Showing 51001 words to 54000 words out of 71752 words

Chapter 18 - YAN BIYU NE BOOK COMPLETE BY MRS KD.doc

Mrs KD   

29 Sep 2025

1975

shi, kallon shi Abdullah yayi yace "jiya fa ba kaci komai ba ka kwanta" "banason cin komai nifa yanzu" "Irfan karfa tunanin yarinyar nan yasa ka illata kanka fa" bece komai ba yadau tea din da aka kawo mai yafara sha, bayan sun gama suka nufi class, har an fara lecture, shiru ajin se karar A.C zama sukai, cikin class din,

yanatashi sallar asuba yayo alwala yafuce masallaci, acan ya tarar da Daddy, gaishe shi, yayi ya amsa, bayan an idar da salla, Daddy ya daga hannu yana ta addu'a, a zuciyarsa, addu'ar Allah yashirya mai Irfan kawai yake ya tsare mai shi acan, yakara shirya dukan zuri'arsa, seda Sawban yajira Daddy yagama addu'a kana suka taho tare, kallon Sawban Daddy yayi yana fadin "Sawban hankalina yaki kwanciya tunda Irfan yatafi, rashin ganinsa atare da mu nima yadameni" "Daddy ka kwantar da hankalinka inshaallah zakai alfahari da Irfan" "ina fatan hakan Sawban banason ganin dana ya lalace" "bakomai Daddy Allah na tare damu baki daya kuma addu'ar dakake mana bazata fadi banza ba" "Allah yamuku albarka baki daya" "ameen" Sawban yafada, part dinsa Daddy yashige, shima Sawban yashige, Sawban yana shiga yadau azkar yayi, bayan yagama ya fada toilet yayo wanka, bayan yafuto, yazo ya shirya tsaf cikin suite baka, dan yau zeje daya daga cikin kamfanin su zasuyi meeting da ma'aikatan, be futo ba se karfe 9:00am yafuto yanufi part din Mommy, bakowa se yan aiki dake shirya breakfast kan dining, gaisheshi sukai ya amsa, kana ya nemi guri ya zauna, ya bude laptop dinsa, yana kara duba baya nai kan kamfanunuwan da Daddy yabashi yaja ragamar su, dan akalla zasuyi goma, na iya Nigeria, yana nan zaune har agogon da ke falourn yabufa karfe 10:0am, hakan yasa yamike yanufi dining, serving dinsa me aikin tayi, kana yafara ci, ba jimawa Mommy tafuto, dining din ta zauna, Sawban yace "Mommy good morning" "lafiya" abunda tafada kenan, me serving dinsu ce ta matso zata zubawa Mommy breakfast, ta dakatar da ita, Sawban ne yakalle ta yace "Please Mommy ki cire damuwa a ranki rabonki da abinci tun jiya fa" "banajin yunwa ne" tafada lokacin da Daddy yafuto, zama shima yayi akai serving dinsa, kana yafaraci kallon Mommy yayi yace "yabakya ci" "taya za' ai naci abinci bansan halin da d'ana yake ciki ba" numfasawa yayi kana yakama hannunta yace "d'anmu yana lafiya" "toya zan tabbatar da hakan bayan ba waya a hannunsa ballantana naji yaya yake" "karki damu zanbashi waya a hannunsa" "to inason jin muryarsa yanzu" "yanzu ance yashiga class se sun futo kici abincin kafun su futo" shiru tayi batace komai ba, Sawban yace "Mommy please dan Allah kici nima nafuson naga kinci abinci kafun na futa" "to shikenan naji zanci" daga haka tafara cin abincin, seda Sawban yaga tanaci kana ya mike don ya wuce, "Daddy zan wuce" "ok seka dawo nima me bi yau zanje Niger gurinsu Abba amma inaga 2 days zanyi kawai" "to daddy Allah ya tsare, ka gaidamun shi sosai da kuma yar tsohuwa" "lallaima yaron nan uwar tawa ce yar tsohuwa" "sorry Daddy namanta ba ita ba" daga haka yafuce,

bayan ta kammala shiryawa, tafuto, ta tsaya gaban mirror tana kallon kibar da tayi, turo kofar akai, Joseph ne yakaraso ya ajiye ledojin ya kama hanya ze fuce, tayi saurin fadin "dakata" juyowa yayi yana kallonta, kana tace "kaje ka sanar dashi yau dinan yazo maida ni gidanmu, dan wlh bazan kara kwana gidannan ba" shiru Joseph yayi yana kallonta takara cewa "nasan karya yake ba inda yaje, tunda dama yasaba karya, komadai meye ni yazo yamaida ni gidanmu kawai" "yimun shuru angaya miki oga yatafi America" yafada cikin gurbatacciyar hausarsa, tsaki taja kana tace "ai kaima munafuki ne, yariga yace ma karka fada ai, to wlh bazan kara kwana gidannan ba" takaici ne ya isheshi ya bude kofa yafuce, "oho kaika sani danni ko abincinma bazan ci ba wlh yau sena bar gidannan"

Safiyya ce tafuto cikin abaya ashh colour, kallon kawarta Amal tayi wacca kum cousine dinta ce, "tashi muwuce kinga 12;00pm tayi" "to ai dama nike nake jira" "ok bara nacewa Mama muntafi" daga haka tawuce bedroom din Mama, tana shiga tadda ta tana shirya kaya a akwati, "kai Mama harkin fara shirya kayan tafiya bikin" "toke zanjira" "Mama yanzu fa zama mutafi karbo dinkin" "toki sauri dan kinsan 2:30pm nidai zan wuce" "to Mama yanzu ma kuwa" daga haka ta fuce, key din motarta ta dauka tana fadin "Amal muje ko" daga haka suka fuce, a hanya Amal ke tambayar Safiyya Sawban, "yananan kuma inanan ina cigaba da turamai letter, jiya da daddare ma na tura mai message" "nifa gani nake mutuminan baze karbi soyayyar ki ba fa" "kinga Amal karki karyarmun da gwuiwa" "to ai shikenan seki ta fama"

AMERICA
basu futo lecture ba se 4:30, hakan yasa daga nan kawai suka wuce cin abinci, daya daga cikin bodyguard din Irfan ne, yakaraso yana mikawa Irfan waya kirar iPhone, "yallabai gashi inji me gida yace abaka" yana fadin haka yagane Daddy yake nufi, karba yayi kawai, kana yamai alamar yabar gurin, Jay ne yakaraso inda suke yana fadin "hy guys" kallonsa sukai Abdullah yace "yaushe kuma kadawo" "najema lecture mafa" wayar da aka kawowa Irfan ce ta dau ruri, hakan yasa yadauka yana karawa a kunnensa, "Irfan Daddy dinka ne" "oh Daddy ina wuni" "lafiya lau kana lafiya dai ko" "ina lafiya Daddy" "ok yayi kyau ga Mommy dinka tanason jinka" "ok bata" karba Mommy tayi tana fadin "my son kana lafiya" "Mommy karki damu ina lafiya" "yawwa hakan nakeso se yanzu hankali na ya kwanta" "Mommy dan Allah karki sawa kanki damuwa ina lafiya" "ok Irfan dan Allah ka kula kasan dawa zaka zauna" "ai Mommy nasamu abokai nagari karki damu" "ok to Allah yama albarka" "ameen" daga haka sukai sallama, kallonshi kawai su Jay suke dan basusan me yake cewa ba, dayake da hausa yake maganar, bayan ya gama yakallesu, yace "iyaye nane" "ohh yau dai kadan ji dad'i tunda kaji muryar Mommy dinka" murmushi kawai yayi kana yafara cin abincin

NIGERIA
bayan ta idar da sallar azahar, lokacin 2:00pm har tayi, ganin shiru Joseph bezo ba, kuma dai-dai lokacin yake kawo mata abincin rana hakan yasa tamike, tabude kofar tafuce, kallon ko ina take, kana tahau liftar da zata saukar da ita kasa, dayake lokacin da Irfan yana nan suna fita garden, seda ta sauka falourn kasa, kana tanufi babbar kofa da zata sadata da farfajiyar gidan, tsayawa tayi tana tunanin pin din kofar, tajima tana safa da marwa a gurin dan batason numbobin dazata danna kofar ta bude ba, wani abune yafado mata ta tuna lokacin dazasu garden, yazo sa numbobin, yaki sakuwa, itakuma ta dinga cewa yayi sauri, "na tuna lokacin naga numbobin, guda shida ne to amma ai na manta" tafada a fili, matsawa tayi tashiga dannawa tasa, 456789 yasamata rock password, jim tayi ta tsaya tama rasa me zatayi, durowoyin falourn tashiga budawa tana duba takardun dake ciki, dayake ta iya karatun itama, kawai dai lokacin bata nutsuwa ne idan anayi kuma se taga dama take zuwa, seda tafuto da takardun falourn tas amma bataga wata alama ba, gefe takoma ta tsaya ta yanke shawarar komawa kawai, wata karamar drower ta hango gefen tv hakan yasa tanufi gurin, ta janyo, wani book ne me dauke da hotonshi ajiki, hoton ta karewa kallo kana tace "kamar na Allah" kana tabude book din, numbobi tagani, kowanne numbobi guda 6 ne, haka tashiga saka numbobin, duk wacca tasa se kofar tasa mata ronck password, se a na karshe, data sa, aikam kofar ta bude, wani tsalle ta daka, ta cillar da book din, ta fuce, bodyguard din ta hango, daga can nesa, seta ratsa ta jikin motocin gidan tanufi gate, tayi sa'a kuwa a bude yake, hakan yasa tabude tafuce da gudu, tunda tafara gudu, bata tsaya ba seda taga tayi nisa da gidan sosai, titin ba kowa se motoci dake wucewa tsilla tsilla, hakan yasa taci gaba da tafiya,





=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

MRS (K D)
??

Romantic=??


Hot loved'?


Marubuciyar littafin
SOYAYYA DA IZZA
Ayanzuma nakara kawomuku wani sabon book
dina me suna (YAN BIYU NE)
ku biyoni domin kuji ya labarin ze kasance
karki bari abaki labari my sister

free page yakusa karewa=?/?=?/? kuyi maza ku fara biyan kudin ku=ذ?=ذ? kafin free page yakare=?
?=?
? ku hanzarta kubiya danjin cakwakwakiyar dazata faru nan gaba=??=??=??

ku biya ta wannan hanyar

=?G?=?G?=?G?

paid book 300
account number 9045749823
bank name Opay bank
shedar biya ta wannan number =?G?=?G?=?G?
09030849138 WhatsApp only
ko kuma katin waya ta wannan number
09045749823 Airtel
*************************************


DOMIN SHIGA GROUP NA YAN BIYU NE YA DANNA RUBUTUN KASAN NAN=?G?=?G?=?G?=?G?
https://chat.whatsapp.com/BcgtqAM3mDe4JRTJQzOoAF



DUK ME SON LITTAFIN YAN BIYU NE DAGA FARKO YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA=?G?=?G?=?G?=?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J




page 33


_________________________________________________________________________________________

______________"Safiyya zanyi tafiyata fa" "Mama ganinan fa" tafada tana futowa daga cikin falourn, "kedai indai za ai tafiya dake sekin batawa mutum lokaci" "kai Mama Amal nace tasamun power bank dina a jaka bata samunba" "sannu ke bazaki sakaba" "toya isheni kumuje" daga haka suka shiga motar, Safiyya ce tayi driving dinsu, waka tasa, cikin speaker din motar tana bi, Mama tace "Safiyya kashemun wakar nan" "Please Mama dan Allah kibarmu muji ko kadan ne" "matsalar tafiya daku kenan" ita dai Safiyya bata kara magana ba taci gaba da driving dinta,

tagaji sosai, saboda tayi tafiya me nisa, ga tafarajin kishirwa na damunta, hango wani restaurant tayi can gefen titi, hakan yasa tace bara ta tsallaka ko zata samu ruwa, hakan yasa ta nufi titin, horn taji an danna mata da karfi, kafun tajuya taga motar, seji tayi anyi sama da ita,
"Safiyya kin bige mutum fa" "nashiga uku Mama banganta ba" murfin motar suka balle suka futa, kallon A'isha sukai datake kwance a kasa, "mun shiga uku yanzu yazamuyi da ita" "kunga ku dauko ta musata a mota mukaita asibiti" Amal da Safiyya ne suka dauketa suka sata amotar, Mama takarbi driving din suka nufi asibiti, hankalinsu ya tashi gaba dayansu, zaro ido Safiyya tayi ganin jini duk ya bata rigar A'isha ta kasanta, "Mama jini " "jini kuma naga kuma bata wani ji ciwo ba ballantana jini yafuto" "wlh Mama dagaske jini ne" Amal tafada, "bara nayi sauri mu kaita asibitin" daga haka Mama takara sauri,

AMERICA
suna zaune cikin Library saboda assignment din da aka basu, hakan yasa sukazo Library, Abdullah ne kadai ke karatun, Jay chatting ma yake, shikuma Irfan yayi shiru, yana tunanin daya saba wato tunanin love Win sa, yan mata ne su uku suka shigo cikin Library din, dukansu turawa ne, ta tsakiyarsu ce tace "nifa kunsan ba karatu zanyi ba hutawa kawai zanyi" se lokacin na kalli yarinyar dan na gano muku wacce iri ce>?#?, farace farin nan irin na turawa gashinta brown, sanye take da riga iya cibiya se skirt wanda ko gwuiwar ta be kaiba, bakinta yasha jan baki, circle eyes dinta blue, kafarta sanye da takalmi me tsine, hucewa sukazo yi ta kusa da Irfan dake zaune dabemasan dasu ba, takalmun kafarta ne ya goce tafada kan Irfan dake zaune, jin mutum samanshi yasa yayi saurin dagowa yana kallonta, yayin da ita ma shi take kallo, kamar wacce yamata kama da wani, saurin tureta gefe yayi yamike yana kallon su Jay "nawuce room sekun tawo" daga haka yafuce daga cikin Library din, "Abdullah nima nawuce seka tawo" "muje kawai nima nagama ai" daga haka suma suka fice, daya daga cikin kawayen ta ne ta tabata tana fadin "Jessica kalau kuwa" se lokacin ta dawo hayyacinta, kujera tasamu ta zauna, kana tace "gaskiya mutumin nan yayimun over" "kamarya" "nakamu da sonsa" "me to Tonny dinfa" "ke dama banga wanda yafi Tonny ba to yanzu nagani" "lallai Jessica kinason ki jazamana ko" "kinga niba wannan ba inason bayanai akansa, inga taya zan Sullo mai"


cikin gaggawa aka karbeta, suka shiga da ita, taimakon gaggawa suka bata, har lokacin bata farfado ba, hankalinsu Mama yakara tashi, hakan yasa da nurse din tafuto Mama tayi saurin tareta tana faWin, "nurse yajikin yarinyar" "ki kwantar da hankalinki Hajiya, mun mata allura ne danta samu hutu, kuma bataji ciwo ba, ammafa ina me baku hakuri, dan tayi barin cikin dake jikinta" "what ciki kuma wannan karamar yarinyar" "bakusan tanada ciki ba" "bamu santa ba ma accident mukai shine muka kawota asibiti" "tohhh dai cikin jikin ta yazube" "kinga nurse kimin wata alfarma, tunda kince bataji ciwo ba a jikinta" "eh batajiba kawai dai barin datayi ne ta zubar da jini" "ok zan baki kudi kikula da ita, idan ta tashi tafada miki gidansu ki kaita dan Allah" "amma Mama bekamata mutafi ba mubari ta farfado mana" Safiyya tafada tana kallon Mama "ke baki da kai bakiji me aka ce ba tayi barin ciki yarinya karama kamar wannan" bata rai Safiyya tayi batace komai ba, Mama taciro kudi dayawa tamikama nurse din, takarba tana fadin "Hajiya baki da matsala zan kula da ita harta farfado" "okay nurse nagode" daga haka suka wuce, ita dai Safiyya ba'a son ranta ba,
NIGER
wani farin dattijo ne zaune kan kujera, hannunshi rike da jarida idanshi sanye da farin glass kana gani kasan medical ne, kamarshi tafuto sosai da Daddy, hotonshi na hango jikin bangon dakin, tun yana saurayi, se asalin kamarsa da Daddy suka bayyana, kasan hoton akasa, ALH. ISYAKU ME DALA, hakan ya tabbatar mun shine kakan su Irfan, kuma mahaifin Daddy, wani mutum ne yashigo falourn kana ganinsa kasan bodyguard ne, "Abba alhaji ya iso" murmushi yayi kana yacire glass din fuskarsa ya kalli mutumin yace "yana ina" "yana part din Hajja" "ok" yafada yana ajiye jaridar dake hannunsa, yamike yanufi kofa, shima bodyguard din yana binsa a baya, part din Hajja yanufa, suna zaune kan kujera, da ita da Daddy, tanata tambayarsa Sa'adatu wato Mommy, zama Abba yayi kan kujera yana faWin "uwa ta ga danta" mikewa Daddy yayi yanufi gurin Abba ya durkusa kusa da kafafunsa yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login