Showing 63001 words to 66000 words out of 71752 words

Chapter 22 - YAN BIYU NE BOOK COMPLETE BY MRS KD.doc

Mrs KD   

29 Sep 2025

1973

har ita Hadizan ma an hanata, Jummai tafada mun" "toku ina ruwanku idan ba munafunci ba" A'isha tafada cike da tsiwa, "aikuwa da ruwanmu tunda kannen kawayenmu ne, muna gani bazaki lalata masu yara ba" "so take tajasu harkar iskancin data je" "ke bakiga har wani kyau takara ba, asace ka amma ka kara kyau kayi kiba, kowa yana gani yason iskancinta taje" "mutafi kawai zan fadawa Jummai din taja masu kunne" daga haka sukatafi, "A'isha kiyi hakuri kinji" Fatima tafada tana dafata, hawaye ne suka zubo mata, kawai tayi gaba tabarsu anan,
tana shiga gida, tafashe da kuka, aikam gabadaya suka futo har baba dayazo, suna tambayar ta meya faru, "baba wai me namasu ne suke ta cemun yar iska, ni bazan ma kara zuwa makarantar ba" "haba A'isha ki kwantar da hankalinki kinji karki damu" "to ni baba su dena cemun yar iska mana" "kinga A'isha tsokana ce kawai irin tasu, maza jeki cire uniform kizo kici abinci" shigewa tayi ciki, "malam tun muna kwantarwa da yarinyar nan hankali nan gaba zamu rasa abun fada mata idan takawo kara" "shiyasa nace aurar da ita zanyi, amma ubanta yace wai bata isa ba, wacce mafita muke da ita datawuce mu aurar da ita" baffa yafada cike da fada, "baffa ni dama gani nayi A'isha tayi kankanta da aure, amma tunda abun yazo haka kawai ace yaturo iyayensa, ayi magana a aurar da ita din, Allah yasa haka shine alheri a tare da ita" baba yafada, "to Allah ya shiga lamarin dai" Inna babba tafada suka amsa da ameen su duka





=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

MRS (K D)
??

Romantic=??


Hot loved'?


Marubuciyar littafin
SOYAYYA DA IZZA
Ayanzuma nakara kawomuku wani sabon book
dina me suna (YAN BIYU NE)
ku biyoni domin kuji ya labarin ze kasance
karki bari abaki labari my sister

free page yakusa karewa=?/?=?/? kuyi maza ku fara biyan kudin ku=ذ?=ذ? kafin free page yakare=?
?=?
? ku hanzarta kubiya danjin cakwakwakiyar dazata faru nan gaba=??=??=??

ku biya ta wannan hanyar

=?G?=?G?=?G?

paid book 300
account number 9045749823
bank name Opay bank
shedar biya ta wannan number =?G?=?G?=?G?
09030849138 WhatsApp only
ko kuma katin waya ta wannan number
09045749823 Airtel
*************************************


DOMIN SHIGA GROUP NA YAN BIYU NE YA DANNA RUBUTUN KASAN NAN=?G?=?G?=?G?=?G?
https://chat.whatsapp.com/BcgtqAM3mDe4JRTJQzOoAF



DUK ME SON LITTAFIN YAN BIYU NE DAGA FARKO YA DANNA RUBUTUN NAN NA KASA=?G?=?G?=?G?=?G?
https://whatsapp.com/channel/0029VahPZYb6WaKlZQvivt0J




page 37


_________________________________________________________________________________________

______________Yau kwana uku, kenan Usman na zuwa gurin A'isha, amma sam taki yadda da soyayyar shi, ko yazo sedai yayi ta surutansa shi kadai, bata kula shi, se harara da tsaki da take aikamai, dama dakyar baffa ke korata, ta tafi, yau ma kamar kullum, yazo zance, dakyar baffa ta fatattaka ta ta futo, koda taje ko kallonsa batayi ba, se tsaki data dinga yi, hakan be dameshi, dan a cewarsa kuruciya ce tasa take hakan, harya gama surutunsa yatashi ze tafi ko kallonsa batayi ba, kallonta yayi cikin murmushi yace "A'isha gobe inshallah iyaye na zasuzo kawo kudin aure" "mtssss sedai wata amma badai niba" "nidai kena keso kuma ke zan kawo wa" tsaki taja tashige gida, shi kuma yakama hanya yafuce, tana shiga ta baje tsakar gida tana ihu tana shushura kafa" "waike A'isha bazaki taba hankali ba" "rabu da ita sena dauko tsumangiya na dake ta tukun" baffa yafada, "toni baffa dan Allah seka hadani da wancan mutumin, kanajifa wai kudin aure na ze kawo gobe" "eh mana gobe inshallah zasuzo kawo kuWin aure" "nidai gaskiya banason wani aure yanzu bazanba" "ke kika sani mungama magana mudai" tashi tayi ta nufi daki tana rusa kuka,


Sangaren Usman kuwa yana komawa gida, yasamu mahaifinsa, yasanar dashi, yafadama iyayen A'isha gobe za'a kawo kudin aure sa, "masha Allah, ai nayiwa su kawun naka magana insha Allah gobe sesu kai" "Allah yakaimu baba" "amma Usman sedai da daddare akai, saboda ina karasa bincike ne, kasan ance aure ayi bincike" "tom baba shikenan Allah yasa muji alheri" daga haka yamike ya nufi dakin mahaifiyar sa, "Umma kina zaune" "ina nan azaune yanzu na idar da sallar isha" "Umma surukarki fa takusa zuwa" "Allah yakawota lafiya na lura dai kanason yarinyar nan" "ai Umma yarinyar ce takai as???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ota, sema kinganta" "to naji tashi kaje kadau abincinka kaci" daga haka yamike ransa fess,

AMERICA
dasafe suna cikin shiryawa zasu wuce class, sukaji an bude kofar room din nasu anshigo, juyawa sukai su duka, Jessica suka gani, karasowa take harta isa cikin bedroom din, Jay ne yakalle ta yace "waike kinada hankali kuwa zaki shigomana daki" yatsanta takai saman lebbanta tace "shishhhh" alamar Jay yayi shiru "kinsan dai doka ce shigowa hostel din maza ko" "kosu kansu wadanda sukasa dokar basu isa ba a gurina" Irfan dakansa ke duke tunda tashigo yana aikin sa igiyar takalmin sa, kusa dashi tanufa ta zauna gefensa, ta dafa kafadarsa, tace "kaga ina sonka ne shiyasa nake bibiyarka" mikewa yayi yana kallon su Abdullah yace "kumuje nagama" yana fadin haka yanufi kofar futa, da sauri tasha gabansa tana mai wani mayen kallo kamar zata lasheshi, tace "katsaya ko sau daya ne muyi magana, bafa iya nice zan karu dakai ba, kaima zakaji daWi" se lokacin ya dago da idonsa yana kallonta, yace "ke baki da hankali, na lura bakinsan wace ke ba, haka zalika bakisan waye ni ba, ni bana da lokacinki kaf cikin rayuwata to kadama ki sa ran zakk nasarar shawo kaina, danni ba irin mazan dakike mu'amala dasu ba" shiru tayi batace komai ba dan maganganunsa sun sagar mata da gwuiwa, fucewa yayi suma su Abdullah suka bishi, harsuka fuce tana kallonsu, daga baya kuma itama ta fice,
NIGERIA
yau Friday, shirinsa yayi cikin shadda fara kal, yafuto yayi kyau tamkar wani balarabe, futowa yayi yanufi part din Mommy, bata falour hakan ne yasa yawuce bedroom dinta kai tsaye, samunta yayi tana waya, da alama da Daddy take waya, zama yayi kan kujera, yadau wayarsa yana dannawa, seda tagama takalleshi, tace "harka futo ne" "Mommy ina kwana" "lafiya lau" "nafuto yau zanje gidan rediyo najima banje ba, daga nan zanje gidan mutuminnan na tayasa murnar ganin jikarsa" "eh hakan yayi muje kayi breakfast"

"gaskiya Mama banji daWin abunda mukayiwa yarinyar nan ba" "Safiyya ya kike so nayi, a gabanki akace tayi barin ciki" "to Mommy du da haka dai aimune muka buge ta, kuma muya kamata mu kula da ita" "bikiga nabada kudi dayawa ba a kula da ita" "uhmmm wadannan nurse din da ba tsoron Allah suke ba" "kinga Safiyya ya ishe ni tashi kibani guri" mikewa Safiyya tayi jiki a sanyaye tafuce daga bedroom din Mama, Safiyya na komawa bedroom dinta, tadau wayarta tashiga kiran Sawban, har sau uku amma be dauka ba, hakan yasa ta tura mai da text din Friday,

bayan an sauko sallar Juma'a, mahaifin Usman yashigo gida, Umma na ganinsa tasan ba lafiya ba, dan ransa a hade, sannu tamai, be amsa ba yanemi kujera ya zauna, "lafiya kuwa" "hmmmm ba lafiya ba, dau waya ki karawomun yaron nan, kice duk inda yake yazo inason ganinsa" "lafiya meya faru" "kiyi abinda nace, idan yazo kyaji" waya Umma tadauka ta latso lambar Usman bugu biyu ya daga, ta sanar dashi sakon mahaifinsa, shima hakalinsa yatashi hakan ne yasa yabaro gurin aikin da sauri yadawo gida, ba jimawa Usman yashigo gida, cikin falourn yashiga, tarar dasu yayi a zaune, shima yasamu guri ya zauna, kallonshi mahaifinsa yayi yace "Usman game da yarinyar dazaka aura ne, a binciken danayi ya tabbatar mun ba yarinyar aure bacd" "meyasa me aka fada kanta" Usman yafada yana zaro ido, "yarinyar nan anfadamun kwanaki ta gudu ta bar gida, kuma ba'son ina taje ba, hakan yasa mutane suka dinga cecekuce akan ta tafi yawon iskanci, kaf unguwarsu ansani, akwai wanda ma ya tabbatar mun da yaganta a asibiti tana gwajin ciki" "subuhanallahi ita yarinyar" Umma tafada, "wannan duk kazafi ne baba sam ba gaskiya bane baba yarinya ce karama fa taya za tayi haka" "Usman ba mutum daya ne yabada sheda akan hakan ba, kaga kuwa ai ba karya ne ba, kuma ni sam bazaka auro mun yarinyar data gama watsewa a waje ba, kowa yasan haka" "gaskiya kam indai hakane nima sam ban bada goyon bayan ka aure ta ba" "amma umma ina sonta" "kaga kacire ta a zuciyarka, maza kabani number mahaifinta, nasanar dashi anfasa, kada suyita jiranmu" jiki a sanyaye Usman yamikawa mahaifinsa waya,

A'isha na zaune tsakar gida, Inna babba na tsefe mata kai, baffa yashigo, sannu da zuwa sukai mai su duka, kana yadubi A'isha yace "da bikije masallacin ba gashinan ninaje har na dawo" "nifa baffa ba kin zuwa nayi ba, kawai dai ni futar ma yanzu bana sha'awa" "kyaji dashi dai, kin sakamun cajin wayar tawa danace kisakamun kafun nafuta" rufe baki tayi da tafun hannunta tace "la wlh baffa namanta bara naje nasaka ma" "wannan yarinya bansan yaushe zakiyi hankali ba inaga sekinje gidan mijin naki" tana shiga ta tarar da anakiran wayar, tana katsewa ta takashe wayar tasa a caji saboda kar ayi ta kira kuma taki cajin, jiyo muryar aunty Zainab yasa tafuto da gudu, rungumeta tayi tana fadin "aunty Zainab oyoyo" "Aisha zaki yadda nifa" "kai aunty Zainab" tafada tana cikata, zama aunty Zainab tayi kan tafara gaidasu, suka amsa, shidai baffa fucewa yayi, "amarya ashe yau za'a kawo kudi" bata rai A'isha tayi tace "nifa bawani aure dazanyi" "ai naga yadda za ai wannan zaman auren tab" "ah ai tayi hankali kuma ba kamar da ba" "to ai kullum girma take" ita dai tana jinsu bata kara magana ba,


yau tunda yaje office yake ta aiki, dan har tsarin program din da akeyi duk ya sauya su, hakan ne yasa be tashi ba se karfe 6:30pm, Abubakar yakira, yace suje gidan baffa, dan indai yawuce gida bashida time din daze je, hakan yasa Abubakar shima ya tattara takardunsa dan shima daganan gida ze wuce, tunda kusa da gidansu baffa yake, Abubakar yabawa driving din, lokacin magaruba ne yayi hakan yasa yace su tsaya suyi salla, parking sukai suka shiga wani masallaci,

aunty Zainab ce ke shirin tafiya, dan suna wahalar abun hawa, idan dare yayi, dan haka tace bazata jira akawo kudin ba ma, tunda dai sungama aikin snaks daza a bawa masu kawo kudin, A'isha ce tayi tsallen bidige tace se ta bita, su Inna sukace bazataje ba, baffa zeyi fada amma sam tace ita dai ta gaji da zaman unguwar tafuson tabi aunty Zainab, ba yadda suka iya da ita, haka suka kyaleta tabita, baffa nadawo yace ta ina, su Inna suka ce mai tabi Zainab, beyi fada ba, saboda yasan ba futa takeyi ba, wayarsa yadauko daga caji, yaga ashe kashe mai ita tayi, yace "kai wannan yarinya ashe kashemun wayar tayi, watakila ma masu kawo kudin zasuyi ta kirana" "to malam ka kunna mana seka kirasu" "eh kunnawa zanyi nakirasu" yaro ne yashigo da sallama, duk suka amsa masa, yaron yace "wai ana sallama da baffa" "kaje kace ina zuwa" daga haka yaron yafuce, "watakila ma sune suka zo, sunkira sunji akashe inaga" "kafuta kasamesu to" daga haka yafuce, tsaye yagansu jikin mota, suna ganinsa suka karasa kusa dashi, "ah kune ashe bara nafuto da tabarma" daga haka yakoma ciki, "sune suka zo ko" "basu bane wannan yaron ne me gidan Abubakar watakila yafada mai anga A'isha shine yazo ya taya mu murna" mikamai tabarmar Inna karama tayi ya karba yafuce, samunsu yayi dasu baba da kawu Salisu suna gaisawa, tabarmar Salisu ya karba ya shimfida masu, suka zauna, gaida baffa Sawban yayi, ya amsa, kana yamai murnar ganin A'isha, yacemai ya gode, Abubakar ma gaidashi yayi ya amsa, kana yace "baffa ina tajin wata magana cikin unguwarmu" "uhmmm nasan ma maganar baze wuce ta yama dudin da akeyi nacewa A'isha ta tafi yawon karuwanci" kawu Salisu yafada, "sam banji dadin maganar nan ba, kuma ninasan ba gaskiya bane" Abubakar yayi maganar "to inbandama abun mutane taya za ai yarinya karama ace wai taje yawon karuwanci" baba yakarashe maganar cike da takaici, Sawban najinsu bece komai ba, amma yasan tabbas suna cikin matsala, "baffa wai haryanzu masu kawo kudinnan basu kiraka ba" "wlh Salisu yarinyar nan ce takashe mun wayar se yanzu na kunna" "Salisu kuWin wa za 'a kawo kuma" "na A'isha mun yanke shawarar aurar da ita" "baffa be kamata ku aurar da A'isha ba yarinya ce fa kuma ga karatunta bata gama ba" Abubakar yayi maganar "mafutarmun kenan idan ba haka ba A'isha zata dinga fuskantar tsangwama da kyara ko a yanzu ma ana mata, har makaranta" baba yafada, shidai Sawban be samusu baki ba, ganin ba huruminsa bane tunda beson yarinyar ba, wayar baffa ce tashiga kara, hakan yasa yazarota daga aljihu, "yaron daze aureta Aisha ne watakila kosun tawo kawowa" yafada yana daga wayar "Assalamu alaikum" baffa yafada, Usman yace "wa'alayka salam baffa ina yini" "lafiya lau Usman" "baffa akwai matsala" "matsala kuma tame d'annan" "baffa mahaifina yace bazan auri A'isha ba" "saboda me kuma me tayi" "yayi bincike ne anbashi labaran karya, baffa ance A'isha ba yarinyar kirki bace" "inalillahi wa'inna'ilaihi raji'un" abunda baffa yafada kenan, aikam gabadaya suka zuba mai ido, "baffa kayi hakuri nayi kokarin fahimtar dashi amma sam yaki, baffa wlh banzo gurin A'isha dan in yaudareta ba, har cikin zuciyata inasonta, baffa kayi hakuri dan Allah" "shikenan yaro bakomai" daga hak baffa ya ajiye wayar, kallonshi baba yayi yace "baffa lafiya kuwa" "yafasa auren A'isha, sunyi bincike anfada masu karya, mahaifinsa yace baze aure ta ba" "subuhannallahi kai wannan wacce irin rayuwa ce yanzu haka rayuwar A'isha zata zama" "kenan haka mutane zasu dinga bada shedar karya akanta" "tabbas kuwa haka zasuyi ta bayarwa kuma duk wanda yazo abunda zasuyi ta fadamasu" Abubakar yafada cike da takaici dan koshi abun yabata mai rai, "baffa kayi hakuri, kabarsu kawai nan gaba zasu gane kuskurensu kan nasu yaran" Sawban yafada wanda tundazu be samusu baki ba se yanzu, "yarona wannan sam bazezo karshe ba, munshiga tashin hankali lokacin da A'isha ta bata amma kamata yayi data dawo muyi farin ciki, amma sam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login