Showing 27001 words to 30000 words out of 56708 words
Chapter 10 - WASIKAR JINI! COMPLETE Book By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
asare kuma guiwoyina sukayi
sanyi na
aiyana a raina cewa shikenan duk burina da
shirina ya ruguje bazan taba samun abinda ya
baroni da
kasarmu ba.
Lokacin da yarima yazid yazo nan a
zancensa sai yarima zainur ya dubeshi yayi
murmushi sannan ya zaiyane masa duk abinda ya
faru a gareshi tun daga lokacin da suka rabu
kawo iyanzu,koda jin wannan al'amari sai
hankalin yarima yazid ya dugunzuma ainun ya
dubi zainur cikin alamun tsananin damuwa yace
kai yanzu dawa zakayi shawara bisa wannan
sharadi da sarauniya lazwara tazo maka dashi?
Zainur ya gyada kai yace babu wanda zanyi
shawara dashi face kai.
Cikin matukar mamaki yazid yace saboda me
zakayi shawara dani alhalin kana da makusanta
kuma
aminai ai kamata yayi kaje kayi shawara da
sarkin yaki ko kuma gimbiya nauwara amma bani
ba,kai gimbiya nauwara ce ma tafi cancanta da
baka shawara tunda itace ta fara sanar dakai duk
sirrin dake cikin wannan al'amari.
Koda jin haka sai Yarima zainur ya kada kai yace
gimbiya nauwara ba zata iya taimaka mini ba
kamar yadda na gaya maka da farko cewar
inason ka dada gamsar dani akan addininka da
ubangijinka,saboda haka inaso mu ajiye batu
neman taimakon gimbiya lazwara a cikin tafiyar
da zamuyi izuwa inda wasikar jini take,me zai
hana mu dogara da ubangijinka akan ya bamu
kariya idan harnaga irin karfin ubangijinka da
kuma isarsa a cikin wannan tafiya mai mugun
hadari da zamuyi lallai zan karbi addinin naka
tunda gabannin ma mu isa inda WASIKAR JINI
take,
koda yarima zainur yazo nan a zancensa sai farin
ciki ya lullube yarima yazid yace na amince da
wannan shiri naka kuma ina mai tabbatar maka
da cewa ubangijina
bazai bani kunya ba lallai zaka sha mamaki kuma
zakaga abubuwan al'ajabi da idanunka yanzu
inda matsalar take shine ya za'ayi musan hanyar
daya kamata mubi
don zuwa inda WASIKAR JINI take?
koda jin wannan tambaya sai yarima zainur yaja
dogon numfashi ya ajiye sannan ya dubi yazid
yace kafin nanda cikar sati biyu zamu sani,yazid
yace yaya akayi kasan cewa zamu sani din kafin
cikar sati biyu?
Wanda ya sanar dani batu WASIKAR JINI shine
ya sanar dani hakan amma fa ina zargin cewa
sarkin yaki haiman ya san komai akan WASIKAR
JINI amma bansan
dalilin da yasa yake boye mini ba,kuma ina mai
tabbatar maka da cewa wadanda suka san batun
WASIKAR JINI A garin nan kaf basu wuce mutum
biyar ba daga ni sai nauwara,sai sarki da kuma
mahaifina waziri ridwan.koda jin wannan batu sai
yarima yazid ya jinjina kai ya dubi zainur yace
abinda nakeso dakai shine ka kula da kanka
sosai domin mahaifinka zai iya sa ido sosai
akanka kai da
sarkin yaki haiman kuma duk yadda zaiyi yasan
duk halin da kuke ciki sai yayi ba don komai ba
sai don yasan hanyar dazai bi ya rigaku zuwa
inda WASIKAR JINI take.
Zainur ya numfasa yace tabbas
sarkin yaki yayi mini nuni da hakan,ma yanzu dai
mubar wannan magana haka muje na raka ku
cikin
kasuwa don na fuskanci cewar so kuke kuje kuyi
siyayya.
Yazid yayi murmushi yace wannan gaskiya ne.
Nan take yarima yazid ya yafito Ardadu da hannu
ya taho garesu kafin Ardadu ya riske su tun sun
kara gaba inda zainur ya dubi yazid yace yakai
abokina inason fa ka sani cewa hali zanen dutse
ne don haka bana jin cewa Ardadu zai ajiye
dukkan miyagun halayensa gaba daya kuma bana
fidda ran
cewa wata ran zai iya cin amanarka don haka
jansa a jikinka abune mai hadari.
Naso ace tun sa'adda kukayi gamuwar farko ka
aika dashi barzahu domin barin mugun iri
kamarsa a doron kasa ba karamin ganganci bane,
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part C
.
Naso ace tun sa'adda kukayi gamuwar farko ka
aika dashi barzahu domin barin mugun iri
kamarsa a doron kasa ba karamin ganganci bane,
sa'adda yarima yazid yaji wannan batu sai yayi
murmushi yace tabbas abinda ka fada gaskiya ne
amma inaso ka sani cewa a halin yanzu Ardadu
yana cin albarkacin wata babbar rigane daya
sanya wacce ita ce take bashi kariya daga
gareni,ba
wata riga bace wacce Ardadu ya sanya ba face
addinin musulunci daya karba,muddin yana yin
abubuwan da Allah ya wajabta masa bani da ikon
kashe ko cutar dashi face ya kauce daga kan
hanyar tafarkin gaskiya abinda nasani kawai
shine indai bashi da rabo a cikin wannan addini
na gaskiya tofa watarana saiya saba dokar Allah
wacce zata bani
damar na kawar dashi don haka shine zai zabawa
kansa abinda zai fishsheshi.
Nan take dai su biyun sukayi shiru basu sake
cewa uffan ba sukaci gaba da kutsawa cikin
kasuwar kuma adaidai wannan lokaci ne ardadu
ya iso daf dasu suka cigaba da tafiya tare su
ukun.
.
Al'amarin Sarkin Yaki Haiman kuwa lokacin daya
baro gidansa bisa doki da nufin ya tunkari fadar
saiyabi wata hanya wacce bama ita ya saba bi
ba,ita dai wannan hanya yankece ta bayan gari
dole ne mutum ya ratsa ta gefen wani daji
sannan ya dawo kan hanyar cikin garin Hanya ce
mai sauri wadda nan da nan zata kai mutum
izuwa gidan sarautar birnin latul harus cikin
kankanin lokaci.
Koda sarkin yaki ya iso tsakiyar dajin dake
wannan hanya saiyaji alamun motsi a cikin
duhuwoyin dake zagaye da tsakiyar hanyar da
yake kai,abinka da tsohon mayaki wanda yasan
shirin abokan gaba kuma yasan duk irin tuggin da
ake amfani dashi wajen harin sumame sai yayi
sauri yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak ya baza
idanunsa da kunnuwansa izuwa cikin duhuwoyin
tsawon yan dakiku bai sake jin motsin komai
ba,kwatsam saiga wata barewa ta fito da gudu
daga cikin ciyayi ta nausa yamma ta kasa tsere
da wata damisa,koda ganin hakan sai sarkin yaki
yayi
murmushi kuma ya saki jikinsa yaci gaba da
tafiya abinsa cikin kwanciyar hankali.
Kash rashin sani yafi dare duhu ashe a can gaba
kadan wasu dakarun sumame ne a kwance cikin
duhuwar bishiyoyi suna
sanye da korayen tufafi wadanda kalarsu ta saje
data ciyawar wajen kuma duk sun rufe fuskokinsu
idanunsu kadai ake gani suna dauke mugayen
makamai boye a jikinsu.
Adadin wadannan dakaru sunkai dubu kuma sun
kware ainun a iya yaki.Saida sarkin yaki haiman
ya karaso tsakiyar wadannan
dakarun sumamen sannan suka mike tsaye a tare
sukayi masa kawayanya nanfa aka fara kallon
kallo a tsakaninsa dasu.A sannan ne shugaban
dakarun wani dogo mai kirar sadaukai ya ratso ta
tsakiyarsu ya iso kusa da sarkin yaki suka
karewa juna kallo
sannan shugaban dakarun sumamen ya tuntsire
da dariya.Lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa
ya nuna haiman da dan yatsa ya daka masa
tsawa yace yakai haiman idan kanason ka tsira
da rayuwarka ka bamu abinda muke bukata
yanzu take.
Koda jin wannan batu sai sarkin yaki haiman ya
bushe da dariya sannan ya dubi shugaban
dakarun yace amma dai kai ka cika wawa mara
tunani in banda hankalinka ya gushe ta yaya kake
zaton zaka iya bani tsoro da batun mutuwa,shin
ka mantane cewa nine wanda ya siyar da
rayuwarsa sau babu adadi ya shiga tsakiyar
abokan gaba yana sara da suka,bansan iyakar
adadin rayukan da takobina ta dauka ba,zuciyata
ta dade da kekashewa ga barin tsoron ganin
zubar da jini,ai MAKASHIN MAZA MAZA KAN
KARSHI.
.
idan ku yan fashi ne masu neman abinci ku fadi
ko nawa kuke so zan iya baku amma idan wani
abu kuke nema wanda zakuyi amfani dashi
wajen cuta da kasata ko al'ummata tofa bazaku
samu ba saidai koni koku wani ya zama gawa
anan wurin.
Koda jin wannan batu sai ran shugaban dakarun
ya baci ya dakawa haiman tsawa yace kai
dakata haka ba cacar baki ce ta kawo mu ba ko
bata lokaci abinda muke so ka bamu shine
taswirar
hanyar zuwa inda WASIKAR JINI take wacce sarki
Aiyuba ya baka,bamu wannan taswirar yanzu
yanzu ko kuma mu kashe ka mu dauka daga
jikinka.
Sa'adda shugaban dakarun yazo nan a zancensa
sai sarkin yaki haiman ya kamu da tsananin
mamaki bisa yadda akayi wadannan dakarun
sumame suka san abinda ya faru tsakaninsa da
sarki alhalin a sirrance sukayi komai a cikin
turakarsa kuma gimbiya nauwata ce kadai a
wajen sannan yana da tabbacin cewa babu yadda
za'ayi nauwara ta tonawa mahaifinta asiri tunda
tamkar ta tonawa kanta ne,saboda makiyanta ta
baiwa makamin da zasu iya hallakata dashi ne.
Lokacin da sarkin yaki haiman yazo nan a
tunaninsa sai ya fusata ainun zuciyarsa ta kama
tafarfsa kamar zata kone kawai saiya zare
takobinsa ya dubi shugaban dakarun sumamen
cikin tsananin fushi ya daka masa tsawa yace kai
tsohon makiri karen farautar azzalumai kayi sani
cewa daku da
wanda ya turoku tsakanina daku sai kisa.
Kafin shugaban dakarun ya budi baki yace wani
abu tuni haiman ya dako tsalle sama daga kan
dokinsa ya kaiwa shugaban dakarun mummunan
sara a wuya da nufin ya cire masa kai,cikin bakin
zafin nama shugaban dakarun ya sunkuya ya
kaucewa saran amma duk da haka saida kafin
takobin ya shaftare wani bangare na rawanin
daya rufe fuskarsa dashi.
Take rawanin ya kwance ya fadi gefe amma sai
haiman yaga cewa bakuwar fuska ce wadda bai
taba gani ba a cikin birnin latul harus,al'amarin
daya tabbatar masa da cewa lallai wadannan
dakaru
hayarsu aka dauko.
Nan take sauren dakarun sukayi
caa akan sarkin yaki da nufin suyi masa rubdugu
su sassara shi amma sai ya zame musu alakakai
ya rinka tarwatsasu da karfin tsiya yana kare
dukkanin harinsu kuma ya kawo musu sara da
suka ta sama da kasa gefe da gefe.
Wani irin salon fada haiman ya rinkayi ya zamana
cewa yana katantanwa a sama da kasan dakarun
kuma ya hada da gabza musu naushi da bugu
amma saboda kwarewar dakarun a iya yaki gami
da tsananin nacinsu da taurin zuciya sai gashi
suna shanye duk irin dukan da yake musu duk da
cewa yana hada musu jini da majina kuma yana
saran sassan jikinsu jini na zuba amma basu fasa
kara matsarsana suna kai masu mugayen hare
hare.
Shi kuwa shugaban wadannan mugayen dakaru
sai kawai ya koma gefe daya yaja tunga ya zuba
ido domin yaga iyakar jarumtakar haiman da
iyakar juriyarsa.
Wohoho manyan jarumai sune wadanda suka
saba dayin karo da maza komai yawansu kuma
sune wadanda basusan tsoro ba sannan komai
wuya komai tsanani basa gudu a filin daga saidai
a gudu a barsu ko kuma a ci karfinsu a kashe su
a wajen.
Saida aka shafe sa'a uku cur ana bakin artabu
tsakanin sarkin yaki haiman da wadannan dakaru
ya zamana cewa ya kashe mutum dari uku da
arba'in a cikinsu amma shi baije kasa ba mma fa
anyi masa
manyan raunika gudu uku a jikinsa har jiri ya fara
dibarsa sakamakon jininsa dake zuba amma
saboda
bakin naci irin nasa yaki yaje kasa da zarar
dakarun sun yunkura masa sai kaga shima ya
afka musu yaci gaba da yakarsu cikin gagarumin
karfi tamkar a sannan ne ya fara yaki....
Nima ganin wannan gumurzu yasa na tsaya
kallo...
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part D
.
Tamkar a sannan ne ya fara yakin.Al'amarin daya
fara tsorata ragowar dakarun kenan suka fara ja
da baya musamman da sukaga cewa gawarwakin
yan uwansu fa karuwa sukayi ba raguwa ba.A
hakan dai aka cigaba da wannan yaki har Haiman
ya sake samun nasarar kashe mutum dari biyu
da ashirin da uku ba tare da an sakeyi masa rauni
ko daya ba,al'amarin daya fusata shugaban
dakarun kenan ainun ya dakawa yaran nasa
tsawa yana mai umartarsu dasu ja da baya su
bashi wuri.Nan take
kuwa su duka sukaja da baya shugaban dakarun
ya zare takobinsa sannan ya kama rigar jikinsa
da hannu daya ya yageta koda Haiman yaga
tsananin
girmansa da kuma tarin kwarjininsa gami da
murdewar jikin nasa sai yaji zuciyarsa ta buga da
karfi domin ya tabbatar da cewar a yadda ya
jigata dinnan kuma jini ke zuba a jikinsa bazai iya
hallaka wannan basamuden kato ba,amma kuma
daya tuna
cewa wannan yaki fa da yakeyi yaki ne na ceton
kasarsa da al'ummarsa dama gaba dayan
mutanen duniya daga sharrin azzalumai sai yaji
dukkan tsoro ya kau daga zuciyarsa nan take yayi
wuf shima ya yade rigar jikinsa ya daure raunin
da yafi zubar da
jini a jikinsa don tsaida jini,sannan ya gyara
tsayuwarsa yana mai fuskantar shugaban
dakarun
suka fara kallon kallo,kwatsam sai suka rugo da
gudu izuwa kan juna suka ruguntsume da sabon
azababben yaki.
Wohoho!Masifa ba'a sa mata rana
duk sa'adda karfi ya hadu da karfi tofa bala'i
yazo kenan kuma sai mai rabon ganin badi shine
zaikai
labari.
Lokacin da wadannan zaratan jarumai biyu suka
kacame da masifaffen yaki suka wanzu suna
masu kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin
bakin zafin nama da juriya da jarumtaka ta ban
al'ajabi sai suka dimautar da duk dakarun dake
wajen,kuma suka tashi hankalin duk wani abu
mai rai dake cikin dajin domin babu shiri
tsuntsaye suka kama yin kaura suna barin
shekarsu.
kananun dabbobi kuwa suka kama guje guje suna
fadawa cikin ramukansu suna buya,ba komai ne
ya haddasa hakan ba face bishiyoyin dake wajen
ma basu tsira daga sharrin kaifin takubban
jaruman biyu ba domin duk sa'adda dayansu ya
kaiwa dayan sara da zarar ya goce ya sami
bishiya saidai kaga bishiya ta rabe
gida biyu komai girmanta haka ma idan naushi ya
kawo ya sami bishiya komai girman saita jijjigo
daga cikin kasanta ta fadi kasa.
Nanfa suka tayar da kura dajin gaba daya yai
fururu,su kuwa sauran dakarun sumamen da suka
dimauce suka firgita bisa ganin wannan mugun
bakin artabu da akeyi da shugabansu basu san
sa'adda suka rinka cika wandunsu da iska ba
suna neman wajen buya,saida aka shafe sa'a
daya da rabi ana wannan fafatawa dayansu bai
sami nasarar cutar da daya ba,ba shiri
kowannensu yaja da baya sukayi cirko cirko suna
haki da kallon juna kamar zakaru,damar da suka
samu kenan suka dan huta kuma suka shiga
tunanin dabarar da zasuyi domin su sami
nasara.Ashe kowannensu dabara daya ce tazo
masa ta sauya salon fadan,aikuwa sai suka
yunkura suka tasowa junansu cikin mugun nufi
lokaci guda.
Suna haduwa suka kacame da masifaffen yaki
amma wannan karon sai suka hada da kaiwa
juna naushi da bugu da hannu da kafa,faruwar
hakan keda wuya sai yakin
ya sauya yanayi domin a sannan sarkin yaki
Haiman ya gane kuskurensa saboda shugaban
dakarun ya fishi karfin damtse nesa ba kusa
ba,idan Haiman ya
jurewa shugaban dakarun naushi biyar a lokaci
guda sai kaga ya shanye duka amma da zarar shi
kuma yayi masa naushi daya sai shugaban
dakarun ya yarda takobin hannunsa yacigaba da
gabzawa haiman naushi a fuska da ciki har sai
haiman ya yarda takobin nasa kuma ya rinka
faduwa kasa jini na tsartuwa abakinsa.
Saida shugaban dakarun ya yiwa Haiman laga
laga yaga ko kyakkyawan motsi bayayi sannan
yazo kansa ya tsaya ya zura hannunsa cikin
aljihun rigarsa ya fiddo wannan fata mai dauke da
taswirar dajin Hajarul Aswad.
Cikin tsananin farin ciki shugaban dakarun ya
bushe da dariyar farin ciki,kawai sai ya zaro wata
katuwar
wuka daga kugunsa ya daga sama zai kirbawa
Haiman a kirjin,kawai sai yaji an ruke hannunsa
ta
baya wani irin riko mai tsauri da zafin gaske har
yaji kamar hannun nasa zai karye.Ba shiri ya saki
wukar dake hannunsa ya juya da kyar.
Ba wani ya gani ba ruke da hannunsa face
Sarauniya Lazwara koda yaga ashe ma yarinya ce
ta ruke masa hannun nasa saiya
firgita ainun yayi zaton cewa aljana ce ta rukeshi
don haka saiya sume a tsaye nan take ta saki
hannun nasa ya sulale kasa,duk wannan abu
dake faruwa Haiman baya cikin haiyacinsa baima
san wanda ke tsaye akansa ba.Saida sarauniya
Lazwara ta gama
dinke raunikan dake jikin sarkin yaki haiman ta
shafa masa magani sannan ya farfado daga
dogon suman da yayi ya dawo cikin haiyacinsa
sosai,koda ya bude
idanunsa yayi arba da sarauniya Lazwara zaune a
gabansa sai shima ya firgita yadan ja da
baya,koda ta fahimci cewar ya tsorata da ganinta
saitayi murmushi ta dubeshi tace kwantar
dahankalinka yakai sarkin yakin birnin Latul
Harus ashe har zaka
kasa shaidani don mun rabu tsawon shekaru
takwas
kacal,nice fa sarauniya Lazwara.Koda jin wannan
batu sai mamaki ya turnuke haiman ya yunkuro
da
kyar ya gyara zamansa yana mai jingina bayansa
a jikin wata bishiya sannan ya dubi Lazwara yace
godiya a gareki ya shugabata tabbas kin ceci
rayuwata data dukkan al'ummar dake wannan
nahiya gaba daya,caraf sai Lazwara ta tari
numfashinsa tace
basai kayi mini bayanin komai ba domin babu
abinda ban sani ba,ina zaune a can cikin birnina
cikin turakata na ganka a cikin madubin tsafina
kanayin yaki da wadannan abokan gaba,koda
naga
sunci karfinka zasu hallaka ka sai nayi amfani da
karfin sihirin tsafina na baiyana anan na ceci
rayuwarka,yanzu ga abinda yaso ya
kwata a hannunka.Nan take Lazwara ta mikawa
Haiman wannan fata mai dauke da taswirar
hanyar zuwa dajin Hajarul Aswad ya karba
sannan tace ka
sake adana wannan fata da kyau domin wanda
yake farautarta yafi wuta zafi,kuma yafi annoba
masifa,kuma yafi kowane irin ciwo radadi da zugi
zan cigaba da baka kariya da taimako
gwargwadon
iyawata har izuwa ranar da zaka yadda kuka
shirya kai da sarki Aiyuba amma idan ka koma
gida ka
sadu da danka Yarima Zainur ka gaya masa nace
lallai ya saki reshe ya kama ganye,tunda ya hada
kai
da wannan bafatake domin bazai taba kaishi ga
nasara ba saidai hallaka.
Ka gaya masa cewar har yanzu lokaci bai kure ba
yana da sauran dama da zaizo har fadata ya
karbi taimakona bisa ka'idar dana shimfida
masa.
Koda gama fadin hakan sai sarauniya Lazwara ta
bace tamkar bata taba wanzuwa ba a wajen,cikin
karfin hali sarkin yaki haiman ya mike tsaye
yabar wajen yaje inda dokinsa yake yana dingishi
da kyar ya kama dokin ya haye kansa sannan ya
sakar masa linzami ya tunkari hanyar gidan
sarki...
SHIN SARKIN YAKI ZAI IYA TSARE WANNAN
TASWIRA HAR IZUWA LOKACIN DA ZAI DANKATA
A HANNUN YARIMA ZAINUR?
TSAKANIN WAZIRI RIDWAN DA YARIMA ZAINUR
WAYE ZAI ZAMA SARKI BIRNIN LATUL HARUS?
WACE IRIN BAKAR WAHALA YARIMA ZAINUR DA
WAZIRI RIDWAN ZASU SHA A CIKIN DAJIN
HAJARUL ASWAD?
SHIN ZAINUR ZAI CANZA SHAWARA YA KOMA
WAJEN SARAUNIYA LAZWARA?
WANE IRIN TAIMAKO YARIMA YAZID ZAI BAIWA
YARIMA ZAINUR A CIKIN TAFIYARSU TA ZUWA
DAJIN HAJARUL ASWAD?
YAUSHE NE SARKI AIYUBA ZAI MUTU KUMA ME
ZAI FARU BAYAN MUTUWARSA TASA?
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyar (5)
Part A
.
WAZIRI Ridwan na zaune cikin kujerar turakarsa
tare da matarsa Gimbiya Ra'isa suna cikin
matukar farinciki tana shayar dashi ruwan barasa
yana ta faman kyalkyala dariyar murna sai ta tari
numfashinsa tace,yakai mijina waishin meye
tabbacinka cewa wadannan dakarun sojan haya
zasu iya hallaka sarkin yaki su karbo maka
wannan taswira ta zuwa Dajin Hajrul Aswad?
Koda jin wannan tambaya sai waziri ridwan yayi
murmushi yace yake Ra'isa nasan iyakar
jarumtakar sarkin yaki haiman
kuma nasan ta wadannan dakarun sojan haya
don haka ko kada bani da shakka akan nasararsu
a kansa.Ina mai tabbatar miki da cewa daga
yanzu a koyaushe zaki iya ganin an kawo min
wannan taswirar.Gama fadin haka keda wuya sai
babban hadimin waziri ridwan yazo bakin kofar
turakar yayi gyaran murya yace ya shugabana ga
bakonka na dazu da safe ya dawo.Koda jin haka
sai waziri Ridwan ya mike tsaye zumbur cikin
dimbin farinciki
ya dubi Ra'isa yace ai dama na gaya miki bari
naje na karbo taswirar ki gani.
Kai tsaye waziri ridwan ya bude kofa ya fice daga
cikin turakar ya isa can babban falo inda yake
ganawa da dukkan bakinsa.Yana shigowa falon
sai zuciyarsa ta buga da karfi ba komai ne ya
haddasa hakan ba face ganin shugaban dakarun
sojan hayar nan a tsaye kansa a sunkuye cikin
alamun rashin nasara kuma babu taswira zuwa
dajin Hajrul Aswad a hannunsa.Koda ganin waziri
Ridwan sai shugaban dakarun ya zube kasa bisa
guiwoyinsa ba tare da ya dago da kansa ba ya
budi baki yace ya shugabana ka yafe min mun
kasa cika wannan aiki.Koda jin wannan batu sai
ran waziri ridwan ya baci zuciyarsa ta kama
tafarfasa kamar zata kone kuma jikinsa ya kama
tsuma kamar
wanda ake sokawa allura,bai san sa'adda yasa
kafarsa ba ya doki kirjin shugaban dakarun.
Duk da girman shugaban dakarun saida ya fadi
kasa.
Cikin tsananin fushi Waziri Ridwan yace ta yaya
kuka kasa samun nasara akan haiman alhalin na
tabbatar da cewa kun fishi karfin damtse da
juriyar yaki?
Yanzu kana nufin kace kenan duk makudan
kudaden dana baku sun zama a banza kenan?
Koda jin wannan tambaya sai shugaban dakarun
ya yunkura da sauri ya mike zaune ya dubi waziri
ridwan yace,ya shugabana hakika na sami nasara
akan sarkin yaki
haiman domin saida nayi masa laga laga na
sumar dashi kuma take na ciro taswirar zuwa
dajin hajarul aswad a jikinsa amma faruwar
hakan keda wuya sai
naji an cafke hannuna ta baya anyi mini wani irin
mugun riko wanda naji kamar hannun zai
ruburbushe.Koda na juya na kalli wanda yayi mini
wannan ruko sainaga ashe wata yarinya ce ma
karama wacce shekarunta ba zasu haura sha
ba.Take na gane cewa aljana ce bansan sa'adda
na