Showing 66001 words to 69000 words out of 71752 words

Chapter 23 - YAN BIYU NE BOOK COMPLETE BY MRS KD.doc

Mrs KD   

29 Sep 2025

1971

hakan ya gagara, shiyasa na yanke shawarar aurar da ita, na rabata da karatunta, to auren ma gashi an lalata shi" "baffa ka kwantar da hankalinka Allah ze kawo mata mafuta" Sawban yafada, "waye ze aureta, koda ma mutum yanace ze aureta, to da iyayen sa sunyi bincike za a fadamasu karya nan, kuma ba iyayen da zasu yadda dansu ya aure ta ba" baba yakarashe maganar yanajin zafi a zuciyarsa, "ni badan zamn A'isha da matata bazeyiwuba da baffa ni zan aureta" Abubakar yafada "ai Abubakar hakan bazeyiwuba" shiru Sawban yayi zuciyarsa na rayamasa yace ze aureta kawai, to amma me zecewa dasu Daddy da Mommy, 'Sawban ka aureta kawai kaga dama Mommy ta matsa ma kayi aure, kaga seka aureta ka Kaita gurin Mommy, seka sata school, kaga base kun zauna matsayin mata da miji ba, sekayiwa Mommy wayo kace karatu take tukun' zuciyarsa ke masa maganganun nan, "yallabai yakamata kawuce dare yanayi" maganar Abubakar ce tadawo dashi tunanin dayake, "baffa idan ka amince nizan aureta" kallonsa dukka sukayi cike da mamaki, "eh idan kun amince nizan aureta, a yau dinan" "ah ah yaro baka dace da A'isha ba" "ah ah baffa tunda ninace zan aureta to zan aureta" "mu gode Allah yasaka maka da gidan aljanna ya rabaka da iyayenka lafiya" baba yafada har yana kukan murna, hannunsa Sawban yakama yana fadin "kadena kuka baba namuku alkawarin zankula da ita" "bani da bakin dazanma godiya yaro kasharemun hawaye na lokacin dayake kokarin zuba Nagode" "dan Allah baffa kudenamun godiyar nan kuna sani inajin wani iri" "to me muke jira a daura auren mana" haka aka daura aure baffa yazama waliyin Sawban shikuma kawu Salisu yazama waliyin A'isha, aka daura aure akan sadaki Naira dubu hamsin, godiya suka dinga yima Sawban har seda yagaji, baffa ne yace mai gobe yazo yadauketa, yace to, daganan ze sanar da iyayensa yayi aure, har bakin mota suka rakashi yashiga yatafi, sukuma suka shige gida







=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

MRS (K D)
??

Romantic=??


Hot loved'?


Marubuciyar littafin
SOYAYYA DA IZZA
Ayanzuma nakara kawomuku wani sabon book
dina me suna (YAN BIYU NE)
ku biyoni domin kuji ya labarin ze kasance
karki bari abaki labari my sister

free page yakusa karewa=?/?=?/? kuyi maza ku fara biyan kudin ku=ذ?=ذ? kafin free page yakare=?
?=?
? ku hanzarta kubiya danjin cakwakwakiyar dazata faru nan gaba=??=??=??

ku biya ta wannan hanyar

=?G?=?G?=?G?

paid book 300
account number 9045749823
bank name Opay bank
shedar biya ta wannan number =?G?=?G?=?G?
09030849138 WhatsApp only
ko kuma katin waya ta wannan number
09045749823 Airtel
*************************************


DOMIN SHIGA GROUP NA YAN BIYU NE YA DANNA RUBUTUN KASAN NAN=?G?=?G?=?G?=?G?
https://chat.whatsapp.com/BcgtqAM3mDe4JRTJQzOoAF



DUK ME SON LITTAFIN YAN BIYU NE DAGA FARKO YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA=?G?=?G?=?G?=?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J




page 38

LAST FREE PAGE
_________________________________________________________________________________________

______________Tunda yakoma gida, yashige part dinsa, yayi wanka, ya zauna, yana tunanin taya ze sanarwa dasu Mommy yayi aure, karar bell taji hakan yasa yamike taje ta bude kofar, "yallabai madam tana son ganinka" tafada cikin harshen turanci kanta a duke, kadamata kai kawai yayi, alamar yaji, daga haka itakuma tafuce, komawa ciki yayi, yadau wayarsa, kana yafuce, yana shiga ya tadda ita a folour a zaune, karasawa yayi yana zama gefenta, kallonshi tayi tace "ashe kadawo" "eh Mommy nadawo" "bakai dinner bafa, ko bakajin yunwa ne" "eh Mommy banajin yunwa" "to shikenan" 'Sawban kafadawa Mommy andaura ma aure' 'ah ah Sawban kabari idan kazo da yarinyar seka mata bayani' kowanne bangare na zuciyarsa da abunda yake saka mai, 'anya banyi kuskuren auren nan ba' yafada cikin zuciyarsa, "Sawban bara nashiga ciki inason na kwanta dawuri nagaji" "tom Mommy seda safe" daga haka tawuce, shima mikewa yayi shima yafuce,

"malam anya kuwa bakai hanzarin bawa yaronnan auren A'isha ba" "to dai yanzu koma mene aikin gama ya gama tunda tazama matarsa" kawu Salisu yafada, "bakusanshi ba bakusan waye mahaifinsa ba bakusan meye sana'ar sa ba wato idan ma dan yankai kaine kun riga kun daura mata aure dashi" Inna babba tafada cikin fada "Inna nifa a ganina yaron nan yaron kirki ne, saboda yanayinsa ma ya nuna, kuma ai ga Abubakar yasanshi, kuma yason gurin aikinsa" baba yafada "to nima abunda nagani kenan nifa na yadda da yaron nan, kawai ku kwantar da hankalin ku Inna kumata fatan alheri" kawu Salisu yayi maganar, "nidai mun riga mungama magana, kuma gobe zezo yadau matarsa" "to ai shikenan Allah yakare ta" ameen suka amsa su duka,


wayar aunty zainab ce tahau kara, datake hannun A'isha tana game, "A'isha kamar ringing din wayata nakeji ko" aunty Zainab tayi maganar datake cikin kitchen "eh aunty Zainab gashi" tafada tana mikamata wayar, kana tashige falour inda yaran aunty Zainab suke suna kallo, wayar tadauka ganin baban A'isha ke kiranta, bayan tadauka yafada mata komai daya faru, kana yace, gobe tadawo da A'isha mijinta ze tafi da ita, aunty Zainab tayi mamkin abun, amma kawai tace to, seda sukai sallama, takashe wayar, tazuba masu abinci, kana tashiga falourn itama, abinci ta ajiye masu, kana tabawa A'isha nata "aunty Zainab nidai nida su Ikram zaki hada mana" "kai A'isha rigimarki tana da yawa, to kuci dasu" "yawwa Ikram kutawo nan muci" matsowa su Ikram sukayi, suka faracin abincin, ita dai aunty Zainab tama kasa kai abincin bakinta, kallon A'isha kawai take tana tunanin ya zatayi idan taji andaura mata aure,

AMERICA
fotowa yayi daga wanka daure da tawul, "ina Jay ne ko be dawo ba" "ai sedai mu hadu dashi a class" "nifa har na matsu nagama wannan school din nkoma Nigeria" "Irfan ace dai ka koma ka tarar A'isha tayi aure" juyowa yayi da sauri yana kallon Abdullah, "kadena maganar nan dan Allah karkasa zuciyata ta buga" "tab lallaima wato zuciyar ka zata buga, idan kuwa hakan ya tabbata ai sedai ka mutu" "kai Abdullah asama tayi auren wlh kowa ta aura seya saketa, dan A'isha tawace ni kadai" "lallaima idan kuma yana sonta fa kuma itama tana sonshi seka rabasu" "ai wlh kozan karar da gaba daya dukiya ta seta dawo gareni" "kaidai Allah yadorama ciwo me wuyar warkewa" "kaga kabar maganar nan ma katashi kashirya muwuce class" mikewa Abdullah yayi yashiga toilet dan yayi wanka, shikuma yaci gaba da shiryawa, yana jinjina maganar Abdullah cikin zuciyarsa,

NIGERIA
karfe 2:00pm aunty Zainab tace Aisha tashirya zasu koma gidan baffa, ba'ason ranta ba A'isha tashirya, bayan sun gama komai suka tafi, har yaran aunty Zainab, bayan sun isa rai a bace A'isha tashiga gidan, su Inna kam suna ganinta haka suka ki kulata, saboda sunsan rigimarta, zama aunty Zainab tayi suka fara gaisawa, "ke kuma bazaki gaida mu ba ko" zumbura baki tayi tace "to meyasa kukace adawo dani" "au dalilin dayasa kike fushi kenan" "ai ko fushi bama ki faraba, se anzo tafiya dake" saurin kallon Inna karama tayi tace "ina zamuje" "inadai zakije" "gidan miji mana" "wlh nidai kam ba inda zani, ai nafadawa baffa banaso yanace" "A'isha ai dole ne duk muma baki ga a gidan mazajenmu muke ba" aunty Zainab tafada da sigar rarrashi, "nidai kam ba inda zani wlh" "seki bari idan iyayen naki sunzo ke fadamasu ba inda zaki" su baffa ne baba suka shigo, gaishe dasu aunty Zainab tayi suka amsa, mikewa A'isha tayi tanufi gurin babanta tana fadin "baba kafadamasu nidai banason wani aure" kumatunta yakama yace "ki kwantar da hankalinki ba dadewa zakiyi acan ba, nida kaina zanzo na dauke ki kinji yar baba" "to baba amma" "kinga yar baba kwantar da hankalinki kinji" "tom" kawai tafada, kallon baffa baba yayi yace "baffa inason yanzu naje gida zan dan bincika naga kozan samu bayani game da mahaifiyar A'isha, dan gobe nakeso nakoma bakin aiki na" "gaskiya kam hakan yakamata bara na daukoma makullin katafi" daga haka baffa yashige dakinsu, "baba ina zakaje nima zan bika" "ah ah yar baba zanje gida ne yanzu zan dawo" komawa tayi ta zauna jikin Inna babba, "se shegen son yawon tsiya ance zaki tafi gidan miji kintsaya kina bata rai" Inna karama tafada, "nifa Inna ba inda zani ato" "ni wlh ina tausayin yaron daya aureta, dan wlh seta samai ciwon kai, dan wawwatarta ta yar fari tanan" "Inna ai zatayi hankali bazata dinga fitina ba" "wannan din Allah yasa tayi" ita dai A'isha sai zumbura baki take tana hade rai, "gashi kaje kayi maza ka dawo kafun yaronnan yazo daukanta kuyi sallama" "to baffa inshallah" daga haka baba yafuce,

motarsa baba ya hau yanufi gidansa, da tun rasuwar A'isha be kara ko kallon hanyar gidan ba, a kofar gidan yayi parking, kana yafuto, seda yakarewa gidan kallo, yana tuna ranar dasuka fara kasancewa shida mahaifiyar A'isha a gidan, da wannan tunanin ya karasa yasa makullin ya bude kofar, yashiga, komai na gidan yayi kura sosai ga yana, da haka dai ya shiga, dakin, kallon dakin yake, yana tunanin matarsa, yana ganinta cikin idanunsa, zaune kan gadon tana mai murmushi, besan sanda hawaye suka gangaro fuskarsa ba, yasa hannu ya share, yana faWin "Allah yajikanki A'isha Allah yakai rahama kabarinki" yakarashe maganar hawaye na kara zuba a idanunsa, drowarta yanufa ya bude, har yanzu tana yadda take, futo da kayan ciki yafara, yana duddubawa, seda yafuto da komai, amma bega komai ba, hakan yasa yamayar da kayan, yashiga bude sauran durowoyin yana dubawa, shima ba komai, haka yadinga dubawa, kusan awa biyu amma bega komai ba, "shikenan tunda bansamu wata makama ba na neman danginki, zan binka kawai akan abinda nasani, zanje Niger din kawai, nayita tambayar gidansu A'isha, kozan shekara, gwara na sauke nauyin da ke kaina, kar aikai matakin da A'isha zata tambayi dan mahaifiyar ta da kanta" yayi maganar cike da damuwa, zama yayi gefen gadon, yana tunanin ta ina ze fara tafiya Niger batare dayason ina yanufa ba, wata takarda ya hango karkashin gadon, hakan yasa sunkuya yadauko, ya karkade kuarar dake jiki, ya bude, rubutu ne kamar haka

mijina ina fata zaka samu karanta wannan takardar ko bayan bana raye, dan ni ayanzu inajin bazan iya rayuwa ba, koda na haifi abinda ke ciki na, inajin lokaci na yayi, shiyasa na rubuta maka wannan takardar, dan kar na tafi da hakkin abunda zan haifa dama kai, na boye muku asalin wacece ni, ina fata idan nabaka labari na, zakayi kokari ka nemo dangina, za kai abunda na haifa gurin mahaifina yaganshi, nason zeyi murna duk da ni bana raya, mahifiyata ma nason zatayi matukar farin ciki idan taga, jikanta.
Alhaji Isyaku me dala, sananne ne kowa yasanshi, mahaifiyata, kuma Hajiya bilkisu, inada yayye guda biyu, yaya Mu'azzam dakuma yaya Abdullahi, mu yan asalin kasar Niger ne, muna zaune a babban burnin ?asar wato niemay, mun tashi cikin so da kulawa, dan duk abunda muka bukata muna samu, saboda mahifinmu nada matu?ar kudi, nice yar auta agurin mahifiyata, kuma mahifina yasamun sunan mahaifiyasa, shiyasa gaba daya gudanmu anaji dani,
sanadiyyar barina gida ya ta'allaka ne da harin da aka kawo wa mahaifina, mahaifina Alhaji Isyaku me dala, yana da tarin makiya da wadanda muka sani dama wadanda suka bani mamaki, ranar Friday ranar da bazamu taba bantawa ba, a hanyar dawowar mahaifinmu gida, yaje banki ya karbo kudadensa daze sai wata masana'anta a kasar Niger, a hanya yan fashi suka tare shi, ranar se akayi rashin sa'a yace ma da bodyguard dinsa baya bukatar su bishi, hakan yasa yan fashin suka samu dama, suka karbi kudin hannunsa, dasunka kimanin biliyan arba'in, kuma suka harbeshi a kirji, da alama turowa akai su kasheshi, a lokacin kwamishinan yan sandar kasar Niger yazo wucewa takan titin, sunajin jiniya suka gudu, shikuma lokacin yaji karar harbi, hakan yasa suka duba, suna dubawa suka ganshi, suka daukeshi suka kaishi asibiti, muna zaune aka kira mahaifiyar mu a waya aka fadamata, hankalinta yatashi sosai hakama namu nida yayye na, muka dunguma muka tafi asibitin, anan ne muka tarar da anshiga dashi za ayi mai aiki acire mai bullet din, bayan an anyimai aiki, kwamishinan yan sanda suka fara bincike, amma sam basu samu wani makama ba, hakan yasa mahaifina yace su bar binciken kawai, bayan ya warke yadawo gida, kaninsa Alhaji Nasiru yashiga damuwa matuka, saboda shi kadai ne dan uwansa, daya rage, ranar Litinin na shirya tsaf danna wuce gurin aiki, saboda ina aiki a daya daga cikin kamfanin mahaifinmu, kuma nice babba a kamfanin, lokacin dana isa office dina, na tarar da file dayawa saman table dina, dayake na kwana biyu banje office dinba, ganinsu dayawa, yasa dauki rabi, tafuta danna kaiwa uncle Nasiru office dinsa, ya ragemun su, dayake shima nan yake aiki, ina zuwa bakin kofar office dinsa, naganosa dashi da mutane, har na juya sena tsaya jin an ambaci sunan mahaifina cikin maganar, "ai naso kun kasheshi ma, danni iya wannan kudin baze ishe ni ba, yaya Isyaku nada dukiyar da bazata taba karewa ba, kuma nima inason na mallaketa, amma sam yaki bani dama, sedai yayita Wora yaransa kan harkar komai ni ina gani, danayi magana seyace sena sauya halina" lokacin daanji abunda uncle Nasiru yake fada na girgiza sosai dan ban taba tunanin ze iya sawa akashe mahaifinmu ba akan dukiya, hakan yasa naciro wayata nafara video, "ai oga kabamu dama mukara kaimai wani attacking din, wancanma yan sanda ne suka iso shiyasa" "to kushirya ranar laraba zeje meeting a hanyarsa ta tadawowa ku kaimai hari, zance zan rakashi base ya tafi da bodyguard ba" "shikenan angama oga" "yallabai madam aisha na dauka" aikam ganin sun ganni yasa nayi maza nafuce kada suce zasu karbi wayar, "dakata karka bita, nason yanzu zatayi sauri ta tafi gida danta nunawa yaya Isyaku video data dauka, saboda haka ku tareta a hanya ku kada kumata kamai ku dauketa kukaita gidan gonta" "angama yallabai" nikam ina futa motata nashige na nufi hayar gida jikina har yana bari, a hanya mutanen uncle Nasiru suka tareni, suka samun bindiga, inaji ina gani suka tafi dani wani gida, ba jimawa bayan sun kaini sun kulle ni a wani daki, uncle Nasiru yazo, banyi mamkin ganinsa ba saboda dama nasan baze taba barinaba, "yarinya wato zakije ki tonamun asiri ko, kuma aganinki sena barki" "haba uncle meyasa zamayiwa Abba haka be cancanci haka ba" "yaro man kaza, ni badamu da dashi ba, kamar yadda nadamu da kudi, dan haka ke kuma zaki tazama anan har lokacin dazansa a kasheki" "uncle nagodewa Allah da ba Abba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login