Showing 57001 words to 60000 words out of 71752 words

Chapter 20 - YAN BIYU NE BOOK COMPLETE BY MRS KD.doc

Mrs KD   

29 Sep 2025

1968

haka ta wuce tabarshi a tsaye, rike da baki "wato ya tabbata dai yarinyar nan yawon karuwan cinta ta tafi, oh yarinya karama kamar wannan waitasan meye karuwa ci" daga haka dai ya tafi yana juyawa yana kallonsu,
layine yazo kansu, hakan yasa suka mike suka shiga, macece doctor din, bayani sukai mata, hakan yasa taturasu lab, dan ayimata gwaji, haka suka nufi inda tace, yar karamar roba aka bawa A'isha akace taje toilet takawo fitsarinta, haka ta tafi tana kunkuni tana fadin "to idan kuma mutum bayaji fa" haka dai tayo ta kawo musu, seda suka gama gwaje-gwajen su kana suka basu, takardar, office din doctor din suka koma, suka bata takardar, ta duba, ta tabbatar musu da A'isha bata da ciki, hamdala su baffa sukayi, suna godewa Allah, daga nan suka nufi hanyar gida, ita dai A'isha mamaki take tana tunanin wato karya yamata kenan dayace tanada ciki, to amma nurse Maryam karya tamata kenan,

AMERICA
futowa suke daga class, din, Irfan da Abdullah da Jay ne suka futo, Jessica ce tasha gaban Irfan tana mai wani kallo, be kalleta kawai yasa kai ze wuce, aikam takara tare shi, tana fadin "inason magana dakai ne" Abdullah ne ya kalleshi ganin ko kallonta yakiyi, hannu tamikamai tana fadin "sunana Jessica, kaifa" hannun nata yabi da kallo kana yadago yakalleta, itama shi take kallo, baki yabude zeyi magana sekuma yafasa, yana wucewa, da ido tabishi, kawai suma su Jay binsa sukai abaya, seda suka shiga room dinsu Abdullah yace "Jessica fa cazatayi tana sonka" "eh mana bataga yana da jiki me kyau ba, kasan ita tanason namiji me hallita me kyau" Jay yakare she maganar yana dariya "to baga saurayinta Anthony ba" shidai Irfan yanajinsu beyi magaana ba "me bi tagama dashi ne take neman wani" "aikam nidai bazaata taba samu na kalleta ba ballantana nayi hulda da ita" "kai Irfan ka yadda mana yarinyar ta iya salon futa hayaci" Jay yakarashe maganar yana dariya "ai dani da zuciyata dakuma jiki na, dukka na A'isha ne" "to mayen A'isha" Jay yafada, "nayima kaina alkawarin bazan sake kallon wata ba, bazan kara rabar wata ba, bazan kara bari wata ta tabani ba, indai ba A'isha ba" kallonshi kawai sukeyi, kana Abdullah yace "Lokacin sallar la'sar yayi" mikewa sukai kowa yashige toilet dinsa
NIGERIA
suna shigowa A'isha tafada jikin aunty Zainab tana fadin "washhhh.....aunty nagaji" su baffa ne suka shigo, aikam dukansu suka zuba musu ido, zama sukayi, "to mugodewa Allah A'isha bata da ciki" "alhamdulilah" suka fada gabadayansu, "Inna babba wanka zanyi" "to maza jekiyi maan" daga haka tashige ta debi ruwa tashiga bayi, sukam suka cigaba da hirarsu,




=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

MRS (K D)
??

Romantic=??


Hot loved'?


Marubuciyar littafin
SOYAYYA DA IZZA
Ayanzuma nakara kawomuku wani sabon book
dina me suna (YAN BIYU NE)
ku biyoni domin kuji ya labarin ze kasance
karki bari abaki labari my sister

free page yakusa karewa=?/?=?/? kuyi maza ku fara biyan kudin ku=ذ?=ذ? kafin free page yakare=?
?=?
? ku hanzarta kubiya danjin cakwakwakiyar dazata faru nan gaba=??=??=??

ku biya ta wannan hanyar

=?G?=?G?=?G?

paid book 300
account number 9045749823
bank name Opay bank
shedar biya ta wannan number =?G?=?G?=?G?
09030849138 WhatsApp only
ko kuma katin waya ta wannan number
09045749823 Airtel
*************************************


DOMIN SHIGA GROUP NA YAN BIYU NE YA DANNA RUBUTUN KASAN NAN=?G?=?G?=?G?=?G?
https://chat.whatsapp.com/BcgtqAM3mDe4JRTJQzOoAF



DUK ME SON LITTAFIN YAN BIYU NE DAGA FARKO YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA=?G?=?G?=?G?=?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J




page 35


_________________________________________________________________________________________

______________Wayar Irfan ce tadau kara, hakan yasa yaajanyota daga saman bed dinsa, yana daukan wayar, daga cikin wayar akace "hello" jin muryar dan uwansa kuma gudan jininsa wato Sawban yace "kai bro kaine" "nine ya kake ina fata kana lafiya ko" "toh kusan haka amma ina fama da kewarku sosai" "ohh karka damu bro ai yanzu da waya zamu dinga yin waya" "ina Mommy" "Mommy tana gida" "fatan dai tana lafiya ko, kuma kana kulamana da ita" "kwarai kuwa ina kula da ita ai" "Daddy na fa yana ina" "yana Niger yaje gurinsu Hajja" "lallai Hajja anacan baki har kunne danta yazo" dariya Sawban yayi kana yace "bro ka kula tunda Daddy yaje Niger to sesun yimai maganar aurenmu bamuyi ba haryanzu, kuma kaga nafu tausaya maka, kaine a kasar, watakila ma su daura mak aure atawo da matar, kasan tsohon nan yanason ganin tattaba kunnensa" Irfan yakarashe maganar yana dariya, "kai bro Allah ma ya kiyaye" "am nace dan Allah katuromun number Joseph inasan zanyi magana dashi" "badai wani abun bane ko" "bakomai bro please katura mun yanzu" "ok" daga haka suka yi sallama, Abdullah ne ya kalleshi yace "da alama dai da Hassan kuke waya" "eh shine bakaji daWin dana ji ba wlh" "gaskiya kam zakaji" "nifa Irfan inason ganin wannan Hassan din naka, saboda inga ko kuna kama" Jay yafada "tab kamar ma tabaci, ai da zaku gasnsa bazama ku banbance muba, sedai idan magana mukai" "kai haba dai ya kuke da mutane" "eh mutane basu gane mu biyu bane, wanj zubin za a ganni akirani da Sawban kuma na amsa, wataran kuma shi akirashi da Irfan, kuma ya amsa, bama tsayawa bambance wa mutane kamanninmu, dan bazasu taba ganewa ba sedai idan kamana irin mugun sanin nan shine zaka iya bambamcemu, kaga kamar iyayenmu suna bambance mu, amma family sam basa ganemu, dasu da kakanni mu, sedai kawai mubisu ahaka" "tab gaskiya kunyi kokarin rabuwa da juna" "kadai bari Jay inason dan uwana sosai wlh" "dashi da A'isha wa kafi so" Abdullah ya tambayeshi da sigar tsokana "uhmmm Abdullah kenan shi ai jinina ne, ita kuma rayuwa tace A'isha, dukansu ina sonsu" "to ga kuma Jessica" Jay yafada yana dariya, "uhmmmm wannan ita a mahaukiciya nake daukanta, dan duk macen dazata tunkaro ni inba A'isha ba to mahaukaciya zan kalleta" "tab wannan A'isha dazata ce kafada wuta ma da gudu zaka afka" "wlh indai zata soni kuma tayi farin ciki to ko zan fada" "inka mutu tasoka a lahira" "zandai sha wuya, kaga inna warke se musha soyayya" "wai nikam A'isha nan shekarar ta nawa ne da har ka mace kanta" "14 years fa abun takaici" Abdullah yafada "wayyo Irfan ba kalau kake ba 14 fa yarinya ce dama ke wahalar da zuciyarka" "kunga ya isheku kuyi abunda yadamemu kawai" dariya sukai kana suka hada baki sukace "tohhh na A'isha" pillow ya jefa musu, suka kara shekewa da dariya,

NIGERIA
4:30pm bayan tayi wanka tayi sallar la'sar, tashirya cikin kaya atamfa dinkin riga da zani, aka caba kwalliyar aljanun da da take yi, su baffa suna tsakar gida, a zaune, yana basu labarin yaga malam kalla, suke cewa, "ai malam tun malam kalla yaganku to seta Allah dan karkaso kaji sharrin daze lakaba" "kubarshi shida Allah zato zunubi koda yakasance gaskiya" futowa tayi daga daki, baffa yakalleta yace "kaini Yusufu wannan yarinya nason kwalliyar aljanu" zumbura baki tayi gaba tace "kai dama baffa ai bazan tabayin kwalliya kace nayi kyau ba, sedai kadinga hadani da aljanu" "yo da kinyi kyau meze hana nafada" "baba nayi kyau ai ko" "kinyi" "yawwa bara naje gidansu Hadiza da fatima" "to sekin dawo, amma dan Allah ki kula Banda tsokana kinji" Inna babba tafada tana nuna ta "barta tayima ai taga me tsokana tajanyo mata" "kai nifa bance zanyi tsokana ba" daga haka ta fice, baffa ne ya kalli baba yace "kasan Allah Umaru bazan kara yimaka magana akan kaje ka nemo dangin mahaifiyar yarinyar nan ba" "kayi hakuri baffa zanje gidan ne bansamu lokaci bane" "karma kaje idan ta tambayeka dakanta kaga ai sekasan amsar dazaka bata" "inshallah ma baffa baza akai lokacin ba" "da da yafiye ma"

gidansu fatima tawuce, tana zuwa tayi sallama tashiga, babar su fatima ce zaune a tsakar gida, gaisheta A'isha tayi, ta amsa sama sama, hakan be damu A'isha ba, tace da ita "Umma fatima tana nan" a yatsine tace "bata nan" mamaki ne yacika A'isha ganin yadda babar Fatima ke mata, kuma da sam ba haka takeba, "ke bikiji me nace ba, bata nan, kuma bana bukatar kikara dawowa, dan na yanke alakar ku da yarinya ta" "Umma saboda me menayi makk" "bayan yawon karuwancin dakika tafi shine kike gani zanci gaba da bari Fatima tana kulaki" kallonta kawai A'isha keyi, jin abunda tafada, kai A'isha tasa tafuce daga gidan, "wlh badan babar Fatima bace data gane wace A'isha, gidan su Hadiza tanufa, aikam tana zuwa ta tarar Hadiza na wanke wanke, mikewa Hadiza tayi tana rungume A'isha, "yanzu azuciya ta nake cewa zanje gidanku" "ai ni ganima nazo, zauna kibani labarin abunda akayi lokacin da bana nan" "kai yar baba kina nan da halinki ko" "sedai idan ba'a taboni ba" "ingayamiki, ranar da kika bata, washe gari mukaje makaranta, bikiji abunda yan group din su Rabi suka dinga fada ba" "dalla to ki fadamun abunda suka fada mana ko tsoronsu kike ne" "haba dai tunda kika dawo kuma karyar mutum, nasan zaki taremun" "to inajinki" "suka dinga cewa wai Allah yakara ma da aka sace ki, wai Allah yasa karki dawo ma gaba daya kowa ya huta" "kan jakar bala'in nan Kur'ani se sunce kan uwarsu, sunsan halina sarai" "nima abunda mukace kenan nida fatima" "ke naje gidansu fatima, babarsu semun wani kallo take na wulakanci" "za'a rina, ai malam kalla kaf ya zagaye unguwar nan yana cewa kin tafi yawon karuwanci" "tsinanne munafuki haka ze kare a gulma" "muma nan yaya Mudam yazo yana ta fada, idan yasake ganina dake seya karyani" "yaya Mudam din ke fadar haka, ina Umma ne" "Umma batanan, kuma ita bata yadda ba, amma kinga yaya Jummai, uhmm" Hadiza tafada tana nuna mata cikin daki "au yaya Jummai tana ciki" "tana ciki bata jiyoki bane da ta futo" "oh ni shatu kice haka ake kallona cikin unguwar nan" "ke naga kin kara kyau da kiba, baki tambaye ni saurayinki ba Madu" "Allah Hadiza zan dura maki ashar" jin haka yasa Hadiza tayi shiru, yayar Hadiza ce tafuto daga daki, ganin A'isha yasa tace "ke Hadiza bakiji me yaya Mudam yafada kan yarinyar nan ba" "kai yaya Jummai wlh duk kazafi ne fa" "bawanj kazafi, nina yadda, dama nasan dole A'isha zatai talla da kyawun ta, kuma kinsan maza binta zasuyi" "haba yaya Jummai be kamata kimin wannan shedar ba" "dallah yimun shiru kinje kin gama yawon iskancinki zakizo kijamun kanwa ko, gashi dama ance anganki a asibiti gurin yan ciki" "ke Jummai bafa tsoronki nake ba fa, karki ga ina miki shiru ki dauka na sauya daga yacca nake da" "zaki aikata fiye da haka ma ai ba kunya gareki ba" "wlh fadi ki kara fada, bani da kunya duk uban da ya yimun wlh sena tumurmusa kansa" "yar baba dan Allah kiyi hakuri kitafi" Hadiza tafada tana kama A'isha "zaki cikani ko sena wanke ki da mari" jin haka yasa Hadiza cikata, danta san seta maretan kamar yadda tafada, "banza karuwa kawai, ke kin isa ma nayi fada dake" mayafinta A'isha ta cire ta damare a kugunta kana tace "ai kawai ki tawo idan ba tsoro ba, kiga yadda ake fasawa mutane baki" sanin sarai A'isha zata iya fasamata bakin ne yasa tace "Allah ya sawwake ni ai ba sa'ar yinki bace" takarashe maganar tana shigewa daki "kiyi hakuri A'isha" "dalla matsa can" tafada tana tunkude Hadiza ta fuce, gida tanufa kai tsaye, ranta a bace, "yan mata3" bata jiyo ba taci gaba da tafiya, da sauri yasha gabanta, wata uwar harara ta daka mai, tace "malam kauce kaban guri" "Allah yabaki hakuri amma dan Allah kibani ko minti 1 ne" harara takara banka mai ta murgude bakk, tawuce, binta yaci gaba dayi harta shige cikin gida, saurayi ne ba fari bane, kuma ba baki ba, bashi da wani tsayi sosai, juyawa yayi yakoma, yana fadin "ai naga gidansu"
tana shiga, tafada jikin Inna babba tana ihu, baffa dake cikin daki yafuto yana fadin "kai wannan yarinya da rigimar banza take" "A'isha meyafaru ne kike kuka" Inna babba tafada tana dagota, "Inna duk ba sune suke cemun wai yar iska ba naje yawon karuwanci" "wa iyazu billahi, munshiga uku" shikam baffa kasa magana yayi, Inna karama ce tace "A'isha kwantar da hankalinki, kada ki sake damun kanki idan wani yakiraki da yar iska, tunda ke kinsan ke ba ita bace, sam kada ki damu kinji" "to amma Inna karama harce sukai wai anganni a wajen gwajin ciki" "wannan duk aikin malam kalla ne, muma yayi munafurci kamar yadda yakewa wasu" "kai wannan mutum Allah wadaran shi" "A'isha tashi kije ciki kiyi salla" mikewa tayi tana shigewa, "gaskiya ina tausayin rayuwar A'isha, zata fuskanci kyara da tsangwama" "mutane basu da hankali sam yarinya karama kamar A'isha zasu dinga kira da karuwa, alhalin bama tasan kalmar ba" shidai baffa shiru yayi, yasa kai yafuce masallaci,
bayan an idar da salla baffa yazauna a masallaci yana lazimi, mutanen dake bayansa ne, daya daga ciki yace "kai wannan yarinyar fa da ake maganar ta a majalisa dazu kakanta ne fa wannan" "wacce akace an sace ta ko ashe yawon iskanci ta tafi" "ita bashine ma ake cewa anganta a gurin gwajin ciki ba" "tab aikam dole musa ido kan yaranmu, karta bata mana su" ?asa ?asa suke maganar, ran baffa ne ya Saci, hakan yasa yatashi yanufi kofar futa, "kai kardai yaji me muke cewa" gida baffa yanufa, yana zuwa ya nemi kan tabarma yazauna, Inna babba ce tace dashi "malam akawo ma abinci ne" "ah ah barshi" "malam lafiya kuwa" Inna tafada tana zama kusa da shi "tabbas A'isha zata fuskanci matsala

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login