Showing 15001 words to 18000 words out of 56708 words

Chapter 6 - WASIKAR JINI! COMPLETE Book By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

uban ihu kuma ya fashe da matsanancin
kuka,da kyar nauwara ta rarrashe shi tace hakuri
zakayi yakai dan uwana domin haka kaddararka
ta kasance ka zama babban makiyin
mahaifinka,ina mai shawartarka daka guntse
bakinka kada ka kuskura bari mahaifinka yasan
wannan al'amari tun yanzu domin idan ya sami
tun yanzu zai kasheka kuma ka
zauna a cikin shirin komawa birnin arnan daji
domin ci gaba da karbar horon yaki a wajen
sarauniya
lazwara nida kaina zan raka ka mu nemi wannan
alfarma kuma na tabbatar da cewa ba zata ki ba.
koda zainur yaji wannan batu sai yayi shiru ya
kurawa Nauwara idanu ba tare da yace komai ba.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part C
.
Koda Zainur yaji wannan batu sai yayi shiru ya
kurawa Nauwara idanu ba tare dayace komai ba.
*** *** ***
Al'amarin su Ardadu da Yarima Yazid kuwa
lokacin da suka cigaba da tafiyarsu kasar Lahul
Harus,tunda suka taho babu abinda yake dakatar
dasu face sallah da cin abinci kuma sun kwashe
kwanaki uku akan hanya suna wannan
tafiya,saida sukayi nisa sosai sai
suka hangi wasu matafiya a can gaba dasu sun
nufo hanyar daga gani sunje kasar latus harus ne
sunci kasuwa hanyar ta biyo dasu.Koda ganinsu
sai Ardadu ya cika da tsananin farinciki domin ya
gaji
da tafiyar kasar da suke gashi Yarima Yazid sauri
ne dashi tafiya suke kamar masu gudu gudu sauri
sauri dan haka ne baya korafi,idan an tsaya yin
sallah domin ya gwammace ayi ta sallah da
wannan
tafiya,sosai ya gaji.Dan haka sai ya dubi Yarima
yace,ya shugabana wai mai ya hana muka fito ba
tare damun samun dawakai ba,mun hau domin
rage mana nisan tafiya,kana sane da cewa tafiyar
da doki zaiyi ta yini daya itace wadda mu zamu
yita a kwana
uku,kaga kenan da akan doki muke tafe da tuni
yau kwananmu tara kenan akan hanya.
Koda Yarima Yazid yaji wannan batu sai yayi
murmushi yace ai tafiyar kasa tafi dadi,dalili
kuwa baka dauke da nauyi face nauyin kanka da
ace yanzu da doki muke tafe da tuni mun takura
shi kuma yanda mu kanmu bamu da yawan
guzuri shima zai kasance bashi da
guzuri,kaga kenan da tuni yanzu yunwa ta
addabeshi a uzurinsa da banasa ba,kaga yanzu
mu zamu iya
jakuri ba kamar shi ba yadda yake dabba.
koda jin wannan batu daga Yazid sai Ardadu yayi
shiru daga bisani yace maganarka gaskiya ce
amma kuma aishi dokin dama anyishi dan ya
taimakawa bani adama,in
hakane kuwa koda ya mutu wajen bauta mana
kamar yayi jahadi ne,dan haka inason kayi hakuri
da
abinda zai faru yanzu domin ya zama dole mu
samu dawakan da zasu rage mana nisan tafiya
sannan mu samu karin guzuri.Dajin haka sai
yarima ya dakata
ya nunashi da yatsa yace bana bukata in kuwa
ka kuskura ka kwace abin wani rabuwarmu
tazo.Ardadu dajin haka sai yaja bakinsa yayi
shiru badan ya hakura ba,tabbas ko baiyi kwacen
doki ba sai yayi na dukiya,koda Ardadu yayi
wannan tunanin saiya dubi Yazid yace todai ya
kamata mu tsaya anan mu yada zango ni yanzu
na fara gajiya baya ga haka ina jin bawali.Koda
Yazid ya dubi sama sai ya fuskanci rana tayi
haske sosai lokacin sallar azahar ya nufo
take ya aminta da batun ardadu duk da cewar bai
yarda dashi ba.Adaidai wannan lokaci shima
Yazid
ya dauki salkarsa na ruwa ya nufi can bayan wani
dutse dan yayi bawali shi kuwa Ardadu sai ya tafi
can yamma da inda Yazid ya nufa cikin sauri
sauri ya nufi cikin daji ya rinka gudu.
Shi kuwa Yazid sai ya fito daga inda ya nufo har
ya samu guri ya kwanta bai jima da kwanciya ba
lokacin sallah yayi koda yayi alwala ardadu bai
dawo ba dan haka sai
ya dan jirashi dansuyi jam'i amma shiru ganin
kada lokaci ya kure sai ya tada sallar har saida
yayi raka'a biyu sannan ardadu ya fito da
hannunsa rike da wandonsa alamar yana daure
mazarin wandon.Nan ya zauna yayi alwala kamr
yanda Yazid ya koyar dashi,da yake Yazid basa
kan hanya har
wadannan mahaya sukazo suka wuce yazid bai
lura ba haka suma basu lura dashi ba.
Bayan sun kammala sallah sai Yazid ya dubi
ardadu yace wai ina kaje ka dade haka?
Dajin haka sai Ardadu ya danyi murmushi yace ai
cikina ne ya murda dan har saida na kosa da
tsugunno.
Yarima ya dubeshi sosai cikin rashin yarda yace
ban yarda dakai ba yakai ardadu ka sanar dani
gaskiya.
Ardadu yayi murmushi yace wacce gaskiya kuma
ai batun boye boye ni
dakai ta kau bazanyi sata ba bazanyi cuta ba
haka bazan ci zarafin kowa ba,wannan shine
alkawarin dake tsakanin nidakai kuma bazan saba
maka ba.
Koda jin haka sai Yazid ya danyi shiru yace idan
ka saba fa wane hukunci zan dauka akanka?
Ardadu dajin haka sai shima yadan yi shiru gami
da duban Yazid da murmushin yake yace,ka
hakura da tafiya dani kamar yanda kaso hakura a
baya.
Ni bazan hakura da tafiya dakai ba domin ka
zamo wani jigo na wannan tafiya,hukuncin dazan
dauka daishine idan harka saba to babu shakka
yaki zamu sakeyi
dakai sabo wanda babu wanda zai rabamu saidai
mutuwa.
Koda Ardadu yaji wannan batu sai gabansa ya
fadi take ya dubi Yarima Yace a'a gaskiya a
wannan ba hukunci bane yakai shugabana kadai
samu wani.
Yarima Yazid ya girgiza kai yace ba
shawara na nema daga gareka ba babu abinda
zai hana haka face ka kadaita zuciyarka da
aikata sabawa mahaliccinka.
Ardadu yayi shiru yana tunani daga bisani ya
dago kai ya dubi Yazid yace amma...sai yayi
shiru da bakinsa Yazid bai damu da tambayarsa
abinda yayi niyar fada ba sai suka cigaba da
tafiya,basuyi nisa da tafiyar ba sai Yazif ya dubi
ardadu yace,menene labarin WASIKAR JINI?
koda jin wannan tambaya sai Ardadu ya fadada
murmushinsa domin tun dazu abinda yakeson yaji
Yarima ya tambayeshi kenan,amma yayi shiru
yayi biris,nan take ya gyara baki yace,WASIKAR
JINI wata wasika ce da aka samar da ita ta
hanyar yin tawada da jinin wasu manyan jarumai
da suka shude su tara a cikin kasar latul
harus,itadai wannan wasika
da itane ya jawo habbakar arzikin kasar latul
harus kuma da ita ne sarki aiyuba yake takama
domin shi
kadai ne ya samu ikon karantata saidai ayanzu
akwai waziri ridwan da kuma dansa Zainur suna
nan suna shirye shiryen neman wannan wasikar
su karantata.Idan har waziri ridwan ya karanta
wannan
wasikar to birnin latus harus zai wargaje,zama
lafiyarsa zai bankwana tashe tashen hankula
zasu tsaya kaida fata a cikin birnin wanda mu
barayi wannan itace damar da muke nema domin
muyi
+Abbas Abdulkadir hada hada+.wadaka.Koda
Yarima Yazid yaji wannan batu saiya daka masa
tsawa da cewa kai ka manta a wane matsayi
kake yanzu da kake kiran kanka da barawo?
Koda jin wannan batu sai Ardadu ya tsuke
bakinsa sannan yace tuba nake ya shugabana ina
amfani ne da shirinmu na baya.Yazid yayi shiru
yace ina saurarenka.Nan take Ardadu yacigaba da
sanar dashi in kuwa har yarima zainur ne ya
samu damar mallakar wannan wasikar har ya
karanta ta to birnin
Lahul harus zai kasance cikin zaman lafiya da
lumana.
Koda Yarima yaji wannan batu sai Ya dubi
Ardadu yace idan ni ne kuma na mallaketa?
Dajinwannan batu sai Ardadu ya tuntsure da
dariya saida yayi ta isheshi sannan ya dubi yazid
tace ai ko a mafarki bana jin zaka iya mallakar
wannan wasikar domin kuwa yarima Zainur da
mahaifinsa sune kadai suke da damar da zasu iya
daukar wannan wasikar
harsu karantata kai kuwa baka da karfin da zaka
gwabza dasu har ka hanasu dauka,
idan kuwa a misali ka dauki wannan wasikar to
baka da damar
yin aiki da ita domin kuwa bazata taba yin
amfani a gareka ba domin baka kasance jinin
sarautar kasar
latul harus ba.
Koda jin wannan batu sai Yarima
Yazid shima ya tuntsire da dariya wannan dariya
ita ta saka Ardadu shiga tsananin mamaki ya
dubi yazid yace ya shugaba na ina dalilin wannan
dariya ahalin da nake sanar dakai mummunan
al'amari.
Dajin haka sai Yarima Yazid yayi murmushi yace
ba komai ne ya bani dariya saida kake sanar dani
wahalar mallakar wani abu daga cikin kasar
mushrikai matsafa,meye abin wahalar raba arne
da makami?
Da zuwa nan a batun Yazid sai Ardadu tace ai
kuwa wannan arne ba karamin takadir bane
domin kuwa dukkaninsu sun fika kyakyawar
hanyar da zata kaisu
ga samun wannan wasikar domin kuwa shi
yarima zainur zai samu taimako daga wata
kankanuwar
yarinya dake dajin dake makwobtaka dasu,shi
kuma waziri ridwan zai samu taimako ne daga
tsafi da kuma amininsa sarki Marwatu,kai kuma
naga baka da wani taimako daya wuce nawa ni
kuwa bani da karfin dazan iya kallon wannan
zarata da niyar yin
yaki dasu.
Dajin haka sai Yazid ya daga yatsansa daya ya
nuna sama yace hakika babu abin bauta face
UBANGIJIN MUSULUNCI ni ko kai babu abin
dogaro a cikin wannan tafiyar ubangijin daya
haliccemu ya
halicci duniya da duk wani abu da yake cikinta shi
zai bani ikon daukar wannan wasika kuma ba
burina na karantata ba burina na hana azzalumai
yin aiki da ita dan haka muje zuwa.
Koda gama fadin hakan sai yarima yayi gaba shi
kuma Ardadu ya bishi a baya har suka isa wani
guri da dawakai guda biyu suke tare da tarin
dukiya a gefe ga abinci.
Da ganin wannan dukita sai Yarima ya dauke kai
shi kuwa Ardadu sai ya dubi Yazid yace ya
shugabana ina dalili zaka dauke kai daga kyauta
da ubangijin musulunci ya bamu,lallai wannan
kyauta ce daga
gareshi domin kawo mana dauki a bisa tafiyarmu.
Yazid ya dubeshi yace bata haka
ubangijinmu yace mu nema ba,wannan dukiyar
wani ce ba tamu ba dan haka kada ka kuskura ka
taba su kazo mu cigaba da tafiyarmu.
Koda jin wannan sai Ardadu yace kada kayi haka
yakai Yazid wannan
dukiya da dawakai bana kowa bane face na
wadannan mahayan da suka nufo mu ni na ruke
su
suka bani kaga kuwa idan har muka tafi muka
barsu anan zasu mutu su bushe ko barayi su
sace su dan haka kazo mu tafi dasu.
Dajin wannan batu sai Yarima Yazid ya dakata ya
nufi Ardadu ya zare gatari da takobin da suke
jikinsa ya mike masa daya yace
babu abinda zai rabani da kai sai mutuwa yakai
wannan mayaudari macuci maha'inci.
Koda fadar haka sai yaja da baya ya tsaya yana
jiran Ardadu amma ardadu ko motsi baiyi ba
ganin haka yasa Yazid ya daka tsalle ya nufeshi.
YAUSHE NE SARKI AIYUBA ZAI FADI YA MUTU?
TSAKANIN YARIMA ZAINUR DA WAZIRI RIDWAN
DA KUMA YARIMA YAZID WAYE SAI SAMI
NASARAR GANIN WASIKAR JINI?
WANE MATAKI SARKI MARWATU ZAI DAUKA IDAN
YA FARFADO DAGA SUMA DA YAYI YAGA AN
GUNTULE MASA BABBAN DAN YATSANSA NA
HAGU?
SHIN WANE IRIN BAKIN YAKI ZA'A KWAFSA
TSAKAKIN ARDADU DA YARIMA YAZID?
Mu hadu a WASIKAR JINI littafi na uku don jin
cigaban wannan labari.
Ina mai baku hakuri na rashjin jina jiya da kukayi
saka makon rashin chaji a wayana. Da patan
zakumin uzuri,
in Allah yakaimu anjima da dare ina dauke da
cigaban littapin ammana sai naga masuso da
yawa.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Uku (3)
Part A
.
Lokacin da Yarima Yazid ya dako tsalle sama ya
kaiwa Ardadu Mugun sara da addarsa sai Ardadu
yai sauri ya kare saran don ceton rayuwarsa
amma sai Yazid yasa kafarsa ta dama ya doki
cikin Ardadu.
Take cikin nasa ya kulle ya fadi kasa yana
murkusu gami da kuma kallon wuya a lokacin da
numfashinsa ya kama sarkewa kamar zai
mutu.Har Yarima Yazid ya sake daga addarsa
sama zai fille
kan Ardadu cikin tsananin fishi sai kuma ya
fasa,cikin sanyin jiki Yazid ya ajiye addarsa
sannan ya dubi Ardadu cikin alamun tsananin
takaici yace abinda ya hanani kasheka yanzu abu
daya ne kuma
ba wani abu bane face kai musulmi ne.Babu wata
hujja da zatasa musulmi ya kashe dan'uwansa
musulmi face ya aikata zunnubin daya cancanki
kisa.
Ayanzu kai ka aikata laifin sata don haka
hukuncin laifin sata zan maka yanzu.
Kafin Ardadu ya budi baki yace wani abu tuni
Yarima Yazid ya shammace shi ya sare wuyan
hannunsa na hagu,nan take Ardadu ya kwala
uban ihu lokacin da hannun nasa ya guntule
kuma jini yai tsartuwa kawai sai Ardadu ya sulale
kasa sumamme.
Lokacin da Ardadu fardado daga suman da yayi
saiya tsinci kansa akan doki guda,doki na tafiya
dashi a gefensa kuma Yarima Yazid ne bisa wani
dokin.Suna hada idanu sai Yarima Yazid yayi
masa murmushi yace,yakai Ardadu ina tayaka
murna bisa sauke nauyin zunubin dake kanka na
sata,ka sani cewa idan ka sake yin sata zan sake
sare daya hannun naka lafiyayye ka zamo
cikakken kuturu mara yatsu goma.Kana gani dai
yanzu ka rasa yatsu biyar
saboda haka sai ka kiyaye,koda jin wannan batu
sai hawayen takaici ya zubowa Ardadu
yace,yanzu ashe
har hukuncin sata yakai matsayin a yankewa
mutum hannu?
Yarima Yazid yace kwarai kuwa ai sata babban
laifi ne a addinin musulunci saboda ayi nuni da
haka ne akayi wannan hukunci mai tsauri.Koda
gama fadin hakan sai Yarima Yazid yai shiru bai
kara cewa komai ba,shi kuwa Ardadu banda
kukan zuciya da tsananin bakin ciki babu abinda
yake fama
dashi a cikin ransa.
Haka dai suka cigaba da tafiya ba sassauci suna
masu durfafo birnin latul harus domin gano a
inda wasikar jini take.
Acan cikin birni na latul harus kuwa lokacin da
sarki marwatu ya farfado daga suma da yayi
sakamakon babban dan yatsansa na hagu da
sarki Aiyuba ya
guntule masa sai ya mike zaune zumbur kamar
wanda ya farka daga mafarki mai ban tsoro ya
kama waige waige gami da duban dakin da yake
ciki a lokacin da yake kokarin tunani domin ya
gano waishin abindake faruwa a gareshi mafarki
ne ko kuwa gaske ne kwatsam sai yaji an turo
kofar dakin an shigo.Ba wani bane ba ya shigo
face Waziri Ridwan fuskarsa cike da annuri nan
take sarki
marwatu yayi dogon ajiiyar zuciya ya dawo cikin
haiyacinsa kuma a lokacin ne ya tuno da duk
abinda ya faru tsakaninsa da sarki Aiyuba a
fada,cikin firgici ya daga hannunsa na hagu,koda
yaga babban dan
yatsansa na hagun a guntule sai ya takarkare ya
kurma uban ihu.A lokaci guda kuma ya fashe da
kukan bakin ciki,koda ganin haka sai waziri
ridwan ya zauna akan gefen gadon da sarki
marwatu yake ya dafa kafadarsa yace kwantar da
hankalina yakai abokina kayi sani cewa kada
mage ba yanka bane,tabbas yanzu sarki aiyuba
ya sami lagonka tunda ya rabaka da gaba daya
sirrikanka na tsafi kuma ya wulakantaka ya
tozarta darajarka a gaban mutane amma ka sani
cewa lokaci zaizo wanda zakayi ramuwar gayya.
Na sani cewa bazaka iya daukar fansa ba akan
sarki aiyuba amma zaka iya dauka akan 'yarsa
gimbiya Nauwara kuma ina mai tabbatar maka da
cewa wannan lokaci yana daf da zuwa,sa'adda
waziri ridwan yazo nan a zancensa sai sarki
marwatu ya dubeshi cikin alamun kaduwa da
tsananin mamaki yace yakai tsohon abokina
menene
hujjarka ta cewa wannan lokaci yana daf da
zuwa?
Koda jin wannan tambaya sai waziri ridwan ya
kyalkyale da dariyar mugunta lokaci guda kuma
saiya turbune fuska yace bincike ya nuna mana
cewa sarki aiyuba na dauke da cutar ciwon zuciya
kuma
ba komai bane ya haddasa masa wannan ciwo ba
face bakin cikin sani cewa 'yarsa gimbiya
Nauwara
bazata taba gadar karagar mulkinsa ba.tabbas
sarki aiyuba yaso ace 'da namiji ya haifa ba mace
ba,na sami labarin wannan cuta tasane daga
bakin babban
likitansa wanda ya aminta dashi dari bisa dari
abinda bai sani bashine a duniya bashi da
makiyin da yafi wannan likita nasa saboda
maganin ma da yake bashi yana sha yana karawa
cutar karfi a hankali ba tare da ya ankara
ba.Koda jin wannan batu sai mamaki ya kara
turnuke sarki Marwatu yace yakai abokina
menene ya haddasa kiyayya tsakanin sarki
aiyuba da wannan liktan nasa harda yake yi masa
wannan mugun tanadi?
Koda jin wannan tambaya sai
waziri Ridwan ta sake bushewa da dariyar
mugunta a karo na biyu sannan yace ai labarin
ne mai tsawo kayi hakuri Zan baka wannan labari
nan gaba idan
lokacin daya dace ka sani yayi,abinda nakeso
dakai yanzu shine kayi shiri ka koma izuwa
kasarka ka
cigaba da tafiyar da harkokin mulkinka kamar
yadda ka saba kada ka kuskura ka nunawa
talakawanka gajiyawarka harsu gane cewa yanzu
baka da karfin
sihirin tsafi,ka sani cewa kowa yana tsoronka a
kasar taka ko dan saboda karfin damtsenka da
iya
yakinka,ka cigaba da hakuri har izuwa lokacin da
hakanmu zai cimma ruwa,da zarar sarki aiyuba
ya fadi zan aiko kazo cikin gaggawa domin
musami damar cika burinmu.Koda jin wannan
batu sai sarki Marwatu ya dubi waziri ridwan
cikin alamun mamaki
yace bangane abinda kake nufi ba,zaka kirani
bayan ya fadi,kana nufin da zarar ya kwanta
rashin lafiya ko kuwa da zarar ya mutu?
waziri Ridwan yayi ajiyar zuciya yace ai da zarar
ya kwanta rashin lafiya a lokacin da ciwo yayi
tsanani zanyi wata gagarumar ta fiya neman
wasikar jini,dole saina sami wasikar jini na
karantata sannan zan iya hawa karagar mulkin
kasar nan,a halin yanzu duk duniya babu wani
mahaluki wanda ya isa ya iya karanta wannan
wasikar jini har ya iya zama sarki a wannan kasa
tamu kuma ya mallaki wannan dukiya mai
tsananin yawa ta sarki aiyuba face ni da dana
yarima zainur,amma duk yadda zanyi saina
tabbatar da
cewa hannu na ya riga na dana kaiwa kan
wasikar jini.
Koda jin haka sai sarki marwatu ya jinjina kai
cikin alamun mamaki yace to waishin yanzu
kenan kai da danka zaku iya zama ABOKAN
GABA.
Waziri Ridwan ya turbune fuska yace kwarai kuwa
kuma idan harna gama yana nema ya zarce mini
matsala zan iya kawar dashi.Koda jin wannan
batu sai mamaki ya turnuke sarki marwatu yace
haba yakai abokina yarima zainur nefa dakai
danka a duniya.
Waziri Ridwan yayi dan guntun murmushi yace
nasan da haka aini a wajena dashi da babu duk
dayane tunda tsakanina dash babu wata shakuwa
kuma yafi kaunar makiyana fiye dani.
Sarki marwatu ya gyada kai a lokacin daya mike
tsaye yace babu
matsala zan zauna a cikin sauraron jin sakonka
kuma ina mai tabbatar maka da cewa zan baka
dukkan gudunmawa wajen ganin burinka ya cika
amma ka zamo mai cika alkawari a gareni.
Waziri Ridwan yayi 'yar gajeriyar dariya yace
kada ka damu yakai abokina lallai zaka sameni
mai cika alkawari shin yanzu kana da wata
bukata da kakeson a biya maka kafin ka tafi
izuwa birninka?
Sarki marwatu yayi ajiyar numfashi yace kwarai
kuwa inada bukata guda daya inason ka turo mini
sarkin makera na garin nan
akwai abinda nakeson ya kera mini kafin na bar
garin nan naku.Koda jin wannan batu sai waziri
ridwan yayi murmushi yace nasan abinda kakeso
a kera maka kuma kayi babbar dabara domin ta
hakane kadai zaka kawar da tunanin mutane akan
abinda ya sami babban dan yatsanka na hagu ka
tafi izuwa masaukin naka yanzu nan zan turo
maka sarki makera.Gama fadin hakan keda wuya
sai sarki marwatu yayi murmushi sannan ya juya
ya fice daga cikin turakar.
Lokacin da sarki ya isa masaukinsa sai dakarun
dake tsaron masaukin suka tareshi da albishir na
cewa sarkin makera na zaune a cikin falonsa
yana jiransa.Cikin tsananin mamaki sarki
marwatu ya jinjina kai kawai saiya kunna kai
cikin
babbar turakar yana murmushi yana shiga kuwa
yayi arba da sarkin makera zaune akasa bisa
kilishin dakin.
koda sarkin makera ya ga sarki marwatu tsaye a
kansa sai ya zube kasa wanwar ya kwashi
gaisuwa
sannan yace ya shugabana na amsa kiranka me
kake bukata daga gareni?
Sarki marwatu yayi murmushi yace yakai sarkin
makera kayi sani cewa
ina da bukatar ka kera mini hannu na karfe
wanda zan sanyashi akan hannuna na hagu kuma
na iya sarrafashi ba tare da ido ya gane cewa na
sanya hannun ba.
Koda jin wannan batu sai sarki makera ya jinjina
kai yayi shiru tsawon yan dakiku kadan sannan
ya dubi sarki marwatu cikin biyayya yace ya
shugabana wannan aiki ne mai wahala wanda
ba'a taba yin irinsa ba kuma zaici kudade masu
yawa.
Kodajin haka sai sarki marwatu yayi murmushi
yace kudi ba matsala bane ko nawa ne ake
bukata zan bayar,matsala itace tsawon kwana
nawa zaka iya kammala wannan aikin?
Sarkin makera yayi dan nazari sannan yace zan
iya kammala
wannan aiki a cikin sati daya da kwana biyar.
Koda jin haka sai sarki marwatu ya kyalkyale da
dariya sannan ya fiddo jakar kudi cike da lu'u lu'u
ya yafewa sarkin makera ita batare daya kirga iya
adadin lu'ulu"un dake ciki ba yace,ga wannan
kaje
ka fara aiki idan basu isa ba ka aiko na kara
maka.
Hannun sarki makera na rawa ya dauki jakar
lu'ulu'u ya kama godiya kamar zai yiwa sarki
marwatu sujjada ya mike tsaye yana mai cewa ya
shugabana ai wannan kudi ya isa a kammala
komai.
Nan take sarki marwatu ya sallami sarkin makera
ya tafi shi kuwa marwatu saiya zauna a turakar
yayi tagumi yana mai fadawa cikin dogon tunani
na bakin ciki da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login