Showing 54001 words to 56708 words out of 56708 words
Chapter 19 - WASIKAR JINI! COMPLETE Book By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
wata asara domin shahada ce mukayi.
Ni ina ji a jikina wadannan makiyan Allah ba zasu
taba samun nasarar mallakar wannan wasikar jini
ba.
Caraf sai Yarima Zainur ya tari numfashin
Haiman yace tabbas abinda ka fadi gaskiya ne
yakai Abbana kuma zamu cigaba da addu'ar Allah
ya kare mu daga sharrin su waziri Ridwan kuma
ya bamu sa'a akansu mu kawar dasu da zalunci
mu kafa addinin Allah a wannan nahiya.
Su Haiman na cikin wannan zance ne waziri
Ridwan da sarki Marwatu suka taho garesu suna
kyalkyala musu dariyar mugunta,da isowarsu daf
da bakin kejin sai
waziri Ridwan ya zura hannunsa cikin kejin ya
cafi makoshin Zainur yace kai yaro kayi asara,a
baya sarkin yaki da sarki Aiyuba sun gagareni
kuma sun jima suna kunsa mini bakin ciki,sun
kare dukkan hanyoyin cigaba rayuwata kuma
lokaci yayi da zan dauki fansa akanka.
Tunda shi tasa ta kare gashi can kwance akan
gangar mutuwa,a yau dinnan abokinka Yazid da
gimbiya Nauwara zasu kawo mana Taswirar
zuwa kogon Hajarul Aswad,mun yaudare su da
cewa zamu basu ku a maimakon
taswirar suna shigowa cikin wannan tanti zamuyi
musu kofar rago mu hallaka su mu dauke
taswirar sannan kuma muyi muku kisan gilla.
Tabbas na tabbata da cewa ba zasu iya tafiya su
barku ba dole ne suzo suyi kokarin ceton
rayuwarku.Koda gama fadin haka sai Ridwan ya
saki makoshin Zainur ya dubi sarki Marwatu suka
bushe da
dariyar mugunta tare suna cikin kyalkyala dariyar
ne sarkin yaki Haiman ya tari numfashinsu yana
mai daka musu tsawa yace,ku tsofaffun
azzalumai kuyi sani cewa rana da yawa ta
barawo ce rana
daya jal ta mai kaya.
Tabbas kun dade kuna sheka ayarku a doron kasa
kuna zalunci kuna tara dukiya ta gurbatacciyar
hanya,babu mai iya taka muku
birki sai Mahaifin Gimbiya Nauwara.Yau sarki ya
fadi amma kuyi tunani da hankalinku da
kwakwalwarku an sami jarumi ma'abocin addinin
musulunci wanda shine zai kawo karshenku.
Ina mai tabbatar muku da cewa sakon da
manzonku zai dawo dashi saiya girgiza
ku,kowannenku sai
hantar cikinsa ta kada.
Kafin sarkin yaki Haiman ya gama rufe bakinsa
kuwa sai sukaji sukuwar doki an nufo
sansanin,cikin hanzari waziri Ridwan da
sarki Marwatu suka waiga baya sai sukaga ashe
manzo Ubaiyu ne ya dawo.
A guje Ubaiyu ya ratso cikin sansanin da doki,da
isowarsa sai yaja tunga a gaban su sarki
Marwatu ya sauko da sauri daga kan dokin ya
zube kasa gabansu sannan ya dago kai ya
zaiyane sakon dasu yarima Yazid suka
bashi cewar ba zasu zo wannan sansani ba kuma
ba zasu bayar da taswirar ba face a tsakiyar
dajin
Hajarul Aswad.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Takwas (8)
Part C.
.
FACE A TSAKIYAR DAJIN HAJARUL ASWAD.
KODA JIN WANNAN BATU SAI RAN SARKI
MARWATU DANA WAZIRI RIDWAN YA
BACI,ZUCIYOYINSU SUKA KAMA TAFARFASA
KAMAR ZASU KONE,CIKIN FISHI SARKI
MARWATU YA DUBI RIDWAN YANA MAI ZARE
TAKOBINSA YACE,tunda dai sun hanamu taswirar
zuwa dajin hajarul Aswad banga amfanin
fursunonin da muke tsare dasu ba kawai mu
kashe su.
Waziri Ridwan yayi sauri yasha gaban sarki
Marwatu ya dubeshi cikin matukar damuwa yace
a'a idan muka kashe su yarima Zainur yanzu har
abada ba zamu sami wannan taswirar ba bare
mu
mallaki wasikar jini zo kaji wata magana.
Nan take Ridwan ya kama hannun sarki Marwatu
ya jashi izuwa can gefe daya suka tattauna
sukayi kuskus na tsawon yan dakiku suna gama
tattaunawa ne suka tara gaba dayan mayakansu
suka basu
umarnin a fara shirin cigaba da tafiya kuma a
shirya makaman yaki.
Nan take kuwa aka shiga debo takubba,mashi da
kibiyoyi aka shiga wasa su ana rarrabawa
mayaka kai kace YAKIN DUNIYA za'a
tafi.
Koda Zainur ya ga yadda dubunnan daruruwan
dakaru keta kai kawo a cikin sansanin suna ta
shirye shiryen yaki sai nan take idanunsa suka
ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa.
Al'amarin daya baiwa Haiman da matarsa
mamaki kenan Haiman ya dubi Zainur cikin
alamun kaduwa yace yakai dana ina dalilin zubar
da
wannan hawaye naka?
Zainur yasa hannu ya share hawayensa sannan
ya dubi Haiman cikin nutsuwa yace yakai abbana
kaga wadannan dubunnan daruruwan dakarun da
yawansu magidanta ne,suna da mata,'ya'ya da
yan uwa kuma dukkaninsu jama'ar birnin mu ne
amma dayansu ba zai tsira da rayuwarsa ba duk
mutuwa zasuyi a cikin dajin
hajarul Aswad.
Kaga kenan matayensu zasu zama
zawarawa,yayansu kuma zasu zama marayu,basu
da ikon gudun shigowa nan dajin saboda tsoron
waziri ridwan,haka suma dakarun yakin da sarki
Marwatu ya taho da su daga kasarsa zasu mutu
a
cikin jahilci batare da sun amfani addinin gaskiya
ba sun dandani dadinsa da kuma rahamar dake
cikinsa.
Koda Zainur yazo nan a zancensa sai jikin
Haiman dana matarsa yayi sanyi suka kurawa
dakarun yakin idanu suna masu jin
tausayinsu.Kafin cikar sa'a daya an gama shiri
tsaf an kwashe komai a sansanin an zaburi
dawakai da gudu an durfafi hanyar da zata kaisu
izuwa dajin hajarul aswad.
Idan mutum yaga wannan falfala azababben gudu
kuma yaga yawansu dole ya firgita yayi zaton
cewa karshen duniya ne yazo.
*
A can cikin dajin hajarul aswad kuwa lokacin da
sarauniya Lazwara,Yarima Yazid da gimbiya
Nauwara suka falfala da azababben gudu izuwa
cikin dajin Hajarul Aswad suka shafe sa'o'i suna
gudun batare da sun gaji ba sai suka iso wani
katon fili wanda ke cike da wata irin ciyawa mai
taushi tamkar kilishi aka shimfida gaba daya a
wannan gaili.
A zagaye yake da wadansu irin dogayen bishiyoyi
tamkar babu hanyar da mutum zai iya bi ya
wuce.
Da isowarsu wannan wuri sai sarauniya Lazwara
ta kwalawa Yazid kira suka tsaya da
Nauwara.Lazwara ta karaso garesu tana
haki data kalli Yazid da Nauwara taga ko haki
basayi kuma babu alamar gajiya a tare dasu duk
da wannan tsananin gudu da suka sha sai ta
kamu da tsananin mamaki amma saita basar ta
dubi Yazid tace,nanne tsakiyar dajin Hajarul
Aswad,
anan ya kamata mu tsaya mu tunkari su sarki
Marwatu ayita ta kare,idan mun sami nasarar
kashe su mu karasa kogon hajarul aswad mu
dauko wasikar jini idan kuma sune suka sami
nasarar kashe mu sune zasu je su dauko wasikar
jini su mallaketa su cigaba da yin mulkinsu na
zalunci,ina mai tabbatar muku da cewa gaba
dayan masifun dake cikin
wannan dajin anan wurin suke kuma kowacce
masifa daya ta ninka ta waccan halittar dana
kashe a cikin kogin kankara sau uku babu abinda
zai kwace mu anan face tsananin sa'a da kuma
iya yakinmu da juriyarmu amma badai karfin sihiri
ba.
Caraf sai yarima Yazid ya tari numfashin
sarauniya Lazwara yace ni dana san cewar
ubangijina zai bamu kariya ke kuma sai mu gani
idan tsafinki zai kareki idan kuma baki da
tabbacin hakan to ki karbi addininmu yanzu take
nayi miki alkawarin babu abinda zai sameki,koda
jin wannan batu sai Sarauniya Lazwara ta
kyakyale da dariya tace ai inda tun farko ban
yarda da kaina ba bazan yarda na biyo bayanku
ba har na iso nan.Lallai inda babu kasa anan ake
gardamar kokawa,nidai burina shine na rayu har
izuwa lokacin da za'a zo dasu yarima Zainur nan
kuma naga wadanda zasu sami nasarar dauko
wasikar jini tsakanin su sarki marwatu da mu.
Koda jin wannan batu sai mamaki
ya turnuke Nauwara da Yazid saboda basu san
dalilin da yasa sarauniya Lazwara take son taga
isowar Yarima Zainur wannan wuri ba.
Har Nauwara ta bude baki zata tambayeta dalilin
sai kawai sukaji kasa ta kama girgiza,kafin
dayansu yayi wani yunkuri saiga wadansu irin
samudawan dodanni suna faso kasar suna fitowa
su dayawa ba adadi suka yiwa su yarima Yazid
kawanya sai gashi su Yazid sun zama yan mini
mini tamkar an ajiye yan tsaki uku a tsakiyar
dubunnan kaji.
Sudai wadannan dodanni suna da matukar tsawo
gami da kaurin jiki kuma fuskokinsu nada
matukar muni da ban tsoro idanuwansu jajaye ne
tamkar dan buda aka gasa a cikin wuta.Jikinsu
gaba daya a murde yake cike da kwanji da jijiyoyi
tamkar duwatsu aka cure gaba dayan wadannan
dodanni suna ruke da wani irin gabjejen sungumin
itace mai dauke da wani irin tsini cako cako mai
yawa a
samansa.Duk da tsananin jarumtaka irinta yarima
Yazid saida ya firgita bisa ganin wadannan
dodanni da kuma yawansu amma daya tuna cewa
yana tafarkin daukaka kalmar Allah ne sai dukkan
tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa.
Kawai saiya zare takobinsa ya gyara tsayuwarsa
yana jira yaga
dodon dazai fara kawo masa
+Abbas Abdulkadir Hada Hada*
Hari.Itama Sarauniya Lazwara saita zare
takobinta ta gyara tsayuwarsa.Gimbiya Nauwara
kuwa kasa zare tata takobin tayi saboda tsoro ta
koma bayan
yarima Yazid ta tsaya jikinta na karkarwa.
Koda Yazid yaga yadda Nauwara ta tsorata ainun
da ganin wadannan dodanni sai yayi mata rada a
kunne yace ki tsuguna kasa kuma kada ki
kuskura ki motsa daga nan wajen daidai da taku
goma.
Gama fadin hakan keda wuya sai dodannin suka
afkawa Yazid da sarauniya Lazwara aka
ruguntsume da azababben yaki,ai kuwa ana fara
wannan yaki ne Yazid da Lazwara suka raina
kansu
kuma suka san cewa sun gamu da gamonsu.
Sudai wadannan dodannin basa jin sara da suka
a jikinsu domin duk sa'adda takubbansu Yazid da
Lazwara ya hadu da jikinsu saidai kaji wata irin
kara na tashi tamkar karfe da karfe ne suka hadu
kuma
tarwatsin wuta ne ke tashi.
Haka kuma basa jin naushi da bugu domin da
zarar su Yazid sun naushe su hannunsu ne
sagewa suji kamar dutse suka nausa.
Bugu da kari dodannin suna da matukar zafin
nama domin kafin su Yazid su kai musu hari
guda su sun kai musu uku nan da nan suka
kuntata Yazid da Lazwara suka fara galabaitar
dasu,wani abin mamaki shine babu wani dodo
daya kaiwa Nauwara hari a inda take tsugune
amma jikinta sai karkarwa yake tana kallon
gumurzun da akeyi cikin tsananin tsoro da tashin
hankali.
Ashe Yazid ya karanta wata addu'a ta
musamman ya tofa adaidai wurin da Nauwara ta
tsuguna.
Ana cikin wannan mugun artabu ne wani dodo ya
shammaci sarauniya Lazwara ya gabza mata
wani wawan naushi a fuska,saboda karfin naushin
saida tayi katantanwa a tsaye sau uku a lokacin
da gudan jini ya furzo daga bakinta ta langwabe
zata fadi kasa sumammiya.
Koda ganin haka sai yarima Yazid ya dimauce bai
san sa'adda ya kwala kabbara da karfi ba ya cafo
Lazwara da hannu daya ya goyata a bayansa
kuma ya afkawa dodannin da mugun sara da
suka cikin bakin zafin nama na gaban kwatance a
lokacin da yaji wani
irin gagarumi karfi ya shige shi,ai kuwa sai gashi
takobinsa na daddatsa dodanni duk tsananin
yawan dodanni sai ya zamana banza domin an
rasa wanda zai iya koda lakutar jikin Yazid kuma
sai kutsawa ta cikinsu yake yana bazar
dasu,sassan jikinsu ya rinka shawagi a sama
yana zubowa kasa
jini jikinsu ya rinka tsartuwa da fantsama.
Wohoho.. idan kaji ana ki gudu to sa gudu ne bai
zo ba.
Koda sukaga irin mummunar barnar da yazid keyi
musu kuma suka tabbatar da cewa ba zasu
iya kasheshi ba sai suka ruga izuwa cikin
ramukan da suka fito.Ramukan suka rufe kansu
tamkar basu taba wanzuwa ba a wajen sai
gawarwakin yan uwansu kawai a kwance rututu a
filin daji.
Adaidai wannan lokaci ne Yazid ya sauke
Lazwara daga bayansa a kasa.
Koda ya ga har yanzu a sume take bata farfado
ba sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya
dimauce bai san sa'adda ya fisge battar ruwa ba
a jikin Nauwara ya budeta ya zazzage ruwan
akan fuskar Lazwara,faruwar hakan keda wuya
sai Lazwara ta farfado tana mai jan dogon
numfashi.
Koda ta bude idanunta taga dubunnan
gawarwakin dodannin zube a kasa kuma ta dubi
yarima Yazid taga takobinsa da duk jikinsa ya
rine da jini sai kawai ta bude baki tace nayi imani
da
ubangijin musulunci wanda ya baka karfin da ka
kashe wadannan dodanni,ina ragowar dodannin
suke?
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube
Yazid da Nauwara,yazid ya dubi Lazwara yace
bazan baki amsar tambayarki ba sai bayan na
shigar dake cikin addinina,nan take yazid ya
biyawa Lazwara kalmar shahada ta maimaita
sannan ya dubeta yace ragowar daodannin sun
koma cikin ramukan da suka fito.
Koda jin haka sai Lazwara ta mike tsaye tace
zasu sake fitowa don haka mu zauna a cikin shiri.
Gama fadin hakan keda wuya sai suka jiyo
sukuwar gubu daruruwan
dawakai an durfafosu suna daga kai sukaga ashe
su sarki marwatu ne suka taho cikin shigar
yaki,akan gaba kejin dake dauke dasu Haiman ne
bisa wani keken doki.
Wannan runduna tun daga nesa ta fara razana,ba
komai ne ya razana su ba face hango
gawarwakin wadannan dodanni da kuma hango
Yazid face face a cikin jini takobinsa ma ta rine
da jini.
Koda ya rage saura baifi taku ashirin ba tsakanin
rundunar su sarki marwatu da su Yazid sai
rundunar tayi turjiya suka tsaya cak
aka fara kallon kallo har saida kura ta lafa
sannan waziri ridwan ya dubi yazid,lazwara da
nauwara
yace yaku abokan gaba gamu mun iso tsakiyar
dajin hajarul aswad dauke da yan uwanku idan
kuma kuka ki bamu wannan taswirar dayanku
bazai tsira da rayuwarsa ba,ku dubi kanku
sannan ku dubemu kun sancewa ko ba'a gwada
ba linzami yafi karfin baki kaza,
kai Yazid kabar ganin cewa ka kashe wadannan
dodanni kai kadai to mu ba dodanni bane mutane
ne wadanda sunfi aljani ma hatsabibanci da
jarumtaka.
Koda waziri ridwan yazo nan a jawabinsa sai
Sarauniya Lazwara tayi caraf ta tari numfashinsa
tace kai tsohon azzalumi kayi sani cewa kunyi
babban kuskure da ganganci
da kuka kawo kanku nan dajin domin baku isa ku
iya ketare nan wajen ba a raye bare har ku isa
kogon hajarul aswad ku dauko wasikar jini.
Gaba dayanku sai kun zama gawa.Koda jin
wannan batu sai waziri ridwan ya bushe da
dariya yace ke
yarinya kiyi sani cewa kowa ya rigaka kwana dole
ne ya riga ka tashi,duk masifun dake cikin dajin
nan munsan dasu kuma mun dauki mataki a
kansu.
Caraf sai sarauniya Lazwara ta sake tarar
numfashin ridwan tace na yarda kun san masifun
amma ai sani daban haduwa daban,idan kuna
ganin cewa zaku iya dasu gasu nan ku jaraba mu
gani.
Tana gama fadin hakan saita juya ya dubi yarima
Yazid tayi masa wata inkiya shi kuma saiya
kwala kabbara ya naushi kasa da hannunsa guda
take ramukan dodannin nan suka bude dodannin
sukayi fitar burgu daga cikin karkashin
*Abbas Abdulkadir Hada Hada*
kasa,maimakon dodannin su afkawa su Yazid sai
suka juya da gudu suka afkawa su sarki Marwatu
aka ruguntsume da masifaffen yaki.
Kaico ananfa KASUWAR CINIKIN DAUKAR
RAYUKA ta bude,dodannin suka rinka ragargazar
dakarun su
sarki Marwatu suna yi musu mugun kisan
gilla,abinda ya daurewa kowa kai a wajen shine
ko dodo daya bai nufi inda kejin dasu Haiman
yake ba kuma ta cikin dodannin Yazid ya kutsa
yaje ya sare kubar da aka kulle kejin kofar ta
bude ya fito dasu Haiman daga ciki ya tafi dasu
can inda Nauwara
da Lazwara ke tsaye.
Koda Nauwara ta hango dan uwanta Yarima
Zainur saita ruga gareshi ta rungumeshi cikin
tsananin farin ciki,ita kuwa Lazwara sai taje
gaban Zainur ta dubeshi cikin murmushi tace
masoyina dama na kudurce a raina
anan ne zan baiya maka SIRRIN ZUCIYA ta lallai
tun a farkon haduwa ta dakai na kamu da
tsananin sonka kuma a halin yanzu nima na karbi
addinin Yazid shin kasa so na?
Koda jin wannan tambaya sai Zainur yayi wuf ya
janye jikinsa daga cikin na Nauwara ya dubi
Lazwara cikin tsananin farin ciki
yace nima tun a farkon haduwarmu na nutse a
cikin KOGIN SON...
Cikin sauri Nauwara ta rufe bakin Zainur da tafin
Hannuta tace kabar sauran bayani saimunga
yadda karshen wannan yaki zai kasance,nanfa
duk su biyar din suka mayar da hankalinsu izuwa
inda ake fafata wannan masifaffen yaki.
Rabin sa'a aka shafe ana wannan yaki ya
zamana cewa wadannan daodanni sun kashe
gaba dayan dakarun sarki Marwatu,Sarki
Marwatu da Waziri Ridwan ne kadai suka rage a
raye kuma
kowannensu ya sami mugayen raunika kimanin
guda bakwai a jikinsa.
Suma in badon tsananin karfin damtsensu ba da
karfin Sihirinsu da tuni sun dade da
mutuwa.Dodannin na shirin karasa kashe su sarki
Marwatu da waziri Ridwan kenan sai Yazid ya
daka musu tsawa take suka kame kam tamkar
gumaka.
Nan take Yazid ya fara kiran sunayen Allah
tsakaka yana yi masa kirari,faruwar hakan keda
wuya sai jikin dodannin gaba dayansu ya kama
tsattsagewa suka ringa rugujewa suna zubewa
kasa suna zama gari.
Nan da nan dodannin suka hallaka
gaba dayansu guda daya bai tsira da rayuwarsa
ba.
Sarki Marwatu da waziri Ridwan na ganin haka
sai suka cika da tsananin al'ajabi gami da
takaici,a
wannan lokaci ko motsi ba zasu iyayi ba
sakamakon jinin dake zuba a jikinsu kuma indai
ba'a gaggauta dinke raunikan nasu an tsayar da
jinin dake zuba ba na da wani lokaci zasu iya
mutuwa.
Koda Marwatu da Ridwan suka fahimci cewar
lallai zasu hallaka idan ba'a taimake su ba suka
kama rokan su Yarima Yazid dasu cecesu.Yarima
Yazid ya matso daf dasu ya tsaya ya dubesu
yace ina karfin mulkin naku kuma ina karfin
damtsenku dana sihirin tsafinku,ku ceci
rayuwarku mana da abubuwan da kuka dogara
dasu,kun gani da idanunku ayau babu wani karfi
wanda yafi na ubangijin musulunci.
Kodon saboda dubunnan rayukan da kuka sa
suka salwantar ba zamu ceci rayuwarku ba
mutuwa ce kadai zata fanshe zunubanku a
wannan doron kasa,ina mai tabbatar muku da
cewa daga yau tsafi ya daina tasiri a wannan
nahiya gaba daya kuma zalunci ya
kau sai adalci a tsakanin masu mulki da
talakawa.
Yanzun nan zamu karasa kogon hajarul aswad
mu kone duk abinda ke cikinsa sannan mu koma
izuwa kasashenku mu kafa tutar addinin
musulunci.
Koda gama fadin hakan sai Yarima Yazid ya juya
ya koma inda su Zainur ke tsaye suka rankaya
gaba dayansu suka kara nausawa
cikin dajin na hajarul aswad suka bar sarki
marwatu da waziri ridwan suna murkususu suna
kukan nadama gami da kakarin mutuwa.
Kafin cikar dakika dari duk su biyun sun sandare
sun zama gawarwaki.
Kamar Yadda Yarima Yazid ya fada
hakan al'amarin ya kasance wato sun isa har
cikin kogon hajarul aswad suka dauko wasikar
jini suka
koneta faruwar hakan keda wuya kogon dutsen
gaba daya ya kama rugurgujewa.
A guje suka fito daga cikin kogon ba tare da
dayansu ya hallaka ba.
Lokacin da su Yarima Zainur suka dawo gida sun
riske mahaifin Gimbiya Nauwara ya mutu don
haka sunyi kuka da bakin cikin rashin karbar
addinin gaskiya da baiyi ba.
Nan take aka kafa tutar addinin musulunci a
gidan sarautar sannan suka dunguma izuwa
birnin sarauniya Lazwara nan take aka kaddamar
da musulunci bayan nanne aka daura aure Yarima
Zainur da Lazwara,Yarima Yazid da Nauwara
sannan aka sake dawowa birnin su Nauwara aka
baiwa Yarima Zainur sarautar garin
wato ya gaji sarki Aiyuba.
Shi kuma Yazid ya dauki matarsa Nauwara suka
tafi can kasar su,komi ya dawo daidai yadda ya
kamata,aka cigaba da zaman lafiya a cikin
nahiyar da addinin irin na musulunci aka kautar
da tsafi da bautar gumaka.
.
TAMMAT BI HAMDULILLAH!!!
.
ALHAMDULILLAH. Khairun Anillahul Wahidul
Qahhar.
A Nan Muka Kawo Karshen Wannan Littafi Mai
Suna Wasikar Jini.Dafatan ya kayatar,nishadantar
tare da wa'azantarwa.