Showing 54001 words to 57000 words out of 71752 words

Chapter 19 - YAN BIYU NE BOOK COMPLETE BY MRS KD.doc

Mrs KD   

29 Sep 2025

1974

"Abba ina yini" hannunshi yakama, ya dawo dashi kan kujera kusa dashi kana ya dafa kafadarsa yace "lafiya lau Mu'azam ya matarka" "tana lafiya Abba tace na gaida ku" "ina jikokina kuma duk suna lafiya" "Abba suna lafiya" "Masha Allah duk da sunki zuwa ma" "Abba aikine yasa amma inshaallah zasuzo " "aikin me sukeyi kuma har garama Hassan amma Usaini ba abunda yake yi ai" "yanzu mutumin nawa ne me zamam banza" Hajja tafada "yo zaman banza mana" "ai Abba nabasu harkar kula da sauran kamfanoninmu dake Nigeria yanzu suna kula dasu" "ai gara tunda sunki aure, ga dan uwanka nan har yayi jikoki kai kana zaune" "wlh Abba bansan meye matsalar su ba basasan zancen aure" "ai barsu nakusa na nema musu mata cikin dangi" Hajja tafada tana dariya "ai Hajja abunda yakamata kenan" "kunyi waya kuwa da dan uwan naka" "eh Abba munyi waya haryake sanar dani asarar da akai a kasuwancinmu nacan Dubai" "ai dama shi kasuwanci ai haka yake watarana ka kirga riba watarana kuma ka kirga faduwa, Allah dai yamana jagora kukuma Allah yamuku albarka baki daya" ameen suka amsa duka "hajja nifa faten doya da waken nan naki nakeson ci yau" Daddy yafada "ah se inyima ai, haryanzu baka dena son shiba tun kana karami" "Hajja ba abinda nakejin dadinsa irin faten doya da wake" "Mu'azzam amma dai zakaje kaduba jikin mahaifin Sa'adatu duk da dai ma yaji sauki" "haka tace mun yaji sauki data zo" "du da haka kaje ka dubashi kafun ka koma" "to Abba inshallah" hira Abba da Daddy sukeyi, ita kuma hajja tamike tanufi kitchen, dakanta tashiga hadawa dan nata abinci,
NIGERIA

karfe 6:00pm A'isha tafara bude idanunta, ganinta tayi kwance kan gadon asibiti, hakan yasa tamike da sauri tana karewa dakin kallo, tuni kwakwalwar ta ta tuna mata da abunda yafaru da ita, saukowa tayi daga kan bed din, tabude kofa tafuce, kallonta kowa yake riga da wando ne jikin ta, se dan mayafi data yane kanta, hanyar futa ta nema daga asibitin, nurse din ce ta hangota hakan yasa tanufeta da sauri, tana fadin "ina zaki kuma" kallonta A'isha tayi kana tace "ina ruwan ki" "ke nutsu ni aka bawa alhakin kula dake" zuciyarta ce tafara raya mata kodai, yagano ta gudo ne shiyasa yasa abiyota da mota, se suka bugeta kuma suka kawo ta asibiti a kula da ita, katse mata tunani nurse din tayi dacewa, "kinga yarinya kifadamun inda gidanku yake sena kaiki" da sauri tace "gaida nake" "ok muje na kaiki" wani irin farin ciki ne ya lullubeta jin zata koma gida, futa sukai a tare suka samu napep suka fadamai inda ze kaisu, seda takaita har kofar gidansu kana ta kalleta tace "nan ne gidanku" "eh nan ne" "to zaki iya tafiya danni bazan shiga ba" "Nagode dakika kawo ni gida" "bakomai jeki" daga haka tafuta cikin zumudi da farin ciki, seda nurse din taga shigarta kana tace ma me adaidaitar su tafi, cikin gidan tashiga da gudu, dai-dai lokacin Inna karama tafuto daga bayi, dagudu ta isa gurinta , cikin mamaki Inna karama ke kallonta, tana tunanin kodai mafarki take, "A'isha kece ko mafarki nake" "Inna karama nice ba mafarki kike ba" "yaya3 zokiga A'isha ta dawo" aikam dagudu Inna babba tafuto daga dakinta "A'isha kece kika dawo garemu, Allah mun godema ka A'isha" gabadayan su farin cikinsu yakasa boyiwa, godiya ga Allah kawai sukeyi, guri suka samu suka zauna, A'isha tace "ina baffa" "sunje masallaci shida babanki" "baba yazo yana nan" "eh yazo" "dama zamu sake ganinki A'isha ina kika shige haka harmun fudda rai mun dauka kin mutu ma" su baffa ne da baba suka shigo gidan, tsayawa sukai turuss suna kallon A'isha, dagudu tamike tanufi gurin babanta ta rungume shi "A'isha tace ta dawo A'isha kece kika dawo" cikin zubar da hawayen dadi tace "baba nice na dawo" shima hawaye ne suka biyo kuncinsa, ya daga hannu sama yana fadin "Allah na gode maka daka dawomun da A'isha gida Allah na gode ma" "alhamdulillah3" abunda baffa ke fada kenan, gurin baffan tanufa ta rungume shi tana fadin "baffa nayi kewarku dayawa naji kamar bazan kara ganinku ba" "rahamar ubangiji bata karewa A'isha mun godewa Allah daya dawo mana dake" waya baba yadauka yashiga kiran su anty Zainab da kawu Salisu, aikam cikin murna suka ce gasunan zuwa,


se karfe 8:00pm Sawban yadawo a gajiye, hakan yasa yana dawowa yafada toilet yayi wanka, kana ya kwanta saman bed yana hutawa, dan yagaji sosai, wayarsa ce tadau ruri, yaduba yaga Abubakar ne ke kiransa, hakan yasa yadaga yana fadin "Abubakar ya akayi" "am yallabai dama kwana biyu bakazo office ba ga shi yan siyasa nata kawo kudi dan ai musu talla" "no Abubakar kada ka sake kuma kasanar da duk ma'aikatan kada wanda ya karyamun doka" "tom yallabai amma yakamata kazo office" "bana da time din zuwa office yanzu kaji da komai" "ok yallabai angama" daga haka yakashe wayar, idanuwansa ya lumshe yana tunanin halin yan siyasar mu na yanzu, da bazasuyi komai dan Allah ba,

abinci Inna babba take bata abaki, itakuma se wani shagwaba takeyi musu, kowa nata tarairayar ta kamar wata jaririya, "wai yar baba waye yayi kidnapping dinki ne" kawu Salisu yafada yana kallonta "kawu Salisu wani tsinanen mutum ne yasace ni" "ina yakaiki to kuma kinsan shi ne" baffa yamata tambayar "baffa wani gida yakaini kamar ma ba kasar nan ba, nataba ganinshi lokacin damuka dawo daga makaranta, har na tsokaneshi" "wato tsokanarsa kikai ko Allah yaso be yanke miki wuya ba" Inna karama tafada, "amma dai be miki komai ba ko" aunty Zainab ta tambaye ta "aunty wlh kullum se nace yabari se yaki" "bangane ba tabaki yake yi" Inna babba ta tambaye ta cikin kosawa tace "eh Inna" labarin yadda zamansu yakasance da Irfan tashiga basu, gaba daya jikinsu yayi sanyi salati kowanensu kawai yake yi "munshiga uku ya lalata mana yarinya baffa" "shikenan ya cucemu gashi tace ya gudu shi yasa itama ta gudo" shidai baffa takaici ne ya ishe shi yakasa magana, ita kanta A'isha jikinta yayi sanyi ganin yadda duk fara'arsu ta gushe, "Allah ya isar miki A'isha yaje shida Allah" baffa yafada, tun a daren mutanen unguwa suka fara shigowa suna musu murnar dawowar A'isha, har karfe 10:00pm mutane na shigowa, harda Abubakar, dayazo ne baffa yace mai yafada ma me gidansa anga yarinyarsu, ta dawo, ganin yadda yake dawainiya da abun, amsawa Abubakar yayi yace inshaallah gobe ze sanar dashi, A'isha kam har gajiya tayi da mutanen dake shigowa, kawayenta su Hadiza kuwa, dasuka shigo, inbanda tsalle da murna ba abunda suka dingayi a tsakar gidan har ita A'isha, abunda yadinga bawa kowa mamaki ganin A'isha tayi fess fatar ta takara nurjewa ga wata kiba datayi, hakan yasa kowa yazo yaganta seyayi gulmar ta, wasu har ca suke yi kodai yawan karuwancinta ta tafi basu duba yarintar ta ba,







=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

MRS (K D)
??

Romantic=??


Hot loved'?


Marubuciyar littafin
SOYAYYA DA IZZA
Ayanzuma nakara kawomuku wani sabon book
dina me suna (YAN BIYU NE)
ku biyoni domin kuji ya labarin ze kasance
karki bari abaki labari my sister

free page yakusa karewa=?/?=?/? kuyi maza ku fara biyan kudin ku=ذ?=ذ? kafin free page yakare=?
?=?
? ku hanzarta kubiya danjin cakwakwakiyar dazata faru nan gaba=??=??=??

ku biya ta wannan hanyar

=?G?=?G?=?G?

paid book 300
account number 9045749823
bank name Opay bank
shedar biya ta wannan number =?G?=?G?=?G?
09030849138 WhatsApp only
ko kuma katin waya ta wannan number
09045749823 Airtel
*************************************


DOMIN SHIGA GROUP NA YAN BIYU NE YA DANNA RUBUTUN KASAN NAN=?G?=?G?=?G?=?G?
https://chat.whatsapp.com/BcgtqAM3mDe4JRTJQzOoAF



DUK ME SON LITTAFIN YAN BIYU NE DAGA FARKO YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA=?G?=?G?=?G?=?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J




page 34


_________________________________________________________________________________________

______________Yauma Irfan kwana yayi yana sallar dare yana karatun Kur'ani, besamu bacci ba se bayan asuba, bacci me dad'i ya kwashe shi, tunda yagane idan yayi sallar dare da karatun Alqur'ani zuciyarsa nayin sanyi, hakan yasa kullum se yayi, da addu'ar Allah ya tsare mai A'isha da abunda ke cikinta, dan kullum soyayyar ta karuwa take azuciyarsa, musamman idan yana tuna mood din dasuka kasance tare, koda yaushe idan yana tunawa, feeling dinta ke takura mai, yaji bashi da wani buri illa yaji shi ajikinta, haka idan yatuna dadin dayake sha idan ya kusance ta, seyaji wutar kaunarta na kamashi, hakan yasa kullum bashi da aiki se tunaninta, tamkar wani zautacce, kewarta ce kawai ke da munsa tare da masifaffiyar soyayyar ta data riga tashiga jininsa, kuma bayajin ze dena sonta ko bayan ransa, bayajin zeyi rayuwa da wata mace ko bayan ba ranta,

dasafe Sawban daya fito, ya tarar da Mommy na zaune a falour, hakan yasa yamatsa kusa da ita ya zauna, yakamo hannayen ta yace "Mommy na ina kwana" "lafiya lau Sawban katashi kalau" "Lafiya lau Mommy kamar kina cikin damuwa" "kwarai kuwa, ina tunanin yakamata kayi aure Sawban nasamu me debemun kewa idan bakwa nan" tausayi Mommy din tabashi yace "kiyi hakuri Mommy lokacin auren nawa beyi ba" "Sawban bakasan kaga kaima ka haifi yara ne, ni inason ganin jikoki na sun cikamun gida, ku kadai Allah yabani, kuma dakyar nasameku, shi yasa nakeson ganin ya'yan ku nima" hannunta yakama yace, "Mommy ki kwantar da hankalinki zanyi kidena sa damuwa aranki Please" gurgiza mai kai tayi, kawai , dantasan bayin zeba kawai dai yafada ne danya kwantar mata da hankali, daya daga cikin masu girki ce tazo ta sanar dasu, breakfast ya kammala, hakan yasa suka mike suka nufi dining din, serving dinsu tayi kana tabar gurin, bayan sun gama ci, Sawban yayiwa Mommy sallama yafuce, kamfaninsu yanufa, beje gidan rediyon sa ba ko talabijin dinsa, kawai yawuce sauran kamfaninsu dan ya tabbatar komai na tafiya dai-dai


" Aisha karkije gidan mutane da safen nan" "kai Inna karama dan Allah kibarni naje" "wlh ko zakije se anjima" "A'isha kibari anjima se kije ko" Inna babba tafada cikin sigar rarrashi, "to naji zan bari se anjima" koko da kosan da Inna karama keyi Inna babba tazuba ma A'isha, ci tafara tana fadin "gaskiya nayi kewar koko da kosai" murmushi kawai su Inna sukai mata, kana takara cewa "nifa Inna kunsan saboda me nakeson zuwa gidan su Hadiza" "saboda dame" "saboda inje na tambayeta dawa dawa ye sukai gulmata da bana nan kuma suwa sukai mun Allah yakara" "kai A'isha haryanzu bazaki fasa neman rigima ba ko" "Inna babba ai nasan yan unguwar nan ba sona suke ba, kuma nasan Hadiza zata fadamun koma waye" "ai ita tayi hankali ba kamar ke ba" "tab Hadiza ce tayi hankali, tsaya kiga yanzu ina zuwa zata fara bani labarin abunda yafaru da bananan, kuma wlh duk wanda naji yayi munafurci na Alkur'ani sena durje bakinsa koma waye" "to yar masifa bama inda zaki muga ta tsiya" baffa yafada lokacin dayake futowa daga dakinshi, tura baki gaba tayi tace "kai baffa dan Allah yaushe rabona dana gansu zanje ne fa mu gaisa" tafada tana zumbura baki "komadai menene ba inda zaki" ture abincin tayi tana fadin "ni nama koshi bazan ci ba" "karki ci din, kukawomun nawa karin maza" baffa yafada yana kallon su Inna, jitai cikinta yadan murda, hakan yasa ta tunawa tayi da maganar cikin jikinta, hakan yasa da sauri ta kalli su Inna tana fadin "la baffa inafa da ciki" koko da kosan da Inna karama ta dauko zata kaiwa baffa, ya fadi kasa tajuyan tana kallon A'isha, "ciki kuma A'isha" Inna babba tafada idonta kan A'isha da tayi tsuru tsuru tana kallonsu, gabaday nufota sukai, baffa yace "waya fada miki kinada ciki" "baffa nurse Maryam ce, kuma shima yafadamun" "munshiga uku ya sabautamana yarinya ciki fa" "kunga duk ba wannan ba, ke tashi mutafi asibiti a bincika agani" baffa yafada yana kallon A'isha, baba ne yashigo gidan, da sallama, "baffa kajini shiru ko, wlh bako nayi se yanzu yatafi" ganin sunyi jugum jugum yasa baba fadin "Inna lafiya kuwa" "Umaru baya ta haihu" "kamar ya kenan baffa" "wai A'isha nada ciki" "ciki" baba yafada yana zaro idanu, gaba daya jikinta yayi sanyi, datasan zasu shiga firgici haka da bazata faWa musu ba, "to yanzu ya za'ayi da cikin" "ni canai tazo muje asibiti kawai a bincika" "eh hakan ma yayi ke A'isha tashi muje" shigatayi tadauko hijabinta tazo suka tafi asibitin

AMERICA
tahowa sukai su uku, zasu shiga class, dan yau basuyj lecture ba se 2:0pm, hakan yasa basu futo ba se yanzu, danshi Irfan bacci ma ya hauyi, dan dama yanzu baya bacci da daddare, sedai yayi ta salla yana addu'a, dan Abdullah yafada mai, lokacin yakamata ya dage ya tashi tsakar dare yadinga nafila yana kai kukansa gurin Allah, yadena zama wani tunani, hakan yasa kullum baya runtsawa se anyi asuba, hakan dayakeyi bakaramun kwantar mai da hankali yakeyi ba, yaji cewa aransa A'ishan sa tana lafiya, tare da babyn sa, kullum daya zauna shida Abdullah bayamai zancen kowa sena A'isha, yayi ta gayamai hakayenta, shagwabarta, da tsiwar datake yimai, da rigimarta, danta iya rigima, shikam Abdullah yayi ta dariya, yana tayashi da addu'ar, Allah mallaka mai ita su rayu tare rayuwa ta har abada, hakan yasa yake kara son Abdullah, yakeson kasancewa dashi, saboda yanason A'isha,

NIGERIA
bayan sunje asibitin suka zaune layin da ake test din ciki, wani makocin su baffa ne ya ganosu, yanufo inda suke, dama anyi mai shedar gulma, hannu yamikawa baffa yana fadin "ah malam Yusufu barka" "yawwa barka ya gida malam kalla" ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????"lafiya lau, asibiti kukazo ne" "eh wlh malam kalla" "to Allah yakara sauki, A'isha asibiti akazo" A'isha kam kauda kai tayi, ganin ba wanda yakara magana yasa yabar gurin, seda yayi gaba, yaga wata nurse yake tambayar ta "yata dan Allah can layin menene" "lafiya dai ko malam" "lafiya lau yarinya kawaidai tambaya nake" "oh layin yan test din ciki ne" "ciki fa" "eh mana da matsala ne" "ah babu Nagode" daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login