Showing 45001 words to 48000 words out of 56708 words

Chapter 16 - WASIKAR JINI! COMPLETE Book By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

an
boye sai aka bar
tantuna uku kawai kuma akayi mutum mutumi na
dakaru guda shida kacal aka tsaida su a
kusurwoyin sansanin hudu.
Kai har wuta aka kunna a tsakiyar sansanin aka
ajiye dakaru na mutum mutumi guda hudu a
zaune sun kewaye wutar alamar cewa dumi sukeji
saboda dama a na cikin
lokacin matsanancin sanyi ne.Gama yin hakan
keda wuya sai su Yarima Yazid suka bar wajen
gaba dayansu sukaje suka biye dawakansu kuma
suka hau saman bishiyoyi suka zazzauna bayan
kowannensu ya lullube jikinsa da ganyaye gaba
daya,idanunsu ne kadai a waje kuma tazarar dake
tsakaninsu da sansanin batafi kamu talatin ba ya
zamana cewa a saman sun yiwa sansanin
KAWANYA.
Haka dai su yarima Yazid suka cigaba da lampo
akan bishiyoyi kamar birirrika, abu kamar wasa
har saida rana ta fadi ko motsin wani abu basu ji
ba ko a cikin dajin kuma basu hango wata
runduna ba mai zuwa.
Al'amarin da yasa zuciyar kowa ta karaya kenan
kuma guiwarsu tayi
sanyi.Kuma duk suna rike da kwari da baka.Sai
Nauwara ta sauke bakanta kasa ta cire kibiyar ta
mayar da ita cikin kuttun kibiyoyin dake goye a
bayanta kuma ta shimfida bayanta akan reshen
bishiyar ta kishingida tana mai duban Zainur cikin
alamun karayar zuciya tace yakai dan uwana ina
ganin cewa wancan abokin naka tunanin banza
yayi kawai har da yake tunanin cewa makiya zasu
biyo bayanmu,banda abin sama shiga ba duba
yakeyi ba kuma ba tsafi ba,akan wane dalili
zuciyarsa zata raya masa cewa ana biye
damu.Koda jin wannan jawabi sai Yarima Zainur
ya bata rai ya dubeta cikin alamun fishi yace idan
kowa a sansanin nan namu bai yarda da abokina
ba ni na yarda dashi dari bisa dari tunda dai
nasan
cewa baiyi imani da komai ba face Allah to nima
na gasgasta duk maganarsa kuma duk irin
umarnin
daya bani zan bishi.Kada kiyi garaje a cikin
wannan al'amari ki zamo mai hakuri da zuba
idanu,lallai zaki sha mamaki.
Gama fadin hakan keda wuya kuwa sai suka jiyo
sukuwar dawakai
daga nesa a bangaren gabas,cikin hanzari kowa
ya dana kwari da bakansa ya tabe,dama Yarima
Yazid da sarkin yaki Haiman sun gayawa kowa
cewa kada kowa yayi wani yunkuri face sun bayar
da
inkiya.
Sannu a hankali sautin gudun dawakan ya rinka
karuwa wanda har yasa kasar dajin gaba daya ta
fara rawa sai kace miliyoyin kofatun dawakai ne
ke sukuwa.In badon zuciya irin ta musulunci ba
da tuni su Yarima Yazid sun firgita sun zubar da
makamansu sun falfala da gudu domin tsira da
rayukansu.
Ai kuwa koda rundunar ta matso kusa hatta
sarkin Yaki Haiman saida zuciyarsa ta buga da
karfi bisa hango sarki Marwatu da Waziri Ridwan
akan gaba cikin
gagarumar shigar yaki ga dubban daruruwan
miyagun dakaru a bayansu masu tsananin
kwarjini
da ban tsoro tamkar sa ci babu kuma dukkaninsu
suna dauke da muggan MAKAMAN YAKI sai ihu
suke gami da kururuwa suna karawa dawakansu
kaimi tamkar zasu tashi sama.
Koda ganin wannan BAKAR RUNDUNA sai Yarima
Yazid ya fara yiwa Allah kirari a cikin zuciyarsa
yana ambaton sunayensa tsarkaka bisa neman
taimakonsa.Kamar
sarkin yaki Haiman,Zainur da gimbiya Nauwara
sun san abinda yarima Yazid keyi sai suma suka
kama kiran sunan Allah a cikin zukatansu suna
masu neman tallafinsa.
Hakika duk wanda ya dogara da Allah to Allah zai
iya masa duk abinda ya gagareshi,nan take su
Sarkin Yaki Haiman sukaji dukkan tsoro ya kau
daga cikin zukatansu sannan kuma sai sukaji
wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinsu.
Saida ya rage saura baifi taku goma ba tsakanin
wannan runduna da sansanin nasu yarima Yazid
sai sarki Marwatu ya tuna cewa sunyi
ganganci da basu tsaya ba.
Sun tabbata da cewa babu wani tuggun da ake
shirya musu a farko
amma sai yayi tunanin cewa an shirya musu,nan
take sarki Marwatu ya wangame bakinsa ya bude
muryarsa da karfi yana mai bayar da umarnin a
tsayar da dawakai kada a fada cikin sansanin
amma ina BAKIN ALKALAMI YA BUSHE.Saboda
ihun dakarun nasu da karar kofatun dawakansu
dake kartar kasa ya danne sautin muryar tasa
kuma ga kura ta turnuke sama da kasa kowa
baya shaida kowa sosai.
Wohoho.
AJALI idan yayi kira dole ne a amsa,ai kuwa
wadannan dubbunan
daruruwan dakaru na fadawa cikin sansanin sai
ruwan kibiyoyi gami da fikakkun rassan bishiyoyi
suka rinka soke su har dawakansu ma suka rinka
zubewa kasa MATATTU.Koda na baya sukaga
yadda na gabansu ke ta zubewa kasa tamkar ana
sassabe a hona sai suka firgita ainun suka kada
linzamin dawakansu suka juyo da baya,amma sai
suka rinka jin ruwan kibiyoyi da fikokin rassa na
barar dasu kasa.Daga can kuma sai kasa ta rinka
riftawa dasu suka rinka fadawa cikin
ramuka,fikakkun rassa na tsire su suna
mutuwa.Nanfa dakarun suka dada dimaucewa
domin bala'i yakai bala'i saidai kaga jini na
tsartuwa da feshi dakaru na rusa ihu da kururuwa
suna zube kasa matattu
™Abbas Abdulkadir hada hada™ Sama da
kasa,gabas da yamma,kudu da arewa ruwan
kibiyoyi suke sha ba kakkautawa.Koda
mutum ya sami nasarar fita daga cikin sansanin
saidai kawai yaji kasa ta rufta dashi ya
hallaka.Saida aka shafe kusan sa'a daya da rabi
ana wannan ruwan kibiyoyi da fikakkun itatuwa
dakarun su sarki Marwatu nata mutuwa tamkar
ana karkado busasshen fure daga jikin bishiyoyi
ya zamana cewa kimanun kaso daya da rabi na
dakarun sun hallaka.Da kyar da sidin goshi Waziri
Ridwan da sarki Marwatu suka tsira da rayukansu
amma saida kowannensu ya sami mugun rauni a
jikinsa,shida waziri Ridwan a damtsen hannunsa
na dama kibiya ta soke shi ta hudashi ta faso
bayan hannun.Saboda tsananin zafi da zugin da
yaji sai ya kasa zare kibiyar,ga jini nata zuba
amma a haka ya rinka rarrafe da rub da ciki ya
samu ya ruga cikin daji ya buya a cikin duhuwar
bishiyoyi.Shima sarki Marwatu da sauran dakarun
nasa haka suka samu da kyar suka isa inda
waziri
Ridwan yake kowannensu dauke da mugun
rauni.Shi Sarki Marwatu ma a cinyar ta hagu
kibiya
ta soke shi ya fadi kasa sai janyoshi akayi a kasa
a wulakance aka tserar da rayuwarsa da kyar.
.Sai bayan su sarki Marwatu sun iso cikin
wannan duhuwar ciyayi ne suka sami nutsuwa
suka kafa sansani kuma suka zagaye
sansanin da dakaru don tabbatar da tsaro.A
sannan ne aka shiga yiwa masu rauni
magani,sarki
Marwatu da Waziri Ridwan kuwa saida likita ya
basu wani maganin bacci mai karfi suka bingire
sannan aka iya cire musu kibiyoyin dake jikinsu
aka sa musu magani.Duk su biyun babu wanda
ya
farfado sai bayan sa'a uku a firgice duk su biyun
suka farfado suka mike zaune a cikin tantin da
suke kwance.
Koda suka kalli junansu kuma suka
tuno da irin mummunar barnar da'akayiwa
dakarunsu acan sansanin su yarima Yazid kuma
suka dubi raunikan dake jikinsu sai suka kamu da
tsananin bakin ciki zukatansu suka kama
tafarfasa kamar zasu kone.
A cikin hadin baki kowannensu ya wangame baki
ya kwarara uban ihu na bakin ciki mai tsananin
firgitarwa take sautin ihun nasu
ya cika dajin gaba daya da amsa kuwa,daga cam
sai sarki Marwatu ya dubi Waziri Ridwan cikin
tsananin fishi da takaici da bakin ciki yace,yaya
akayi wadannan abokan gaba sukayi mana irin
wannan muguwar mamaya?Menene dalilin da
yasa basirarmu ta toshe har muka afka musu
cikin
gaggawa haka ba tare da munyi tunani da nazari
ba?
Waishin menene dalilin da yasa sihirinmu na tsafi
yaki tasiri akansu.
Lokacin da waziri Ridwan yaji wadannan
tambayoyo daga bakin sarki Marwatu saiya kawo
gwauron numfashi ya ajiye
sannan ya dubi Marwatu cikin alamun nutsuwa
yace yakai abokina kayi sani cewa ahalin yanzu
yarima Zainur ya hadu da wani takadirin aboki
wanda ya kasance ma'abocin ADDININ
MUSULUNCI waishi Yarima Yazid.Karfin sihirin
tsafin Yarima Yazid ne yasa muka kasa samun
nasara akansu.Idan har muna son mu mallaki
wannan taswirar ta zuwa dajin Hajarul Aswad
dole ne mu
kashe wannan bakon jarumi kafin su riga mu
zuwa can kogon na Hajarul Aswad,karfin
damtse,iya yaki ko sihirin tsafi ba zasu sa mu
sami nasara ba akan wannan takadirin bakon
jarumi amma
kowannen dan adam yana da lago kuma yana da
rauni dole ne muyi amfani da rauninsu da
lagonsu
kafin mu sami nasara akansu.
Koda jin wannan batu sai Sarki Marwatu yayi
ajiyar zuciya yace ta yaya zamu gano rauninsu
da lagonsu,kayi sani cewa nayi mummunan bakin
ciki bisa ganin yadda su Yarima Zainur suka
kashe mini dubunnan daruruwan dakaruna da
kuma yadda muka sha
bakar wahala a wannan YAKIN SUNKURU da
sukayi mana,ni yanzu babban burina shine mu
rama abinda sukayi mana naga jinin jama'arsu
ya zuba da yawa akan kasa su kuma mu kamasu
a raye
muyi ta gana musu azaba mafi radadi a doron
kasa har ta zamo sanadin ajalinsu.
Ta yaya kake ganin wannan bukata zata biya?
Koda jin wannan tambaya sai Waziri Ridwan ya
bushe da dariya mugunta lokaci guda kuma ya
murtuke fuskarsa yace ka bani kwana uku rak
zanyi tunani a kan
hakan.
Tab kuji Mugayen azzalumai wanda zuciyarsu ta
kekeshe da zalunci.Bayan defeat din da akayi
musu duk sun manta da yadda suka tsira da kyar
har Sarki Marwatu ana jansa da a kasa domin a
tsirar da rayuwarsa.
Lallai sun cika azzalumai.Bari in dakata anan:
Dafatan littafin yayi so karku bani kunya.
Like, comment and share necessarily
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Bakwai (7)
Part B.
.
ZANYI TUNANI AKAN HAKAN.
KODA JIN HAKA SAI MARWATU YA ZAZZARO
IDANU YACE YANZU KANA NUFIN KACE BA ZAMU
CIGABA DA BINSU BA HAR SAI BAYAN KWANA
UKU?
Ai kuwa zasu iya bamu tazarar da ba zamu iya
cimmu su ba.Waziri Ridwan yayi dan guntun
murmushi yace kwantar da hankalinka abokina ai
ba daina binsu zamuyi
ba kuma duk tazarar da zasu bamu zamu iya
riskarsu a cikin kankanin lokaci.
Abu mai mahimmanci shine mu karbe wannan
taswirar dake
hannunsu kafin su isa can kogon Na Hajarul
Aswad,ina mai tabbatar maka da cewa su kansu
yanzu basu san inda suka dosa ba daman basu
fara amfani da taswirar ba amma tabbas tunda
sunga sun sami wannan gagarumar nasara
akanmu zasu iya fara amfani da ita a gobe.
Ai dama taswirar zata fara aikine a karkashin
wancan daji da sukayi mana wannan mummunar
barna,ina mai yi maka alkawari cewa kafin su isa
karshen wannan daji zamu kashe dukkanin
dakarunsu su kuma zamu kama su a hannu muyi
yadda muka so dasu.
Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube sarki
Marwatu yace na yarda da kai abokina domin
nasan halinka tun muna yara babu abinda zaka
sa a gabanka ya gagareka,lallai kana da mutukar
sa'a da rabo.
Koda jin haka sai suka bushe da dariya a tare
suna masu rungume junansu.
Wannan shine abinda ya faru a tsakanin sarki
Marwatu da Waziri
Ridwan bayan sun kaiwa su yarima Zainur harin
bazato domin suyi musu kisan farat daya amma
sai akayi KAIKAYI KOMA KAN MASHEKIYA.
*
A Can sansanin su yarima Yazid kuwa bayan kura
ta lafa abokan gaba sun gudu sai kowa ya fito
daga cikin maboyarsa aka kama yin kabbara
saboda farin cikin nasarar da akayi a wannan
yaki.Nan take yarima Zainur ya rungume yar
uwarsa Gimbiya Nauwara shi kuma sarkin yaki
Haiman saiya rungume yarima Yazid yana mai yi
masa godiya dasa masa albarka.
Haiman ya janye jikinsa daga cikin na Yazid ya
kama hannunsa ya
jashi izuwa kan wani dutse suka zauna a lokacin
da Zainur da Nauwara suka juyo suka zuba musu
ido.Koda Yazid ya hada ido da Nauwara sai yayi
sauri ya sunkui da kansa kas don kada ta
fuskanci cewa akwai wani abu a ransa game da
ita.Tabbas yarima Yazid yaji son Nauwara a cikin
zuciyarsa
kawai tsananin dauriya ce da kawaici tasa ya
danne zuciyarta sa kuma ya kasa furtawa ko
nuna abinda ke cikin ran nasa.
Sarkin yaki Haiman ya dubi Yazid a cikin nutsuwa
yace yakai wannan gwarzon jarumi mai dumbin
hikima da basira kayi sani cewa yau shekara
ashirin da biyar kenan ina ruke da mukamin
sarkin yaki,kuma na halacci yakoki a kalla guda
talatin da uku amma ban taba
ganin yakin da ya bani tsananin mamaki da
al'ajabi irin wannan da mukayi yau ba.
Ka tuna cewa gaba dayanmu bamu kai mutum
dari uku ba amma sai gashi mun sami nasara
akan mutane sama da dubu dari biyar.Ban tava
ganin tugu da dabarar yaki ba irin wannan dakayi
mana,in badon kai musulmi bane nima haka da
sai nace ba mu bane mukayi yaki su Waziri
Ridwan ba Aljanu ne suka yake su.
Koda jin wannan batu sai yarima
Yazid yayi yar guntuwar dariya sannan yace ai
dama shi aikin Allah haka yake kada kayi
mamakin
cewa akwai sa hannun mala'ikun Allah a cikin
wannan gumurzu da mukayi musamman idan kayi
la'akari da tsananin yawan wadannan abokan
gaba,ya kamata a ce tun a farkon fara yakin duk
makaman da muka tanada sun kare amma sai
gashi ana cigaba dayi musu ruwan kibiyoyi da
fikokin itatuwa duk yawan nasu sai gashi ya
zama na banza,ina mai tabbatar maka da cewa
idan har bawa zai tsare dokokin Allah kuma ya
sallama komai nasa a gareshi to inda duniyar nan
kaf zata taru tofa baza'a iya cutar dashi ba,amma
yayin da mutum daya jal a cikin miliyoyin
musulmai ya aikata wani zunubi to fishin Allah
zai iya sauka
akan gaba daya al'umma,bisa wannan dalili ne
nake son ka dada tara jama'ar nan taku kaja
musu
kunne ka shaida musu cewa su kiyaye duk irin
dokokin dake cikin addinin musulunci kamar
yadda
a kullum nake zaiyana musu kuma mu ruke
gaskiya dasu,kada su rude su sabi ubangiji.
Koda yarima Yazid yazo nan sai sarkin yaki
Haiman yace tabbas zan shaida musu kamar
yadda ka umarceni.
Ina da tambaya guda daya a wajenka yanzu
menene abinyi a garemu?
Zamu kwana ne anan wurin sai gobe mu cigaba
da tafiya ko kuwa
yanzun nan zamu cigaba da tafiyar.Lokacin da
yarima Yazid yaji wannan tambaya sai yayi shiru
ya sunkui da kansa kasa yana tunanin har izuwa
tsawon yan dakiku,daga can kuma saiya daga kai
ya dubi Haiman yace masu iya magana sunce
zama waje daya tsautsayi ne inji kifi tunda a
koyaushe za'a iya kawo farmaki.
Duk da cewa mun kashe da yawan wadannan
abokan gaba kuma mun raunana da yawansu
zasu iya fusata su sake kawo mana wani harin
na bazato domin daukar fansa.
Kai koda ma basu kawo mana harin ba zasu iya
turo yan leken asirinsu domin suga halin da
muke ciki sanann su san irin harin daya dace su
kawo mana.
Shi yaki dan zamba ne da yaudara don haka
yanzu ma dole me sake yaudararsu zamu bar
sansaninmu kamar yadda yake ba zamu cire
tantuna ba zamu kara yawan dakarun tsaro na
mutum mutumi kuma mu kunna fitilu da daddare
tamkar muna nan a cikin sansanin hakanne zai
bamu damar mu sake nausawa cikin daji har mu
isa karshen wannan daji da muke ciki inda
taswirar Dajin Hajarul Aswad zata fara aiki.
Idan Allah ya taimake mu har daren ya shude
abokan gaba basu gano cewa bama cikin
sansanin nan ba to tabbas zamu basu tazarar da
ba zasu iya riskarmu ba har mu isa can kogon
Hajarul Aswad mu dauko
wasikar jini.
Koda jin wannan hikima sai murna ta kama
sarkin yaki Haiman nan take kuwa ya kira
dakarunsa ya sasu suka sake hada mutum
mutumi kimanin guda ashirin aka sake zubasu a
cikin sansanin,daga nan kuma aka...
*Abbas Abdulkadir Hada Hada*
kunna fitilun wuta tsirarru suka kewaye sansanin
saboda kada fitilun su yawa su haska mutum
mutumin tun daga nesa a gane cewa ba dakaru
bane na gaske,gama wannan shirin keda wuya
sai
su yarima Yazid suka hada nasu inasu suka bar
wannan wuri suka nausa cikin daji.
Saida suka shafe sa'a bakwai suna tafiya basu
riske dajin ba har ya zamana cewa kowa ya kosa
a sannan ne yarima Yazid ya dubi sarkin yaki
Haiman yace ya kamatu mu yada zango anan
saboda na fuskanci cewar jama'a sun gaji kuma
gashi yamma tayi magriba zata iya riskarmu nan
da cikar sa'a guda,zaifi kyau muyi sallah muci
abinci in yaso mu yanke shawarar abinda ya
kamata muyi walau
cigaba da tafiya ko kwana anan.Koda jin wannan
batu sai sarkin yaki Haiman yayi murmushi yace
yakai Yazid ai duk abinda kazo dashi dashi za'ayi
aiki saboda kaine jagoran wannan tafiya a
yanzu.Yazid yayi murmushi yace yaza ayi kace
nine jagoran wannan tafiya alhalin a cikin
nahiyarku muke kun fini sanin duk inda muka
dosa
kuma kun fini sanin sirrikan wadannan dazuzzuka
naku.
Haiman ya numfasa yace gaskiya ne abinda ka
fada amma ai ni ba dan kai ba yanzu tuni gaba
dayanmu nan mun hallaka don dayanmu bazai
tsira ba daga sharrin abokan gaba.
Nan take aka shiga kafa tantuna ana shirya musu
shimfidu domin a zauna a huta.
A wannan lokaci ne wasu daga cikin dakarun
suka sami damar cin abinci.
Nanfa kowa ma ya shiga kimtsa cikinsa ita kuwa
gimbiya Nauwara sai ta koma gefe daya tayi
tagumi ta fada tunani mai zurfi.
Ba komai take tunani ba face halin data baro
mahaifinta wanda
tasan cewa abune mayuwaci su sake ganin
fuskokin juna,nan ta aiyana a ranta cewa tuni ma
waziri Ridwan da sarki Marwatu sun riske su har
cikin fada sun kashe su.
Koda gama aiyana hakan sai nan take idanunta
suka ciko da kwalla suka fara zubar da hawaye.A
daidai wannan lokaci ne yarima Zainur yazo
gareta rike da wani akushi cike da abinci,Zainur
ya zauna daf da Nauwara ya dubeta
yace ga abinci nan kici don na tabbatar da cewa
akwai yunwa a jikinki?
Koda jin haka sai Nauwara ta
dago kai ta dubeshi idanunta sharkaf da hawaye
tace bana sha'awar naci abinci saboda ina cikin
mugun bakin ciki,nan take hankalin Zainur ya
dugunzuma ainu ya dubeta cikin tsananin alamun
damuwa yace haba ya yar uwata ke kuwa
menene ya jefaki cikin bakin ciki haka alhalin
kowa anan
yana farin ciki da wannan nasara da muka samu
wacce bamu taba zato ba?
Koda jin wannan tambaya sai Nauwara ta girgiza
kai tace hakika
nayi matukar farin ciki bisa wannan gagarumar
nasara da muka samu amma duk sa'adda na
tuno yadda karshen rayuwar mahaifina zata
kasance sai bakin ciki ya turnuke ni na tsani
wannan akida daya dauka ta iyayensa da
kakaninsa.A kan wane dalili bazai karya alkawarin
daya daukar musu ba ya karbi addinin musulunci
yayi watsi da tsohon addininsu na bautar gumaka
da tsafi,yanzu gashi
ma lokaci ya kure babu mamaki tuni masu sarki
Marwatu sun shiga garin sun ci shi da yaki,nasan
cewa bazasu barshi a raye ba.Koda Gimbiya
Nauwara tazo nan a zancenta saita fashe da
kuka,al'amarin daya jefa yarima Zainur da kowa
kenan cikin matukar tausayinta,zainur ya
rungumeta a kirjinsa ya shiga rarrashinta yana
mai bata baki har izuwa tsawon yan dakiku.Koda
yaga taki ta daina kukan saiya janye jikinsa daga
cikin
nata ya mike tsaye ya tafi wajen yarima Yazid ya
jashi izuwa gefe daya sannan ya dubeshi cikin
alamun tsananin damuwa yace kai kadaine zaka
iya kwantarwa da yar uwata hankalinta ta daina
wannan kuka.
Koda jin haka sai idanun yarima
Yazid suka zazzaro ya dubi zainur cikin alamun
firgici da mamaki yace yaya kai da kake dan
uwanta na jini baka kwantar mata da hankali ba
sai ni.
Zainur yayi murmushi yace akwai dalilin da yasa
na fadi hakan amma bazan gaya maka dalili ba a
yanzu sai nan gaba,inaso ka sani cewa a duniya
babu abinda Nauwara keso sama da farauta a
cikin daji,inason a yanzu take ka gaiyaceta ku tafi
farauta ku biyu rak izuwa cikin daji nasan zata ci
duk abinda kuka farauto in ba haka ba kuwa
saidai ta kwana da yunwa tana kukanta.
Yayin da Yarima Yazid yaji wannan batu sai
hankalinsa ya dugunzuma yace shin baka san
cewa a addinin
musulunci haramun ne namiji ya kadaita da
macen da bata kasance muharramarsa ba?
Zainur yace nasan da haka amma ai addinin ya
yarda da wata lalurar don kawar da wacce ta
fita,bare ma na yarda da imaninka da kuma
tsoron Allah,nasan ba zaka taba yin abinda bai
dace ba ga yar uwata.Kada ka manta cewa shi
kansa mahaifin namu cewa yayi ya danka
amanar Nauwara a hannunka,ka biya mini
wannan bukata dana nema a gareka domin ka
ceto lafiyar Nauwara in ba so kake gobe da safe
ta tashi da matsananciyar rashin lafiya ba.
Koda jin wannan batu sai jikin Yarima Yazid yayi
sanyi ya rasa abinda zaiyi kawai sai ya mike
tsaye ya shiga cikin tantinsa ya dauko KWARI DA
BAKAnsa gami da takobinsa kuma ya gyara
damarsa.Koda ya fito daga cikin tantin sai yaga
yarima Zainur tsaye a gabansa yana jiransa,kawai
sai Zainur ya sanya hannu a cikin aljihun
wandonsa ya dauko wannan taswirar ta zuwa
kogon Hajarul Aswad ya mika masa yace idan
baka tare dani sanaji kamar bazan iya kula da
wannan taswira ba,ka ajiyeta a hannunka zanfi
samun nutsuwa da kwanciyar hankali koda wani
abu zai same mu anan inason kayi iya kokarinka
ka isa kogon Hajarul Aswad ka dauko wannan
wasikar jini ka koneta wannan ne kadai abinda
zakayi ka jadda addinin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login