Showing 39001 words to 42000 words out of 56708 words

Chapter 14 - WASIKAR JINI! COMPLETE Book By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

ya mutu.
*
Lokacin dasu Yarima Zainur suka durfafi cikin
dajin suka kama tafiya saida suka shafe yan
sa'o'i suna tafiya dama yarima yazid ne akan
gaba,kawai sai akaga yaja linzamin dokinsa ya
tsaya cak.
Nan take kowa ya tsayar da nasa dokin akayi tsit
a lokacin da yarima yazid ya kama raba idanunsa
yana kallon gabas da yamma kudu da
arewa,kawai sai ya juyo ya dubi gaba dayan
abokan tafiyarsa yayi musu inkiya suyi
shiru,kuma kada wanda ya motsa daga inda yake.
Nan take yarima yazid ya shiga karanta wadansu
addu'o'i na musamman,faruwar hakan keda
wuya saiga wata runduna ta mayakan sumame
su da yawa sunzo sun gifta ta gabansu bisa
dawakai a sukwane dauke da muggan makamai
suna ta waige
waige da kalle kalle.
Nanfa su sarkin yaki suka firgita
ainun domin sunsan cewa ko ba'a gwada ba
linzami yafi karfin bakin kaza,tabbas cikin dakiku
kadan idan
wadannan dakarun sumame sukayi musu rufdugu
zasu gama dasu komai irin kokarin da zasuyi
kuwa saboda ido ba mudu bane yasan koma
kuma da ganin kura kasan zata ci mutum.
Ba zato ba tsammani sai su sarkin yaki haiman
sukaga Allah bai baiwa wadannan dakaru ikon
ganinsu ba duk da cewa gasu sunzo daf
dasu,wani lokacin ma har
bangaren su sukeyi amma basu gansu ba.Haka
dai wadannan dakarun sumame suka gaji da
neme neme da dube dube suka gaji sukabar
yankin wajen gaba daya.
A sannan ne yarima yazid ya hango wani kogon
dutse a can gabansu nan take ya bayar da
umarni aka karasa can.
Ba tare da wata gardana ba kuwa daga dayansu
suka durfafi wannan kogon dutse.
Da isarsu sai sukaga yazid ya tsaya a bakin kofar
kogon bayan ya shiga cikinsa ya duba ko ina ya
tabbatar da cewar babu wani abu mai cutarwa a
cikinsa saida kowa ya gama shiga cikin kogon
sannan yarima yazid ya tofa wata addu'a ta
musamman a kofar kogon sannan shima ya
shiga.
Bayan kowa ya zauna ana hutawa kuma an
dauko guzurin abinci anci ansha,sai sarkin yaki
haiman ya yunkura da kyar ya mike tsaye yana
mai dogara sanda ya taho inda yarima yazid ke
zaune ya
zauna kusa dashi suka fuskanci juna sannan yace
yakai wannan dan ssarki kayi sani cewa tabbas
yau naga abin al'ajabi a tare dakai kuma zuciyata
ta karkata izuwa ga wannan addini naka,na sani
cewa
inada karfin sihirin tsafi daidai gwargwado amma
sihirin wadancan dakarun sumamen da suka fito
farautarmu ya ninka nawa sau goma,amma sai
gashi
sunzo har gabanmu kuma sun kasa ganinmu.
Ina ganin haka na gamsu cewa ba kowa bane ya
bamu kariya face ubangijinka saboda naga
lokacin da
kake ta karanta wadansu addu'oi a cikin ranka na
neman tsari.
Sa'adda haiman yazo nan a zancensa sai farin
ciki ya kama yarima yazid yace tabbas nayi
murna da Allah ya nufeka da fahimtar hakan,to ka
sani cewa muddin muna cikin wannan kogon
dutse babu wani mahaluki walau mutum ko aljan
da ya isa ya
shigo har nan ya cutar damu,kai hatta dabbobi
da kwari ma ba zasu iya zuwa kusa da mu ba.
Albarkacin addu'ar dana karanta na tofa a bakin
wannan kogo.
Kafin yarima yazid ya gama rufe bakinsa kuwa
saiga wani AYARI na kuraye kimanin su arba'in
sun fito farautar abinda zasuci,kallo daya
zaka yiwa kurayen ka gane cwa suna cikin
tsananin yunwa domin sai zazzaro harsunansu
suke suna
lasar duwatsu da kasa kuma suna dalalar da
yawu.
Koda kurayen suka hango alamun mutane a cikin
kogon da su yarima yazid ke ciki sai suka ruga
da gudu domin su kawar da yunwar su suna kar
™Abbas Abdulkadir Hada Hada™
tar kasa da faratan kafafunsu tamkar sunci
babu.Koda suka iso daf da bakin kofar kogon
dutsen
sai sukayi turjiya suka kasa shiga ciki suka kama
koke koke sunaja da baya.Ba komai ne ya
haddasa
hakan ba face ji da sukayi kamar zasu babbake
saboda wani irin azababben hucin zafi dake
fesowa
daga cikin kogon dutsen.
Ba shiri kurayen suka juya da baya da gudu suka
nausa wani bangaren daban na dajin.
Adaidai wannan lokaci ne su haiman sukayi
doguwar ajiyar numfashi suka dawo cikin
hayyacinsu.
A sannan ne haiman ya dubi yarima yazid yace
tabbas yanzu nayi imani da cewa babu wani
ubangiji wanda ya cancanci a bauta masa face
ubangijin musulunci don haka a shirye nake
yanzu na karbi wannan addinin mai daraja.
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube
yarima yazid har ya budi baki zaice wani abu
kawai sai yaga yarima zainur,gimbiya nauwara,
da dukkan hadiman sarkin yaki sunzo gabansa
sun durkusa sun dubeshi cikin hadin baki suna
masu cewa muma munyi imani da wannan addini
naka.
Take Yarima yazid yaji hawaye ya zubo masa
saboda farin ciki,ba tare da bata lokaci ba ya biya
musu kalmar shahada suka maimaita amma sai
yazid ya lura da wani hadimi gudu daya wanda
ya tsuke bakinsa yaki biya kalmar shahadar.Yazid
yayi shiru bai tonawa hadimin asiri ba,
amma sai ya aiyana a ransa cewa lallai zaisa ido
a kansa tunda bai sani ba ko ya biya kalmar
shahadar ne a cikin zuciyarsa bai biyata a fili ba
tunda shi imani a zuci yake ba a baki ba.
.
Kaico!Allah ka shiga tsakaninmu da munafiki
domin kuwa sharrin munafuki yafi na barawo
takaici da bakin ciki domin shi munafuki tamkar
haske yake yana jikinka
yana morarka amma kuma yana yi maka babbar
illah.
Ashe wannan munafukin hadimi yaron waziri
Ridwan ne kuma yafi shekaru goma sha biyar
yana bauta a gidan sarkin yaki kuma da gaiya
waziri ridwan yasa aka siyarwa da haiman shi a
matsayin
maraya saboda yasan cewa haiman baya ajiye
bawan da ba maraya ba a gidansa,kuma tun
wannan bawa yana yaro yake zuwa gidan waziri
ridwan a sirrance yana kai sirrin gidan haiman
bisa duk abubuwan da yake shiryawa.
WASIKAR JINI
Littafi Na Shida (6)
Part C
.
Yana kai sirrin Haiman bisa duk abubuwan da
yake shiryawa.
A tsawon wadannan shekaru sarkin yaki haiman
yana matukar mamakin yadda waziri yake sanin
abubuwa nasa dayawa na sirri,amma sai yayi
zaton cewa da karfin sihirinsa na tsafi ne yake
sani
bai san cewa yana da munafuki a jikinsa ba.
Lokacin da wannan munafikin bawa ya fito daga
cikin kogon
dutse sai ya falfala da gudu ya tunkari hanyar da
zata kaishi cikin gari,yana cikin gudunne yayi
kicibus da wadannan dakarun sumame na sojan
haya sunyi masa kawanya ba tare da fargabar
komai ba saiya dubesu yayi musu wata inkiya.
Koda ganin haka sai suka sauke makaman dake
hannunsu kasa.
Shugaban su ya dubi bawan yace meye labari?
Waishin a ina kuka buya muka nemeku sama da
kasa a cikin wannan dajin muka rasa.
Koda jin wannan tambaya sai bawan yace ai wani
takadirin
bako ne ya bamu kariya da irin sihirinsa muna
can baya cikin wani kogon dutse kuzo muje na
kaiku
wajen ku shiga ku hallaka su.
Nan take bawan ya juya da baya da gudu su
kuwa dakarun sumamen suka rufa masa baya
cikin murna da mugun nufi.
Koda bawan da dakarun sumamen suka iso bakin
wannan kogon dutse sai suka yi turjiyar dole bisa
jin wannan hucin zafi mai tsananin gaske.
Hatta shi kansa bawan wanda dazun nan ya fito
daga cikin kogon sai ya kasa komawa.
Al'amarin dayayi matukar baiwa dakarun
sumamen mamaki kenan suka rasa dabarar da
zasuyi su shiga cikin kogon dutsen.
Koda ganin haka sai shugaban dakarun sumamen
ya bada izini
aka dawo baya kadan aka tsaya akayi cirko cirko.
A sannan ne shugaban dakarun ya dubi sauran
yaransa yace mu tsaya a nan harsu gaji da buyan
su fito ai duk tsiyadai ba zasuyi ta zama a ciki ba
har abada.
Idan yunwa bata fito dasu ba kishirwa zata fito
dasu.
Haka dai dakarun sumamen suka zuba ido akan
kofar kogon dutsen suna rike da makamansu
kawai jira suke suga wani ya fito daga cikin
kogon dutsen su rafkeshi amma har gari ya waye
babu wanda ya fito,asalima su yarima yazid basu
san abindake faruwa ba a kofar kogon
dutsen,domin barcinsu suke ta sharawa tamkar
suna cikin ainihin gidajensu na kwana.
Saida asuba tayi yarima yazid ya tashi kowa
domin ayi alwala ayi sallah sannan suka hango
rundunar dakarun sumamen acan bakin kofar
kogon dutsen,nanfa hankalin kowa ya dugunzuma
banda na yarima yazid.
Koda yazid yaga haka saiya dubesu haiman a
fusace yace ashe imaninku mai rauni ne ban sani
ba,shin kun mantane da cewa tun jiya Allah ya
nuna muku ikonsa ya hana kuraye ma'abota jin
yunwa shigowa cikin wannan kogon dutse ya
kareku daga sharrinsu?
Koda jin wannan batu sai jikin kowa yayi sanyi
suka kama yin istigfari,yarima yazid yayi gyaran
murya sannan yace yanzu zamuyi alwala mu
gabatar da sallah sannan mu roki Allah akan ya
bamu sa'a akan wadannan abokan gaba kuma ya
karemu daga sharrinsu,da izinin Allah zakuga abin
al'ajabi.
Koda gama fadin hakan sai kowa ya kama yin
alwala sannan yarima yazid yawuce gaba yayi
jasu,bayan an idar da sallah sai akayi addua'a
kamar yadda yazid ya fada.
Ana gama shafa adduar sai kawai akaga sarkin
yaki haiman ya mike tsaye zumbur kamar bai
taba ciwo ba ya zare takobinsa yana mai cewa
duk wanda yayi imani da Allah ya biyoni mu
afkawa wadannan abokan gaba.
Nan take yarima yazid,zainur gimbiya nauwara da
sauran gaba
dayan hadiman haiman ma suka zare takubbansu
suka kwala kabbara suka ruga waje da gudu,
aikuwa suna haduwa da dakarun sumamen sai
aka ruguntsume da azababben yaki mai tsananin
ban tsoro da ban al'ajabi domin nan take su
yarima yazid suka zamewa dakarun sumamen
alakakai sukayi ta ragargazarsu.
Duk inda suka sa gabansu saidai kaga mazaje na
zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona cikin
abinda bai wuce rabin sa'a ba su yazid suka
kashe kaso biyu a cikin kaso ukun dakarun.
Koda dakarun sumamen suka lura da irin
mummunar barnar da akayi musu sai tsurarun
suka cika wandonsu da iska suka ruga izuwa
cikin daji a dimauce domin su tsira da rayuwarsu.
Nan take su yarima zainur sukayi kabbara suka
kuma yi godiya ga Allah bisa wannan gagarumar
nasara daya basu.
A cikin wannan kogon dutse su yarima yazid suka
kara yada zango har wani daren yayi da niyar
cewa gobe da sassafe zasuyi shiri su cigaba da
tafiya don riskar dajin hajrul Aswad yake inda
wasikar jini take.
*
Al'amarin waziri Ridwan tunda ya tura manzo
izuwa ga wadannan dakarun nasa na sumame
dake cikin daji sai ya zuba idanu domin yaga
dawowar manzon yazo masa da labari mai dadi
amma sai yaji shiru kamar maye yaci shirwa.
Al'amarin daya dugunzuma hankalinsa kenan ya
kasa zama ko tsayuwa bis wannan dalili ne ya
kama dokinsa a cikin daren yahau ya fice daga
cikin birnin shi kadai ya
tasamma cikin daji.Koda yazo wannan daji na
karshe wanda dagashi sai birnin nasu sai kawai
ya
hango sansanin dakarun yaki daga can nesa
kada.
Al'amarin dayayi matukar bashi mamaki kenan
domin shi kadai a saninsa babu wata kasa a
nahiyar wacce ta isa ta kawo musu harin
bazato,nan take zuciyar waziri ridwan ta baci
kuma zuciyarsa ta
kama tafarfasa kamar zata kone don haka saiya
tunkari wannan sansani na mayaka batare da
shakkar komai ba.
Ai kuwa yana matsawa kusa dasu sai dubunnan
dakaru suka taso masa akayi masa kawanya
daga masu mashi sai masu takubba.A
sannan ne waziri ridwan ya hango tutar birnin
sarki marwatu a cikin sansanin.
Koda ganin tutar saiya kyalkyale da dariyar farin
ciki ya kwalawa sarki
marwatu kira yace yakai abokina sarki marwatu
maza ka fito ka taryi abokinka ridwan.
Sarki marwatu na cikin tantinsa a kwance yana
barci yaji kamar a mafarki ana kiransa.
Aikuwa saiya farka a razane koda kunnuwansa
suka jiyo sautin muryar
™Abbas Abdulkadir Hada Hada™
waziri ridwan saiya mike zumbur ya ruga waje da
gudu,ridwan na hango marwatu saiya sauko kasa
daga kan dokinsa shima ya ruga gareshi suka
rungume juna cikin tsananin farin ciki.
Nan take sarki Marwatu ya kama hannun ridwan
ya jashi izuwa
cikin tantinsa aka kawo musu giya da nama suka
fara ci,a sannan ne waziri ridwan ya dubi sarki
marwatu a cikin wani irin kallo na rashin yarda
yace shin har yanzu kana kan burinka ne nason
ganin ka
mallake kasata ko kuwa so kake kawai ka rama
wulakancin da dan uwana yayi maka?
Koda jin wannan tambaya sai sarki marwatu ya
bushe da dariya sannan yace ai labari na samu
cewa zaki ya kwanta shi yasa na gaggauta kawo
ziyara domin na
debi rabona kafin sauran dabbobin daji su dasa
masa wawaso.
Dajin wannan batu sai waziri ridqwan ya sake
bushewa da dariya a karo nabiyu sannan ya
turbune fuskarsa yace dubeshi cikin tsananin
fushi yace yakai abokina ni dakai KAR TA SAN
KAR ne,na sani cewa baka yafiya amma duk da
haka nasan kuma ka dade da burin ganin ka
mallaki birnina.To
ka sani cewa ko dan uwana ya mutu yau babu
wanda ya isa ya hau kan karagar mulkinsa face
wanda ya mallaki wasikar jini ya karanceta ka
sani cewa a halin yanzu makiyana sun fito domin
zuwa kogon hajrul aswad inda wasikar jini take.
Nayi iya bincikena na kasa gane inda wannan
kogon yake kuma taswirar zuwa wajen tana
hannun sarkin yaki haiman.
Inason ka taimaka mini mu bazama farautar
sarkin yaki a cikin dajin nan domin mu kamashi
mu
kashe kuma mu dauki taswirar,nayi maka
alkawarin idan muka sami wannan nasara zamu
raba wannan kasa tawa biyu ka dauki kaso daya.
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube
sarki marwatu ya rumgume waziri ridwan suka
kama kyalkyala dariyar mugunta da murna suka
ci gaba da kora ruwan giya suna ciskar naman
kazan dake gabansu.
*
A can kuma kogon dutse kuwa da dare yayi sai
su gimbiya nauwara suka kasa barci saboda
fargabar gagarumar tafiyar dake gabansu da
kuma sanin hadarin dake cikinta.Koda Yarima
Yazid ya fahimci
halin da suke ciki saiya dubesu yace yaku yan
uwana ku kwantar da hankalinku ku sani cewa
ba'a
zama wani a banza dole sai an sha wuya.
Inda kunsan labarin sarki Uzaima da Sarauniya
Aryala da ko kadan baku damu kanku ba.
Koda jin haka sai nauwara ta dubeshi tace
wacece kuma sarauniya Aryala?
Yarima yazid yace ga kadan daga cikin labarinta.
°°°°°°A.A Hada Hada°°°°°°
SARKI UZAIMA na zaune bisa wata kujera ta
alfarma a tsakiyar turakarsa ta barci ya caba ado
saiga shugaban dakarunsa ya shigo tare da
sarauniya Aryala,koda ganinsu sai sarki Uzaima
ya mike cikin tsananin farinciki ya taho garesu
yana mai yiwa Aryala barka da zuwa kuma ya
bude hannayensa da nufin ya rungumeta.Kawai
sai Aryala ta daga kotar
takobinta guda ta tokare kirjinsa da ita tace babu
wani da' namiji daya taba rungumata face
mahaifina, kana son karya wannan alkadari nawa
ne?
Koda jin wannan batu sai sarki Uzaima yayi
murmushi sannan ya juyawa Aryala baya ya nufi
inda wani teburi yake mai dauke da tambula na
ruwan inibi ya fara zuba ruwan inibin a cikin
kofuna
biyu yana mai cewa haba tauraruwar taurari shin
kin manta ne cewa kece kika fara karya
alkadarina na jarumtaka a duniya har kika kaini
kasa?
Menene idan na rungumeki a matsayin matar
dazan aura?
Koda jin wannan batu sai sarauniya Aryala ta
bushe da dariya tace hakika wannan mafarki naka
yana da kamar wuya ko kuma ince yayi daidai da
tatsuniyar yara mara kan gado.
Bincike ya nuna cewa har nabar duniya babu
wani 'da namiji dazai zama mijina saboda me
kake son wahalar da kanka a banza?
Sarki Uzaima yayi dan guntun murmushi a lokacin
daya juyo ya taho gareta rike da kofuna biyu na
inibin na gilashi cike kowanne da ruwan inibi ya
mika mata guda ta rike.
Bata sha ba shi kuma sai ya kurbi nasa sannan
ya dubeta cikin tsawa yace kamar yadda kike yin
mafarki zaki iya sauya alkadarinki haka nima
nake mafarkin sauya nawa,na gani a cikin
madubin tsafina cewa ba zakiyi aure ba amma
hakan baya yana nufin cewar ba zaki iya samun
haihuwa da wani
ba.
A takaice na gane cewa nine wanda zaki sami
juna biyu dashi,babu makawa sai wannan
kaddara ta faru,mai zai hana tun yanzu ki kare
darajarki da kimarki ki aureni domin 'danmu yayi
alfahari da cewar an haifeshi akan tafarkin aure
mai daraja tsakanin sarki da sarauniya.
Kapin sarki Uzaima ya gama rufe bakinsa tuni
sarauniya Aryala ta tari numfashin tana mai daka
masa tsawa tace kada ka sakeyi min batun
aure,shin kana ganin cewa zaka iya yi mini fyade
ne?
Sarki Uzaima ya gyada kansa cikin murmushi
yace ai bakin rijiya ba wajne wasan makaho
bane,ni kaina nasan cewa bazan iyayi miki
fyade ba da karfin tsiya amma ki sani cewa maso
abinka ya fika dabara wannan shine dalilin da
yasa na hana dakaruna shigowa nan kuma na
rantse da gemun iyayena ba zaki fita daga cikin
turakar tawa ba face na sanki 'ya mace,kuma
bada karfin tsiya bukatata zata biya ba,sirrin
yana jikin wannan kofin da kika rike a hannunki a
jikin kofin an shafa wani
sinadari wanda tuni ya shiga dukkan kofofin fatar
jikinki,nan da cikar yan dakiku kadan zaki rasa
gaba daya karfin jikinki ko tsayawa ba zaki iyayi
ba kina ji kina gani zan sarrafaki yadda duk nake
so.
Koda jin wannan batu sai sarauniya Aryala tayi
jifa da kofin dake hannunta ta kama goge tafin
hannunta a jikin rigarta.
Da ganin haka sai sarki Uzaima ya kyalkyale da
dariya ya dubeta yace wannan shine ihu bayan
hari,ai BAKIN ALKALAMI ya riga ya bushe.
Cikin tsananin fishi Aryala ta zare tagwayen
takubbanta ta yunkura da nufin ta afka masa
kawai sai ta kame a inda take domin ji tayi kamar
an zare gaba dayan lakar dake jikinta,jim kadan
kuma saita bingire kasa ta baje.
™Abbas Abdulkadir Hada Hada™
A lokacin da taji ta kasa koda motsa dan
yatsanta guda,sarki Uzaima ya dubeta ya sake
kyalkyalewa da dariya a karo na biyu sannan
yazo kanta ya durkusa
yace yake abar KAUNATA,abar BEGE NA kiyi sani
cewa a wannan duniya kaf yanzu babu abinda
nake SO sama dake,inda zaki bani gurbi a cikin
zuciyarki kuma ki zabeni a matsayin mijinki na
aure da kin
sami cikar dukkan burinki na duniya,to amma
kaddara ta riga fata,ni ma babu yadda zanyi dole
ne
na kau da batun aure a tsakaninmu muddin
inason na cika nawa babban burin na samun
magaji.
Koda gama fadin hakan sai sarki Uzaima ya ajiye
kofin inibin dake hannunsa yasa hannayensa biyu
ya
dauki sarauniya Aryala yaje ya shimfideta akan
gadonsa,koda ya fara cire maballan rigar jikinsa
sai
yaga ta kura masa idanu hawaye na zubo mata.
Nan take yaji ya kamu da tsananin tausayint
amma daya tuna burin dake gabansa sai kawai
yaci gaba da kokarinsa har saida hakansa ya
cimma ruwa.
Hawaye bai daina shatata ba daga cikin
idanuwan Aryala har Uzaima ya kammala abinda
zaiyi,a sannan ne ya kura mata idanu yace,ki
gafarceni yake MASOYIYA ta,daga yau zan kula
dake a matsayin matata a cikin wannan babban
gidan sarauta nawa,kuma na baki
dukkan jin dadin rayuwa da duniya har izuwa
lokacin da zaki sami rabo daga gareni wato juna
biyu,zan kula da lafiyarki yadda ko kuda bazan
bari ba ya taba lafiyarki.
*
A can bakin kofar turakar sarki Uzaima kuwa
lokacin da Barde Husum yaga sarauniya Aryala ta
dade bata fito daga cikin turakar sarki Uzaima ba
sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya kama
hannun
Jarumi Damzur ya jashi izuwa gefe daya ya
dubeshi yace yakai Damzur ka yi sani cewa
tabbas akwai wani abu dake faruwa wanda ba
daidai bane,nasan halin Aryala mutumce wadda
batayin magana mai tsawo,tunda har kaga ta
dade haka da yawa bata fito ba daga cikin
turakar sarki Uzaima lallai ba lafiya
ba.
Koda jin wannan batu sai nan take idanun Jarumi
Damzur suka kada sukayi jawur,zuciyarsa ta
kama tafarfasa kamar zata kone,kawai sai ya
dubi Husum yace maza kaida dakarunka ku
taimaka mini zan
fasa dakarun dake gabanmu da karfin tsiya na
shiga har can cikin turakar Sarki Uzaima,amma
dole ne
mutum daya ya biyoni ciki domin ya taimaka mini
wajen dauko sarauniya koda zamu risketa a cikin
mugun yanayi,zanyi kokarina naga mun gudu da
ita daga cikin gidan sarautar nan mun mayar da
ita can
birnin Nurul Ansar,wannan shine aikina kuma
shine alkawarin dana daukar mata.
Koda jin wannan shawara sai barde Husum yace
an gama ya shugabana,nan take duk su biyun
suka zare takubbansu suka afkawa dakarun dake
gabansu suka
hausu da SARA da SUKA,koda ganin haka sai
sauran yan uwansu dakaru suka kawo
dauki.Nanfa wuri ya yamutse,ihun mazaje da
karafkiyar karafa ya cika gidan sarautar gaba
daya,dakarun sarki Uzaima dake kan katanga rike
da KWARI da BAKA sai suka dimauce suka rinka
sakin harbi ta ko ina,al'amarin daya janyo suke
rinka kashe yan uwansu suma kenan basu lura
ba.
Wannan itace damar dasu jarumi Damzur suka
samu suka tarwatswa dakarun dake bakin kofar
turakar da karfin tsiya suka kunna kai cikin suna
masu falfala azababben gudu.
Sarki Uzaima nacan a gaban sarauniya Aryala
yanayi mata
sambatu sai ya jiyo ihun mazaje da karafkiyar
karafa acan wajen turakarsa a firgice ya mike
tsaye zumnur ya ruga izuwa inda takobinsa da
garkuwarsa suke domin ya dauko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login