Showing 42001 words to 45000 words out of 56708 words

Chapter 15 - WASIKAR JINI! COMPLETE Book By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

su daga jikin
bangon da suke rataye amma kafin hannunsa
yakai kansu tuni Jarumi Damzur ya dako tsalle a
sama ya doki gadon bayan sarki uzaima.Sarki
uzaima yayi sama fuskarsa
ta gwaru da bangon dakin ya fado kasa
sumamme,cikin hanzari Jarumi Damzur ya dauki
sarauniya Aryala ya sabata a gadon bayansa ya
sake rugowa waje har ya dawo inda ake
gumurzu,da karfin tsiya yaci gaba da tarwatsa
dakarun sarki uzaima yana saransu da sukarsu.
Barde Husam na taimaka masa amma saboda
tsananin yawan dakarun guda dubu biyu da dari
bakwai ya rage sauransu dari uku da biyu kacal.
A haka dai suka ci gaba da azababben yaki har
tsawon dakiku masu yawa,da kyar da sidin goshi
gami da dabarun yaki suka iso har farpajiyar
gidan sarautar suka tasamma inda bargar
dawakai suke,a sannan ne fa dakarun sarki
Uzaima suka sake tuttudowa da yawan gaske
tamkar daga cikin kasa suke fitowa sukayi musu
rubdugu...
.
waye zai iya tuna mana sunan extract din labarin
da yazid yake baiwa su gimbiya nauwara?
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Shida (6)
Part D
.
Suka sake tuttudowa da yawan gaske tamkar
daga cikin kasa suke fitowa sukayi musu
rubdugu..
.
Wohoho!
Idan Jarumi ya cika jarumi tofa ba'a ganin
jarumtakarsa sai idan yaga mutuwa muraran a
lokacin da zuciyarsa ke dauke da babban
buri,burin su jarumi Damzur shine su sami damar
guduwa da sarauniya Aryala daga cikin gidan
sarautar kafin sarki Uzaima ya farfado daga
dogon suman da yayi,don haka sai suka cigaba
dayin yakin da dukkan karfinsu ya zamana cewa
duk inda suka sa gabansu saidai kaga maza na
zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona.
Kaico a wannan lokaci ne aka kashe ragowar yan
uwansu dakaru mutum dari uku ya zamana saura
su biyu kacal suma din babu wanda ba'ayi masa
rauni ba sama da guda biyar a jikinsa ba.
Gashi dai jini na zuba a jikinsu amma basu fasa
tarwatsa dakarun ba,a haka suka isa inda
dawakai suke suka haye kansu suka zaburesu da
gudu ana harbo musu kibiyoyi da masu,su kansu
sun gama sallamawa cewa mutuwa
zasuyi tunda babu yadda za'ayi dawakansu su
iya shallake doguwar katangar gidan sarautar
amma ba zato ba tsammani sai sukaga dawakan
nasu sun daka tsalle sun shallake katangun kuma
sunci gaba da gudu suna masu nauwasa cikin
daji,a guje aka bude kofar gidan sarautar dakarun
suka biyo bayansu a guje domin su cimmasu.
Adaidai wannan lokaci ne sarki Uzaimana ya
farfado daga dogon suman da yayi koda ya bude
idanunsa ya dubi ko ina a cikin turakar yaga babu
sarauniya Aryala saiya kwarara uban ihu mai
tsananin firgitarwa nan take ya
mike tsaye zumbur ya dauko kayan yakinsa ya
ruga izuwa waje yana isowa filin gidan sarautar
yayi arba
da gawarwakin dakarunsa dana su sarauniya
Aryala,sai ya tambayi ina sarauniya Arayala take.
Nan fa aka gaya masa cewa an kashe mata
dakarunta gaba dayansu amma shugaban
dakarun nata da mataimakinsa sun sami nasarar
saceta akan doki sun gudu amma anbi sawunsu.
Koda jin haka sai sarki Uzaima ya sake kwarara
uban ihu ya ruga
izuwa cikin bargar dawakansa ya kamo wani farin
ingarman dokinsa ya haye kansa ya zabureshi da
gudu yabi sawun dakarun da sukabi su jarumi
Damzur.
Lokacin da su Jarumi Damzur suka nausa cikin
daji da sarauniya Aryala bisa doki suna tsala
gudu sai suka cigaba da sakarwa dawakansu
linzami kamar zasu tashi sama,kai da gani kasan
cewa
gudun ceton ransu sukeyi kodai su tsira ko kuma
su hallaka.
Duk wannan abu dake faruwa har a sannan
sarauniya Aryala bataji karfin jikinta ya dawo ba.
Duk irin azababben gudun da sukeyi sai da suka
rinko jiyo sautin sawayen dawakan dakarun da
suka biyo su,ashe dawakan dasu jarumi Damzur
suka hau na
musamman ne wadanda suka sami horon gudu
da tsallake gine gine masu tsawo.
Tunda safe aka fara wannan tseren guda har
saida rana ta fadi ya zamana cewa su Jarumi
Damzur sun baiwa dakarun sarki Uzaima tazara
mai yawa kuma har sun fita
daga cikin iyakar kasar sannan dakarun suka
hakura suka daina binsu suka juya da baya.
Ai kuwa suna juyawar sukayi cikibus da sarki
Uzaima a sukwane bisa farin dokinsa,yana
ganinsu yaja linzamin dokin yayi turjiya yana mai
daga kafafunsa sama gami da haniniya,koda sarki
Uzaima ya dubi gaba dayan
dakarun yaga basa tare da sarauniya Aryala saiya
kurma uban ihu ya zare takobinsa yahau
dakarunsa da sara saboda tsananin fishi ba shiri
dakarun suka tarwatse suka bazama izuwa cikin
daji suna neman wajen buya don tsira da
rayuwarsu.
*
Al'amarin su Jarumi Damzur kuwa basu daina
gudu akan dokin ba har saida suka tabbatar da
cewa sunyi nisa ga barin iyakar birnin Kisra sun
shiga cikin yankin dazuzzukan birnin kisra sannan
suka tsaida dawakansu suka fado kasa daga kan
dawakansu a matukar galabaice tamkar ransu zai
fita.
Da kyar suka yiwa kansu magani suka dinke
raunikan dake jikinsu.Sarauniya Aryala kuwa bata
dawo cikin haiyacinta ba gami da samun karfin
jikinta har saida sanyin asuba ya kada a sannan
ta farka daga barci.
Koda ta bude idanunta ta tsinci kanta a cikin daji
kuma taga jarumi Damzur da Barde Husum zaune
a gabanta saita takarkare ta kurma uban ihu
sannan ta fashe da matsanancin kuka da kyar su
jarumi damzur suka rarrasheta tayi shiru sannan
jarumi damzur ya dubeta yace ya shugabata ina
dalilin wannan kuka naki?
Aryala tasa hannu ta share hawayenta sannan
tace sarki Uzaima ya kawar da Budurcina ya
karya alkadarina.
Koda jin haka sai jarumi Damzur da Barde Husum
suka kamu da tsananin bakin ciki har idanuwansu
suka ciko da kwallah.Aryala ta cigaba da magana
cikin sheshsheka tana mai cewa yanzu da wane
ido zan kalli mahaifina wanda ke kwance cikin
jinyar rashin lafiya yana son yaga dawo wata gida
cikin nasara dauke da dukiya mai yawa.
Da wane idanu zan kalli jama'ata alhalin na kasa
kare kaina bare na kare rayuwarsu da
mutuncinsu,ku kanku gashi nasa kunsha bakar
wahalar da kuka kusa rasa rayukanku,ni kan
yanzu rayuwar duniya ta fita daga raina gwara
ma ku taimaka mini ku kashe ni idan
kuka ki kashe ni to lallai zan kashe kaina.
Koda sarauniya Aryala tazo nan a zancenta sai
jarumi Damzur da barde Husam suka fashe da
kuka suka shiga rokonta akan ta janye wannan
manufa tata kuma sukayita bata baki akan ta
hakura ta yarda su maida ita birnin nurul
ansar,duk da cewa sarauniya Aryala tana son ta
koma gida ta iske mahaifinta a raye amma sai
bakin cikin abinda ya sameta yasa taji bata son
sake saduwa dashi.
Da kyar da sidin goshi dai su jarumi Damzur suka
shawo kan sarauniya Aryala ta amince akan a
cigaba da tafiya don isa birnin nurul ansar.
Nan da nan suka cigaba da tafiya ba sassauci ya
zamana cewa basa yada zango komai dare komai
rana face sun gaji likis ko kuma duhu yayi
yawa,cikin sa'a suka shafe kwana
™Abbas Abdulkadir Hada Hada™
tara suna tafiya batare da sun hadu da wani
mugun abuba sannan suka iso birnin nurul
ansar.Tun daga nesa suka hango an sauke tutar
masarautar daga
kan kofar birnin,zuciyoyinsu suka buga da karfin
gaske a wannan lokaci sarauniya Aryala na bisa
doki Jarumi Damzur na kasa yana jan dokin nata
shi kuma Barde Husum na biye dasu bisa daya
dokin,kawai sai sarauniya Aryala taja linzamin
dokin nata ta tsaya cak ta dubi barde Husam
tace babu lafiya a kasata kodai mahaifina ya rasu
ko kuma ancimu da yaki.
Ka ruga cikin birnin ka gano abin dake faruwa.
Koda jin wannan umarni sai jarumi
Husum ya sakarwa dokinsa kaimi ya nufi cikin
birnin nurul ansar.
Jim kadan saiga barde Husum ya dawo garesu
jikinsa a sanyaye kuma kansa a sunkuye,koda ya
iso daf dasu ya dago kansa sai sukaga idanunsa
sunyi sharkaf da hawaye take sarauniya Aryala ta
kwalawa mahaifinta kira ta fashe da matsanancin
kuka,saida Aryala ta shafe sama da sa'a daya da
rabi tana kuka sannan ta nutsu ta dubi
su jarumi Damzur tace tunda har ban dawo gida
na iske mahaifina a raye ba bana bukatar
sarautan idan
a cikinku akwai mai sha'awar yaje ya karbi
karagata yanzu anan zanyi rubutu kuma na buga
hatimina
bisa shaidar cewa na bashi karagar tawa.
koda jin wannan batu sai jarumi Damzur da Barde
Husum suka fashe da kuka,jarumi damzur ya
dubeta yace yake jarumar jarumai kiyi sani cewa
banga amfanin rayuwata ba muddin bana tare
dake saboda kece kika tsamoni daga cikin
mummunar rayuwa kika
mayar dani mutum,nasan menene adalci da
soyayya alhalin adacan babu abinda nasani face
zalunci da
kiyayya.
Bani da abinda zan saka miki dashi face nayi
bauta a karkashinki har izuwa karshen rayuwata.
Shima barde Husum saiya dubi sarauniya Aryala
yace tun ina yaro karami iyayena suka mutu
mahaifinki ne ya reneni tamkar dan cikinsa kuma
yasa aka koyar dani horon yaki har na zama
babba
a cikin dakarunsa,shine ya bani macen dana aura
tazo ta mutu a lokacin haihuwarta ta farko kuma
shine ya bani gida da dukiya mai yawa,bai taba
neman wata alfarma a wajena ba sai sau daya
alfarmar kuwa itace kafin mu baro birninmu ya
rokeni akan na kula dake kuma na tsare lafiyarki
da rayuwarki har izuwa karshen rayuwata.
Dame zan sakawa mahaifinki bisa abinda yayi
mini a rayuwa
face na cika alkawarin baki tsaro.Lallai ina tare
dake har izuwa karshen rayuwata.
Koda Barde Husum yazo nan a zancensa sai
sarauniya Aryala ta sauko daga kan dokinta ta
rungumesu duk su biyun ta fashe da kuka gaba
dayansu saida suka jima a kankame da juna
sannan suka janye jikinsu daga cikin nata suka
dorata akan doki suka kauce daga kan hanyar da
zata kaisu birnin nurul ansar suka nausa cikin
daji batare da sanin inda ma suka dosa ba.Haka
dai su sarauniya Aryala suka cigaba da tafiya har
saida suka shafe sati uku suna tafiya sannan
suka iso wani kauye dake cikin wata nahiya
daban da tasu,suna sauka a bakin wannan kauye
sai sarauniya Aryala ta kamu da tsananin rashin
lafiya ya zamana cewa zazzabi mai zafi ya rufeta
kuma ta rinkayin kumallo.Nanfa hankalinsu ya
dugunzuma suka karasa cikin wannan kauye da
sauri suka biya kudi aka kaisu gidan wata likita.
Koda aka kwantar da Aryala a cikin wata bukka
likitar tazo ta dubata saita dubi su jarumi Damzur
cikin murmushi tace ai ba wani abu bane ya
samu yar uwarku,ta sami juna biyu ne.
Koda jin wannan batu sai Aryala ta kurma uban
ihu kuma ta mike tsaye zumbur kamar
mahaukaciya ta rarumo wuka zata daba a cikinta.
Da kyar jarumi Damzur da barde Husum suka
riketa suka kwace wukar dake hannunta.
Nanfa ta fashe musu da matsanancin kuka na
bakin ciki.Daga wannnan rana Aryala ta tsani
kanta kuma ta tsani juna biyun da take dauke
dashi,babu abinda batayi ba don ta lalata juna
biyun datake dauke dashi amma sai abu ya
faskara haka dai su jarumi Damzur suka cigaba
da sa ido akan Aryala har cikinta ya tsufa ya cika
wata tara.A ranar da nakuda tazowa Aryala ne
akayi abin mamaki da baza'a taba mancewa
dashi ba domin a ranar ne kauyen gaba daya ya
sauya hadari ya gangamo alhalin lokacin
bazarane bana damina ba,aka rinka tsala ruwan
sama tamkar da bakin kwarya,kuma a ranar ne
dabbobin daji suka firgice suka shigo cikin gari
suka cudanya da mutane ba tare da son cutar
dasu ba.
A ranar ne jama'a sukayi ta hako zinare,lu'u lu'u
a ko ina cikin kauyen daga sauran kauyukan dake
makwabtaka dasu domin wannan bakon jaririn
dan baiwa da aka haifa.
Daga wannan rana Aryala taci gaba da rainon
jaririnta,jarumi damzur da barde husum kuwa sai
sukayi wata katuwar gona suka kama noma a
cikinta inda suka sami albarkar noman suka
zamo babu tamkarsu a harkar noma a kauyen
gaba daya.
Sannu a hankali jaririn Aryala yacigaba da girma
ai kuwa yana cika shekara shida a duniya sai
Damzur da Barde Husum suka fara koya masa
yaki.
Lallai barewa batayi gudu ba danta yayi
rarrafe,aikuwa shekara shidan ne wannan yaro
wanda ake kira da suna Goga ya rinka yin
gagarumar jarumtaka wacce ta ninka wadda
mahaifiyarsa tayi sau goma domin tun a sannan
yake iya fada da karti arba'in ya kaisu kas
saboda tsananin karfin damtsensa da iya
yakinsa.
Lokacin kuwa da ya cika shekara goma shi kadai
yake shiga daji yayi farautar yan fashi komai
yawansu sai yazo da kawunansu ya lodosu akan
dokinsa yazo dasu cikin kauyen,saidai kawai
mutane suyita al'ajabin wannan jarumtakar
tasa.A wannan lokaci ne aka samasa suna
Jarumi Sha Yaki ba don komai akasa masa
wannan suna ba sai saboda yana iya shafe
kwana uku yana yin yaki batare daya gaji ba.
Wata rana ya dawo daga yin farauta a daji sai
kawai yaji mahaifiyarsa dasu jarumi damzue suna
hirar abinda ya faru tun kan a haifeshi don haka
saiya labe
™AbbAs AbdUlkAdIr hAdA hAdA™
yana sauraransu a sannan ne yaji tarihin yadda
aka sami cikinsa da yadda bakin cikin hakan yasa
ta
hakura da kasarta da mulkinta.Koda jin wannan
labari sai hawaye ya zubowa Goga Sha Yaki yaji
ya
tsani sarki Uzaima da dukkanin sarakunan dake
waccen nahiyar ma,take ya dauki alwashin cewa
saiya kawar da dukkanin sarakunan ya kafa
sabuwar daula tasa da karfin tsiya......
Koda Yarima yazo daidai nan a labarinsa sai
kawai ya fahimci asuba tayi,al'amarin da yayi
matukar bashi mamaki kenan nan take ya katse
labarin dayake baiwa su Nauwara yace kowa ya
tashi ayi alwala domin gabatar da sallar asuba.
Koda jin haka sai kowa ya cika da mamakim
yadda akayi har asuba tayi basu sani ba saboda
dadin labarin da yake basu.
SHIN SU YARIMA YAZID ZASU ISA KOGON
HAJRUL ASWAD A RAYE SU DAUKO WASIKAR
JINI?
WANE IRIN MUGAYEN MASIFU ZASU HADU DASU
AKAN HANYA KAFIN SU ISA CAN?
TSAKANIN WAZIRI RIDWAN DA YARIMA ZAINUR
WAYE ZAI GAJI SARAUTAR?
INA LABARIN SARAUNIYA LAZWARA?
SHIN ITAMA ZA'AYI WANNAN TAFIYA TARE DA
ITA?
MENENE DALILIN DA YASA LOKACIN DA GIMBIYA
NAUWARA DA YARIMA YAZID SUNA GANIN JUNA
SAI ZUCIYOYINSU SUKA BUGA DA KARFI?
Godiya ta musamman Ga Allah (SWT)Madaukakin
Sarki,Mai Rahama Mai jin Kai daya bani ikon
Kammala "Wasikar Jini" 1-6.
kuma zamu cigaba da 7 insha Allahu
ina neman goyon bayan ku 100% kamar yadda
nake tare daku da fatan bazakuban kunyaba ta
wajen comment da like and share..
Littafi Na Bakwai (7)
Part Â.
.
Yauwa wa BAYAN SU YARIMA YAZID SUN IDAR
DA SALLAR ASUBA ANYI ADDU'A AN SHAFA A
CIKIN WANNAN
KOGON DUTSE.Sai Yarima Zainur ya dubi sarkin
yaki Haiman tace yakai Abbana yanzu zamuyi
bankwana daku anan ni da Yazid mu tafi izuwa
can kogon Harul Aswad in yaso kai da uwata da
gimbiya Naurawa da dakarunka sai ku cigaba da
zaman jiranmu har Allah ya dawo damu domin
kuwa rayuwarku zata zama a cikin mummunan
hadari idan har kuka fita daga cikin wannan
kogon
dutse saboda na tabbatar da cewa a yanzu haka
Waziri Ridwan da dakarunsa nan nan suna
farautarmu.
Kafin Zainur ya gama rufe bakinsa tuni Sarkin
yaki Haiman ya tari numfashinsa yana mai cewa
haba yakai dana saboda wane dalilin zaka hanani
yin wannan gagarumar tafiya wacce ko mutum
mutuwa yayi a sanadinta tamkar shahada ce yayi
tunda akan nufin daukaka KALMAR ALLAH muke.
Ka tuna cewa na sami lafiyar jikina tamkar ban
taba yin wani ciwo ba.Ka tuna da yakin da
mukayi da wadannan dakarun sumame yadda
Allah ya bamu sa'a akansu a cikin kankanin
lokaci.
Dan haka ni yanzu babu abinda nake shakka ko
nake tsoro face ubangijin musulunci.
Dani da matata da dukkan wadannan hadimai
nawa da kuma
gimbiya Nauwara duk sun sallama rayuwarsu
domin daukaka kalmar Allah saboda haka kawai
muyi
tafiya tare gaba dayanmu.
Wuya bata kisa kuma dole sai ansha wuyar
sannan akan sha
dadi,wannan tafiya da zamuyi itace kadai babbar
madogarar da zamuyi amfani da ita wajen
jaddada addinin gaskiya a wannan nahiya gaba
daya.
Koda sarkin yaki Haiman yazo nan a jawabinsa
sai gimbiya Nauwara taji wani irin gagarumin
farin ciki
ya lullubeta bisa jin cewa tare da ita za'ayi
wannan tafiya dik da cewa tasan halin data baro
mahaifinta a kan gangarar mutuwa.
Tuni itama a cikin zuciyarta ta yanke kaunar sake
saduwa da mahaifin nata tunda tasan cewa bashi
da niyar karbar addinin gaskiya bare ya sami
dace da samin
babban rabo a wajen Allah.
Ba tare da wata gardama ba shima Yarima Yazid
ya amince da suyi wannan tafiya tare gaba
dayansu.Nan da nan kowa ya kimtsa suka hau
dawakansu suka fita daga cikin wannan kogon
dutse suka nausa izuwa cikin daji.
Saida sukayi tafiya mai tsawo batare da sun hadu
da komai ba har rana tayi sosai.Yazid ya
shawarci Yarima Zainur dasu yada zango a
wannan wuri ayi sallar azahar kuma a ci abinci in
yaso a cigaba da tafiya.
Batare da wata gardama ba kuwa ya amince da
wannan shawara.Bayan an idar da sallah an fara
cin abinci ne kwatsam sai yarima
Yazid ya cire hannunsa daga cin abincin ya mike
tsaye zumbur ya kurawa gabas idanu.Al'amarin
daya razana kowa kenan a wurin kuma yasa
yarima Zainur ma ya tsaya ga barin cin abincin
ya mike
ya dubi Yazid cikin kaduwa da mamaki yace,yakai
Abokina lafiya kuwa naga ka daina cin abincin ka
mike tsaye zumbur haka?
Me yasa ka kura idanunka izuwa gabashin
wanann daji?
Sa'adda Yarima Yazid yaji wannan tambaya sai
yayi ajiyar zuciya yace inaji a jikina cewar a
koyaushe za'a iya kawo mana hari na MAMAYAR
BAZATO daga gabashin wannan dajin.
Zuciyata tana gaya min cewa akwai abokan gaba
a bayanmu masu farautarmu kuma nan da lokaci
kankani zasu riskemu anan.
Koda jin wannan batu sai Yarima
Zainur yayi dariya yace waishin a mafarki aka
nuna maka wannan al'amari ko kuwa hasashen
kawai
kakeyi?
Yazid ya dubi Zainur fuskarsa a murtuke babu
alamar raha ko wasa yace ba mafarki nake yi
ba kuma ba almara bace.Yau da gobe ce tasa na
kiyasta faruwar hakan.kuma ni Allah hore mini
baiwa irin wannan tahin abinda zai faru tun kafin
ya farun.
Koda jin haka sai sarkin yaki Haiman ya dubi
Yarima Zainur yace yakai dana ka sani cewa
nima nayi imani da abinda yarima Yazid ya fada
dan haka ya zama wajibi mu dauki matakin
gaggawa.
Yakai Yazid yanzu menene abinyi?Yazid yayi
ajiyar numfashi sannan ya dubi Haiman yace
maza kasa a kwashe komai namu daga nan
aboye acan gaba kadan amma abar tantuna
kamar guda uku.
Mu duka zamu ja da baya mu buya a cikin
duhuwoyi amma mu zagaye wannan sansani
muna masu dana KWARI DA BAKA.
Kafin nan zamu haka kasa mu binne tarkuna
kamar guda dubu kuma zamu daddaura mugayen
tarkuna a saman jikin bishiyoyi suma kamar guda
dubu.
Cikin kaduwa da mamaki Haiman ya dubi Yarima
Yazid yace ta yaya
kake zaton cewa zamu iya kammala wannan aiki
a cikin kankanin lokaci kuma a tunaninka makiyan
da suke biye damu suna da yawan da har sai
munyi musu wadannan mugayen tarkuna haka?
Yazid ya gyada kai yace kwarai kuwa makiyan
dake binmu sun ninkamu yawa sannan kuma sun
fitowa ne da gagarumin shiri domin su hallakamu
kuma su rabamu da wannan taswira ta zuwa
kogon Hajarul Aswad.Lallai idan mukai gaba da
gaba dasu sai sun karar damu gaba
dayanmu.Hakan ma da zamuyi yan dabaru ne mu
dana musu tarkuna
na bazato ba iya karar dasu zamuyi ba,amma
zamuyi matukar razana su har su karaya su ja da
baya,mu kuma sai musan wata sabuwar dabarar
da zamuyi musu.
Illa haka zamuyi ta fafatawa dasu har mu isa
kogin Hajarul Aswad.Abinda nasani kawai shine
yayi da tafiyar ta nutsa damu dasu duk
rayuwarmu tana cikin hadari sai mai yawan rai
zai kai labari.Abinda nake so daku shine musa
aranku
cewa ubangijin gaskiya na tare damu kuma shine
kadai zai kare mu daga dukkan abin ki.Ya bamu
nasara bisa abinda mukasa a gabanmu.Koda
gama fadin haka sai Yarima Yazid ya zabi mutum
ashirin daga cikin yaran sarkin yaki suka tafi
izuwa cikin daji da gudu sukaje suka saro rassan
bishiyoyi
akazo aka fikesu.Wasu aka binne su a karkashin
kasa wasu aka tabesu aka daddaure su a saman
bishiyoyi cikin duhuwar ganyaye.Saidai su Yarima
Yazid suka shafe kusan sa'a daya da rabi suna
wannan aiki,kuma duk sa'adda Yazid yake
™Abbas Abdulkadir hada hada™
kokarin hada tarko sai yaga Gimbiya Nauwara ma
tana kwaikwayon abinda yakeyi kuma sai gashi
tana yinsa mai kyau da inganci kamar tasan
yadda akeyi.
Al'amarin daya daure mai kai kenan ya bashi
mamaki.Da zarar Nauwara taga zata hada idanu
da Yarima Yazid sai tayi sauri ta kau da kanta
saboda ta tsare darajarta da kimarta ta 'ya mace
kuma yar
sarki.Ba komai ne yasa hakan ba face ta fahimci
cewa tabbas zuciyarta ta kamu da son wanann
kyakkyawan saurayi ma'abocin kyau da kwarjini
amma sai tayi alkawari da zuciyarta cewar ba
zata nuna masa sirirn zuciyarta ba face ya fara
tuna mata da kansa.
Tabbas rashin sani yafi dare duhu.Inda Nauwara
tasan waye Yazid a bangaren kunya da kuma
danne SIRRIN ZUCIYArsa da batayi gangancin
yanke wannan hukuncin ba.
Bayan an kammala kafa tarkuna a cikin karkashin
kasa da saman bishiyoyi kuma dukkan
kayayyakinsu an kaisu can gaban sansanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login