Showing 45001 words to 48000 words out of 71752 words

Chapter 16 - YAN BIYU NE BOOK COMPLETE BY MRS KD.doc

Mrs KD   

29 Sep 2025

1976

abinsha ne yakawo musu kwalbobin giya kusan guda biyar tare da cup, daya daga cikin abokanasu ne yazuba musu a kofinan, mamakine yacika su lokacin dasuka ga Irfan yadauka yashanye, kara zubaima yayi, yadauka yashanye, nan suka gane ba kalau ba, dan sunsan bayason shan giya, haka suka dinga bashi yana sha, harse da yabugu sosai, yadena gani sosai, Esha ce ta hango shi, hakan yasa tanufo inda yake, tana zuwa ta zauna, kana takai hannunta saman kirjinsa tana shafawa, janye hannunta yayi, yana kokarin mikewa, "what giya" Esha tafada dan tasan bayashan giya, "waya bashi giya acikinku" "kina nufin danneshi zamuyi mu dura mai dakansa yasha" "Irfan meke damunka haka" be kula taba yanufi hanyar futa yana tangadi, Joseph na hangoshi ya nufoshi, yana fadin "oga kabugu fa" cikin muryar maye yace "ni ban bugu ba, mutafi gida" budemai mota yayi ya taimaka mai yashiga, shima yashiga yajasu, yanufi gida kamar yadda ogan nasa yafada, suna zuwa gida, Joseph yayi parking, kana yafuto ya bude mai kofa, part din Mommy yawuce yana tangadi, kararrawa ya danna, me aiki tazo tabude mai, "yallabai sannu da zuwa" batare daya amsa mata ba taga yana kokarin fadowa kanta, aikam dasauri tamatsa, yashige ciki, gaba dayansu suna falour azaune, yashigo, yana tangadi, yafada saman kujera, mikewa sukai gaba daya suna kallonsa,





=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

MRS (K D)
??

Romantic=??


Hot loved'?


Marubuciyar littafin
SOYAYYA DA IZZA
Ayanzuma nakara kawomuku wani sabon book
dina me suna (YAN BIYU NE)
ku biyoni domin kuji ya labarin ze kasance
karki bari abaki labari my sister

free page yakusa karewa=?/?=?/? kuyi maza ku fara biyan kudin ku=ذ?=ذ? kafin free page yakare=?
?=?
? ku hanzarta kubiya danjin cakwakwakiyar dazata faru nan gaba=??=??=??

ku biya ta wannan hanyar

=?G?=?G?=?G?

paid book 300
account number 9045749823
bank name Opay bank
shedar biya ta wannan number =?G?=?G?=?G?
09030849138 WhatsApp only
ko kuma katin waya ta wannan number
09045749823 Airtel
*************************************


DOMIN SHIGA GROUP NA YAN BIYU NE YA DANNA RUBUTUN KASAN NAN=?G?=?G?=?G?=?G?
https://chat.whatsapp.com/BcgtqAM3mDe4JRTJQzOoAF



DUK ME SON LITTAFIN YAN BIYU NE DAGA FARKO YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA=?G?=?G?=?G?=?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J




page 30


_________________________________________________________________________________________

______________Daddy ne yakalli Mommy yace "me hakan ke nufi" bata da bakin magana dan ita kanta Irfan yabata mamaki, "Sawban kasan Irfan na shaye shaye iyee" "no Daddy bayayi bansan yakai yau yasha ba" "duk abunda yafaru laifin kune da baku sanar dani ba, to wlh zan dau tsatstsauran mataki a kansa" "kayi hakuri dan Allah wlh baya yi tsautsayine" wata uwar tsawa Daddy yadakawa Mommy wadda tasa ta yin shiru "kada wanda yasake a cikinku ya roke ni dan sena hukuntashi" Mommy tasan tabbas tunda Daddy yace seya hukun tashi to tabbas seya yi, abunda take gujema Irfan kenan, dan Daddy mutum ne me zafi, kuma bayason abunda ze taba mutuncinsa, "Sawban ciromun wayarsa daga aljihunsa" tsayawa Sawban yayi yana kallon Daddy, "ok bazakayi ba matsa" hannu Daddy yasa a aljihun Irfan yaciro wayarsa, "mutumin banza ka rasa me zakayi se shaye shaye kuma giya, ina ai ba a gidana ba, idan ma abokan harkata sukaji dana nashan giya ai mutunci na seya zube a idonsu, yacca suke kallona mutumin kirki, to wlh bazaka jamun zagi ba, ina tunanin yanzu kun girma kunyi hankali nine harda damka muku kasuwanci ku rike, ashe ba hakaba ne, to ni sam bazan bar dan cikina ya lalata rayuwar saba, yanzu idan Abba yaji Irfan nashan giya ni kaina sai raina ya baci har kema" ya nuna Mommy da tuni tafara hawaye, yana gamawa yashige yabar gurin "Mommy shikena Irfan yajama kansa abunda nake gayamai kenan amma yaki ji" Sawban yafada yana kallon Irfan din da idanunsa a rufe, yanajin maganganunsu amma baya ganewa, "ni yanzu bansan wanne hukunci Daddy dinku zeyi mai ba, bansan ya rabani dashi" "wlh Mommy nima bansan ya rabamu bazan iya jure rashin saba" "koma mene ai shiya jazawa kansa bayajin magana" "amma Mommy duk abun Irfan ban taba gani yasha giya ba" zama Mommy tayi kusa dashi takamo hannayensa tana fadin "Irfan me kayi haka, meyasa ka aikata haka, kasan Daddynku bayaso meyasa" takarashe maganar tana kuka "Mommy kiyi shiru, insha Allah Daddy ze sauko, abu daya zaki taimakamana dashi, ki daure ki shawa kansa kada ya hukunta Irfan" "Sawaban kasan halin Daddynku sarai baya magana biyu, tunda yace ze hukunta shi to seya hukunta shi, sedai zan rokeshi dan Allah yamai sassauci" "Mommy dan Allah ki kokarta" "ok kadaukeshi ka kaishi part dinsa" "tom" mikar dashi yayi, ya rikeshi suka fuce, itakuma Mommy tanufi gurin Daddy, bayan yakaishi bedroom dinsa ya kwantar dashi saman bed, tuni yabaje yafara bacci, kallonsa Sawban yayi yace "bro meyasa zaka lalata rayuwar ka kasan bazan iya jure ganinka cikin wani hali ba, kaine rayuwa ta, bazan iya jure rashin kaba" blanket yadauka yarufeshi kana yafuce,
Mommy tana shiga bedroom din Daddy, ta gashi yanata kai kawo, a hankali takarasa kusa dashi, tace "dan Allah kayi hakuri, nina tabbata ba haka kawai Irfan yasha giya ba" "kinga dakatamun banson jin komai, kome yafaru ai laifin kine, nasha sanar dake idan kinga yaranan na aikata abu na rashin gaskiya ki gaggawar sanar dani, amma bikiyi ba, inason nabawa yarana tarbiyya me kyau ko dan na samu salama ranar gobe kiyama, bansan kudin danake dashi yashagaltar dasu, koda yaushe Abba yana fadamun ku akaita abun alkhairi kar kudin danake dashi ya rudeku, kullum maganarsa kenan, kuma munbi maganarsa gashi munzama mutanen kirki dani da dan uwana, amma kalli abunda danki ya aikata" "nasani kabasu tarbiyya dai-dai gwargwado, amma kamai uzuri ba laifinsa bane" "kinaso nayimai uzuri gobema yakara aikatawa, shi baya koyi da Hassan dinsa yadda yake gudanar da rayuwarsa, baya bashi sha'awa" "kayi hakuri dan Allah ko bazaka yafemai ba ka sassautamai hukuncin" "kinsan ina matukar son yarana, duba da mun jima kafun musamu haihuwa, kuma gashi sune su biyu ya'yan mu zan iya bada komai saboda su" "nasani shiyasa nakeso kamai sassauci" "kije ki kwanta dasafe ki jira hukunci na" daga haka shima yanufi bed din ya kwanta ya rufe idanunsa, sam bayajin bacci, yana tunanin me ya kamata yayi"
a toilet din takwana, dan batasan sanda bacci yadauke ta ba, alwala tayi, kana tafuto, tayi sallah, ta zauna saman sallayar tayi tagumi, dan ta gaji da zama cikin gidan, tana nan zaune taji anbudo kofa, bata ko dago ba, dan tayi tunanin shine, Joseph ne , karasowa yayi kusa da ita, da ledoji hannunsa, gani tayi ya zo har inda take abunda be taba ba, taga ya durkusa, kallonshi, takeyi, tanajiran ganin me zeyi, magana yafara cikin hausarsa wacce daker ake ganewa yace "madam inason sanar dake, kinyi kuskure da kikace bakya son oga, saboda oga na sonki sosai, ban taba ganin oga yashiga damuwa akan mace ba se akanki, oga mata ne ke binshi yana wulakan tasu, kina da matukar sa'a a rayuwar ki, kiyi kokari kiyi amfani da damarki, ta soyayyar da oga yakemiki" harya gama bata dago ta kalleshi ba, seda taji yabude kofa yafuce, kana ta dago, 'kenan dagaske yanasona kamar yadda yafada, to amma ai da yanasona baze dingayimun abunda banaso ba' tayi maganar cikin zuciyar ta, haka ta dunga tunane tunane, danko abincin ma kasa ci tayi,

bayan yatashi dasafe yaganshi a part dinsa, seya fara tunanin waye yakawoshi, 'watakila Joseph ne' yafada a zuciyarsa, tashi yayi ya shiga toilet yayo wanka yafito yashirya, neman wayarsa yashigayi dan ya kira Joseph yaji lafiyar A'isha, yaduba amma be gantaba, hakan yasa yayi tunanin ko ya barta a mota, futowa yayi yanufi part din Mommy, ba kowa, kawai se ya zauna, yana tunanin ko wanne hali love ke ciki, shigowar Sawban ce takatse mai tunanin daya ke, yakalleshi, zama Sawban yayi yana kallon dan uwan nasa, "yawwa blood aramun wayarka na kira Joseph inaga na manta wayata a mota" "bro wayarka na gurin Daddy" "Daddy kuma me yakai wayata gurin Daddy" abunda yafaru Sawban yafada mai, hakan yasa yadafe kai yana fadin "nashiga uku Sawban yanzu yazanyi" "ka kwantar da hankalinka kajira muji me zece" kalmar innalililahi wa'inna'ialaihi raji'un, ita kawai yake maimaitawa, Mommy ce tafuto, da sauri Sawban yanufeta yana faWin "Mommy ya ake ciki" "Sawban bansaniba kasan baze sanar dani ba" inda Irfan yake takarasa ta zauna, kana tace "Irfan meyasa kayi haka, baka tausayi na ne baka tunanin halin dazan shiga" hannayenta yakama kana yace "Mommy kiyi hakuri ki yafemun wlh ba'a son rainaba, raina ne yabaci" "amma kasan dai Daddy dinku baze barka hakaba" shigowar Daddy ce ta katse su, dukka suka kalleshi, beko kalle suba yawuce dining, dama an kammala jere breakfast, wata yar aiki ce tanufo dining din sanye da uniform, tayi serving dinshi, kana takoma gefe ta tsaya kanta a sunkuye, abincinsa yafara ci kamar ma beson dasu agurin ba, ganin haka suma suka mike suka isa dining din, bayan anyi serving din su Mommy tayiwa yar aikin alamar ta tafi, gaba dayansu ba wanda ya iya dandana abincin , jira kawai suke Daddy yayi magana, bayan ya kammala ci yadau tishu ya goge bakinsa, seda yamike ze tafi ya kalli Irfan yace "kaje ka shirya yanzu, kadauki abunda kake da bukata, yanzu zaka wuce airport, zaka tafi America karo karatu na 2 years, idan kaga dama ka sauya, idan kuma baka ga dama ba kada ka sauya zakai tazama acanne, kuma inada mutanen danasa zasu kula dakai, zasu sama ido sosai, zasu kasance dakai a duk inda kake" yana kaiwa nan yawuce, mikewa yayi yanufi Mommy yakamo hannayenta yace "Mommy dan Allah kije kimai magana wlh Mommy bansan zuwa bazan iya zama ba tare daku ba" "Irfan kasan halin Daddy dinku baze sauya magana ba, ni kaina banson kayi nesa dani, shiyasa koda kuna yara ban yadda kuje wata kasar ba karatu, amma yanzu za a daukemun kai" shikam Sawban yama kasa magana, tunanin yadda ze zauna batare da dan uwansa ba yake "Sawban kaje kabashi hakuri bazan iya zama batare daku ba" "Irfan nima bazan iya ba" "Mommy dan Allah ki taimaka mun bazan iya rayuwa babu love ba" "dole haka zakai rayuwa ba ita" "Mommy wlh zan iya mutuwa" "bazaka mutuba bazaka mutuba" "Sawban bani wayarka nakira Joseph" shigowar Daddy ce ya katse su, "ok ka karaso to jira gamunan zamu futo" yana kashe wayar yakalli Irfan yace "taso zaku wuce" Mommy ce ta isa gabansa da sauri tana fadin "Please dan Allah ka sauya hukuncin nan kada ka rabani dashi kasan yadda nakeson yarana" daga mata hannu yayi, daga nan yawuce yabarta agurin, bayan sunfuto farfajiyar gidan , wani mutum ne yafuto daga wata ?atuwar jib baka, yakaraso har gaban Daddy, hannu yamikamai suka gaisa kana yace, "yallabai an gama komai dayaje school ze fara zuwa ma" "yawwa Nagode zaku iya tafiya yanzu" Daddy yafada yana kallon Irfan wanda gaba-daya yafuta hayyacinsa, inda Mommy take yanufa, ya riko hannayenta kana yace "Mommy kiyi hakuri laifi nane kiyi hauri" tuni hawaye yafara zuba a ida nuwanta ta rungume dan nata tana kuka tana fadin "no Irfan nasan ba laifin ka bane, abu daya zakai mun, kayi kokari kayi karatu kada ka kara aikata wani abun kuma" "namiki al?awari Mommy" daga haka yacika ta, yanufi gurin dan uwansa rabin jikinsa, ya tsaya yana kallonsa, shima Sawban din yana kallon dan uwan nasa, daga haka suka rungume juna, kowanne kwalla nafuta a idanuwansu, "nagode da shawarar da kake bani kuma inshaallah zan yi aiki da ita idan naje can, lokacin ba me bani shawara" "Irfan zanyi kewarka sosai, yanzu nadawo ni kadai bazamu dinga hira ba ko muyi fada" cikashi Irfan yayi yana goge hawaye, yace "amma dai zakai aure kafun nadawo kodan Mommy taji dadi" yafada yana nunashi "ah ah Irfan zan bari kadawo muyi tare" murmushi sukai atare kana suka kara rungume juna, "lokaci yayi fa" Daddy yafada yana kawar dakai, cikashi Irfan yayi, yanufa gurin Daddy, inda Daddyn yajuyar dakanshi gefe, "Daddy kayi hakuri ka yafemun nasan na bata maka rai, bansan natafi kanajin haushina, bazan iya jure natafi ba kana fushi dani, dan Allah Daddy ka yafemun, nama alkawarin zanyi karatu kuma zan sauya kodan kayi farin ciki" tausayin dan nasa ne yakamashi, yaji zuciyarsa ta karaya, tabbas shima zeyi kewar dan nasa, yayin daya daga ido ya kalli Sawban shi kadai, ji yayi zuciyarsa ta karaya, hakan yasa yayi saurin cewa "zaku iya tafiya" yana fadin haka ya juya yawuce ciki, mota mutumin yabudewa Irfan yashiga, kana shima yashiga, har motarsu tafuta daga harabar gidan Mommy da Sawban na tsaye, Irfan na hangosu, Sawban ya rike Mommy tana kuka, "Mommy mu koma ciki" Sawban yafada , ciki suka koma,
jinginar dakansa yayi jikin kujerar yana tunanin ya A'isha zataji, idan taga kwana biyu baya zuwa, shima yazeyi rayuwa batare da ita ba, ya ze zauna batare dayaji dumin jikintaba, ya zata daukeshi, zata dinga mai kallon mayaudari wanda ya lalata mata rayuwa ya gudu ya barta, zata mai kallon makaryaci nacewa yanasonta duk karyane, kiyayyarsa zata karu a zuciyarta, yaron dazata haifa shima ze tashi da kiyayyar mahaifinsa, kuma ze tashi da tsanar mahaifinsa, zece bayasonshi, ya cuci mahaifiyarsa, yaya zeyi ya wanke wannan kiyayyar daga zuciyarsu ko bayan yadawo, wannan tunane tuananen yadingayi cikin zuciyarsa, "ki yafemun A'isha inasonki ina tsananin kaunarki, ba wata mace dazan so bayan ke, ki yafemun" yakarashe maganar hawaye na zuba idanunsa,








=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

MRS (K D)
??

Romantic=??


Hot loved'?


Marubuciyar littafin
SOYAYYA DA IZZA
Ayanzuma nakara kawomuku wani sabon book
dina me suna (YAN BIYU NE)
ku biyoni domin kuji ya labarin ze kasance
karki bari abaki labari my sister

free page yakusa karewa=?/?=?/? kuyi maza ku fara biyan kudin ku=ذ?=ذ? kafin free page yakare=?
?=?
? ku hanzarta kubiya danjin cakwakwakiyar dazata faru nan gaba=??=??=??

ku biya ta wannan hanyar

=?G?=?G?=?G?

paid book 300
account number 9045749823
bank name Opay bank
shedar biya ta wannan number =?G?=?G?=?G?
09030849138 WhatsApp only
ko kuma katin waya ta wannan number
09045749823 Airtel
*************************************


DOMIN SHIGA GROUP NA YAN BIYU NE YA DANNA RUBUTUN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login