Showing 24001 words to 27000 words out of 56183 words

Chapter 9 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf

Advertisement

Kuka muke sosai nida Mama har babu mai rarrasar wani,
Da k'yar baba yaci gaba da fad'in
"Ku kuka da rayuwarku, kuyi k'ok'arin rik'e babunku, kar ku jefa kanku a wani hali saboda
abun duniya" tari sosai yaci k'arfinshi,
Jini ne yabi bayan tarin saigashi gullama gullama yake fita abun tausayi,
Salati muka d'auka nida mama, hakan yasa shima baba ya d'auka yanayi,
Muna direwa shima yana direwa, bai iya furta komai ba sai ajiyar zuciya da yayi wanda shine
fitar ranshi.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Kawai muke fad'i nida Mama.

"Bai mutuba wallahi da ranshi, likita! Likita kazo ka tabbatar mana da Abubakar bai mutu ba,
nasan bazai tab'a tafiya ya barmu ba" Mama ta k'ara fashewa da kuka.

Bayan likita ya shigo ya tabbatar mana da Baba ya mutu, hakan yasa muka k'arfafa kukan
namu,
Da k'yar muka fita daga d'akin saboda gadon da gawar baba take mama ta rik'e da k'arfin
gaske tana kuka.

Sai washe gari aka kai Baba, kasantuwar yamma tayi lokacin da ya rasu d'in, ko kafin akai
gawar a shiryata ma duhu ya fara.

A gidan mutumin daya jagoranci gawar Afrah da Baba muka zauna,
Bayan munyi sati biyu zuwa uku a gidanshi a lokacin har mun fara dayayewa ya samar mana
wannan gidan da muke ciki anan unguwar Tudun wada,
Anan muke rayuwa nida Mamana, sosai kawu Nasiru (wanda ya taimakemu) yake kula
damu tamkar 'yan uwanshi na jini,
Duk lokacinda nama mama maganar mu tafi wurin danginta kona Babana sai tace a'a,
saboda lokacinda zasuyi aure duka danginsu basu soba,
Iyayenta sukace inhar ta auri babana to babusu babu ita har abada,
A gidansu babama haka akace masa,
Sun aminta da hakan sukayi aure sannan suka bari Kaita suka dawo cikin Katsina.
Wannan shine labarina, ina fatan zaki taimakemu inhar kinada halin yin hakan, ki k'watomin
'yar uwata inhar tana raye". Ummimah na gama fad'in haka ta fashe da kuka.

Mama ta share hawayenta tace
"Tabbas duk abunda Aishatu ta fad'a miki gaskiya ne, cutarmu akayi amma an nuna anfi
k'arfinmu ta hanyar dukiya, bamuda galihu ko kad'an".

Cike da tausayi Sultana tace
"Ki daina fad'in bakuda galihu Mama, Allah yana sonku ai, kuma insha Allahu komai ya kusa
zuwa k'arshe tunda har Allah ya jefoni a rayuwarku".

"To waima waye ya fad'a miki muna cikin wani hali?" Mama ta tambaya saboda abun ya bata
mamaki.

"Ni kaina ban saniba Mama, ya b'oye kanshi koma waye,
Amma kuma yanzu duk ba lokacin wannan bane,
Na d'aukar maku alk'awarin zan taimakeku bakin k'arfina, sannan kuma mijina babban
Lawyer ne am sure shima zai taimaka min dan ganin mun gurfanar da Salmah a gaban alk'ali".

Koda duka duba har dare yayi duk basu sani ba,
Da hanzari ta duba wayarta tayi kicib'us da 21 missed calls,
Tashi tayi ta masu bankwana sannan ta fita ta shiga motarta tana k'ok'arin dialing number'n
Umar mijinta.



_gasuwa tare da godiya ga masoya labarin *WATA SHARI'AH* aduk inda suka, nagode da
yanda kuke nuna kulawarku gareni musamman 'yar uwata ko ince Aunty'nmu *Ashnur Pyar,*
Allah yabar zumunci da zaman tare._





°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[5:47pm, 25/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*

{~67~}


Bugu d'aya kuwa Umar ya d'auki kiran cike da zak'uwa yace
"Hello wifey"
"Honey kamin uzuri dan Allah sai yanzu na kula da kiranka",
"Ehh tunanin da nayi kenan dama, ina fatan dai lafiya",
"Lafiya k'alau wallahi, ka jini shiru wallahi na jima a inda naje d'in ne, kuma akwai magana
sosai sai na dawo, barin d'auko su Hafsa sannan mu wuto gidan da sauri",
"Ai su Hafsa tun d'azu suna gida wifey, kuka tayima Hauwa'u wai tunda ba zaki dawo ba ita
gida take so, a dole saida naje na d'aukosu",
"Oh ni Hafsa ba hak'uri, bari to indawo yanzu gani a hanya",
"Ok sai kin dawo" Umar ya fad'a tare da tsinke wayar.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kasantuwar jin matarshi tana lafiya, dama jinta shiru da yayi
yasa hankalinshi ya matuk'ar tashi.

A jerin missed calls d'inda ta tayar harda na Hauwa,
Hakan yasa ta katsa kiranta,
Babu b'ata lokaci itama ta d'auka.
"Maman Hafsa lafiya dai ko?" Ta tambayeta cikin tashin hankali.

"Lafiya k'alau Maman Zarah, na saka wayar a jaka ne ashe a silent take ban sani ba, kin
sanmu lawyers da yawon bincike, saisa kukaji shiru ban dawo ba",
"To masha Allahu Aunty, Hafsa dai basu yarda sun tsaya ba",
"Ehh haka Abbansu ya fad'a min yanzu, bansan mesa ba Hafsa batada yarda, waini gani nayi
ga Zarah nasan zasuyi wasa tare ashe bata yarda ba",
"Wallahi kuwa, bakiga kukanda tasha ba kamar wacce zan cirewa kai".

Dariya Sultana tayi tace
"Ai dama dai ku kuka zab'arwa kanku rigimammiya, ga Haydar d'ina d'an albarka yaro shiru
shiru babu hayaniya sai natsuwa",
Itama Hauwa dariyar tayi
"Ai sai shiru shiru d'in, wannan yaron ai saike, yaro sai b'arna da rashin ji? Yau saida ya fasa
min kaf k'waina dake cikin fridge, tumaturina kuwa saiya fasa ya fara sha sai ya yar ya sake
fasa wani, duk ya gama wulak'anta min kayan fridge, Haydar saike kad'ai Aunty Sultana".

Wata dariyar Sultana tayi saboda Haydar ya bata dariya sosai, itama kanta haka take fama da
b'arnarshi kullum cikin dukanshi take amma kamar tana tunzurashi.
"Aunty Hauwa ai d'an albarkar kenan, danma kun samu ya saka miki albarka a kayan fridge?
D'ana yaron kirkine",

"Wallahi Aunty Sultana zan kashe wayar nan indai maganar d'ankin nan zakina yimin",
"Naji dai Aunty, dama na k'ariso gida yanzu nima, ki gaisarmin da 'yata Zarah, saida safe",
"To saida safe, ki shafamin kan Hafsa 'yar albarka",
"To Aunty Hauwa zan shafa miki kan Haydar d'an albarka".

Murmushi tayi tare da hanginp up na kiran ta miyar da hankalinta ga kwanar gidansu da zata
shiga.

***

Parking tayi bayan ta shuga gidan, da hanzari Haladu ya iso gareta, hand bag d'inta ya
karb'a bayan ya gaisheta,
Ciki ta shiga yana biye da ita har suka isa parlor,
Bayan ta k'arb'i jakar tayi godiya ta kalli inda Hafsa take kwance tayi bacci hawaye duk sun
bushe a idonta,
Murmushi tayi tare da furta
"Hafsa kayan rigima" ta shiga d'akin mijinta.

D'an kishingid'awa yayi yana 'yan rubuce rubuce a wata takarda dake k'ark'ashin wani file,
"Assalamu alaika ya Habeebee" ta fad'a cike da soyayya.

Kanshi ya d'ago fuska d'auke da murmushi yace
"Wa'alaikissalamu ya Habibty",
"Sannu honey, ka jini shiru afwan",
"Babu komai wifey, ina kika shiga ne kika d'auki wannan tsawon lokacin?" Ya tambayeta
bayan ya harhad'a takardun a cikin file, saboda baya had'a aikinshi da kuma kula iyalinshi.

"Ka gafarceni Uncle Umar da bayanin da zan maka",
Saurin tashi zaune yayi saboda yasan akwai matsala, duk lokacin da Sultana zata kirashi da
Uncle Umar to tabbas akwai matsala ne.

"Me farune wifey? Allah yasa lafiya" ya furta idonshi kyam a kanta.

"Uncle Umar na sab'a maka, ka hanani kula wanda yake turo mana text messages d'in nan
amma na kasa hak'uri dole saida na kula,
Wadda yake fad'a mana d'in tana cikin wani hali tabbasa tana cikin matsanancin halin, kuma
tanada tsananin buk'atar taimakonmu, dan Alkah inaso ka taimaka min mu had'a k'arfi da k'arfi
domin k'watar mata fansa".

Kallonta ya sakeyi bayan ya rik'e mata hannu cike da soyayya
"Anything for you wifey".

"Yauwa honey na, sunanta Aisha Abubakar..." ta labarta masa komai tun daga farko har

k'arshe bata b'oye masa ba.

Ba k'aramin tausayawa Ummimah yayi ba shima,
"Lallai ke jaruma ce wifey, kin cika 'yar aljannah, Allah ya bamu ikon taimakonsu",
"Ameen mijina na kaina, Allah kar ya kawo ranar rabuwarmu".

Murmushi Umar ya mata tare da cewa
"Aikuwa dole zamu rabu wifey, akwai ranar da mutuwa zata rabamu".

Wata 'yar k'wallah ta d'igo mata take tace
"How I wish mutuwar ta d'aukemu tare honeyna, ko kuma ta fara d'aukata, bana fatan ka
mutu ka barni saboda bansan yanda zan iya rayuwa idan babu kai ba".

Dod'e mata baki yayi yace
"ki daina wannan maganar Wifey, lets close the chapter, kije Hafsa na can kwance a parlor ki
kaita d'akinsu, Haydar ma yana d'akin Safiyya".

"Ok honey" ta fad'a tare da share hawayen daya fara fito mata.

Bayan ta d'auki Hafsa ta kai d'aki ta koma d'akin Safiyya ta samu Haydar ya mak'alk'ale
Safiyya yana bacci,
Ita kuma sai d'an bubbuga bayanshi take itama baccin yana shirin d'aukarta.

Kallonsu tayi cike da so, a bayyane ta furta
"Allah sarki Safiyya! Akwai soyayya tsakaninki da Haydar, ban san ya zakuyiba idan zakiyi
aure".

Bud'e idonta tayi tayi murmushi ba tare data furta komai ba.

"Yau bacci tunda wuri haka Safiyya? Ko dan bana nan ne?",
"Momy kenan, ai idan bakya gidan nan jinshi nake kamar babu kowa a ciki, mun saba kullum
wannan lokacin muna tare parlor mun fira, amma kuma yau bakya nan, gashi Hafsa ma k'awar
firar tayi bacci tun d'azu".

"Hmm! Wallahi Safiyya wata 'yar matsalace ta tsayar dani",
"Ayyah Momy, Allah ya warware matsalar",
"Ameen Safiyya, kawoshi" ta mik'a hannunta ta karb'i Haydar da jikinshi yayi kace kace da
ruwan tumatur duk ya bushe yayi dabbura dabbura.

D'akinsu ta kaishi ta saka mishi pyjamas d'inshi sannan ta d'orashi akan baby bed d'inshi
blue, Hafsa kuma tana kan nata pink.
Bayan ta tofesu da addu'ah ta fita,
Kai tsaye alwala ta d'auro ta gabatar da sallolin da ake binta na magrib da isha, tayi shafa'i da

wutri sannan tayi addu'ah sosai ta koma d'akin mijinta.

Ta sameshi yana kwance yana jiranta,
Murmushi ta masa sannan ta isa gareshi tana fad'in
"Na gaji wallahi honey" tayi hamma tana kallonshi
"Wallahi honey ba zakaji tausayinsu ba sai idan ka gansu, kaga gidan da suke, kaga halinda
suke ciki, mamanta fa tace tun daga lokacin da abun ya faru yarinyar bata kuma samun walwala
ba, kullum cikin kuka take".

"Allah sarki bayin Allah, insha Allahi komai ya kusa zuwa k'arshe, zamu taimakesu sosai
bakin k'arfinmu, har School ma zata koma da yardar Allah".

"Allah ya yarda mai gidana na kaina" ta kama hannunsa ta bashi peck sannan ta mik'e domin
canza kayan jikinta tana mai k'ara son mijinta, tana kuma k'ara jin dad'in yanda yake da
taimakon mutane.



_Gaisuwa da godiya gareki maman Taslim, ina jin dad'in yanda kike nuna kulawa tare da bibiyar
wannan labarin, Allah yabar zumunci da zaman tare, ya raya mana Taslim d'inmu bisa tafarkin
sunnah, ameen._






°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[3:51pm, 26/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*


{~68~}

Washe gari ta kama ranar lahadi babu aiki,
Hakan yasa da sassafe Sultana ta gyara gidanta ta bad'e ko'ina da k'amshi,
D'akin su Hafsa ta shiga ta samu Haydar baya nan sai Hafsa kwance a gadonta, hakan ya
tabbatar mata da yana d'akin Safiyya.

Kai tsaye d'akin Safiyya ta nufa,
Ta samu Haydar zaune bisa cinyar Safiyya sai zuba mata surutu yake ita kuma tana dariya.
Ganin Sultana yasa Safiyya ta sauke Haydar daga kan cinyarta ta tsuguna har k'asa tace
"Ina kwana momy?".

Da fara'ah Sultana ta amsa da
"Lafiya k'alau Safiyya, an tashi lafiya?",
"Lafiya Aunty, ya gajiya?",
"Ba gajiya, naje d'akin su Haydar ne na samu bayanan, na tabbatarda nan yayo",
"Ehh kuwa nan yayo kam, cikin magagin barci ma yazo, Haydar" ta miyar da kallonta ga
Haydar.

Hakan yasa ya fahimci inda ta dosa,
"Good morning momy" ya fad'a bayan ya duk'a har k'asa.

"Morning my boy, ka tashi lafiya?",
"Lafiya momyna" ya bata amsa yanayi yana wasa da warwaron hannun Safiyya.

"My boy anyi sallah kuwa?",
"Ehh momy Aunty Safiyya tasa nayi",
"Ok muje ayi wanka" ta d'aukeshi suka tafi d'akinsu.

Tashin Hafsa tayi tayi sallah kafin ta gama har Sultana ta gama shirya Haydar.

Bayan ta gama shiryasu duka ta fita parlor, dama kuma ta gama had'a break fast tun tashinta
daga bacci,
Koda ta shiga d'akin Umar ta tayar ya tashi shima har ya shirya,
Murmushi k'unshe a fuskarta tace
"Barka da tashi mai gidana na kaina".

Murmushin ya mata shima yace
"Yauwa 'yar aljannah, kin tashi lafiya?",
"Lafiya k'alau honey, break fast is ready, kai kawai muke jira",
"Alright wifey, idan mun gama akwai maganar da nake so muyi dake",
"Ok ba damuwa". Suka fita daga d'akin tare da nufar dining area.

Bayan sunyi nat Umar yace
"Maganar jiyan nan ce, so inaga kamar ya kamata mu koma gidan tare dake, saboda akwai
'yan tambayoyin da nake so na masu kafin mu shigar da maganar kotu, saboda a tunanina ba
zamusha wata wahala ba a wannan shari'ar".

"Hakane honey, na shirya dama muje kawai, amma kuma jiya nama su Hafsa laifi, ina so muje
tare dasu daga can mu wuce yawo dan in kankare laifina" ta fad'a bayan ta kalli Hafsa ta saki
murmushi.

"Ok muje?" Ya tambayeta
"Ehh muje" ta shiga d'akin Safiyya,
Abunda zata dafa na rana ta shaida mata sannan ta fito da sauri saboda su Haydar har sun
fita parking area ita kawai suke jira.

Kai tsaye gidansu Ummimah suka dosa,
A k'ofar gida Umar ya tsaya bai shiga ba, sai Hafsa da Haydar ma a cikin mota basu fita ba,
Sallamah tayi tare da jinkirtawa har saida aka amsa sallamar.

Kamar jiya ta samu Ummimah tayi tagumi saidai kuma yau babu hawaye, amma kuma kallo
d'aya za'a mata a fahimci tsantsar tashin hankali a tattare da ita,
Bayan sun gaisa ne tace
"Tare nake da mai gidana, Barrister Umar Mohd Bashir",
"Ki shigo dashi ciki mana Sultana" Mama ta fad'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login