 'kwana
dubu na b'arawo, rana d'aya tal ta mai kaya' yau gashi asirina ya tonu abunda ban tab'a zato
ba, nasan tawa ta k'are saboda banida wata hujjar da zan kare kaina" a b'oye tayi maganar
amma bata san a bayyane tayita ba, Baki d'aya kallo ya koma gareta saboda da k'arfi ne tayi maganar kowa ya ji.





_nagode k'warai da yanda kuke bada lokacinku wurin karanta wannan labarin musamman
*Asma'u Umar,* kina d'aya daga cikin manyan fans d'ina ina godiya sosai. Amrah LYSM._





°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[11:13pm, 11/02/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

{~82~}



_wannan shafin tukuici ne gareki *Ummi Agoss,* nagode da bibiyar labarina da kike tare da
nuna zallar soyayyarki a gareni. ILYSM._



*****

Hayani kotun ta d'auka baki d'aya sai cece_kuce akeyi, Alhaji Abu Abu kuwa mutuwar zaune
yayi ji yake tamkar a mafarki ne, Barr. Sa'eed kuwa sai k'arema Gentle kallo yake yana mai
tsananin jin haushinta, inda ace batayi maganar ba da yasan ta hanyar da zaibi dan lalata
waccan maganar, amma kuma duka ta b'ata zancen.
Bubbuga guduma alk'ali yayi da k'arfi sannan kowa yayi shiru,
"Salmah Abubakar kinsan ko me kike fad'i kuwa?".

Cikin hawaye Gentle ta d'aga kanta tace
"Tabbas a duk bayanan da YB yayi babu k'ari ko kad'an a ciki,
Da gaske ni nasa ayiwa Ummimah fyad'e, ni nasa aka satomin k'annenta 'yan biyu duk dan in
guma mata,
Ganin kamar hakan bai dameta ba yasa da nasa aka kashe k'anwarta d'aya daga cikin
wanda aka sato,
Na samu labarin halin da suke ciki kuma na had'a baki da wanda yakeda gidan hayarsu na
maka masa kud'i yaje ya koresu,
A dalilin haka babanta ya had'iyi zuciya ya rasu,
Naso insa a saki Amrah amma kuma koda na samu labarin cewa wasu Indiyawa zasu taimaki
marasa lafiya saina fasa duk dan na b'ata ran Ummimah da mahaifiyarta,
Cikin ana shari'ar nan na tura an satomin wata a matsayin Barr. Sultana, kasantuwar
basusan fuskarta ba yasa suka sato wadda ba ita ba,
Yanzu haka Amrah da mai aikin gidan Barr. Sultana suna wurina amma ba tare suke ba,
Amrah tana Malali quaters can bayan gari, Mai aikin kuma tana cikin k'auyukan Barhim.
Kai cona ni Salmah, na cuci kaina na cuci rayuwata, nasan yanzu tawa ta k'are saboda dole
kotu zata zartar da hukuncinta a kaina" ta fashe da kuka sosai wanda duk wani mai imani dole
sai ya tausaya mata dukda yake ita d'in ba abun tausayi bace.

Shiru ne ya biyo kotun kasantuwar kowa na al'ajabib hali irin na Gentle, ko a littattafan hausa
ko fina finan hausa babu wanda ya tab'a zaton akwai mai hali irin na Gentle,
Babu imani ko kad'an a tattare da ita.

Wasu 'yan sanda mutum biyu ne suka shigo kotu, bayansu Safiyya ce ta jigatu sosai sai
kuma wasu 'yan sandan mutum biyu a bayanta,
Rigar bacci ce a jikinta amma jina jina take tsabar azabtuwa da tayi,
Tayi ba'ki ta rame tamkar ba ita ba.

Kallo kowa ya miyar garesu har suka k'ariso cikin kotun,
Kallon mutane take d'aya bayan d'aya har taci karo da Sultana daketa binta da kallon tausyi,
Rungumar juna sukayi cikin soyayya, sun jima a haka kafin Sultana ta janyeta daga jikinta
tare da samar mata wurin zama daga inda audience suke.

"Mai shari'ah waccan daka gani itace mai aikin da nasa aka sacemin, gata nan ta dawo
bansan dalili ba, bansan yanda akayi ta gudo ba" Gentle ce tayi wannan maganar cikin rud'ewa
sosai tana k'arema 'yan sandan kallo.

"Ko zaku mana bayanin abunda yake faruwa?" Alk'ali ya fad'a bayan ya miyar da kallonshi
ga 'yan sandan,
Kafin su bashi amsa wasu 'yan sandan mutum hud'u suka shigo, hannunsu janye da mutane
duka maza mutum shida kowane da ankwa rataye a hannunshi.
"Ku k'arisa shigowa dasu" wani d'aya ya fad'a daga cikin wanda suka shigo tare da Safiyya.

"Ya mai shari'ah mune 'yan sandan da aka sakamu neman Safiyya tunda aka shugar da
case d'in a station, mun jima muna nemanta sai yau Allah ya taimakemu muka sameta a can
k'auyukan Barhim, wannan samarin kuwa munyi nasarar cafkesu a bayan gidan da suka
b'oyeta" wani d'an sanda ne yayi wannan bayanin cikin natsuwa.
Kafin alk'ali ya sake yin magana wani saurayi ya shigo,
Kallo d'aya na masa na tunoshi lallai shine saurayin Gentle wato Abdul Kadir AK,
Babu neman izini babu komai ya k'ariso daidai gaban Gentle,
"Ya mai shari'ah wannan yarinyar da jake gani muguwa ce, batada halin kirki ko kad'an,
Ashe duk bayan halayenta dana sani bansan tana yaudarata ba, wai ashe tare take da
mahaifina abun kunya har mutane kowa ya sani, da zarar na fita sai a ringa bina da gori ana
yimin surutai,
Bayan kuma duk wasu kugayen halayena itace ta koyamin,
Itace ta sakani na fara yin kisan kai ga abokina kawai dan ya nunarda yana sonta,
Tun daga lokacin dana gane tana tare da mahaifina na d'auki alwashin illata rayuwarta saidai
duk abunda za'ayi amin,
Na tabbatar da akwaa hukuncin kisa akaina daga ni har ita,
Dan haka dole sai kinji makamancin rad'ad'in da naji na tarayyarki da mahaifina" da sauri ya
lalubi aljihunshi,
Wata 'yar kwalba ya zaro ya watsa mata ita a fuska sannan yayi murmushin mugunta ya mik'a
hannunshi ga 'yan sanda da nufin su d'aura masa ankwa.

Ihu ta fasa da k'arfi na azabar da take ji,

Hannunta tasa ta ringa dirzar fuskar wai a tunaninta ko hakan zaisa ta rage jin zafi,
Tattalewa fatar fuskar ta hau yi har tsokar dake jikin fuskar ana gani,
Kamar mahaukaciya take ihu tana tsalle tsalle tana neman agaji.

Mamanta cikin kuka ta taso ta rungumi 'yarta,
Banda kuka babu abunda takeyi, Ummimah dake tsaye gefe sosai ta tausayawa Gentle, koba
komai tun yanzu ta fara girbar abunda ta shuka.

Alk'ali kanshi jikinshi yayi sanyi, lallai al'amarin Allah babu wanda ya usa ya dakatar dashi,
lokaci d'aya Allah ya bayyana gaskiya ya kawo k'arshen shari'ar.
"Kafin kotu ta zartar da nata hukuncin, Salmah zata kwatanta inda suka ajiye Amrah azo da
ita, dole sai anga lafiyarta sannan komai ya wakana, kotu ta bada izini 'yan sanda su tafi suzo
da ita sannan aci gaba, za'a tafi hutun awa biyu kafin nan suma sun dawo, za'aci gaba da
tsaron Salmah, AK da wanda aka kamo har sanda zamu dawo daga hutu" ya buga gudumarsa
sannan ya mik'e ya fice.

Da sauri Mama kamar tana jira ta rugo ta rungumi 'yarta Ummimah,
Kuakn farin ciki sukeyi sosai tare da hamdala ga Allah,
Zarah da Rabiatu ma tasowa sukayi suka dawo gareta suna k'ara tayata murna dukda baca
yanke hukunci ba har yanzu.

Wani d'an sanda maras mutunci ne ya d'aurawa Gentle ankwa da k'onanniyar fuskarta data
gama lalacewa lokaci d'aya kamar ba ita ba.
Rik'eta mamanta tayi tam tak'i sakinta ita kuka Gentle kuka,
"Ke dillah malama ja can, kina sonta ne kika k'i bata tarbiyyar kirki? Gafaramin can kafin inyi
k'asa k'asa dake" yaja hab'ar rigar Gentle da k'arfi tare da fita da ita daga cikin kotun ya kaita
d'akin tsaro.

Cikin kuka maman Gentle ta koma kusa da mijinta,
"Yanzu Alhaji duk kudi'inka kana ji kana gani zaka bari a tafi da 'yarmu cikin ankwa? Shikenan
fa idan aka dawo daga hutu hukunci zaca yanke mata" ta sake fashewa da wani kukan.

"Karki sakemin maganarta kinji na fad'a miki, taya inaji ina gani yarinya zata kunyatani a
gaban jama'a? Kin manta da koni waye? Kin manta da ni d'an siyasa ne sananne? Yanzu fa
shikenan bama za'a fitar dani a primary election ba saboda ansan ko an bani ba zanci siyasa
ba, nikam na yafe Salmah, na barwa duniya ita babuni babu ita, kinji k'arshen maganata" ya
hankad'a babbar rigarsa tare da ficewa,
Masu take masa baya ne suka mara masu baya,
Maman Gentle kuwa tace babu inda zata je dan jarta tafi a kai mata 'yarta wani wuri.
Barr. Sultana kuwa tana wurin Safiyya suna ganawa tana k'ara tausaya mata.


*Bayan awa biyu*

A daidai wannan lokacin ne kotu ta sake cika kamar yanda aka tsara,
'Yan sandan d'azu ne suka shigo tare da wata budurwa waddaa shekarunta ba zasu wuce
sha shida ba,
K'ara murza idona nayi sai yanzu na gane ashe takwarata ce Amrah,
Ta rame sosai ta k'ara tsayi kad'an,
Duk farinta yanzu babushi, ta koma bakca wulik ga kayan jikinta kamar an tonota daga rami,
Gashin kanta kuwa tamkar mahaukaciya haka yake duk ya cukurkud'e.

Cikin farin ciki Ummimah ta cafke 'yar uwarta tana k'are mata kallo,
Bata tab'a tunanin zata sake ganin Amrah ba, sai gashi yau Allah ya had'asu,
Lallai Allah abin godiya, shi yake fitar da gaskiya daga k'arya, sannan yake tabbatar da ita ga
mai ita.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login