Showing 33001 words to 36000 words out of 56708 words

Chapter 12 - WASIKAR JINI! COMPLETE Book By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

kura
mana
idanu ne tamkar baka taba ganinmu ba?
Koda jin wannan tambaya sai yarima zainur yayi
murmushi yace ai ba ku nake kallo ba
™Abbas Abdulkadir hada hada™
ibadar da kukeyi ce ta dauke mini hankalina na
rantse da darajar iyayena da kakannina ban taba
jin
kalmomin dasu ka ratsa raina ba da zuciyata ba
sama da wadanda naji ka ambata a cikin wannan
ibada taka.
Akwai hikima da daraja a cikinsu.Koda jin wannan
batu sai farin ciki ya lullube Yarima Yazid domin
ya fahimci cewa zainur na daf da gane
gaskiya tun kafin ma suyi gagarumar tafiyar dake
gabansu,kawai sai yazid ya dafa kafadar zainur
yace,ya kai abokina ai abinda kaji ma kadanne
daga
cikin kalmomi masu girma na ubangijin
musulunci,da sannu zaka gasgata wannan addini
nawa kuma ka gamsu cewa babu wani ubangiji
daya cancanci a bauta masa face ubangijin
musulunci.Koda yarima yazid yazo nan a
zancensa sai yaga wani hadimin gidan ya shigo
dakin dauke da abinci bisa faranti,take ya ajje ya
fita.
Fitarsa keda wuya sai Yarima Zainur ya dubi su
Yazid yace ai sai
kuzo kuci abinci.Koda jin haka sai Yazid ya dubi
zainur cikin mamaki yace haba yaka abokina shin
ka
manta ne cewar da yammacin nan muka ci abinci
a kasuwa saboda Ardadu bai kawo abincin da
wuri ba.
Zainur yayi murmushi yace ai na kawai ka cire
hannayenka muci abinci duk da haka nasan
baza'a
rasa yunwa ba a jikin ka.
Yazid ya sake yin murmushi ga yarima zainur
yace aini ban taba cin abinci ba sama da loma
uku tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana
saboda a tsarin addini na anason mutum ya raba
cikinsa gida uku.Har Yarima Zainur ya bude baki
da nufin ya tambaya yazid
abinda yake nufi da raba cikinsa gida uku sai yaji
wani hadimin gidan yazo bakin kofar dakin yace
ga manzo daga gidan sarki a gareka.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama
yarima zainur domin shidai a saninsa ba'a taba
aiko kiransa ba daga gidan sarki,don haka sai
yayi zaton kodai wajen
sarkin yaki haiman manzon yazo.Cikin sauri
zainur ya fito daga cikin dakin ya riski manzon ya
dubeshi
yace waye ya aiko ka kuma wajen aka baka
sako?
Manzon ya risina cikin girmamawa yace ya
shugabana mai girma galadima ce ta aikoni
gareka tace lallai tanason ganinka yanzu.
Koda jin haka sai zuciyar zainur ta buga da karfi
ya dubi manzon cikin
kaduwa yace ina fatan dai babu wani abu mara
dadi daya faru a gidan sarki?
Manzo yace mudai babu wani abu da muka gani
ko muka ji ya faru komai na tafiya kamar yadda
aka saba.Koda jin haka sai yarima zainur yayi
ajiyar zuciya yace shike nan bari naje na fito mu
tafi.Take zaimur ya koma cikin dakinsa da sauri
ya kama shirin fita.
Koda ganin haka sai yazid ya dubeshi yace yakai
abokina shin zan iya yi maka rakiya?
Har zainur yayi shiru kamar bazai amince da
rakiyar tasa ba sai kuma ya dubeshi yace babu
matsala ai tafiya mutum biyu tafi daya zo mu
tafi.Cikin murna yarima yazid ya mike da sauri ya
kimtsa suka fita batare da sunce da Ardadu uffan
ba
shima kuma da yake dama akwai mugun nufi a
ransa sai yayi shiru baice dasu kala ba.
Suna fita ya mike tsaye ya leke waje ta tagar
dakin kawai sai ya
hango yarima zainur ya tara gaba dayan hadiman
gidan yana gaya musu wani abu,inda matsalar
take
shine baya iya jiyo abinda yake fada musu.
Take Ardadu ya raya a ransa cewa an kara
matakan tsaro ne a gidan.Nan fa hankalin Ardadu
ya dugunzuma ainun saboda yasan cewa wannan
itace babbar damar da yake da ita wacce zai iya
sato wannan taswira daga jikin sarkin yaki
haiman tunda gashi a cikin gidansa gashi kuma
babu zainur da yazid a kusa,kuma shi kansa
sarkin yaki a kwance yake cikin jinya bashi da
wani karfin dazai iya kare kansa,don haka zai iya
karbar taswirar da karfin tsiya dama tun da suka
zo gidan yayi nazarin gaba
dayan dakarun tsaron yaga gaba dayansu basufi
su goma sha daya ba,su kuwa hadiman basufi su
bakwai ba,don haka ya tabbatar da cewar a cikin
abinda bazai wuce dakika dari biyu ba duk zai iya
gamawa dasu,koda yasuyi masa rubdugi a
matsayinsa na gwarzon mayakin daya saba
tarwatsa ayarin guda ma a daji.
Inda matsalar take shine idan har aka samu
kuskure ya zamana cewa bai sami nasarar dauko
wannan taswira ba tofa shikenan yayi biyu babu
ma'ana bashi babu samun cikon wadancan
makudan kudade wadanda Uraidu yayi masa
alkawari kuma sam bashi da ikon cigaba da zama
da yarima yazid bare ya sami dukiyar da yake
sa ran samu nan gaba a cikin tafarkin addinin
musulunci.
Abinda Ardadu yake kwadayi a cikin addinin
musulunci shine yarima yazid ya gaya masa
cewa akwai lokacin da za'a tafi Jihadi a yaki
manyan kafiran sarakunan nahiyar a sauke su
daga kan karagarsu ta mulki da karfin tsiya.Dajin
wannan albishir sai Ardadu ya aiyana a ransa
cewa zaiyi amfani da wannan dama wajen sace
dukiyoyin sarakunan da aka kashe yana zuwa
yana boyeta a
sirrance ba tare da an sani ba.
Kaico!wanda duk zuciyarsa ta mutu akan son
abin wani tofa mayuwaci
ne ya gane gaskiya saboda imanisa ya raunana
akan yarda da kaddara.
Haka dai Ardadu ya cigaba da sake saken zuci
yana tsaye a bakin tagar dakin yarima zainur har
zainur da yazid suka hau dawakai sukabi manzon
gidan sarki suka fice daga gida,suna fita sai yaga
gaba dayan dakarun gidan sun taru a kofar shiga
turakar sarkin yaki sun kama aikinsu na tsaro.
Koda ganin haka sai ya gane cewa lallai har
yanzu yarima yazid bai gama yarda dashi ba shi
yasa aka gayawa dakarun gidan su kara
tsaro.Kawai sai Ardadu ya bushe da dariyar
mugunta lokaci guda
kuma saiya turbune fuskarsa yace idan har na
bari wannan dama ta wuceni na zama cikakken
wawa.
Koda gama fadin hakan sai Ardadu ya zare
takobinsa ya fice daga cikin dakin Yarima Zainur
ya nufi kofar turakar sarkin yaki gadan-gadan ba
tare da shakkar komai ba,fuskarsa a murtuke
kaida ganinsa kasan cewa babu imani a tare
dashi,kawai so yake takobinsa tasha jini..
.
Toofah Ardadu yaci Amana kuma ya tabe.
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyar (5)
Part C
.
BABU Imani a tare dashi kawai so yake takobinsa
tasha jini.
Koda dakarun tsaron suka hango Ardadu ya
nufosu rike da takobi tsirara sai suma suka zare
takubbansu suka ruga izuwa gareshi,ai kuwa
shima saiya rugo izuwa kansu cikin mugun nufi
tuni ma ya gama aiyana yadda zaiyi musu kisan
farat daya tunda basu fi su goma sha daya
ba,saida ya rage saura baifi taku uku ba kacal su
hadu sai sukaji an daka musu tsawa dasu da
Ardadun duk sai suka tsaya cak suka dubi inda
sautin tsawar ke fitowa wanda ya kasance daga
wani bangare dabam na gidan ne ba daga wajen
turakar sarki ba.
Ba wani bane yayi wannan tsawa face sarkin
yaki,a wannan lokaci sarkin yaki haiman na rike
da wata sanda yana dogarata saboda rashin
karfin jikinsa kuma babu wani makani a
jikinsa.Kawai sai sarkin yaji ya dubi Ardadu yace
yakai wannan tsohon kasurgumin
dan fashi,Ardadu bin Aukas kada ka cutar da
kowa a cikin wannan gida nawa,abinda nakeso
dakai shine
ka fada min abinda kake bukata na baka ka tafi
salin alin,idan dukiya kake so ina da ita nau'i
nau'i shin
zinare kake bukata ko lu'u lu'u ko murjani,inada
yakutu,zubar daji da farar tasa.
Koda sarkin yaki yazo nan a zancensa sai Ardadu
ya gyada kai yace bana bukatar ko dinare daya
da abinda ya danganci dukiya.Abinda nake
bukata kawai shine taswirar zuwa dajin hajrul
aswad na sani cewa tana tare dakai idan har ka
hanani wannan taswirar sai na kashe duk wani
mahaluki dake cikin nan har kai da matarka.
Koda jin wannan batu sai idanun sarkin yaki suka
zazzaro ya dubi Ardadu cikin alamun tsananin
tsoro yace yanzu babu wani abu da zaka iya
karba maimakon wannan taswira,na sani cewa
makiyanmu
ne suka biyaka dukiya mai yawa domin kaci
amanarmu ka sace wannan taswira ka kai
musu,to
ka sani cewa a shirye nake yanzu na baka gaba
dayan dukiyar dake cikin gidannan domin ta
zamo
fansa a kan wannan taswira.
Kafin sarkin yaki haiman ya gama rufe bakinsa
tuni Ardadu ya tari numfashinsa yana mai daka
masa tsawa yace baka da abinda zaka iya
bani,ina mai umartarka daka hanzarta dauko
wannan taswirar ka bani ko yanzun nan takobina
tasha jinin kowa.
Koda jin haka sai hawayen takaici ya zubowa
sarkin yaki haiman cikin
alamun tsananin bakin ciki ya zura hannu a cikin
aljihunsa ya dauko taswirar ya mikawa Ardadu
hannunsa na karkarwa.Ardadu ya fisge taswirar
ya dubata sannan ya bushe da dariyar farin
ciki,kawai
saiya ruga inda bargar dawakai suke ya kwanto
doki guda ya haye kuma ya zabureshi da gudu ya
fice
daga cikin gidan yana mai kyalkyale dariyar farin
ciki.
Al'amarin daya dugunzuma hankalin dakarun
gidan kenan suka rugo izuwa gaban sarkin yaki
haiman,shugabansu ya dubi sarkin yaki a cikin
alamun tsananin damuwa yace haba ya
shugabana
saboda me zaka bari wannan tsohon azzalumi ya
tafi da wannan abu mai matukar muhimmanci da
yafi na rayuwarmu nan gaba dayanmu,shin banaji
kace idan
wannan taswira taje hannun azzalumai shike nan
talakawa sun shiga UKUBA.
Koda shugaban dakarun yazo nan a jawabinsa
sai kawai sukaga sarkin yaki ya bushe da
dariya.Al'amarin daya basu mamaki kenan gaba
dayansu.Haiman ya dafa kafadar shugaban
dakarun nasa yace kwantar da hankalin yakai
Ukasha kayi sani cewa shi kuda ko a wajen
kwadayi akan kamashi,tunda naga wannan
tsohon danfashi tare dasu Yarima jiki na ya bani
cewa saiya
ci amanarsu.
Duk da cewa na sami labarin ya karbi addinin
wannan bako yarima yazid,ina ganinsa a cikin
wannan gida nawa na dauki mataki a cikin raina
kuma na kirkiri dabarar daya kamata nayi.koda
haiman yazo nan a cikin zancensa saiya zura
hannunsa a cikin aljihun wandon ya dauko wata
taswirar wacce ta zama iri daya sak da wacce ya
bawa Ardadu ya nunawa su Ukasha yace,wannan
itace taswira ta gaskiya wadda na bawa Ardadu
jabuce bazata kai makiyanmu izuwa hanyar
gaskiya ba,yaku dakaruna daku da dukkan
hadiman
wannan gida nawa yau kusan shekaru ashirin
kenan ina tare daku,gaba dayanku marayu ne
kuma tunda kuruciyarku na deboku a yakokin
dana fita na rikeku
na raine ku tamkar 'ya'ya na bayan mutuwar
iyayenku babu abinda na rage muku dashi a
rayuwa.
Duk da cewa asalinku bayi ne amma duk aikin da
kukeyi mini biyanku nakeyi,na sani irin amincin
dake tsakanina daku dakuma kaunar da muke
yiwa juna,na sani cewa baku da wanda ya fini
a wannan duniya tunda babu wanda ya taso tare
dashi ya jibanci lamarinku face ni,bisa wannan
dalili
ne naki yarda na bari Ardadu ya yakeku domin
zai iya hallaka kuko cutar da lafiyarka tunda
nasan cewa yafi ku karfi da iya yaki,tunda ni bani
da karfin dazan iya tararsa a yanzu,na sani cewa
zaku iya rufe
sirrina kuma har abada ba zakuci amanata ba shi
yasa nake sanar daku dukkan wanann
al'amarin.Ahalin yanzu kasar nan tamu tana cikin
mugun hadari bisa tarkon makiya saboda a yanzu
haka sarki ya kwanta ciwon AJALI,Kuma
makiyansa so suke su karbe KARAGAR MULKInsa
wannan
taswira itace kadai ta hana su samun nasarar
cika burinsu.
Koda sarkin yaki haiman yazo nan a jawabinsa
sai gaba dayan dakarun da hadiman suka
rungume shi kuma suka fashe da kuka suna cewa
ashirye muke mu sallama rayuwarmu domin ceto
rayuwar jama'ar kasar nan,wannan shine abinda
ya faru a gidan sarkin yaki haiman bayan fitarsu
Yarima
zainur da yarima Yazid izuwa gidan sarki.
Al'amarin su yarima Yazid kuwa lokacin dasuka
iso gidan sarki sai wannan manzo ya shiga
bangaren
gin gimbiya nauwara yayi musu iso,ba tare da
bata wani lokaci ba kua sai aka shigar dasu har
can cikin
turakar tata suna shiga suka iske gombiya
nauwara a zaune ta juya bayanta kanta a
sunkuye.Koda taji motsin shigowarsu kuma ta
gane cewa mutum biyu ne suka
™Abbas Abdulkadir Hada Hada™
shigo sai tayi sauri ta goge hawayen idanunta
sannan ta waigo domin taga wanda yarima
zainur yazo dashi.
Koda ta waigo ta hada idanu da yarima yazid sai
duk su biyun ita dashi zuciyoyinsu suka buga da
karfin gaske.
Al'amarin da babu wanda ya taba jin irinsa a
cikinsu,da yake idanun nauwara sunyi jajur
sakamakon kukan da tasha sai yarima
zainur ya dubeta cikin alamun tsananin damuwa
da firgici yace yake yar uwata menene ya faru
gareki naga alamun kuka a idanunki?.
Koda jin wannan tambaya sai zuciyar gimbiya
nauwara ta karaya har hawaye ya subuto mata
ba tare data ankara ba kawai sai ta dubi yarima
zainur tace ahalin yanzu abbana ya kwanta cutar
ajali kuma baya um baya um um saidai akwantar
a tayar bai iya cin komai hatta ruwa saidai a dura
masa a baki wani lokacin ma ana dura masa
zaiyi amansa,kafin yakai ga
wannan hali yabar min wasiyya guda cewar yabar
amanata a hannunka kuma ya gaya mini cewa
kai da sarkin yakine kadai zaku iya tsirar da
rayuwata da kuma karagar mulkina.
Baya ga wannan yace na gaya maka cewa kada
ka bijirewa sabon abokinka dakayi kuma duk
shawarar daya baka kayi aiki da
ita,shin wannan saurayi dake gabana ma'abocin
kwarjini shine sabon abokin naka?
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
yarima zainur ya kama hannun yarima yace
tabbas wannan shine sabon abokina yarima yazid
'da ga sarki Arsanal na birnin haural yakai
abokina wannan itace yar uwata
gimbiya nauwara wacce na baka labari.Cikin
alamun girmama nauwara da yazid suka gaisar
dajuna sannan yarima zainur ya dubi gimbiya
nauwara cikin alamun tausayawa yace yake yar
uwata kiyi sani cewa ina bukatar naga sarki a
yanzu saboda nasan
cewa ganin karshe zanyi masa don abu ne
mayuwaci naje na dawo daga tafiyar dake
gabana na riske shi.Koda jin wannan batu sai
hawaye ya zubowa gimbiya nauwara tace kuzo
muje izuwa turakar tasa,nan take gimbiya
nauwara ta yunkura da nufin ta wuce gaba izuwa
turakar sarki amma sai yarima yazid yayi wuf ya
shige gabanta yana mai kama hannun zainur
gami da jansa gaba.Batare daya waigo ya dubi
nauwara ba sai yace kiyi hakuri yake gimbiya kiyi
sani cewa ni a addinina mace bata shiga gaban
namiji a yayin tafiya tunda dai zainur yasan inda
zamuje babu matsala.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama
nauwara tace a cikin ranta
wannan wane irin addini ne haka mai alkunya da
kawaici.
Nandai suka dugunzuma su ukun suka shiga cikin
turakar sarki aiyuba.
Sarki aiyuba na kwance bisa gadonsa na alfarma
wadansu hadimansa sun kewaye shi anyi jugum
tamkar ana zaman
makoki,gashi dai sarki ba barci yake ba amma
idanunsa a rufe suka kuma a rame,matuka
sannan tunda ya kwanta wannan ciwo bai bude
idanunsa ba inba don ma alamun numfashin akan
kirjinsa ba da kawai zato za'ayi ya mutu.Da
shigowar gimbiya nauwara tare dasu yarima
yazid sai hadiman suka dare suka basu hanya
suka iso har gaban sarki aiyuba,nan take
nauwara ta zubar da hawaye
sannan ta dubi yarima zainur tace,kaga halin da
abbana yake ciki kuma lallai mutuwa zaiyi babu
yadda za'ayi ya tashi daga wannan cuta,saboda
yagaya mini cewa haka tsarin sirrin tsafinsa yake
cewar da zarar yakai adadin shekarun dayakai
yanzu
akan karagar wannan ciwo zai riske shi,kuma ya
gaya min cewa jinyar kwana gomasha hudu zaiyi
kacal ajalinsa ya cika.
Koda jin wannan batu yarima yazid yayi hailala
yace kaico waya gaya miki cewa akwai wanda ya
isa ya kashe bawa inba ubangijinsa ba?
Kada kuyi imani da tsafi ko camfi domin karyane
ba gaskiya ba ina mai tabbatar miki da cewa
ubangijina zai iya tashin kafadun mahaifinki ko a
yanzu take idan yaso.
Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama gimbiya
nauwara,yarima zainur da dukkanin hadiman
dake wajen,nauwara ta dubi yarima yazid cikin
alamun fushi tace waye kai har da zaka tankawa
tsafin mahaifina?
Shin kanaso ne yanzunnan ka hallaka?
To ka sani cewa shekara da shekaru tun iyaye da
kakankin ban taba jin wanda ya aibata tsafin
gidan nan ba sai kai.
Koda jin wannan batu sai yarima yazid yayi
murmushi yace tabbas daku da iyayenku da
kakanninku tabbas kun dade a cikin bata
mabaiyani,da izinin ubangijina zan
nuna muku gaskiyar abinda nafada.
Koda gama fadin haka sai yarima yazid ya
tunkari gadon da sarki aiyuba ke kwance.
Faruwar hakan keda wuya sai wata irin iska mai
karfin gaske ta banko cikin dakin,wata katuwar
bakar inuwa doguwa sankaleliya
ta baiyana tana mai tsala wani irin kara mai ban
tsoro wacce ta firgita su yarima zainur suka fadi
kasa suna masu karkarwar jiki amma shi yarima
yazid yana tsaye yana fuskantar inuwar.Koda
inuwar ta taso masa zata afka masa saiya tofa
mata addu'a kawai sai akaji inuwar ta sake
kwala kara mai karfin gaske kuma ta fice da gudu
ta cikin tagar daki.
A sannan ne gagarumar iskar data addabi komai
da kowa a cikin dakin ta dauke dif tamkar bata
taba wanzuwa ba.Cikin tsananin mamaki
nauwara,zainur da hadiman sarki suka mike tsaye
suka kurawa yarima yazid idanu,nan take yazid
ya karaso daf da
sarki aiyuba wanda ke kwance kamar gawa,yasa
hannunsa na dama ya dafa goshinsa yana mai
karanta wata addu'a tare da tofa masa ita a
dukkan sassan jikinsa.Faruwar hakan keda wuya
sai idanun sarki aiyuba suka bude ya mike
zumbur ya kama kumallon bakin jini.
Al'amarin dayayi matukar baiwa su nauwara
mamaki kenan kuma ya firgitasu,saida sarki
aiyuba ya gama aman sai yayi ko kadan babu
kwari a jikinsa don haka sai ya koma ya kwanta a
lokacin daya kurawa yarima yazid idanu yana mai
zubar da hawaye.A sannan ne ya bude bakinsa
da kyar ya dubi yarima yazid yace me yasa kazo
ka
karya alkadarina?
Mai yasa kake son karya tasirin daukakata da
kuma gadon iyayena.?
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Biyar (5)
Part D
.
KAKESON karya tasirin daukakata da kuma gadon
iyayena.
Koda jin wadannan tambayoyi sai yarima yazid
ya numfasa yace nayi hakane saboda na nunawa
duniya cewa tafarkin da kuke kai ba shine tafarkin
gaskiya ba,tabbas kuna cikin bata mabayyani
yanzu gashi ka kamu da cutar da kowa yake
ganin cewa babu yadda za'ayi ka warke harka
tsira da rayuwarka,kwana da kwanaki kana
kwance
kamar gawa ba ci ba sha,ba magana,ba motsi da
bude ido saboda bakin sihirin dake jikinka amma
gashi yanzu farat daya da taimakon ubangijina na
tasheka zaune harma ka iya budar baki kayi
magana alhalin kana jiran mutuwarka ne nan da
cikar kwanaki kadan.
Shin wannan bai isa yasa kayi imani cewa babu
abin bautawa da gaskiya ba face ubangijin
musulunci?
Koda yarima yazid yazo nan a jawabinsa sai
sarki Aiyuba ya bushe da dariya.
Al'amarin daya baiwa su gimbiya nauwara
tsananin mamaki kenan,sarki Aiyuba ya sake
yunkurawa da kyar ya mike zaune batare da an
taimaka masa ba sannan ya dubi yarima yazid
yace,kai yazid yanzu kai kana ganin cewa zaka
iya kareni daga kaddarar da ababan bautarmu
suka shirya a kaina,kabar ganin cewa ka tasheni
a yanzu har na iya magana da motsi,ina mai
tabbatar maka da cewa ruhina yana can a dajin
Hajrul Aswad a hannun ababan bautarmu,kuma
ajikin wasikar jini,idan har kanason ka ceci
rayuwata to saidai kaje ka yaki dukkan allolinmu
dake cikin kogon dajin hajrul aswad ka kashe su
su dari tara da casa'in da
tara,sannan kuma ka kone WASIKAR JINI yadda
har abada ba zata sake yin tasiri ba.
Ina mai tabbatar maka da cewa idan ka nufi dajin
hajrul Aswad da wannan manufa saika hadu da
mugayen masifun da zasu shallake
tunaninka,kuma babu yadda za'ayi ka iya tsira
daga wannan masifu bare har ka iya isa kogon
Hajrul Aswad ka kashe allolinmu ka kone
wasikar jini.
Baya ga wannan kayi sani cewa ko masifar da
zaka fuskanta daga dan uwana waziri Ridwan
wanda yake son ya gaje wannan karagar mulki
tawa ta isheka domin bazai taba bari ka sami
nasara ba.
Lokacin da sarki Aiyuba yazo nan a
jawabinsa sai yarima yazid yayi murmushi a karo
na biyu sannan yace,naji yarka tace kabar mata
wasiyar zainur yayi amfani da duk shawarar dana
bashi me yasa kayi imani da hakan alhalin kuma
yanzu gashi ka kasayin imani da abinda zan iya
aikatawa?
Koda jin wannan tambaya sai jikin sarki Aiyuba
yayi sanyi ya sunkui da kansa kas sannan yace
nayi hakane
saboda ni na fison na mutu akan tafarkin da
iyayena da kakannina suka mutu amma ina
sha'awar 'yata ta mutu akan naka tafarkin.
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa
gimbiya Nauwara ta dubi sarki Aiyuba tace haba
yakai Abbana ashe yanzu baka so
ka cigaba da rayuwa tare da ni hat kaga
'ya'yanka da jikokinka?
Koda jin haka sai hawaye ya zubowa sarki Aiyuba
yace yake 'yata kiyi sani cewa na dade da cire
wannan buri daga cikin rayuwata saboda tuni na
bayar da jini na ga ababen bautarmu kuma nasan
cewa bazan kai lokacin da zakiyi aure ba.
Koda jin haka sai Yarima Yazid ya tari numfashin
sarki aiyuba yace yanzu idan na tafi izuwa dajin
hajrul aswad na tsallake duk masifun dake kan
hanyar naje na hallaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login