Showing 6001 words to 9000 words out of 56708 words

Chapter 3 - WASIKAR JINI! COMPLETE Book By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

dandana azabar
sarki Aiyuba domin kuwa bazai taba yafe mana
ba.
Yazid cikin tsananin mamaki ya dubi ummansa
ya durkusa gabanta yace,ya ummin waye sarki
Aiyuba?
Kuma mai zai sa mu dandana azabarsa dan
dukiyarsa ta salwanta shin baisan kaddara ba?
Ummansa ta girgiza kai cikin tarin takaici
tace,Sarki Aiyuba yasan kaddara kuma yana da
tsananin kirki yana kyautatawa al'uma domin
abinsa bai rufe masa ido ba,saidai duk wannan
kyautatawar dason taimakon al'ummar yanayinsa
ne akan kafurai
wadanda suke bautawa gunki,ko kuma suke tsafi,
baya afuwa ga duk wanda ya kasance yana
addini irin namu,baya kaunar musulunci da
musulmai,kuma wannan abu har idan yaje
kunnensa bazai damu ba da asarar da yayi ba,sai
dimbin
farinciki saboda ya samu hanyar dazai kuntata
mana ya samu hanyar dazai tozartamu,tabbas
idan har ba karbar addininsa mukayi ba babu
shakka ko wanda yake cikin kada saiya fimu jin
dadin rayuwa ko kuma wanda ya kasance cikin
karkashin ruwa yana
neman taimako.
Dajin wannan batu sai Yarima Yazid
yayi shiru yana tunanin tabbas yasan labarin
sarki Aiyuba yana ganin shagunansa a kasuwar
garinsu,kuma yanaji a yawan lokaci idan an tashi
lissafin dukiyarsa mahaifinsa hankalinsa kan tashi
ainun.Nan da nan ya shiga cikin damuwa ya
kuma
fara neman hanyar dazai magance wannan
matsala tunda duk rintsi duk tsanani sai ya fitar
da kasarsu
daga cikin masifar sarki Aiyuba koda zai rasa
rayuwarsa ne saidai hanyar dazai bi ya magance
hakan ne bai santa inda zai biba.
Muryar likitan da yake duba lafiyar sarki sukaji su
dukan suka waiga
gareshi,suka zuba masa idanu cikin firgici ba
komai ne ya jefasu cikin firgici ba face ganin
yanda alamun
damuwa karara suka baiyana a fuskar likitan,da
sauri Yazid,Barira da sarkin kasuwa suka nufi
inda likitan yake zaune kusa da sarki da yake
shimfide akan gadonsa na alfarma.Koda zuwa
gabansa sai Yazid cikin kagauta ya dubi likitan
yace,yakai babban amintaccen likitan abbana
shine meye yake damun abbana?
Koda likitan yaji Yazid da wannan tambaya sai ya
dago kai ya dubeshi sannan ya sauke ajiyar
zuciya yace,tabbas sarki ya samu tabuwa a cikin
zuciyarsa wanda ta haddasu bisa faduwa da
gabansa
yayi,ta yiyu sarki yayi gamo da wani abu ne mai
ban tsoro ko kuma akwai abinda ya sameshi
wanda ya firgitashi ainun,dan haka yanzu abinda
nake bukata
shine abarshi ya samu hutu,na tsawon kwanaki
arba'in a cikin wadannan kwanaki sarki zai
fardado a kwana biyu rak,amma koda ya farfado
zai kasance
cikin yanayin mantuwa har tsawan wadannan
kwanaki.
Abin kiyayewa a cikin wadannan kwanki shine
kada wani mahaluki ya sake ya sanar dashi wata
magana da zata tada hankalinsa in har kuwa aka
tunatar dashi to babu mamaki idan zuciyarsa ta
kara bugawa ayi asararshi baki daya.
Dan haka sai a kiyaye da wannan in Allah yaso
zai samu sauki a cikin wannan kwanaki kuma a
kwana arba'in din tunaninsa zai dawo.Koda likita
ya gama yin wannan
jawabi sai hankalin Yazid ya kara dugunzuma
musamman da yaji anacewa idan aka kara
tunatar
da sarki wani abu zai bata masa rai zai iya
asararsa.Nan danan ya dubi likitan yace,Ya likitan
mahaifina kamar wacce magana da wacce
magana ne ya kamata akadaita kunnensa dasu?
Koda likitan yaji wannan tambaya sai ya dubi
Yazid yace,ai duk wani abu da akasan bana dadi
bane kada a sake ayi masa maganar domin kuwa
yin hakan zaisai
danasani ta hau kanmu domin tabbas za'a iya
rasa sarki.
Yazid yayi shiru yana nazari.Ana cikin haka saiga
waziri da galadima duk sun shigo cikin turakar
hankulansu a tashe saboda tsananin firgici har
faduwa sukeyi saboda tsananin firgici.Koda
isowarsu sai Yazid da mahaifiyarsa suka duka
suka kwashi gaisuwa saboda tsananin tashin
hankalin da suke ciki basu ma samu damar amsa
gaisuwar ba,Barira ta fice daga cikin turakar
shima likitan ya tafi bayan yayiwa su waziri
bayanin irin abinda yake damun
sarki.
Waziri ya dubi galadima cikin damuwa
yace,hakika tashin hankali ya tabbata a garemu
wanda kuma bamu da mafita face ubangiji ya
samar mana mafita,masifar sarki Aiyuba lallai
saita tabbata a kanmu domin dama bashi da
wani buri face yaga
mun dakusar masa da dukiya,Gashi yanzu saura
kwanaki goma sha biyar ayi wannan lissafin duka
dukiyarsa anyi asararta.
Hudijam masifa bata da rana sai a lokacin data
tabbata,yakai Galadima ga sarkinmu rai a hannun
Allah,mene dabara?
.
En uwa masu karatu ku basu shawara me yaka
mata suyi?
.
Sai amin apuwa na rashin jina da wuri da patan
za a karbi uzurina.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Daya (1)
Part D
.
Yakai Galadima ga sarkinmu yanzu rai hannun
Allah,menene dabara?
Koda jin haka sai galadima ya gyara murya ya
nutsu sannan tafe,babu dabara babu karfi saina
ubangijin musulunci ai bamu da abinda yafi face
mu mika ragamarmu ga Allah domin kuwa
shine kadai zai iya cetonmu.
Waziri ya girgiza kai gami da gyara zama ya dubi
sarki dake kwance bai
masan sunayi ba,ya maida kansa ga kallon Yazid
daya zuba musu ido cikin tsananin tashin hankali
sannan ya maida kansa ga galadima yace,hakika
maganarka gaskiya ce babu wanda zamu mika
lamuranmu face Allah da ya halicce mu,saidai
kuma ko ubangiji ya horemu da muyi yunkuri
wajen kare kanmu daga dukkan masifar datake
naman kawo barazana a garemu,wanda wannan
hubbasa din da zamuyi shi zaisa Allah yaji kanmu
da rahma ya taimakemu,amma muna kwance mu
dinga tunanin taimako daga gareshi tamkar mun
kasance lusaray ne.
Galadima ya danyi shiru daga bisani ya dubi
waziri yace,maganarka kaima gaskiya ce,ya zama
dole muyi hubbasa domin kare kanmu daga irin
masifar da zata tunkaro mu anan da kwanaki sha
biyar masu zuwa,saidai abin tunanin anan shine
fitinar da zata tunkaro mu ba irin fitinar da suka
saba kawo mana farmaki bane da zamuyi yan
dabaru mu korasu,inason ka sani shi sarki Aiyuba
matsafi ne,baya ga haka kuma ya mallaki dumbin
mayaka marasa iyaka,da idan ya turo mana kaso
daya daga cikin kaso dari na dakarunsa sai sun
cinye namanmu danye,bare nasan mugunta ta
sarki
Aiyuba domin ya tozartamu sai ya turo mana fiye
da kaso goma,yanzu idan ya turo mana kaso
goma daga cikin kaso na adawansa yaya kake
tsammani zamu karke dasu.Koda waziri yaji
wannan batu
saiyayi shiru kawai domin maganar da galadima
ya fadi gaskiya ce,dan haka sai ya gyara murya
yace,abinda ya kamata yanzu ayi shela ana
neman
kowa a fada gobe dan aji shawarwarin kowa akan
abinda zai kawo mana sauki daga cikin masifar
da zata tunkaromu.
Da wannan shawarar ta waziri suka
dasa aya,washe gari da safe bayan an zauna a
fada waziri ya wakilci sarki bisa girmansa da
kuma jin
maganarsa da ake a cikin kasar,ya fara bayani
kamar yanda suka farashi da galadima har kawo
karshen tattaunawarsu.Koda waziri ya gama
kawo musu
tattaunawar da sukayi shida galadima sai ya dora
da cewa duk wanda yake da wata shawara zai
iya kawo tasa domin dai a samu a tsira daga
masifar da zata addabemu.Waziri yayi shiru na
tsawan lokaci batare da kowa yace komai ba
kowanne dake cikin fadar
gabansa ne kawai yake faduwa.Domin tun lokacin
da labari ya iske kowa an sace dukiyar sarki
Aiyuba sai hankalinsu ya dugunzuma ya kuma
kasa kwanciya da kyar aka samu wani attajiri
wanda ake kira da suna Ishalu.Koda mikewar
ishalu sai ya gurfana a tsakiyar taron
yace,tabbas muna cikin tashin hankali da hali na
tsaka mai wuya,abinda nake nufi anan
shine muna cikin tashin hankalin da bamu da
tabbacin fita daga cikinsa sai yanda hali yayi,ni a
tawa shawarar ina ganin a samu mahayi ayi
rubutu na wasika zuwaga sarki Aiyuba a shaida
masa ga abinda ya samu dukiyarsa yayi mana
hakuri ya karo mana kaya idan shekara ta zagayo
sai mu biyashi rabin abinda zamu bashi a
wannan shekara sannan mu bashi na shekarar da
ake baki daya,inyaso wata shekarar ma sai ayi
hakan,kunga kenanan mun jefi
tsuntsu biyu da hogi daya,mun bi yasa kuma mun
cigaba da cinikayya dashi sabanin yaji wannan
batu ta sama,nasan halin sarki Aiyuba zai iya yin
hawa
da dakarunsa yazo ya wulakantamu.Koda
wannan
attajiri yazo nan a jawabinsa sai galadima ya
mike tsaye yace,yakai Ishalu wannan shawara
taka sam
batayi ba,in baka manta ba,akwai yarjejeniya a
tsakaninmu da sarki Aiyuba na rashin yin afuwa
akan duk abinda ya samu dukiyarsa,kada ka
manta sarki Aiyuba ya kwulla wannan kasuwanci
damu ne bisa yahudawa da suka umarce dayayi
hakan suka kuma kimtsa masa ta yanda zai ci
galaba akanmu
idan an kwulla wannan kasuwanci,kayi sani cewa
sarki Aiyuba bai kulla wannan kasuwanci damu
ba
dan samun ribarmu ko dan samun cigabanmu ba.
Ya kulla wannan kasuwanci ne dandai kawai yaci
zarafinmu
ya tozartamu ba dan komai ba duk a cikin
nahiyarsa mu kadai ne kasar da mukeyin addinin
musulunci,kuma yayi iyakarsa kokarinsa akan ya
dakatar damu daga bautar Allah amma hakan ya
gagara,tabbas idan aka tashi dan aike zuwa
kasar Lautul Harus tabbas kafin cikar kwanaki
hudu sai
mashuna sunyi zaman dirshen a cikin
kahonhunan zuciyoyinmu tabbasa sai jini ya
gauraye da kasar
wannan birni na Haural,in gar bamu kasance mu
kafirta ba munbi abinda suke bautawa dan haka
wannan shawarar taka sama bama kaunarta
wata kwatankwacinta duk wanda zai kawo
shawara ya zamana ya kawota daidai da
fahimtarmu.
Koda galadima ya koma ya zauna sai dukkan
jama'ar da suke garin sukayi shiru babu wanda
ya kare cewa kala har aka wuce dakika biyar sai
daga can wani shehin malami da ake kira da
suna Ibini Haisham ya mike tsaye cikin fararen
tufafi kansa da rawani,koda
mikewarsa sai yayi gyaran murya ya dubi
daukacin jama'r da suke zaune yace,hakika
zuciyarmu tayi
rauni kwarai da gaske zuciyoyinmu sun cika da
shakkun wasu zindikai kafurai masu bautar wanin
Allah,lallai daga cikin hasashen karshen duniya
wannan yana daga ciki yaku jama'ar musulmai
kuyi
sani cewa duk irin takamar da sarki Aiyuba yake
ba da koma yake takama ba face sihiri,sihirin
kuma
baikai ayar Allah ba,ina mai son kuyi sani cewar
bazaranar yawan dakaru da sarki Aiyuba yakeyi
akanmu basu isayin komai akanmu ba face mun
barsu duk irin yawansu da tarin bataliyarsu basu
isa suyi nasara akanmu ba saida ikon Allah,lallai
akwai bukatar jajircewa mu shirya kanmu kafin
zuwan wannan rana kamar
yadda kuka sani idan ranar da akai wannan
lissafi ta cika ba a kaiwa sarki Aiyuba dukiyarsa
ba babu
makawa washe garin ranar inuwar gagaruman
sadaukai zasu cika mana birni,zasu yi mana
rumfa da masu zasu haskaka mana rayuwa da
kaifin takubbansu,tabbas hakan gaskiya ne domin
babu
abinda zai hana faruwar hakan tunda dama
abinda suke jira ya samu kenan.To idan haka ne
mai zai hana muma muyi shiri mu fito mu kare
kanmu daga saukar kibiyoyinsu da
garkuwoyinmu,mai zaisa mu fito mu kare
haskakamu dazasuyi da takubbansu mai zai hana
mu zubar musu da jini kamar yadda zasu zubar
nama,idan har muka tashi tsaye da addu'a da
jajurcewa Allah daya haliccemu zai bamu sa'a
akansu to wai ma menene takamar sarki Aiyuba?
Ibn Haisham yayi ajiyar zuciya,Yarima Yazid ya
zuba masa ido tunda aka fara wannan batu sai
yanzu ne yaga abinda yake da bukatar ji,nan da
nan hankalinsa ya fara kwanciya yaji kumarinshi
ya fara dawowa yanzu ya fara jin baiyi asarar
zamowa mai kwazo ba sabanin a baya da yakeji
tamkar shi ba kowan kowa bane a filin daga,duk
irin kokarinsa na korar arnan daji da yanfashin da
yakeyi sai yaji ya tashi a banza,amma yanzu da
ibin Haisham ya fara
nuna cewa suma zasu iya sai hankalinsa ya fara
kwanciya.Ya tsurawa ibin Haisham idanuwa yana
son jin abinda zaice takamar sarki Aiyuba.
Ibn Haisham ya cigaba da cewa takamar sarki
Aiyuba bai wuce
rubutacciyar WASIKAR JINI ba.Wannan wasikar
itace takamar sarki itace takamar duk wani mai
neman daukaka a cikin wannan duniya.Bani da
tarihin WASIKAR JINI amma ina da sani cewa
itace karfin
sihirin sarki Aiyuba itace takamarsa itace sirrin
birninsa tabbas idan waninmu ya mallaki wannan
WASIKAR JINI to babu shakka duk irin takamar
sarki
Aiyuba da bunkasarsa da wani kuri nashi sai ya
saurara kuma sai yayi shayinka,dan haka kafin
cikar
wannan rana da tsufa bai riskeni ba sai naje
kasar na samu wannan wasikar domin na dawo
da ita cikin wannan al'umma tamu ta musulunci
tabbas idan yayi bincike ya gano cewar wannan
wasikar tana cikin wannan kasar,sai ya hakura da
duk wani mugun nufi a garemu sannan kuma
zamu
juyashi yadda mukeso kamar yadda ya juya
ragamarmu,inda ace wannan wasikar zata samu
da basai mun sha wahala mun gwabza yaki dasu
ba,da zarar sunji tana garemu hankulan baki daya
nahiyar nan zai tashi kamar yadda aka maida mu
makaskanta sai mun zo mun zama babu sama
damu.Abin takaicin da kaico babu yanda zamuyi
mu dauko wannan wasikar,amma da akwai
samartaka a tare dani babu abindazai hana ni yin
shiri na tunkari kasar Lautul Harus dan na dauko
wannan wasikar.
Koda jin wannan batu sai baki daya jama'ar dake
gurin sukayi shiru suka nutsu suna kallon Ibn
Haisham shi kuwa Yarima Yazif sai ya mike tsaye
ya dubi kowa dake cikin fadar sannan ya tsayar
da kansa ga kallon Ibn Haisham yace,zuciyata
bata karaya,kuma ban fansar da rayuwata ga
tsoron kafurai ba,zan iya duk abinda ya kamanayi
dan
fansar daukacin al'umma ta,yakai wannan babban
malami ina mai tabbatar maka da cewa a shirye
nake dana yi JIHADI dan haka na shirya yanzu
haka danayi jihadi dan haka na shirya yanzu haka
ka
sanar dani labarin WASIKAR JINI nayi alkawari da
yardar Allah ina nan tafe da ita a cikin kwanakin
da
suka rage mana.
Koda jama'ar dake fadar sukaji wannan batu sai
suka dinga kallon kallo suna masu mamakin
yarima ba don komai ya cikasu ba face shi
yarima tunda ya taso baya kaunar fita koda
wajen kasar dukda ya kasance gagarumin
sadauki bayason fita ko ina koda yan fashin
sumame ne suka kawo hari zuwa cikin kasar da
ya ratattakesu zuwa bakin ganuwar garin
shikenan sai ya dawo bai taba takawa yabar cikin
kasar ba tunda aka haifeahi kawo iyanzu bai san
ko ina ba.
Waziri ya dubi Yarima Yazid
yace,yakai Yarima shin kasan inane kasar Latul
Harus kasan kuwa hadarin da yake ciki
ballantana
kaje da zummar daukar abu mafi daraja daga
garesu tabbas idan kayi wannan gangancin kamar
kana kokarin neman tsayawar numfashinka ne,
yakai Yarima kayi hakuri kayi zamanka anan
domin mahaifinka yana halin MUTUWA KO
RAYUWA ka
duba halin da mahaifinka yake ciki mana,idan
kayi la'akari da irin halin da yake ciki na mutuwa
da rayuwa bai kamata ace kaima ka rasa
rayuwarka a kasuwar daukar rai ba.
Koda jin wannan sai Yarima ya sunkui da kai
daga bisani ya daga kai yace,duk abinda zai faru
rubutaccene daga Ubangijinmu,zamana a cikin
wannan kasa tamu ta Haura bata da wani amfani
inaso ka sani mahaifina yana cikin tsananin
rashin lafiya wanda bazai samu kansa ba sai
washe garin gobe inkuwa ya farka duk yanda
akayi aka sanar dashi abu mara dadi babu
shakkar likitansa ya tabbatar min da zai iya rasa
rayuwarsa, dan haka ya zama dole koda rundunar
mayakan kasar Latul Harus zasu tunkaromu na
fita na tare su dan gudun kada su shigo cikin
kasata har abbana ya farga da halin da ake ciki
hankalinsa ya
gushe zuciyarsa ta buga ya fadi ya mutu,dan
haka ya zame min dole nayi wannan fita a yanzu.
Koda Yarima Yayi wannan furucin sai ya fice
daga cikin dakin taron bai zame ko ina ba sai a
cikin gidansu koda ya isa sai ya riske
mahaifiyarsa a zaune a kusa da mahaifinsa tana
risgar kuka
Yarima ya risina a kusa da ita duk abinda ya faru
ya kwashe ya sanar mata.Koda jin haka sai ta
dubeshi tace,kai kuwa ta yaya kake hangowa
kanka nasara baya ga kaji irin hatsarin da yake
cikin kasar sarki Aiyuba,yakai dana mafi soyuwa
a raina wannan abu da kake kokarin yi tamkar
kana neman tarar aradu ne.Koda jin wannan batu
sai Yarima ya dubi umman tasa sannan ya nuna
mata mahaifinsa dake kwance rai a hannun Allah
yace,wannan Abba nane akwance mutuwa yau ko
gobe,ya ummina kina sane da cewa idan Abbana
ya farfado kafin cikar wa'adin da likita ya sanar
damu ba tabbas sai rundunar sarki Aiyuba ra cika
mana kasa ta batse ta yaya kunnuwan sarki zasu
rufe daga jin sautin karar karafkiyar takubba,ta
yaya kunnensa zai kange daga jin karar tafiyar
kibiyoyi,
ya ummina abinda nakeson sanar dake shine
babu abu mafi masalaha face nayi tattaki zuwa
kasar Latul Harus domin na nemo abinda zai
zamo garkuwa a tsakaninmu da zaluncin sarki
Aiyuba,babu abinda nake bukata daga gareki face
ki samin albarka ya ummina inaji a jikina akwai
alamar samun nasara a kudirina.
Koda yazo nan sai tayi shiru daga bisani
tace,yakai dana ya zama dole na barka kayi
wannan tafiya domin hujjarka tafi tawa saidai duk
da hakan idan ka tafi kana sane da cewa akwai
kananun ayari ko dodannin da suke kawo bara a
garemu,yanzu idan sukaji maganar tafiyarka
kasan saisun addabemu da kawo hari,in kuwa
zasu ci gaba da kawo hari to babu shakka sai
wata rana kunnuwan mahaifinka yaji kuma kasan
abinda yake
wakana daga lalurarsa,dole zaiji kuma zuciyarsa
zata iya bugawa domin kuwa duk cikin kasar nan
babu maharbin da ya wuce kai haka zalika babu
wanda ya
iya yakin sunkuru kamar kai,kai kadaine zaka iya
yin karo da arnan daji na tsawon kwana biyu ba
tare da wani yaji ba,saidai da wannan nake maka
bankwana domin tafiyarka tafi zamanka
alheri.Koda jin wannan batu sai yayi murmushi ya
kuma sumbaci Abbansa ya shiga dakinsa yayi
shigarsa ta mafarauta ya fice daga cikin gidan.
Wannan shine dalilin fitowar Yarima Yazid daga
gida.
Dan haka ya cigaba da nausawa babu ji babu
gani ko waiwaye bayayi,bashi da fata face yaga
yayi tsinke a cikin kasar Latul Harus.
Yarima Yazid yana cikin wannan tafiya saidaya
zo wata kwana da idan ya bita shike nan ya
daina hango ganuwar birninsu ya daina hango
sashin kasarsu gaba daya,koda zuwa wannan
kwanar sai ya
waiga koda waigawaesa sai gabansa ya
fadi,hankalinsa ya dugunzuma ya shiga cikin
tsananin tashin hankali,bai tsaya bata lokaci ba
ya fito da KWARI DA BAKANsa dake sakale a
kafadarsa ya danata a cikin mashi ya koma da
baya cikin tsananin gudu tamkar zai tashi sama.
MAI YARIMA YAZID YA HANGO?
SHIN INA LABARIN YARIMA ZAINUR?
SHIN YARIMA YAZID ZAI SAMU DAMAR
MALLAKAR WASIKAR JINI?
SHIN MECECE MA WASIKAR JINI?
Domin jin duk wadannan tambayoyi sai mu tara a
littafi na gaba don jin amsoshinsu.
Yakuka ce dan naga kamar ma littapin bai
mukuba dan bana kallon commnt din masu cewa
suna so.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyu (2)
Part A
.
LOKACIN da Yarima Yazid ya juya rike da
gwafarsa daya danata sai ya kasance yana wani
gudu mai
abin al'ajabi duk inda yayi taku kamar sau arba'in
a kasa saiya daka tsalle sama ya tafi a cikin
iska,dan haka kafin kace meye wannan ya
kusanci kofar ganuwar birnin Haurul.Ba komai
yasa Yarima Yazid
yin wannan gudu ba face wata kura data taso ta
tokare sararin samaniya,kurar ta toshe kofar garin
ta hada gagarumin hadari a daidai kofar ganuwar
birnin Haural,tsilli tsilli idanuwansa ya fara hango
masa ayarin dakarun yan fashi sunkai kimanin
dubu goma,kowannensu rike yake da makami mai
barazana ga rayuwar dan adam.
Lallai wadannan ayarin yan fashi sun isa abin
tsoro da ja da baya,duk wata jarumtakla idan tayi
tozalo da irin girman wadannan ayarin na yan
fashi da kuma tarin mangara mangaran
makamansu dole shakku ya shiga cikin zuciyarsa
amma abin mamaki yadda Yarima ke cin uban
gudu bashi da buri face ya isa garesu ya hanasu
shiga cikin birninsu ko ta tsiya tsiya. Amma koda
ya kusanto su sosai sai suka
banke kofar birnin suka daga makamansu sukayi
kuwa akan dakarun da suke tsoron kofa.Nan take
suka murkushe su cikin kankanin lokaci suka
kama rufe kofar birnin suka ci gaba da nausawa
cikin garin.
Koda Yarima ya hango sun rufe kofar birnin sai
hankalinsa ya tashi ainun amma da fushinsa ya
kara
ninkuwa ya tabbatar idan ya tsaya kokarin bude
kofar zasu iya isa cikin birnin har suyi barna,sai
kawai ya daka wani uban tsalle ya tashi sama
kamar tsuntsu,koda yayi sama sai ya fara saki
mashin daya dana tun fara hangowarsa dasu.
.
Jarumi Yazid gwarzon jarumi ne masanin iya yaki
da gwafa wannan dalili ne yasa yake iya tarwatsa
dakarun duk yawansu domin idan yana harbi da
kibiya bazakayi
tsammani mutum ne yake tabewa ba yana
sakinta saboda tsananin karfin tafiyar kibiyar,a
duk sa'adda
ya saki mashi ya fita daga cikin gwafa baya
faduwa kasa face ya soke mutum biyar ko shida.
Idan kuwa a kuskure yayi harbin sai wannan
mashin ya soke mutum sama da goma.Dan haka
tun daga sama suka fara jin ana musu ruwan
kibiyoyi,kafin su ankara mazaje sama da arba'in
sun zube kasa matattu ko shurawa
basayi.Dakarun ayarin yan fashin suka ja tunga
suna masu mamakin daga inda akeyi musu
wannan dauki ba dadi,kafin su ankara sai ga
jarumi Yazid ya dira bisa kafafunsa a
gabansu,Yana dirga sai ya kara dame gwafarsa
ya sake jikin iska kafin ta isa garesu ya kara
sakin wasu guda biyu.
Aikuwa sai yanfashin nan suka ci gaba da
zubewa kasa matattu.Koda shugaban yanfashin
yaga irin barnar da Yarima Yazid yake yiwa
yaransa sai yayi wata hatsabiyar kara ya yunkura
ya cire wani
katon katari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login