Showing 27001 words to 30000 words out of 35296 words
Chapter 10 - MIJIN TACE Book 3 Hausa Novels by hafsat Sodangi.docx
ciki ne kawai ya ishe ta.
To miji yayi mata shigo-shigo babu zurfi ya
dodana mata romo a baki ta dauka a haka za su
122
dauwama yanzu kuma bata yi aune ba sai taga ba shi
da lokacinta.
Jiya fa yana shigowa ko gaida su Baba bai tsaya
yayi ba ya juya ya tafi abinshi, yana Can wurin
wancan din, ni naji kamar ana cewa ma wai ciki ne
da ita sai ta haife za'a daura auren.
Ni kam a wannan lokacin na sakankance na
yarda na kuma mika wuya cewar bakin cikin Ado ne
zai kashe ni.
A wannan lokacin Goggo Ayalle da Babba
Tanimu sun yi matukar kula da ni, don su a nasu
ganin rashin lafiya nake yi, don ita na baiwa ma
cefanen da Adon ya aiko dashi.
Hajiya kuma tazo tayi min shara da duk wani
abinda ya kama na tsabtace min wurina, bana cin
komai sai in Goggo ta matsa min ne nake yarda in
sha ruwan tea ko farau-farau din da kullum Baba
Tanimu yake aiko min dashi.
Na rarne nayi matukar fita hayyacina, in ban da
kukan bakin ciki babu abin da nake yi, kewar iyayena
da 'yan uwana da dangina, musamman Babana tayi
matukar mamayar zuciyata.
Babu abin da nake nadamar shi irin sanya
Babana bacin ran da nayi akan Ado, gashi tun abin
bai je ko'ina ba ko shekara cif ba a cika ba har
alhakin shi ya kama ni, na soma ganin sakamalkon
123
abin da nayi 'kwai da dutse.
Kullum bayanin da mai babban allo yake yi min
kenan ya ce min basa karo, ya kan yi min irin wannan
bayanin ne kuwa a duk lokacin da na soma gaya
mishi abinda Baban nawa yake yi mana mu da
Innarmu.
Ashe ma Baban nawa mutumin kirki ne mai
kuma adalci ban taba sanin hakan ba kuma sąi a
yanzu, a wannan lokacin da nake dandanar bakin
cikin Ado.
Ran Litinin da sassafe ya zo gida babu wanda
yayi zaton ganinshi a lokacin tunda ranar nema ranar
da ya kamata ace ya tafi. Ni kadai ce a dakin ssai ko
Hasiyan da ke kai-kawon gyara min wuri.
Ina kwance a kan katifar ya wurgar da abin da ke
hannunshi yazo ya daga ni ya zaunar da ni na ki
zaman na koma na kwanta, kina hauka ne
Humairah? Kina hauka ne da ki ka maida kanki
haka?
Yanzu in ban da nayi wa Bala waya ya ce min
ba ki da lafiya sai kiyi ta zama a haka? Za ki kashe
kanki ne? ban tanka mishi ba, tun zuwanshi da safe
har Azahar ban bude baki nayi mishi magana ba.
Na riga na kudurawa zuciyata in dai zuwan da
ya yi ban yi mishi magana ba ne yasa shi yi min
hukuncin da yayi min, to na daina yi mishi magana
124
VAvi min abin da yafi wannan tsanani.
Har aka yi Sallar La'asar bai ji na bude bakina
na ce wa weai wani abuba, balle yasa ran zan yi
mishi na kuma ki yarda da cewar da yayi in tashi
muje asibiti,
Ina kallonshi ya jawo wayarshi, kalaman shi
suka fahintar da ni da Innata yake yin maganar
gaskiyar abinda ya faru tsakanina dashi, ya gaya
mata abin da nayi mishi da wanda shima yayi bai
rage komai ba.
Haka nan bai kuma fara ba, da kuma halin da
ake ciki a yanzu duik sai de ya gaya ata.
Ban ji ita abin da take gaya mishi ba amma na
ji shi yana amsa mata da to Inna sai kuma neji shi
ya ce mata to gata, nayi kamar in ki kar6ar wayar
sai kuma naga to in ranta ya baci fa?
Alhalin bacin ran Babana shi kadai shi ne ya yi
min wannan sanadin, to in ya hada har da nata fa?
Ya ya zan yi? Nasa hannu na karbi wayar ina jin ta
soma yi min magana naji muryarta.
Sai kawai na soma kuka, kuka kuma mai
tsanani ina jin itama ta gane ina cikin bacin rai mai
sanani ne yasa ta talkaita maganar tata da cewar
tunde dai ya zabe ni ya kawo maganar gabana ina
ganin ya kamata ta kare don girmarma ni yayi.
125
Ga manya nan a gidan naku bai kai maganar
gabansu ba saboda yana ganin in na gaya miki zaki
ii, in kuma kin ga ba za kiyi min wannan alfarmar
ba duk matar da ki ka gani a dakinta tana zaune, to
hakuri talke yi.
Ba kuma zai yiwu ace kina zaune da miji amma
ba za ki girmama shi ba, in yaja sai kema ki ja
saboda lina ganin kin isa. Wannan ba tsarin aure ba
ne na Shari' a ya zama auren 'yan iska.
In kuma kin ga irin shi ki ka fi sha'awa sai kiyi,
sannan zan yi miki kashedin ki daina fada da shi a
gaban yan uwanshi. Ki rike sirrin da ke tsakaninki
da mijinki, ki gamsu da alherinshi tun ba ki kure
hakurinshi ba.
Inda za ki daina jin jita-jita kuma kina amfani
da zato to da zai fiye miki amfani, in kin yarda da
abinda na gaya miki ki bashi hakuri, na ce mata to.
Tana kashe wayar na sunkuyar da kaina kasa
na ce mishi, kayi hakuri, bai taba tsammanin abin
da zan gaya mishi kenan ba, wata Kila jira yake yi
mu gama maganar shi ya bani hakurin.
Dadi ne yayi matukar kama shi yesan in na ce
ta sani ba shi hakurin, dawowa kan katifar ds nake
kwancem yayi ya dago ni ya kwantar a jikinshi inna
tana sona Humaira, in ma dai ke ce ki ka fahimce ni
126
irin fahimtar da tayi min?
Sau dava nake fadin gaskiyata ta yarda da ita,
amma ke baki yarda da ni ba, yaya za'ace miki na
ajiye wata mata a wani wuri ki yarda? Sannan in
ban da Inna tayi miki magana ta saki ki bani hakuri
ke kina shirin muyi tashin hankali ne.
Ni kuma ba ki sani ba tausayinki nake ji na
rabo ki da iyayenki da danginki na kawo ki cikin
nawa na ajiye ki ni da ki ke ganina ban cika son
muna samun matsala da ke ba.
Iyaka dai ba zan yarda da wasu halayen da ki
ke fito min da su ba ne don ko da ki ke jin ana ce
min 'MIJIN TACE' in ma dashi ki ke lura to na
rantse miki ni ba shi ba ne.
Sannan masu kawo miki bayanin abinda nake
yin dama ko menene? Da yake zama sanadin fada a
tsakanina da ke in na nemi aure a danginsu fa za su
jagoranci a bani in kuma kina ganin karya ne to.
Na daure fuska na ce to a baka mana sai me?
Rannan haka muka kwana da Ado maganganu
masu kwantar min da hankali yake tayi min na
yanda zamu fahimci juna mu zauna lafiya, ban
tanka mishi ba muka yi kwanciyarmnu yana
kankame dani a jikinshi bai kuma nemi komai ba
daga gare ni.
127
Washegari tun daga fitowarshi Masallaci Sallar
Asuba ya yi shiri ya ce min zai tafi Danja, na ceto
sai ya dawo, nayi mishi addu'ar da ta dace in yi
mishi, ya kama hanya ya tafi.
Wunin rannan ma ban fito ba ina dakina, ina
kwance kan katifata tunanin al'amura kawai nake
yi a zuciyata. Hasiya tazo tayi min duk abinda ya
kamata tayi min ta tafi ta bar ni ni kadai.
Tuni na kudurawa zuciyata bin hanyar da zan
zauna lafiya da mijina, in daina daukan zancen
wani ko bin shawararshi tunda na gane hakan ba
zai amfane ni da komai ba.
Sai dai yayi min sanadin wahala da 6acin rai
mai tsanani, babu kuma wanda zai agaza in da wani
abu sai dai ma in an gane halin da nake ciki ayi ta
zundena ana yi min dariya.
Don haka na yanke wa kaina shawarar ajiye
makaman fada in bi hanyar lallama da rarrashi da
bin umarninshi akan komai in dai baya sabawa
Shari'a ba ne shima kuma nasan da wuya yasa na
saba shari'ar.
Don kuwa mai kokari ne akan kiyaye dokoki
tunda na gane abin da ake yi wa wasu mazan a
kwashe kalau shi kam ba zai lamunta ba dama
kuma Hausawa suna da karin maganar da suke
128
cewa, wai in da wani yayi rawa aka yi mishi kari,
in wani yayi to dukan tsiya yake sha.
Nayi sallar La'asar nasa ruwa nayi wanka irin
wanda na dade ban yi ba, don kuwa rabona da in yi
wanka har na manta, tun da bakin cikin Ado ya
kwantar da ni. Ni da kaina tsamin jikina nake ji.
Na fito nayi alwala don yin sallar magarib da
Isha'i, sannan na zauna nayi shafa mai kyau na
gyara jikina sosai tun daga gashin kaina har farcena
babu abin da ban gyara ba.
Sanyi ya sauka min har cikin zuciyata saboda
ni' imar tsabta da na sau, kai kazanta dai musiba ce,
ni da kaina na gayawa kaina hakan.
Nan da nan na mike na canza zanin gadon da
ke shinfide kan katifar na shimfida, wankakke,
gogagge, na fesa freshner mai sanyin kamshi na
kuma kunna turaren tsinke a bayan gida na jawo
dan kofan tsaki gina na koma dakina na zauna ina
jiran lokacin Sallar magrib tayi.
Cikin zuciyata dai bani da wata matsala illa
jiran in gabatar da sallolina insha tea in kwanta
tunda nasan ni da ganin Ado watakila sai gobe da
yamma ko kuma ma ranar Allhamis.
Na idar da Sallar Isha'i na kulle kofata na dawo
ina hada tean da zan sha kafin in kwanta tunda ban
129
yi girki ba ban kuma aika an karbo min abincin
gida ba sai naji ana taba kofa nayi maza naje na
bude don ganin ko waye?
Sai naga Ado na kauce daga kofar ya shiga
nayi mishi sannu da zuwa ya amsa da har kin rufe
kofar ne? na ce mishi eh, yana cire kayan jikinshi
alamar wanka yake shirin yi yana tabayata me ki kaa
girka ne?
Cikin natsuwa na ce mishi ban yi giki ba
saboda ban san zaka dawo ba, in ba zan dawo ba ba
za ki girka abin da za ki ci ba? Kin ga irin ramar da
ki ka yi kuwa? Ya maida rigarshi ya fita.
Tunda Ado ya dawo ranar Talata da yamma bai
sake tafiya Danja ba yana gida bai kuma fita ko'ina
in ba sallama aka yi dashi ba.
Zuwa nayi na gayawa Princepla da yake akwai
fahinta a tsakanin na ce mishi akwai matsala a
gidana, ya ce to in je ya bani wannan satin sai na
roki wani Malami ya taimaka min da darussan
nawa don kar yara su cutu.
Ya dago idanuwanshi ya kalle ni doon a kwance
yake sanda yake maganar. Sai dai kuma gashi na
dawon tun ba aje ko'ina ba har na gundure ki kin
gaji dani ban tanka mishi ba don nasan me yake
nufi.
130
Tun daga wannan lokacin mu'amallar Inna da
Ado tayi matukar karuwa, na kuwa gane hakan ne
daga yawan kiranta da nake ganin yanayi, ba zai
yiwu sai rikici ya taso min a gida in rinka kiranta
tana kwantar min da fitinar ba.
Abinda ya gaya min kenan rannan da na ji su
suna magana ban kula shi ba, na dai san kawai yana
ganin girmanta da darajarta yana kuma girmamata
da iyakacin gaskiyar shi.
A wannan lokacin ne na gane gaba daya mataan
gidan bakin su daya ne haduwa suke yi suyi
maganganinsu kan abinda ya shafe ni ni da Ado.
Illa iyaka kawai ita Furerah ta ki yarda ta daina
karbar girkina tana yi saboda tana matukar amfana
dashi. A zahiri kuma tana nuna ita babu ruwanta ni
tata ce saboda alherin da nake yawan yi wa
ya'yanta.
Don haka sai na hada su gaba daya nayi musu
jumiah guda daya dukansu ina girmama su bana
kuma jin zafinsu tunda na gane damuwarsu bata
wuce ta kulawar da mijina yake da ni ba.
Ado bai daina zuwa Danja ya kwana ba na
kuma cire raina a kan hakan randa yake gida ma
mafi yawancin lokaci yakan raba dare ne biyu yana
waje bai dawo ba.
131
Ban kuma damu ba duk da 'yan maganganun
da ake yi in an ganni, nasan yana wurin lambunshi
yana lura da yanda ake ban ruwanshi.
Wani lokaci ya dawo ya samu ina zaman
jiranshi, wani lokaci yazo ya samu nayi bacci,
randa yaga zai tashen ya tashe ni in yi mishi abinda
yake so in yi mishi.
Randa yaga zai hakura ya bar ni in yi barcina,
shi yasa ma mafi yawancin lokaci in naji yana tayi
min kashedin kar fa kiyi bacci ki jira ni ce mishi
nake yi gara dai in ka dawo ka tashen, don ba zan
iya wannan dogon hirar ba a wannan duhun ni
kadai.
Yawan itar da nake yi wa Ado akan duhu ya
sanya shi yana fara diban labun nashi ya kashe
kudi mai yawa ya sanya wutar lantarki a gidan
gaba daya.
Ya kuma gyara katangar gidan yayi mata kofa
daya, yayi wa zauren gidan kyakkyawan gyara,
soronshi ya zauna daidai maimakon da da yake
barazanar zubowa, amma bai yi musu gwaninta ba.
Su Ruwaila wai cewa suke yi aikin banza, tun
lantarki yana sabo a Dabai ba a sanya mana shi ba
sai yanzu da ya zama gidan kowa da shi, kuma dubi
hanyoyin nan da muke samu muna shiga makwabta
132
hankali a kwance wai don fitina yasa an toshe.
Yanzu babu halin ka fita sai ka nemi izini, kai
zama da fitinannen mutu dai wuya ne dashi, sai
kayi hakuri.
. Ni kam tunda na gane mijina na kuma gane
halinshi na gane yana sona yana girmama min
mahaifiyata yana tattalin yan kannena sai na.
kudurawa kaina yin hakuri da shi da duk wani abin
da ya shafe shi.
Ban ganin yayi wani abu in ce mishi don me?
balle in je ina tambayarshi dalilin da yasa yayi har
akai ga jallin da zan ce ban yarda ba na daina.
Shi kuma in ya ga nayi mishi ba daidai ba ya
kama zai yi fada tunda shi baya iya ganin an yi bai
tanka ba sai in ba da hakuri ko da kuwa ina sane
nayi don ya ji in da dadi.
Don haka yan uwanshi başa bata min rai
komai suka yi min ban tankawa saboda na san
fitinata da su ba za ta saman mishi farin ciki da
kwanciyar hankali ba ni kuma abinda son ganin ya
samu kenan.
Rannan na dauki wayar Ado na kira Inna don
mu gaisa, tunda zaman jiran fitowarshi daga wanka
nake yi muna cikin hira Innar take bani labarin anyi
ruwan saman farko a Bauchi jiya.
133
Nayi kabbara cikin farin ciki tare da addu'ar
Ubangiji ya sanya damunar ta zamo mai albarka, ta
ce min to amin. Na ce shi kenan Inna za ku dan
samu saukin zafin nan da ake ta fama dashi ko ina.
Don mu ma nan din zafin ne, Inna tayi
murmushi ta ce to mu tun yaushe kuma muka huta
da zafi? Nayi maza na ce, Inna bana ba ayi zafin ba
ne sosai a Bauchi? Ta sake wani murmushin kafin
ta ce min.
"Hala ba ki san mijinki ya aikowa Umar mai
shagon dinkishi kudi ba? Wai azo a sanyawa mai
sunanshi (A.C), ai mu tun nan muka daina jin zafi.
Na ce bai gaya min ba Inna, cikin zuciyata
kuwa tunawa nayi da ranar da naji hirar Ado da
Sa'adatu yana tambayarta mai sunanshi, tana bashi
labarin ai tunda zafin nan yazo baya baccin daree
kwana yake yana kuka wai shi nan ma baya son
zafi.
Ado yana jin anyi ruwan saman farko a Bauchi
ya fitar da hatsinshi da ya noma gaba daya ya kai
kasuwa ya sayar, sai dan kadan ya bari. Dama
tunda' aka yi girbi ya fidda Zakka tun a gona na
baiwa makwabta da 'yan uwa nasu hakkin.
Ya tattara saura ya adana da niyyar sai damuna
ta gabato zai kai hatsinshi kasuwa, don yayi amfani
134
da kudin wajen yin noman wannan damunar.
Ado yana ta shirye-shiryen noma bana na
wannan damunar da muke addu'ar zuwanta lafiya
nima ina nawa shirye-shiryen na rubuta jarrabawata
ta gama Secondary a lokacin nan kuwa ina da ciki
wata hudu.
Sai dai babu wanda ya sani don babu alamar
shi ga ni kuma lafiyata kalau yan matsalolin da
nake dasu ba wasu masu yawa ba ne.
A wannan lokacin babu abin da nake so irin
Ado ya yarda ya barni in je gida in ga iyayena da
yan uwana. Amma sai in yi tayi mishi maganar
yana jna baya ma amsawa sai in ya ji na matsa
mishi da zancen sai ya ce min io wai me za ki jie ki
yiwo ne?
Da Aliya ta dawo daga aikin Hajji sun zo gidan
nan ita da Atika da Sa'a har da Baba karami suka
kawo miki tsarabarki suka yi miki bakunta ta
kwana uku. A wannan dan tsukakken dakin naki
baile ko in ce tsarabarki kike son karbowa.
Inna kuwa kina jin maganarta a waya mai
babban allo in yana son ganinki shi da matanshi
sun san in da kike tunda yazo Hajiya 'yar dubu ma
tazo to wa yai saura? Kullum yayi min irin wannan
maganar bata rai nake yi in daure fuskata in ce
135
mishi su kadai ne yan uwana da dangina?
Babana fa? Sai in hado da Mama don in yi
mishi kara tunda na gane har yanzu yana sonta
yana kuma girmamata, sauran 'yan uwana fa? Sai
ce to ba yanzu ba sai ya duba yaga lokacin da ya
dace.
Rannan muna tare da Ado a dakinmu bayani
yake yi min kan kudin hatsinshi da ya noma bara
wanda sai à wannan lokacin ya sayar da kuma na
lambunshi da ya sayar shima ya adana yana harin
damunar bana da gonakin da yake shirin nomawa.
Bana duk gonakina na gado zan