Showing 51001 words to 54000 words out of 56708 words

Chapter 18 - WASIKAR JINI! COMPLETE Book By Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

tasa.
Koda halittar ta fahimci hakan sai ta tasam musu
su biyun tana jeho musu hannayenta da jelunanta
tana kawo musu mugun duka gami da sara da
suka da kaifin faratan hannayenta.
A karom farkon data kawowa Nauwara sara da
farcen hannunta guda Nauwara ta yunkura cikin
zafin nama ta zare takobinta ta kare saran ai
kuwa sai kafin farcen nata ya raba takobin
Nauwara gida biyu,kafin Nauwara tayi wani
yunkuri tuni halittar ta gabza mata wawan naushi
da jelarta guda a fuska.
Saboda Karfin Naushin saida Nauwara tayi sama
kuma tayi katantanwa sau uku a saman sa'adda
jini yayi feshi daga bakinta ta fado kasa cikin
kogin kankara a sume kuma ta fara lumewa
izuwa karkashin kogin.
Koda Yazid yaga abinda ya faru ga Nauwara sai
ya fusata ainun bai san sa'adda ya kwala
kabbara ba ya daka tsalle sama daga cikin kogin
tamkar daga cikin baka aka cillo shi ya
dankarawa halittar wawan sara a tsakiyar
kanta.Nan take takobin tasa ta rabe gida biyu
amma saboda karfin saran nasa saida halittar
tayi wani uban ruri sakamakon tsananin zafi da
zugin
da taji ta fadi da baya cikin kogin tsundum
tamkar daga sama aka jefo giwa.
kafin halittar ta taso saman ruwan tuni Yazid yayi
nutso kasa ya dauko
Nauwara yayi ninkaya izuwa bakin gaba ya
shimfideta a kasa amma ko alamar numfashi
babu a tare da ita.
Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalinsa
kenan ya fara kokarin dawo da numfashinta yana
mai danna kirjinta.
Kawai sai yaji tasowar wannan halittar daga
karkashin kogin.
A fusace Yazid ya juyo ya kura mata
idanu.Halittar ta fito daga cikin ruwan tana tafiya
sululu a kasa tamkar macijiya kuma ta tunkaro
inda yake.Komai dakewar mutum gami da karfin
zuciyarsa idan yaga wannan halittar yayin
fitowarta daga cikin wannan
kogi tana mai baiyana gaba dayan surarta dole
ne ya
*Abbas Abdulkadir hada hada*
firgita.Cikin zafin nama Yazid ya mike tsaye
zumbur ya shafa ko ina a jikinsa yaji babu
makami ko guda daya kawai saiya dunkule
hannayensa yana mai gyara tsayuwarsa sannan
ya shiga
karanta wadansu addu'o'i na musamman a cikin
zuciyarsa a lokacin da halittar ta cigaba da
durfafo shi.
Koda ya fuskanci cewa halittar so take ta kawo
musu cafka su biyun har da Nauwara wacce ke
kwance tamkar gawa sai ya rugo da gudu izuwa
kan halittar ya tareta suka ruguntsume da
azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa
junansu naushi da bugu,ita halittar tana kai masa
duka da dukkan jelunanta amma sai gashi yana
iya kade hannayen nata da jelunan nata cikin
wani irin bakin zafin nama na gaban kwatance
kuma yana mai da mata martani.
Duk sa'adda ya sami nasarar naushin halittar ko
ina a jikinta sai tayi baya a sama tamkar da
majaujawa aka janyeta saboda
karfin naushin nasa amma saboda naci irin nata
sai kaga ta kuma tasowa sun cigaba da
artabun.Kokarin halittar kawai shine ta samu ta
kanannadeshi da jelarta guda amma ta kasa,shi
kuma kokarin da yake shine ya samu damar
naushinta a fuska ko a kanta saboda ya fuskanci
cewa nan ne lagonta yake,domin sa'adda ya
dankara mata saran nan a tsakiyar kanta saida
idanunta suka wurkile tayi rabin suma ta lume
kasa
a cikin kogon kankarar amma saboda bakin naci
tana farfadowa sai ta taso sama suka cigaba da
artabu.
Saida Yazid da wannan halitta suka shafe kusan
rabin sa'a suna kwamarzuwa tana bugunsa yana
bugunta ya zamana cewa kowannensu naji a
jikinsa amma an rasa wanda zai sami nasara a
cikinsu.
Ita dai halittar tana ta zane masa sassan jikinsa
da jelunanta amma ta kasa sukarsa ko yankansa
da faratan hannayenta,shi kuma ya sami nasara
yana ta gabza mata naushi a fuskarta har idonta
guda ya kumbura subtum yana zubar da
jini,kunnenta guda ya doshe ta daina ji dashi,ko
ina a fuskar tata ya kumbura yayi luhu luhu gashi
dai
ta jigata ainun amma taki hakura sai cigaba da
fadan takeyi.
Ana cikin wannan hali ne halittar ta
shammaci Yazid ta jefa jelarta guda izuwa kan
Nauwara ta kanannade ta ta dagata sama.
Koda ganin haka sai jikin Yazid ya yi sanyi ya ja
da baya.
Koda ganin haka sai halittar ta bushe da
mahaukaciyar dariya mai kama da rurin tsohon
zaki sannan ta dubi Yazid ta bude baki a karo na
farko tayi magana tace,yakai wannan shaidanin
bil'adama kayi sani cewa yau shekarata arba'in
da daya a cikin wannan kogin kankara ina gadin
wannan daji na Hajarul Aswad babu wani
mahaluki daya isa ya ratsa ta cikin kogin nan
walau mutum ko aljan har ya iso nan karshen
gabar batare dana
hallaka shi ba.
Komai yawan runduna kota mutane kota aljanu
saina karkashe su na karar dasu sun zama
gawawarwaki amma sai gashi ka tsalleke wannan
kogi kuma na kasa kashe ka.Yanzu gashi na sami
nasarar dankar abokiyar tafiyarka wacce tayi
dogon suma sakamkon naushi daya danayi mata
dazu,to ka sani cewa har yanzu tana raye ba
mutuwa tayi ba,amma idan kana son ta cigaba da
rayuwa saidai ka tsaya cak a inda kake na matso
gareka na kashe ka batare da kayi yunkurin kare
kanka ba.
Da zarar kayi wani yunkuri na kare kanka ko
cutar dani kuwa zan matse jikin abokiyar tafiyar
taka na kakkarya duk kasusuwan jikinta.
Koda jin wannan batu sai hankalin yarima Yazid
ya dugunzuma ainun ya rasa abinda zaiyi take ya
tuna amanar da yarima Zainur ya bashi akan
Nauwara sannan kuma nan take yaji sonta ya
sake kwarara a zuciyarsa fiye da ko yaushe,kawai
saiya tsaya cak yace na yarda kizo ki kashe ni
amma na rokeki bayan kin kashe ni ki kyale
Nauwara kada
ki taba lafiyarta Koda jin haka sai Halittar ta
bushe da dariya tace aini burina kawai shine na
kashe ka
kuma na hana kowa tsalle wannan kogi saboda
idanban kashe ka ba ka karya lagona kuma ka
rusa tarihin jarumtakata da kwarjini,ina maiyi
maka alkawari cewa lallai bayan na kashe ka zan
sauke
abokiyar tafiyarka kasa amma dole sai dai ta
koma da baya ba zata wuce gaba don tunkarar
kogon
Hajarul Aswad ba.
Koda jin haka sai yazid yace na amince da
hakan,kawai saiya saki jikinsa ya fara kiran
sunayen ALLAH a cikin zuciyarsa yana mai
neman taimakon Allah.
Ita kuwa halittar sai ta cigaba da durfafoshi tana
kyakyala dariyar mugunta,ashe duk wannan abu
dake faruwa tsakanin Yazid da wannan macijiyar
Nauwara ta dade da farfadowa daga dogon
suman da tayi amma saboda tana kanannade a
cikin jelar halittar
a sama babu abinda zata iyayi.Koda Nauwara
taga yadda Yazid ya sallama rayuwarsa domin
ceto tata
sai taji ta kara kamuwa da tsananin sonsa fiye
da ko yaushe kuma sai ta kura masa idanu tana
mai zubar da hawaye saboda tasan cewa lallai
wannan shine gani na karshe da takeyi masa.Nan
dai
halittar ta cigaba da kyalkyala dariyar farin ciki
tana mai kara tunkarar Yazid.Koda ya rage saura
baifi taku biyar ba a tsakanin Halittar da yarima
Yazid sai halittar ta daka tsalle sama da nufin ta
sokawa Yazid faratan hannayenta biyu a
makoshinsa.kwatsam ba zato ba tsammani sai
Yazid yaga halittar ta sandare a sama tamkar
gunki ta fado kasa tim matacciya ko shurawa
batayi ba sakamakon wata takobi data soketa a
kunnenta na dama ta faso cikin kunnenta na
hagu.
Sa'adda jini ya kama tsiri daga cikin kunnen
hagun.
Koda Yazid yayi arba da wanda ke ruke da
takobin sai ya jada baya cikin kaduwa da
mamaki,ba wani bane ba ruke da takobin data
tsire wannan halittar face Sarauniya Lazwara.
Yazid ya dunkule hannyensa biyu yana mai nuna
alamun yin fada da Lazwara wacce ita kuma
fuskarta a cike take da annuri gami da murmushi
a wanann lokaci ne Nauwara ta zaro jikinta daga
cikin jelar matacciyar halittar tasha gaban Yazid
wato ta shiga tsakaninsa da sarauniya Lazwara
ta dubeshi....
Wash littafin da dadi yake dan napiku san karan
tashi..mu hadu gobe
WASIKAR JINI!!!
Littafi Na Takwas (8)
Part B.
.
TA SHIGA TSAKANINSA DA SARAUNIYA LAZWARA
TA DUBESHI TACE WANNAN MAI MULKI KUMA
ABOKIYA CE A GAREMU,ITA CE SARAUNIYA
LAZWARA MAI MULKIN BIRNIN ARNAN DAJI
BIRNIN DAKE MAKWABTAKA DA BIRNINMU.
Koda jin wannan batu sai Yarima Yazid ya dan
saki jikinsa yayiwa Lazwara dan guntun
murmushi kawai sai ya dubi Nauwara yace maza
ki zo mu koma can sansanin abokan tafiyarmu
domin zasu kasance a cikin zulumi da fargabar
rashin ganinmu.
Koda jin wannan batu sai sarauniya Lazwara ta
dubi Yazid a
fusace tace haba malam kai wane irin mutum ne
yaya na ceci rayuwarka data abokiyar tafiyarka
daga hannun wannan azzalumar halitta amma ko
gode mini vakayi ba zaka dauke gimbiya ku tafi
ku barni.
Koda jin wannan batu sai Yazid ya juyo ya dubi
Lazwara cikin nutsuwa yace ai ba kece kika ceci
rayuwata ba ubangijina ne ya cece ni domin
lokacin danaga bani da wata dabara da zan iya
kubutar da rayuwar Nauwara saina kama kiransa
a cikin zuciyata ina mai neman taimakonsa shi
kuma
saiya amsa rokona ya turo baiwarsa wato ke kika
ceci rayuwarmu gaba daya.
Koda jin haka sai sarauniya Lazwara tace ta yaya
ubangijinka zai turo ni na cece rayuwarka alhalin
ni bashi nake bautawa ba?
Yazid yayi murmushi yace ai dake da abinda kike
bauwata da duk wata halitta dake cikin sammai
da kassai ubangiji nane ya halicce
su.
Shine sarki Guda daya wanda bashi da abokin
taraiya bai haifa ba kuma ba a haife shi ba,yana
nan a ko ina kuma yana ji yana ganin komai da
kowa fiye da yadda kusancin ruhi da gangar jiki
yake,idan baki amince da duk abinda na gaya
miki ba ki cigaba da binmu a cikin wannan tafiya
da sannu zaki ga karfin ubangijina da idanunki
kiyi imani dashi.
Koda gama fadin hakan sai Yarima
Yazid yaja gimbiya Nauwara suka nufi hanyar da
zata mayar dasu can sansaninsu da gudu,ita
kuwa
sarauniya Lazwara sai ta tsaya tana tunani da
wasu wasi akan abinda ya kamata tayi.
Koda taga Yazid sunyi nisa sai itama ta falfala da
gudu ta riske su suka cigaba da gudun tare.
Tun kafin su karaso sansanin daga can nesa
hankalinsu ya dugunzuma su ukun sakamakon
hango wani irin
hayakin wuta a sama yayi tsiri ba kyan gani.
Koda hango wannan hayaki sai zukatun su
Nauwara suka buga da karfi suka kara kaimin
gudunsu tun
akan hanya suka fara yin tuntube da gawarwakin
jama'arsu.
Aikuwa sai Nauwara da Yazid suka fara zubar da
hawaye bisa ganin yadda aka yiwa jama'ar tasu
KISAN GILLAH duk da sun san cewa shahada
sukayi.
Cikin dimauta Yazid da Nauwara
suka kara karfin gudunsu Yazid na kwalawa
Haiman da matarsa kira ita kuma Nauwara tana
kwalawa dan uwanta Zainur kira amma sai sukaji
shiru basu amsa ba.
Al'amarin daya kara dugunzuma hankalinsu
kenan,nanfa suka cigaba
da ganin gawarwakin dakarunsu har suka iso
sansanin nasu inda suka iske shi a kone duk
tantunansu da komai nasu kuma ko ina
gawarwaki ne da jini male male a kasa.
Bama su Nauwara ba hatta sarauniya Lazwara
bata san sa'adda idanunta suka ciko da kwalla
ba ta fara zubar da hawayen
tausayi sakamakon ganin irin kisan gillar da akayi
yiwa jama'ar su Nauwara.
Kusa kowace gawa saida akayi gunduwa
gunduwa da ita.
Saida suka dubo ko ina a sansanin amma basu
ga gawar sarkin yaki ba data matarsa da kuma ta
yarima Zainur.
Al'amarin da yayi matukar kara dugunzuma
hankalinsu kenan suka cigaba da kuka ba
sassauci saida suka jima suna kukan sannan
suka dawo cikin hayyacinsu.kawai sai Yazid ya
mike tsaye a fusace ya dubi Nauwara a lokacin
daya dauki
takobi da garkuwarsa yace zo mu tafi can
sansanin abokan gaba domin daukar fansa,na
tabbata sun kashe Haiman,Zainur da matar
Haiman.
Caraf sai sarauniya Lazwara tace Haiman da
matarsa da kuma Yarima Zainur basu mutu ba,su
kadai ne suka tsira da rayuwarsu a wannan harin
sumame da abokan gaba suka kawo musu,amma
sun kama su sun tafi dasu izuwa can
sansanin nasu wajen sarki Marwatu da Waziri
Ridwan domin a raye suke bukatarsu.
Koda jin haka sai Yazid da Nauwara suka sake
fusata Nauwara ta dubi Yazid tace zo muyi sauri
muje can sansanin abokan gaba ayita ta kare
komu ko su.
Dajin wannan batu sai sarauniya Lazwara ta
bushe da dariya sannan ta murtuke fuskarta tace
ta yaya kike zaton cewa ku biyu rak zaku iya
yakar sama da mutum dubu dari uku da doriya?
Ina mai tabbatar miki da cewa idan kuka kai
kanku sansaninsu waziri Ridwan tamkar sun
sayar da
rayukanku ne wai shin ma kun fito ne domin ku
dauki fansa ko kuwa domin kuje kogon Hajarul
Aswad ku dauko wasikar jini ku koneta domin ku
ceto rayuwar al'ummar wannan nahiya?
Ku sani cewa su Waziri Ridwan ba zasu kashe
Haiman da Zainur ba saboda suna son suyi
garkuwa ne dasu domin ku fanshe su da wannan
taswira ta zuwa kogon Hajarul Aswad.
Idan kuka kuskura kuka basu wannan taswirar to
ba zasu baku su yarima Zainur ba zasu kashe su
ne kuma su kashe ku,sannan suje su dauko
wasikar jni su cigaba da yin mulkin zalunci a
wannan nahiya.
Lokacin da sarauniya Lazwara tazo nan a
zancensa sai jikin Yazid dana
Nauwara yayi sanyi sukayi shiru suna tunani.
Daga can sai Yazid ya dago kai ya dubeta yace
to wai ke menene dalilin da yasa kika biyo mu
nan har kika taimake mu?
Shin kema so kike ki yaudare mu ki
sace wannan taswirar daga hannunmu domin ki
mallaki wasikar jini ko kuwa kina da wata manufa
ne daban wacce bamu sani ba?
Koda jin wannan tambaya sai sarauniya Lazwara
taja dogon numfashi sannan ta zauna a kasa
dirshan ta dubi Yazid cikin nutsuwa tace sama da
shekaru hamsin
baya tun kafin a haifeni jama'ata basu taba shiga
harkokin wata kasa ba a wannan nahiya.
Muna zaman lafiya da kowane sarki amma
bincike ya tabbatar mana da cewa muddin waziri
Ridwan ko sarki
*Abbas Abdulkadir Hada Hada*
Marwatu dayansu ya mallaki wasikar jini saiya
yake mu ya kawar damu daga doron kasa yadda
har abada ba za'a sake tunawa damu ba.
Kuma ashe ya zama dole na fito na kare birnina
da jama'ata.
Tabbas ni daku akan aiki guda muke,kafin
Lazwara ta gama rufe bakinta tuni Yazid ya tari
numfashinta yana mai cewa na yarda muna kan
aiki guda amma ba tafarki iri guda ba,mu muna
kan tafarkin addinin musulunci ne ke kuwa kina
kan tafarkin tsafi.Yanzu wace shawara zaki iya
bamu
dangane da wannan al'amari kuma menene
matsayinki bayan mun sami nasarar dauko
wasikar
jini mun koneta,shin zaki karbi addinmu ne ko
kuwa zaki koma kasarko ne ku cigaba da
addininku na tsafi ke da jama'arki?
Sa'adda Lazwara taji wadannan tambayoyi guda
biyu sai tayi gyaran murya tace sai yanzu kayi
mini tambaya mai daraja.
Da farko dai inaso ku sani cewa babu wani
mugun nufi a cikin zuciyata ko son kai a kan
wasikar jini,fata na kawai shine akawar da
zalunci a wannan nahiya a sami zaman lafiya da
kwanciyar hankali.Abu na biyu kuma shine zan
zuba ido naga iya karfin abin bautarku
daga nan zuwa isarmu kogon Hajarul Aswad idan
har naga kun iya dauko wasikar jini da
taimakonsa lallai nima zan karfi addinin naku.
Ina mai tabbatar muku da cewa nan da ko
yaushe zamu iya gani manzo daga sansanin
abokan gaba zaizo ne da sakon cewa idan kuna
son rayuwar Haiman da matarsa da Zainur to
kuje kukai wasikar jini.Koda jin wannan batu sai
hankalin Yazid dana Nauwara ya kara dugunzuma
ainu,
Nauwara ta dubi Lazwara tace wace amsa ya
kamata mu basu ko kuwa zamu bi manzon nasu
ne mukai Taswirar wasikar jinin.
Sarauniya Lazwara ta girgiza kai tace a'a ba
zamubi manzon ba sako zamu bashi kamar yadda
suka aiko.Abinda zaku gayawa manzon shine ya
koma ya gayawa iyayen gidansa cewa ba zaku
bayar da taswirar ba sai acan tsakiyar dajin da
kogon Hajarul Aswad yake.
Wannan wata babbar hikima ce nayi muku sai a
nan gaba zaku fahimci hakan kuma ku gargade
su a kan cewa idan suka kuskura suka taba
lafiyarsu Haiman to a bakacin Taswirar.
Har Yarima Yazid ya bude baki zai tambayi
Sarauniya Lazwara ko wace irin hikima take nufi
da cewar sai a tsakiya dajin Hajarul Aswad zasu
bayar da wannan taswirar sai kawai suka jiyo
sukuwar doki an durfafo wannan konan nan
sansanin nasu,suna dago da kawunansu su ukun
sukga ashe kuwa maganar Lazwara ce ta
tabbata wato manzo ne daga sansanin abokan
gaba.
Jim kadan sai ga manzon ya iso daf dasu yana
mai jan linzamin dokinsa,take dokin yayi turjiya
ya risina a gaban gimbiya Nauwara ya kwashi
gaisuwa.Tana hada idanu da manzon taga ashe
babban hadimin waziri Ridwan ne wanda ake
kira da suna Ubaiyu bin Marwas.Ubaiyu ya dago
kai ya dubi Nauwara yace ya shugabata mai
girma Waziri Ridwan yace na shaida muku cewa
sarkin yaki Haiman da matarsa da kuma Yarima
Zainur na hannunsu a can sansanin sarki
Marwatu idan
har kuna son ku fanshi rayuwarsu to kuje ku kai
musu taswirar zuwa kogon Hajarul Aswad in ba
haka ba kuwa zasu kure muku gudu su kashe ku
kamar yadda suka kashe sauran jama'arku.
Koda Ubaiyu yazo nan a jawabinsa sai gimbiya
Nauwara ta kyalkyale da dariya.
Al'amarin daya baiwa Ubaiyu mamaki kenan yace
haba gimbiya yaya keda kike cikin wannan hali
zakiyi dariya,shin bakya kishin dan uwanki ne
bakya son ya tsira da rayuwarsa?
Nauwara tayi murmushi tace ai idan ma kuka
kashe dan uwana da sarkin yaki farin ciki zanyi
saboda sun sami shahada kuma zasu sami
babban rabo da sakamako na gidan Aljanna.
Ka koma ka sanar da iyayen gidanka cewa ba
zamu basu wannan taswirar ba sai a tsakiyar
dajin Hajarul Aswad.
Koda jin wannan batu sai idanun Ubaiyu suka
zazzaro yace haba ranki ya dade kiyi tunani
dai,caraf sai sarauniya Lazwara ta tari nunfashin
Ubaiyu tana mai daka masa tsawa gami da zare
takobinta tace maza kabar wajen nan ko nasa
takobina na sare kanka.
Kawai kaje ka isar da sakon da aka baka.
Koda jin haka sai jikin Ubaiyu ya kama kyarma
cikin hanzari ya kama dokinsa ya haye ya juya
da baya ya zabureshi da gudu su
kuwa sai suka bishi da kallo har saida ya bace
musu da gani.
Faruwar hakan keda wuya sai sarauniya Lazwara
ta dubi Yazid da Nauwara tace ku tashi mu ruga
da gudu izuwa cikin dajin nan
muyi sauri mu isa can tsakiyar dajin Hajarul
Aswad kafin abokan gabar nan su zo su riske mu
domin
Ubaiyu na sanar dasu sakon ki zasu biyo
bayanmu.
Ba tare da wata gardama ba kuwa sai Nauwara
da Yazid suka mike tsaye suka falfala da
gudu,itama sarauniya Lazwara saita bisu a
gujen,nan da nan tazo ta tsere musu ta basu
tazara mai yawan gaske domin wani irin gudu
takeyi na ban al'ajabi har tashi takeyi sama
kamar tsuntsuwa kai da gani kasan cewa aikin
sihirin tsafi ne.
Koda ganin haka sai shima Yarima Yazid ya
kama yin wata addu'a ta musamman ai kuwa
nan da nan karfin gudunsa ya karu shida na
nauwara.Nan da nan suka zo suka wuce
sarauniya Lazwara kafin ta ankara sun bata rata
mai yawan
gaske.
Nanfa Lazwara ta kara zage damtse iyakar
iyawarta duk dalasimanta na tsafi babu wanda
bata ambata ba domin ta wuce su amma sai ta
kasa.
Al'amarin dayayi matukar girgiza ta kenan yasa
ta firgita da al'amarin ma'abota addinin
musulunci kenan.Saida suka shafe sa'a uku da
rabi suna wannan gudu suna ta gifta bishiyoyi har
ta cikin koramai suke bi suna taka ruwa tamkar
akan kasa suke tafiya.
Wannan shine abinda ya faru ga su Yarima Yazid
bayan su sarki Marwatu sun kaiwa sansaninsu
harin bazato sun kashe gaba
dayan dakarun nasu.
*
A can kuma sansanin su sarki Marwatu kuwa tun
daga lokacin da suka ci yaki a sansanin su sa
yarima Zainur sai suka kamo sarkin yaki Haiman
da matarsa da kuma Yarima Zainur suka jefasu
cikin wani keji a ka dora
*Abbas Abdulkadir Hada Hada*
kejin akan keken shanu aka rinka wulakanta su
akan hanya ana wahalar dasu.Har aka iso
sansanin ko ruwa ba'a basu sun sha ba kuma
ana isa aka fito dasu daga cikin kejin aka daure
su a cikin rana
ba'a kwance su ba saida rana ta fadi aka kwashe
su kamar tsumma saboda tsananin jigata ta
yunwa
da kishirwa bisa wannan dalili suka fita daga
haiyacinsu.
Bayan an mayar dasu cikin keji an kulle ne aka
kawo musu ruwa makurwa uku uku kadai aka
basu gami da abinci loma uku uku kadai aka
basu.
An basu wannan abinci da ruwa ne don kawai
kada su mutu,lokacin da suka danci wannan
abinci ne suka dawo cikin hayyacinsu sai matar
Haiman ta dubeshi a lokacin da hawaye ya zubo
mata tace,yakai mijina yanzu shike nan mu tamu
ta kare kenan an kashe gaba dayan dakarunmu
daga mu mu ukun nan sai Yazid da Nauwara ne
kadai muka rage muma din kuma ga dukkan
alamu mutuwar zamuyi.
Koda jin wannan batu sai Haiman
ya kamo matarsa ya rungumeta a kirjinsa yace
yake matata ina so ki sani cewa wuya bata kisa
kuma ko mutuwa mukayi akan wannan tafarki
bamu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login