Showing 15001 words to 18000 words out of 56183 words

Chapter 6 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf

Advertisement

haka ba" na fashe
da kuka sosai ina k'ara mamakin Salmah.
Cike da izgili namijin da suke masha'ar tare yace
"To wai ita wannan wacece ne Gentle? Taya zaki baru tana fad'a miki magana anyhow?",
Ban ko kalleshi ba saboda banga abunda zan kalla ga mazinaci ba,
Dan haka na koma gareta,
"Kin cuci iyayenki kin kuma cuci kanki, kiyi gaggawar tuba ga Allah saboda Allahu
gafurur-raheem ne, idan kika bi sharud'd'an tuba mai yiwuwa ne ya yafe miki".

"Ke wai ina ruwanki danine? Idan ma abunda yafi zina nayi ina ruwanki? Kija k'azamin jikinki
ki k'ara gaba" Gentle ta fad'a cike da masifa.

"Ke har kinada bakin kiran jikina da k'azami? Ai babu babban k'azamin jiki bayan na
mazinata, ko kun manta Allah mad'aukakin sarki yace "wala taqrabuz-zinah",
Karma mu kusanci zinar barin har mu aikatata, dan haka dan Allah kiyi hak'uri ki rabu da
wannan yaran, Salmah ki koma halayyarki ta baya wadda kika baro gidanku da ita" na k'ara
fashewa da kuka ina k'ara tuno k'awancenmu da ita tun ss1.

"Aisha Kibar wurin nan tun kafin in d'aukar miki mataki" ta sake fad'a tana kallona cikin ido.

"Bazan tafi in bar wurin nan ba Salmah sai idan tare dakene, ki d'auki duk matakinda saki
d'auka dan bazan iya tafiya in barki ke kad'ai ba saboda zaku iya komawa kuci gaba da aikata
mugun aikinda kuke kanyi".

Kyakkyawan mari saurayin nata ya d'aukeni dashi,
Take na ringa ganin bishi bishi kamar zan fad'i k'asa,
Dakewa nayi na had'iye hawayen daya fito min, na k'udura a raina bazan tafi inbar Salmah a
wannan halin ba.

"Ka k'yaleta AK, nasan maganinta" ta fad'a tare da sake juyiwa ta fuskanceni,
"Wallahi sai nasa anyi miki fyad'e matuk'ar baki bar wurin nan ba".

A wasa na d'auki abun saboda wannan maganar ban tab'a zaton zata fito daga bakinta ba,
kuma ni nayi zaton b'acin raine ya sakata fad'in haka,
Dan haka naci gaba da tsayuwa ina jiranta tazo mu tafi.

"Khalifx kuyi mata fyad'e kuma na rok'eku karku sassauta mata, nasan zaku iya ku jata kukai
dajin can inda babu haske" Gentle ta fad'a tare da komawarta cikin mota itada saurayin nata
wanda naji ta ambata da Ak.

Kamar wasa wannan k'artin suka ringa jana da k'arfin tsiya suna k'ara turani cikin daji,
Hankalina ya k'ara tashi sosai ganin da gaske suke abunda Gentle ta sakasu suyi min shid'in
zasuyi.
Ihu nake sosai ina fad'in "Ya Allah ka kareni daga sharrinsu, Baba, Mama kuzo zasu rabani da
*martabata* (Ummi Aisha), amma shiru sabida wurin ihunka banzane saboda babu wanda zai
iya jina.

Samari takwas saida sukayi min fyad'e, idan wannan ya gama sai wannan yazo yayi babu
sassauci,
Gashi kuma cike da rashin imani sukeyin abun, sosai nake jin azaba, tun ina ihu har ihun ma
ya daina fita sai sabbatu da nakeyi wanda bansan abunda nake fad'i ba,
Bayan mutum takwas d'in sun gamane na k'arshen yace
"Manu saura kai, kazo ka gama da ita mu kaita mu jefar, sabida babu alamar ma tanada rai".

Sama sama nake jin maganganun nasu,
Wanda suka kira da Manu yace "haba ai wannan rashin imanin naku yayi yawa, taya
zakuyiwa yarinya fyad'e har ku takwas? Tunda nake a rayuwata ban tab'a jiba ko a labarai, dan
wannan yarinyar ma bana tunanin tana numfashi, gaskiya ta mutu kuma doke zata mutu,
gardawa takwas ba wasa ba", "Kai wawane matsalata dakai Sarki Manu, komai kai kace tausayi, an fad'a maka a iskanci
akwaa tausayi ne?" Wabi daga cikinsu ya fad'a.

"Aini kasan duk iskancina bana yiwa mace dole, sai idan ita ta amince tace taji ta gani
sannan nake mu'amala da ita, sab'aninku da aikinku kenan yima yaran mutane fyad'e" wanda
suka kira da Sarki Manu d'in ne yayi wannan maganar.

Duk abunda akeyi na zama niba rayayyaba ba kuma matacciya ba, Allah dai ya bani ikon

sauraren maganganunsu amma kuma ko idona bana iya bud'ewa.

"Shikenan ai ku d'uketa ku jefar cikin dajin nan, saboda da alama dai ta mutu wannan
gawace",
Ina jin sun fad'i haka gabana ya tsananta bugawa,
Sai jin muryar Manu naji yayi yace "a'a karku jefarta cikin daji dan Allah, ni ku barni in kaita
daga can gefe, yanda za'a iya ganinta cikin sauk'i sai a sallaceta".

D'aukata kuwa yayi yakai daga can gefen titinda zai zartar da mutum cikin humanities, a
hankali ya ajiyeni tun daga nan baccin wahaka ya d'aukeni wanda ban kuma sanin inda kaina
yake ba.


_masu karatu dan Allah kuyi hak'uri da wannan, mura nake fama da ita duk ta kashe min jiki,
da k'yar na samu nayi wannan ma._


_Jinjina maras adadi gareki 'yar uwa mai albarka my dear Xarah bb, tabbas kin zamo wani jigo
a rayuwata wanda bazan iya misaltashi ba, a kullum burinki shine kiga kin faranta min rai,
wannan dalilin yasa nima nake k'ara jaddada miki yanda kike a rayuwata, kinada muhimmanci
sosai a gareni, na gaisheki sosai da duk wasu masoyana na nesa dana kusa, *Amrah luvs you
much.*_




°•°AKA°•°Princess Amrah😘
. NWA
[11:47pm, 18/01/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*


{~62~}

Farkawa nayi na ganni kwance a bisa gadon asibiti,
A hankali na fara bud'e idona saidai kuma idon yak'i bud'uwar tsabar kumbura daa yayi,
Sannu sannu na fara tariyo abunda ya sameni wanda yakr mummunan abu ne,
Kuka na fasa da k'arfi tare da mimmik'ewa a bisa gado ina fad'in "Baba! Mama!! Shikenan sun
rabani da martabata, sun keta min mutuncina wanda ko wace mace take tutiya dashi, wayyo
Allah Babana!" Na rintse idona sosai ina k'ara tuno yanda suka ringa yi dani.

Cike da natsuwa wani likita ya shigo hannunshi rik'e da file,
Sallamah yayi idona rintse na amsa sallamar,
"Alhamdulillah anyi ta barka tunda kin tashi, sannu ko?" Likitan ya fad'a tare da zama bisa
kujerar da aka tanadar domin zaman likitoci idan sun ziyarci maras lafiya.

Jin ya zauna yasa a hankali na fara k'ok'arin bud'e idona,
Idon ya bud'e saidai ba duka ba, saboda wani irin mugun kumburi ne yayi.

"Sannu kinji Aisha?" Ya fad'a tare da ajiye file d'in akan cinyarshi.

Kai kawai na d'aga bayan na gyara kwanciyata, ina mamakin yanda akayi har yasan sunana
Aisha.

"Ya jikin naki?" Ya sake fad'i kyakkyawar fuskarshi d'auke da murmushi,
"Alhamdulillah" kawai na fad'a a tak'aice,
"To masha Allah! Ina fatan dai kinsan abunda ya sameki",
Ban bashi amsa ba sai wani irin kuka dana sake b'arkewa dashi ina k'ara duba kayan dake
jikna, saboda harsu ji nayi na tsanesu baki d'aya.

"Anyway, an kawoki asibitin nan ne kwana biyar da suka wuce, daga School Clinic akayi refer
d'inki zuwa wannan asibitin a lokacin tamkar baki da rai, saboda ma an fidda tsammanin zaku
rayu,
Ganin ciwonki kamar yafi k'arfin clinic d'inku saboda manyan likitocin naku duk sun tafi hutu
basu dawo ba yasa aka kawoki nan,
Ina so ki ajiye hankalinki ki saurareni, karki sake yin kukan nan ki danganawa Allah komai,
saboda dukkan abunda kikaga ya samu bawa to muk'addari ne daga Allah, babu wani bawa
wanda yafi k'arfin k'addara, dan haka ki saurareni da kunnen basira zan miki bayanin komai".

Kai kawai na d'aga masa, ammafa hawayen dake fita har yanzu na kasa tsaidashi daga
sintirin da yake a bisa kumatuna.

Medical glasses d'inshi ya cire ya sak'alashi a lab court d'in daake jikinshi,
Ya k'ura idonshi cikin nawa, da sauri kuwa na duk'ar da kaina k'asa, sabida wani irin k'warjini
naji yamin,
"Bayan nurses na makarantarku sun kawoki na karb'eki emergency nida abokina Dr. Khalid

muka fara duddubaki,
Saidai kuma bamuyi tunanin ciwonki ba, kawaidai mun karb'eki ne muka fara yi miki gwaje
gwaje inda a take muka gane cutar hawan jini datayi miki sabon kamu dan da alama bata wuce
kwana d'aya da kamaki ba,
Bayan mun gamane kamar ance in kalla kawai naci karo da jini a bisa cinyoyinki, baku d'aya
cinyar tayi sharkaf da jini harda gullamarsa.

Hankalina ya tashi sosai nace da Dr. Khalid "kaga babbar matsalar yarinyar nan",
Sosai mukaji tausayinki, nan da nan muka fara duddubaki inda mukaci karo da raunuka sosai
a k'asanki wanda tunda nake a rayuwata ban tab'a ganin ko mai kama dashi ba,
Na tabbatarda wannan fyad'e ne akayi miki, kuma ba wai mutum d'aya ko biyu ne sukayi
aikin ba, saboda yanayin wurin ya rarake sosai da sosai.

Bansan lokacinda na fashe da kuka ba saboda kin matuk'ar bani tausayi, sannan kuma gaki
yarinya k'arama baki wuce 17 ba amma an lalata miki rayuwa,
Aune aune mukayi sosai anan muka tabbatarda baki d'auke da kowace irin cuta, kawaidai
raunukan ne da kikaji,
Harga Allah banyi tunanin zakiyi rayuwa ba,
Ganin yawan jinin da kika zubar yasa nayi miki awon jini nan na tabbatarda bakida jini sosai,
Dan haka na d'ibi nawa jinin kasantuwar zan iya badashi ga kowa na saka miki,
A tak'aice dai kwananki biyar a asibitin nan kuma bakya cikin hayyacinki, shine yanzu wata
nurse tazo gittawa taji muryarki kina sabbatu ta kirani,
Naji dad'i sosai da kuka tashi sabida jinki nake tamkar 'yar uwata ta jini, saboda duk abunda
zai samu wani ko wata sai mutum yayi tunani idan ga wani nashi abun ya faru ya zayyi? Saisa
akeso mutum ya zama mai tausayi da jink'ai ga mutane baki d'aya".

Har ya gama maganar kaina na bisa k'irjina ban sauke ba, sai wani irin rad'ad'i da zuciyata
keyi had'e da tafarfasa,
Na rasa me zanyi inji dad'i, k'asana kam baya ciwo sosai saboda yamin alluran kashe zafi,
Kaina sai azabar ciwo yake yana min barazanar fashewa,
Sunan Allah kawai nake ambato saboda yanayin da nake jin kaina kamar bani ba.

"Inaso kibar wannan al'amarin a hannun Allah, shi yasan wanda suka miki wannan abu kuma
shi zai saka miki, abun yazo da sauk'i tunda babu cutar data sameki, ki daina kuka kinga har
hawan jini ya sameki, ina miki gudun kar tashin hankali yasa zuciyarki kamuwa da wata cuta har
tayi silar rasa numfashinki".
Cike da k'arfin hali nace
"Likita mutuwa itace babban burina a halin yanzu, banida sauran wata martaba, an wulak'anta
min rayuwa, ina fatan mutuwa tazo ta tafi dani akan wannan halin da nake ciki",
Cikin sigar rarrashin yace,
"Ki daina irin wannan maganar Aisha babu kyau kace kafison ka mutu, yana d'aya daga cikin
imani fa wato mutum yayi imani da k'addara mai kyau ko maras kyau, dan Allah ki lallab'i

zuciyarki, ita k'addara bata tab'a tsallake bawa, Allah yasan halinda kike ciki kuma shi zai saka
miki".

Cike da gamsuwa da maganarshi nace "babu komai likita, na yarda cewa wannan *k'addarata
ce* (My dear Zarah bb), na barma Allah komai shine kawai zayyi min sakayya" na share
hawayena da tafin hannuna.

Sallamah mukaji anyi tare da bud'e k'ofar d'akin,
Zarah da Rabiatu ne suka kunno kai a cikin d'akin, room d'insu shine kusa da namu sannan
kuma suma course mates d'inmu ne,
Tun lokacinda Gentle ta fara sake hali wurinsu na fara komawa saboda sunada kyawawan
halaye irin wanda nakeso k'awayena su kasance dasu,
Wani lokacinma idan Gentle bata kwana a hostel ba room d'insu nake tafiya in kwana, suma
myn shak'u dasu amma ba sosai ba.

D'aga kai nayi na kallesu bayan sun shigo likita ya amsa sallamarsu,
File d'inshi ya d'auka sannan ya miyar da gilashinshi yace "Allah ya k'ara sauk'i kinji",
"Ameen" na fad'a a hankali tare da miyar da kallona gasu Zarah.

Cike da tausayi Rabi'atu ta kalleni ta kawar da kanta daga gareni saboda kukan daya kufce
mata,
Zarah ce tayi k'arfin halin cemin "sannu Aisha ashe kin tashi",
"Ehh na tashi yanzu" na bata amsa,
"To ua jikin naki?" Ta fad'a cike da tausayi,
"Da sauk'i".

Rabiatu ta juyo bayan ta goge hawayen itama tamin ya jiki,
Zarah tace,
"Kamar wasa fa a ranar da dare muka jiki shiru har sha d'ayan dare bakizo d'akinmu ba,
bayan kuma kin saba koda ace ba wurinmu zaki kwana ba kina shigowa ki mana saida safe,
Jin shirin yasa muka lek'a room d'inku amma babu kowa a ciki,
Zaman jira mukayi dan a tunaninmu ko kin tafi toilet,
Shiru dai har dare ya nitsa sosai saiga Gentle ta shigo,
Da sauri ku a tare muka mik'e Rabi'atu tace mata "tun d'azu muke nan zaune muna jiran 'yar
uwarki bamu san inda ta shiga ba".
Tsaki kawai tayi ta kama hunce kayanta ko a jikinta,
Kallon Rabiatu nayi itama ta kalleni,
"Dan Allah ki mana magana ko hankalinmu zai kwanta, kin san inda taje?",
Cike da zafin rai tace min "kai daallah malamai ku shafa min lafiya, gata nan na nad'a a kaina
nayi gammo da ita sai ku sauke",
Cikin k'arfin hali nace mata
"Me yayi zafi Gentle? Hak'k'in zaman tarene ai, dan Allah kiyi hak'uri ki sanar damu inda take
idan kin sani".

Bud'ar bakinta tace "wallahi idan baku shafa min lafiya ba kuma zansa a maku yanda akayi da
ita".

Hankali tashe muka fita daga d'akin bamu sake furta komai ba,
Iya tashin hankali mun shigeshi, a daren ranar a rintse babu wacce ta rintsa a cikinmu,
Dan haka washe gari muna gama sallar asubah muka fita nemanki,
Mune har block C muna nemanki amma babu ke babu alamarki,
Dama kuwa bamuyi tunanin zamu sameki acan d'in ba, saboda munsan ke ba mutum bace
mai yawon zuwa wuraren mutane,
A hargitse muka fita bakin gate d'in hostel,
A lokacin har gari ya fara haske,
Securities d'in gate muka tambaya ko sun ganki amma duka amsar d'ayace basu ganki ba,
Wani Baba mai fad'a sosai nasan kin ganeshi,
To harda cewa yake wai "wata k'ilama yawon iskancinta ta tafi shine zakuzo kuna wani
nemanta",
Wallahi ya bani haushi sosai har saida naji kamar in makeshi in huta,
Da haka muka fita daga area'r hostel d'in baki d'aya muka tinkari humanities.

A can gefen titi muka hangi mutum dunk'ule kamar marsa rai,
Cikin tsoro muka fara takawa har muka isa wurin,
Dubawar da zamuyi kuwa sai mukaga ashe kece,
Gaki kwance male male cikin jini kamar an d'iba an zuba miki,
Hannuwa muka d'ora aka muna neman agaji,
Can muka hangi wayarki da 'yar purse d'inki a gangarenda zai shigar da mutum dajin nan,
Bamu jira komai ba Rabiatu ta sab'eki a kafad'a mukayi School clinic dake,
Su kansu hankalinsu ya tashi saboda jinin da sukaga yana fita daga jikinki kamar an bud'e
famfo,
Ganin abun yafi k'arfinsu yasa aka sakaki a mota muna biye dasu aka kawoki wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login