Showing 6001 words to 9000 words out of 56183 words
Chapter 3 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf
sallamar amma har yanzu shiru
ne,
Sallamah ta sakeyi a karo na uku sannan wata murya ta amsa sallamar.
A hankali tayi taku hud'u zuwa biyar ya sadata da cikin gidan.
D'an k'aramin gidane ginin jar k'asa, yana d'auke da d'aki k'waya d'aya tal sai band'aki, daga
can gefe kuma kitchen ne aka zagaye da langa langa, k'asan kuwa duk jar k'asa ne.
"Marhabun, shigo daga ciki mana" matar ta fad'a tana kallon Sultana dukda bata wayeta ba.
"to mama nagode" ta fad'a bayan ta shiga cikin d'akinda matar ta nuna mata ta shiga.
"Sannu da zuwa baiwar Allah" Matar ta fad'a har yanzu tana kallon Sultana,
"Yauwa sannu mama" ta tsuguna k'asa tace "ina yini mama?",
"Lafiya k'alau baiwar Allah, saidai kuma ban wayeki ba",
"Ehh gaskiya dama nasan ba zaki wayeni ba dan baki sanni ba" ta zaro ID card d'inta,
"Sunana Barrister Sultana Saddam Bakori"
Dafe k'irji matar tayi tace "na shiga uku! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah dai yasa lafiya
ba wani abu mukayi ba",
Murmushi Sultana tayi tace "karki damu mama, lafiya lau ba wani abu kukayi ba, zuwana
alkhairine insha Allahu",
"To ina fatan haka Sultana, Ummimah!" Ta kira sunan a hankali.
Daga kan gado wata budurwa 'yar kimanin shekara gona sha takwas ta sauko,
A hankali take tafiya fuskarta bushe da hawaye.
"Waike Ummimah har yaushe ne zaki hak'ura ki daina wannan kukan? Kukan banza tunda
kibsan ba wani magani zayyi miki ba",
Saurin goge sabon hawayen daya fito mata tayi sannan tace "sannu baiwar Allah".
Cike da tausayi Sultana ke kallonta tare da fad'in "yauwa Ummimah, ya gida?",
"Lafiya Sannu da zuwa, barin kawo miki ruwa" ta fad'a muryarta na rawa sosai alamar wani
kukan take shirin tayi.
"A'a ki barshi wallahi bana jin k'ishi",
"A'a indai kinsan ba k'yamarmu kike ba to kisha ruwanmu" Mamar ta fad'a cikin natsuwa.
"Hmm! Me zaisa nayi k'yamarku mama? Kuma fa mutane ne kamar ni, Wallahi kawai dai
bana jin k'ishin ne yanzu daga wani gida nake, amma dai Ummimah ki kawo min kad'an
zansha".
Tashi kuwa Ummima d'in tayi sai gata da kofin roba cike da ruwa,
Mik'awa Sultana tayi aikuwa tajishi da sanyi kamar daga fridge aka d'iboshi,
Kad'an tasha sannan ta ajiye kofin a k'asa ta fuskanci mama da Ummimah.
"Nasan baku sanni ba, kuma bakusan dalilin zuwana wurinku ba",
"Ehh kam hakane, ni a tunanina ma ko kinyi b'atar hanya ne, amma ke nake saurare sai kin
fad'a zan tabbatar ko wurinmun kikazo" mama ta fad'a tana kallon Sultana,
"Wurinku kam nazo mama, Kamar yanda na fad'a maku ni lawyer ce, nazo ne muyi wata
magana idan har ba zaku damu ba",
"Ehh muna jinki Sultana",
Ta bud'e baki zata fara maganar kenan wayarta ta d'auki ruri, hakan yasa ta ta fasa yin
maganar, fiddota tayi daga cikin jaka sannan tayi picking ta kara a kunnenta.
Princess Amrahí ½í¸˜
NWA
[12:50pm, 13/01/2017] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: *WATA SHARI'AH* í ½í¸ª
í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“
í ½í¸ª
Na Amrah A Mshí ½í²“
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)
*_In dedication to Aunty Sdy Jegalí ½í¸˜_*
{~21-30~}
"Hello honey" ta fad'a a hankali,
"Na'am wifey, kina kusa da Hauwa ne? Ina son inyimata ya mai jiki",
Shiru Sultana tayi kafin tace "aikuwa na fita yanzu amma zan koma, saidai ko ka kira
number'nta ko kuma idan na koma in kiraka sai in bata",
"To babu damuwa, idan kin koma d'in sai ki kirani, saboda gaskiya babu tabbas d'in zan samu
zuwa gobe gidan nata dan akwai hidimar data taso min goben"
"Ok honey sai na koma d'in" tayi hanging up na wayar.
Juyowa tayi ga Ummimah da Mama tace "kuyi hak'uri fa mama, maigidana ne ya kirani",
"Uhm babu komai Sultana, bari ki fara ji daga bakin Ummimah sannan nima in fad'a miki
abunda na sani" mama ta fad'a cike da natsuwa.
Ga Ummimah ta juya tace "ina saurarenki Ummimah".
"Asalin sunana Aisha Abubakar ne, amma Mamana da babana suna kirana da Ummimah
kasantuwar sunan kakata wadda ta haifi babana aka saka min, nice babba a wurin iyayena sai
k'annena guda biyu 'yan biyu ne Afrah da Amrah, shekara biyu ke tsakanina dasu tun daga nan
kuma haihuwa ta d'aukewa mamana, dama wurin haihuwarsu Amrah tasha wahala sosai.
Mahaifina nada rufin asirinshi daidai gwargwado, muna zaune a gidan haya a cikin unguwar
Saulawa dake nan cikin garin Katsina, babana yana aiki a wata k'aramar ma'aikata a k'ark'ashin
wani mutumi inda ya zama masinjanshi.
Akwai shak'uwa sosai tsakaninmu, mukan zauna a koda yaushe muyi raha tare da
iyayenmu,
Babana ya sakani a makarantar gwamnati saboda bashi da halin da zai kaimu makarantar
kud'i duk da yanada burin hakan,
Na taso da bala'in son inyi zurfi a karatun boko ina son in karanci fannin education kodan in
gyara rayuwar bokon zamani, hakan yasa nake miyar da hankalina a kowane term, tun yarintata
ni nake d'aukar first position har na shiga secondary School,
Bani da k'awa ko d'aya ni kad'ai nake rayuwata daga ni sai k'annena biyu wanda bana b'oye
masu damuwata suma kuma basu b'oye min tasu damuwar, a raina har nakan tambayi kaina
akan wa nafi so a cikinsu, *Afrah ko Amrah* (namesy Futha) saidai kuma amsar d'ayace, duk
d'aya suke a wurina.
Bayan mun rubuta jarabawar JSS ne Allah ya bani sa'a kuwa na samu sakamako mai kyau,
ina d'aya daga cikin wanda suka zamo na d'aya a cikin kaf class mates d'inmu,
Hakan yasa gwamnati ta d'auki nauyin miyar damu Private School mu uku daga cikin d'aliban
makarantar.
Babana yaji dad'i sosai saboda ya dad'e yana mafarkin ganin ya kaini private school nida
Afrah da Amrah,
Nima naji sosai hakan yasa na sake d'aure d'amarar yin karatu sosai har sai inda k'arfina ya
k'are.
Shigata makarantar na had'u da yara kala kala, wasu 'yan rainin wayone wasu kuma
mutanen kirki ne, amma kuma 'yan rainin wayonsu sunfi yawa.
Ina zaune ni kad'ai kamar ko yaushe na fiddo chemistry note book d'ina ina k'ara duba wasu
equations da akayi d'azu.
Wata yarinya ce tayi min sallamah tare da mik'o min hannu don mu gaisa,
Cikin mamaki na amsa sallamar nima na mik'a mata nawa hannun muka gaisa,
Abunda yasa ni mamaki kuwa dan ban tab'a tunanin akwai irinsu a wannan makarantar ba,
tunda naje babu wadda tayi k'ok'arin yimin magana saidai masu bina da kallon banza
musamman ma yanda sukaga ina participating a cikin class.
Bayan na gyara mata wuri ta zauna ne tace min "sannu",
Nima sannun na miyar mata dashi.
Murmushi ta sakar min ta sake fad'in "naga kaman You're busy ko? Gashi kuma magana nazo
muyi dake".
Ajiye littafin nayi nima na miyar mata murmushin nace "babu komai ai, ina maimaita karatun
d'azu ne kuma ma na gama, ina saurarenki, Allah dai yasa lafiya".
"Ahh lafiya lau karki damu, na kula dake tun shigowarki makarantar nan kinfi son rayuwarki
ke kad'ai, baki damu da rayuwar kowa ba, baki da k'awa ko d'aya ko magana bata dameki ba,
iyakacinki kawai ki bada amsa idan wani teacher yayi tambaya, kina da k'ok'ari sosai kuma
kowane teacher yana alfahari dake, baki dad'e da shigowa makarantar nan ba amma har an fita
outing dake kusan sau biyar ko sau shida, kuma duk wata queeze ko debate d'inda zakuje
zakiyi winning, shine nake son idan babu damuwa me zai hana mu zama friends? Ba dan komai
ba sai dan ki ringa koya min karatu, saboda nidai bana ganewa idan akayi karatu, amma kinga
idan ke kika natsu kika koya min zan gane sosai, amma fa idan babu takura".
Murmushi kawai na miyar mata dashi,
"Babu takura ko d'aya, sai dai matsala d'aya kawai",
Kallona tayi tace "matsala? Wace irin matsala?",
"Nidai kinga ba d'iyar kowa bace ba face *'yar talakawa* (Afrah), bamu da komai sai rufin
asiri, yanzu haka school d'in nan da nake gwamnatice ta d'auki nauyina, iyayena sun min
nasiha sosai akan na guji yaran masu kud'i saboda natsalace dasu, suna da wulak'anta talaka
sosai,
Saisa kullum nake ni kad'ai sabda gudun wulak'anci, gaskiya kiyi hak'uri kinfi k'arfina".
Kallona tayi sosai hawaye ya fara kwaranya daga idonta,
"Mesa zakice nafi k'arfinki? Kin manta cewa da talaka da mai kud'i duk d'ayane a wurin Allah?
Wanda yafi wani shine wanda yafi wani tsoron Allah, dan Allah ki daina wannan maganar, nidai
bani da matsala ko d'aya kuma ki tambaya kiji, indai har kinji na kwanta miki a rai to kiyi
k'awance dani kar kiji komai" tana gama fad'in haka ta goge hawaye.
Shiru nayi mun jima babu wanda ya kuma fad'in komai,
Saida na nisa sannan nace "to ki bari zanyi shawara da mamana, duk abunda ta yanke zan
sanar dake insha Allahu",
"To babu komai, ina fatan zata amince saboda nikam kin kwanta min a rai, ina son mutum
mai irin halinki, gaki da kamun kai sosai duk mazan class d'in nan babu ruwanki dasu kin huta",
"Nagode sosai sai kin jini" na fad'a bayan na sake bud'e littafina,
"Au! Shine ba zaki tambayeni sunana ba ko? To tunda baki damu da ji ba ni ki fad'a min naki
sunan",
Kunya naji sosai nayi mata murmushi,
"Sunana Aisha Abubakar amma anfi kirana da Ummimah, kefa?",
"Sunana Salmah Abubakar, amma Gentle ake kirana dashi",
"Nice name, surname d'inmu d'aya dake kenan?" Na tambayeta,
"Ehh kam hakane".
Da haka har lokacin dawowa break fast yayi, malami ya shigo akaci gaba da karatu daga inda
aka tsaya.
K'arfe uku daidai aka tashi kamar yanda aka saba,
'Yar jakata na rataya a kafad'a, na nufi hanyar titi don in samu keke napep in hau.
Gentle ce da sauri ta ringa k'wala min kira, daga farko ban jita ba sai daga baya, hakan
yasa na dakata na jirata har ta iso inda nake,
"Tunda aka tashi nake rarraba idona ta inda zan hangoki, sai daga baya baseerar in biyoki
tanan hanyar ta fad'o min,
Ina zakije ko tanan ake zuwa d'aukarki?"
Bayan nayi mata d'an murmushi nace "keke napep zan tara in tafi".
Da sauri tace min "a'a dan Allah karki tari napep d'in nan, kizo gaya can anzo d'aukata, dama
neman da nake miki kenan inji idan ba d'aukarki za'a zo ba sai mu tafi dake a ajeki a gidanku".
"A'a nidai ki barshi wallahi nagode",
"Raina baiji dad'i ba idan baki zo mun tafi dake ba, dan Allah kiyi hak'uri mu tafi".
Dafa kafad'arta nayi nace "Salmah kenan, iyayena zasu min fad'a idan sukaga kun bani lift,
kiyi hak'uri babu komai wallahi zan hau keke napep d'in dama kullum ita nake hawa".
Badan taso ba tace "to shikenan sai anjima, ki gaishe dasu mama" ta tafi,
Kallo d'aya za'a mata asan bataji dad'in rashin bintan ba, nima kuma kaina banji dad'i ba,
saidai kuma dole babu yanda zanyi sai dai hakan, babana zai iya yimin fad'a sosai kuma yace
na fara bin yaran masu kud'i ina son in canza hali irin b'ara rayuwata, wanda kuma sam ba haka
bane, kuma na kula da Salmah ko a cikin yaran masu kud'in ma ita batada mugun hali, tanada
halin kirki kuma tanada son kyautatawa.
Da wannan tunanin na isa bakin titi na tsayar da keke napep na hau.
Princess Amrahí ½í¸˜
NWA
[2:16pm, 15/01/2017] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: *WATA SHARI'AH* í ½í¸ª
í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“
í ½í¸ª
Na Amrah A Mshí ½í²“
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)
*_In dedication to Aunty Sdy Jegalí ½í¸˜_*
{~31-40~}
A gajiye na koma gida, da hanzari Mama ta tarbeni ta karb'ar min jakata ta makaranta kamar
yanda ta saba koda yaushe itace take karb'ar jakata idan na dawo daga School.
"Oyoyo Aunty Ummimah" shine abunda ya fito daga bakin Afrah cike da farin cikin ganina.
Murmushi na miyar mata dashi,
"Sannu Afrah, 'yan JSCE, ya jarabawar? Ince dai tayi dad'i"
"Tayi dad'i sosai Aunty Ummimah, ashema babu wahala jarabawar haka nan ake sakamu jin
tsoro",
"Ai dama na fad'a maku babu wahala, ina Amrah ne?" Na tambayeta saboda ban ganta ba.
"Amrah na d'aki batada lafiya, kinsanta ita kingin ciwo ce, kullum daga wannan ciwo sai
wancan ciwo".
"Subhanallahi! Ina zuwa barin dubata" kai tsaye na shiga d'akinmu.
Sosai hankalina ya tashi saboda yanda na ganta sai rawar sanyi take,
Kusa da ita na zauna har ina jin gumin jikinta,
"Sannu Amrah, ashe bakida lafiya".
Muryarta na rawa da k'yar ta iya furta "ehh Aunty",
"Ayyah sannu kinji? Kinsha magani kuwa?",
"Nasha paracetamol sauran wanda nayi amfani dashi last week da banida lafiya".
"Gaskiya ya kamata ace an kaiki asibiti Amrah, zama da ciwo bashi da wani amfani, bazai
yiwu a ringa ciwo daban magani daban ba, kullum saidai ana d'irka miki pain reliever, kar aje
ciwo ya ringa cinki kuma ba'a san kalarshi ba".
Shiru Amrah tayi bata kuma cewa komai ba saidai kuma har yanzu jikinta bai daina rawa ba,
idonta yayi jajur tsabar ciwo da yake cinta.
Muna cikin hakane Mama ta shigo d'auke da School bag d'ita a hannunta,
Bayan na karb'a nace "gaskiya Mama ya kamata akai yarinyar nan asibiti, kinga jarabawa
sunayi kar ciwo ya hanata zana jarabawarta kuma azo a samu matsala daga k'arshe, kinsan
makarantun gwamnatin nan har korarta suna iya yi daga makarantar",
"Hakane Ummimah, amma kema kinsan halin da muke ciki, wurin aikin mahaifinki kusan
wata biyu zuwa uku kenan basu samu albashi ba, harma an fara tunanin rufe company d'in
za'ayi saboda karayar arzik'i daya samu mai company'n ya daina biyan ma'aikatansa albashi,
kinga kuwa ina mukaga kud'in da zamu kai Amrah asibiti?".
Ajiyar zuciya na sauke, tabbas maganar mama gaskiya ne, amma kuma ai baza'a bar yarinya
ciwo ya ringa cinta ba, duk ta jarabawa ma mai sauk'i ce indai tanada lafiya. Ban kuma fad'ar
komai ba kawai na fara cire Uniforms d'ina, saboda har an fara kiran sallar la'asar kuma bana
son makara Islamiya.
Bayan nayi sallah na shirya cikin uniforms d'in islamiyarmu, riga da hijabi milk colour, sai d'an
kwali da wando coffee brown,
Har na d'auki jakata na hau kan k'aramin gadonmu na fuskanci Amrah da bacci ya d'auka
yanzu,
Cikin magagin bacci ta jawo hannuna ya shiga cikin nata, tam ta rik'eni kamar da gangan tayi,
hakan yasa na k'i cire hannuna daga nata hannun har hud'u da rabi ta kusa muna a haka dan
bana son in cire hannuna kuma hakan yasa ta tashi daga bacci.
Mama ce ta shigo ta samemu a haka,
"Ki tashi ki tafi islamiya mana Ummimah, Afrah har ta gaji da jiranki ta tafiyarta