Showing 30001 words to 33000 words out of 35296 words
Chapter 11 - MIJIN TACE Book 3 Hausa Novels by hafsat Sodangi.docx
noma
Humairah ki taya ni da addu'a, nayi murmushi nayi
mishi addu'o'in tun a gabanshi wanda kuma dama
ka'ida ne sai dai in ban yi sallah ba.
Haka kawai ma na kan shi da irin koKarin- shi
da wahalarshi in roki Ubangiji ya sanya mishi
albarka mai yawa a ciki.
Muna cikin hirar ya daga ido ya kalle ni, amma
a anya Humairah ba zan kure hakùrinki, in sa ki
gundura da halayena da dabi'una ba kuwa?
Nayi kamar ban ji shi ba, saboda tunda muka yi
fadan da nace halayenshi da dabiu'unshi ne suka
gunduren ya.maida maganar ta żama ka idar nenman
magana a wurinshi.
136
Ban taba ganin mutum nmai son kai irina ba
Humairah alherin da na samu a noman banan kawai
ya ishe ni in yi miki ginin da za ki zauna a ciki ki
yalwata.
Amma ban yi ba, wai so nake in juya kudin in
sake maida su gona wai da a irin nawa son kan so
nake duk abin da ya fito daga gona in maida shi
gonar a aikin da nake yi in yi tattalin da zan rinka
yi mana hidimominmu.
Ban kula zancen nashi ba, wucewa kawa' nayi
na kwanta a bayanshi.
A warnan noman da Ado ya yi na wannan
damunar ne na gane talaka dai ba karamar wahala
yake sha ba a kasar nan duk abin da zai yi karfin
shi kadai yake yi mishi bai da wani mataimaki
ba dai na Ubangijinshi ba.
An riga an sani sarai babu yanda za'ayi a hada
noman wanda yayi amfani da karfi yayi da na
wanda yayi amfani da hanyoyin noma irin na
zamani wanda bai yiwuwa sai ana da wani abu a
hannu.
Amma an ki a yi wa manomanmu na asali
taimakon da ya dace da su wanda za su sau su
bunkasa aikin nomansu sai kullum ayi ta bayani a
baki a gidajen Radiyo da Jaridu, amma wasu yan
137
tsirarun mutane suke tsare komai su amfana da shi
a bira ne ba tare da ya kai ga manoman na asali ba.
Kullum irin korafi da maganganun da nakeyi
wa Ado kenan a duk lokacin da ya zauna yayi min
bayanin mai dadin ji kan aikin da ake yi mishi a
gonakin nashi in ganshi kuma garau babu wata
alama ta wahalar da zata tayar da hankali a tare da
shi.
Hannu babu bororo balle kanta, bal;e aje ga
jallin yin fason kafa ga ciwon baya da na kugu,
gashi kuma ya tabbatar min da cewar noman nashi
na bana zai nika na bara sau goma ko a fiye da
haka.
Sannan a hakan duk dan wani dama da ya samu
na zama zaka gan shi yana tashe da laptop din shi
bincike yake kara yi kan hanyoyin noma irin na
zamani a kasashe daban-dabarn da suka ci gaba, wai
ya kara koyo da sanin sabbin dabarun noma don ya
kara samun sauki.
A wannan damuwar ta bana sau biyu ina kaiwa
gonakin Ado ziyara sabanin na bara da na ki zuwa
saboda aikin ya wahalar min da mijina da yawa ya
fitar min dashi daga hayyacinshi, don ma shi din
namiji ne.
A duk lokacin da na kaiwa gonakin nan ziyara
138
kuwa tsayawa nake yi in yi ta kallon yabanya,
yanda ta mike fetal ta tafi tayi nisa cikin jeji ban
iya hango karshenta. Gashi ta yi kore shar.
Wani irin dadi ne yake kama ni wani irin sanyi
ya sauka cikin zuciyata, in ji ba ni da wani sauran
nauyi ko kunci da ya addabi zuciyata in ji babu
abin da yafi dacewa da ni irin in kara tsarkake
Ubangijina.
In kara kadaita shi da bauta, in kara jin
tsoronshi saboda ko daga kallon baiyanannun
ayyukanshi na zahiri a kawai wadanda su ba sai
mai hankali da ura ne kawai zai gansu ba.
Misali halittar sama da kasa canzawar yanayi
daga rani zuwa damuna, yanda dan Adam ke shuka
kwaya guda daya ya fitar da daruruwa kasa guda
daya ruwa iri daya ya fitar da nau'o'in tsirrai
daban-daban ya ishe mu zamowa abin lura.
Bin bayan Ado nayi can cikin gonar saboda
hangenshi da nake yi yana ciccire kananan ciyayin
da ke son fitowa da tsirran da bai son gani don in
gaya mishi tunanin da ke damun zuciyata.
A duk lokacin da na kalli yanayin sama ko
yanayin shuka a lokacin da tayi shar a jeji in ji ko
shima tashi zuciyar tana raya mishi irin wadannan
al' amuran,
139
Ban san yanda aka yi ba, ban san ina na
tsunduma wajen aikin ciccire mishi kananan
ciyayin ba sai da na ji shi yana cewa "Ke Humaira
ba fa abin da na kawo ki gonar nan kiyi kenan ba.
Kawo ki kawai nayi ki ganta kiji dadi ki taya ni
yi mata addu'a na rokon Ubangiji ya sanya mata
albarka mai yawa." Na ce mishi amin Kawu.
Taso ni yayi a gaba muka fito daga cikin gonar
muka dawo in da ya ajiye babur dinshi da muka zo
akai, cikin natsuwa ya kalle ni bayan ya burga
mashin din.
"Hau mu tafi mana." Na kalle shi na ce, "uh'uh
yi gaba zan tako da kafa ba zan sake hawanshi kayi
ta tsalle da ni a kan kunya ba."
Cikin natsuwa da nuna kulawa ya ce "Ba kunyaa
ba ce Humairah, hanyar ce babu kyan, na ce eh to
jeka. Ya sauka daga kan mashin din ya shiga tura
shi, ni kuma ina takawa da kafa muna tafiyar mnu
muna hirarmu mai dadi.
Mafi yawancin hirar kuma kan abin da ya shafe
mu ne, haihuwata da ta matso, gonarshi da kuma
aikinshi, kullum hirarmu bata wuce wadaunan
abubuwan guda uku.
Ranar Juma'a sha tara ga watan tara cikin
damuna sosai a lokacin da manoma suke matukar
140
taka tsan-tsan da dan abinda yai saura a hannunsu
saboda tuni karfinsu ya koma gona.
Ita kuma gcnar bata fara bayar da komai ba, na
haifi diyata ta mace lafiyayya, kana ganinta kasan
ubanta manomi ne, taci ta koshi.
Ado ya shigo gida cikin sauri a dalilin ya
kwana a dakin zauren gidanne saboda zuwan da
Sa'adatu tayi. Ina jin shi yana dariya yana tambayar
Goggo Ayalle.
Goggo wai yau ma an yi haihuwa a gidan nan
ko? Tana taya shi dariyar tana fadin "An kara
wata haihuwar. In ce ko dukansu ne suke shirin
haihuwar ne Goggo."
Goggo tayi dariya ta ce, to wa yasan musu ne?
wacece kuma ta haihu yau? Goggo ta ce a'a ashe
baka ji mnai baihuwar ba, ai Aisha ce."
Dib naji Ado yayi, yayi shiru na lokaci mai
tsawo yana sauraron bayanin da take yi, jarumar
yarinya ita kadai ta haihu sai zuwa Kanwarta tayi ta
tashe ni, hatta tsofaffin matannan da suka haihu
basu haihu su kadai ba, sai da suka taso mu muka
zo muka kwana muna zaune da su amma ita..
Ado ya katse ta ya ce to tsofaffin mata Goggo
ba sun san zafi da mutuncin kansu ba, amma ita fa
tana da hankali ne? Goggo ta rufe Ado da fada.
141
Wanne irin magania ne wannan? Yarinya tayi
kokari ba za ka yaba mata ba, bata hutar da kai
biyan kudin asibitin nan na zamani mai tsada ba?
To ni dai ban gode mata ba Goggo in tayi ne
don in yaba mata to ban yaba ba, ya juya ya bar ta
tana tayi mishi fada ina jin shi yana kwalawa
Sa'adatu kira, tayi maza ta fita ta tafi wurinshi.
Aka gama min komai aka dawo dani dakin
Goggo Ayalle wai a nan zan yi jegon, ina zama
Sa'adatu ta sake shigowa rike da kwano, ga
dabonon da Inna ta ce kar ki manta dashi.
Na kalle ta nayi murmushi na ce ai kuwa in ban
da kin tuna da na manta na karba ina ci ita kuma sai
kallon yarinya take yi tana murmushin jin dadi.
Ran Yaya ya 6aci, wai kin zauna kin haihu a
gida baki ga nima fadan da yayi min ba akan wai
ban je na gaya mishi ba. Na ce ai nima kukan
yarinyar kawai naji, in kai mishi ita ya ganta?
Na ce ke Sa'a, kin san nan gidan komai muka
yi za a iya cewa ba muyi daidai ba, ta ce haka ne.
naci dabinon sosai nasha ruwa kamar yanda Innan
ta ce a gaya min, na gyara nayi kwanciyata.
Kan ka ce meye wannan? Sai na ji ni garau
kamar ba ni ce nayi wannan uban wahalar ba.
Jimawa can Ado ya shigo dakin wurin ya nema
142
ya zauna suna gaisawa da Goggo cikin girmamawa
irin wannan alheri ya same muka tashi kana fada?
Ado ya ce kiyi hakuri Goggo raina ne ya baci ana
jaruntaka da wahala ne Goggo?
Ba za ta fada a san bata da lafiya ba? Ta ce to
tunda Ubangiji ya raba su lafiya ai sai muyi mishi
godiya, yayi murmushi ya ce haka ne.
Goggo taci gaba da yi mishi bayani ita haihuwa
ai duk ta wuce yanda ake maganarta, gida da
asibitin duk daya ne. Ubangiji ke yin ikonsa ayi ta
lafiya.
Yayi maza ya sake cewa haka ne Gogg0, mun
gode mishi. Ta tashi ta dauko yarinyar nan wai zata
ba shi ita kamar yanda ta saba kawo mishi sauran
yaran da aka haifa kafin ita a gidan.
Ya ce "A'a Goggo, ai zan ganta a hankali." Ta
ce ai haba? Ai na dauka ba za ka yi kunya ba, ta
maida ita ta ajiye ta fita saboda kiran da Baba ya yi
mata.
Yayi maza ya dawo bakin gadon yasa hannu ya
dauko ta ya kare mata kallo ya tofe ta da addu'o'i
ya maida ita yana kallona cikin murmushi.
Wannan yarinyar ta fito a jikinki Humairah ba
ki samu matsala ba ko? Ban kula shi ba, ya dan yi
waiwaye don kar yayi maganar da wani zai ji shi
143
ganin ba kowa yasa shi matso da bakinshi kunnena
ya fadi abinda yake nufin fadin.
Kallonshi kawai nayi ba tare da na ce mishi
komai ba, hidima sosai Ado yayi sai dai yaja ya
tsaya kan bai yarda ayi taron suna ba, tunda sauran
haihuwar ma duka ragunan suna kawai ya bayar
aka yi ysnka sai sunan da babu taro mai yawa.
Don haka nima ba zai yarda da gayya daga
wani wuri ba, Sa'adatun da tazo ita kadai ta isa.
Ni kam kuka nayi tayi, Goggo ma ta ce akan
me kuwa zaka yi haka? Wadannan yan uwa nata
ka ce ba za su sUnan 'yarsu ba?
Ya ce to 'yarsu tazo cikin tsululun damina
Goggo ba sai suyi hakuri ba, manomi yana hidima
mai tsanani ne da damuna? Goggo tayi dariya ta ce,
wannan shi ne iya shege.
Ni kamn da hankalina ya tashi da hana yan
uwana ziwa suna da Ado yayi sai da naji yana yi
wa Innata bayanin cewar shi din ya riga ya shirya
zuwana gida da zarar mun yada wanka, don haka
kar ayi wahalar zuwan.
Yanda Ado ya bada ragon suna guda daya a
duk haihuwar gidan da aka yi haka nan a wannan
sunan ma rago guda daya ya bayar da safe ranar
suna Baba Tanimu ya fadi sunan da ya sanyawa
144
yarinyar Umahmah.
Gaba daya kowa a gidan mamakin sunan yake
yi, wasu ma tambaya suke yi ina Baba ya samo
wannan sunan kuma? Sai da Baban ya shigo Goggo
tayi mishi tambayar naji yana yi mata bayani.
Sunan jikar Manzon Rahama ne, Goggo tayi
maza ta ce, (S.A.W), rannan da naje wajen wa'azi
naji ana tarihinta na ce to in aka yi wa Adamu
haihuwar ya mace sunan da zan sanya kenan.
Goggo tana dariyar farin ciki ta ce ai kuwa dai
Mallam tunda suna ne mai daraja, ya ce haba don
ma ba ki ji tarihin nata ba."
Duk da nanata haihuwar tsululun damuna da
Ado yayi tayi, hidima sosai yayi min. Mutane da
yawa kuma sun zo, mafi yawanci matan abokanshi
ne da kuma yan uwanshi, nawa yan uwanne
kawai ba su zo ba, shi ne abin da ya dan rage min
jin dadi.
Amma duk da haka na yi wa sunan kwalliya ta
burgewa da ban sha'awa. Lesuna masu tsada guda
biyu da atamfofi super suma guda biyu gami da
shaddojin gezna na asali suma guda biyu, dukkansu
a dinke.
Dinki kuma mai ban sha'awa ya kawo min
gami da takalma da jakakkunansu designers, ki
145
zabi wadanda za ki yi amfani da su.
Na daga ido na kalle shi cikin natsuwa na ce
mishi ya ya zaka kwashi kudi masu yawa haka ka.
saya min irin wadannan kayan? Bai kula ni ba sai
kawai yasa hannu a aljihunshi ya ciro wata sarka da
yan kunne mai kyau English Gold.
Ya miko min ki shirya in ga kwalliyar taki
kafin in fita don Kaduna nake son atfiya, kan
maganar nan da nayi miki. Kar dai ki fasa yin
addu'a ko kina zaune na gayawa Inna ma ta kara yi
min addu'a na ce mishi to.
Sa'adatu ta shigo itama tayi kwalliya mai kyau
atamfar super ce a jikinta itama Adon ne ya bata
don tayi fitar suna.
Nayi kwalliya sosai na kuma yi matukar yin
kyau, shaddar na fara sakawa saboda dinkinta yayi
matukar daukan hankalina.
Nayi dauri mai kyau na sanya sarka da
yankunne, ga agogo da zobe tunda nazo Dabai ban
taba kwalliya irin na ranar ba, mutanen da ban basu
taba sanina cikin kwalliyar da ta dace da ni, tunda
shima Ado kananan zannuwa yake saya min sai ko
yau dinnan.
Ina cikin gyaran daurina Goggo Ayalle sai
kallona take yi tana fadin iko sai Ubangiji sai ga
146
Sa' adatu ta shigo Anti wai kizo ki nuna mishi in da
linka din shi suke na kwatanta mata ta tafi ta dawo.
To kije mana kawai ki bashi tunda ya ce sauri
yake yi zai tafi, nabi maganar ta Goggo na nufi
dakin nawa da na kwana bakwai ban shige shi ba,
komai a kammale sai kanshi yake yi a tsakar dakin.
Na samu Ado a tsaye shima yayi kwalliya rigar
da ke jikin nashi sabuwa ce sai kamshi take yi.
Yana ganina ya rage fara' arshi kai ke kam ko
wayo baki dashi can zan biyo ki dakin Goggo in ga
kwalliyar sunan naki?
Ya sake kallona cikin wani yanayi na sakin
fuska da murmushi alamar ya gamsu da abin da ya
gani, ya ce wannan ita ce asalin Humairar da Inna
ta bani ba wacce na kawo na ajiye a wannan dan
tsukakken dakin ba.
Nayi murmushi don in rama mishi wayan nashi
ya ji dadi, sai na ce mishi ba fa Inna ce ta baka
Humaira ba, Baba da Mama ne suka baka ita.
Ya sake fadada murmushin shi tare da jawo ni
jikinshi har dankwalin nawa ya fadi a kasa,
kankame ni sosai yayi a jikinshi kafin ya ce minni
Inna ce ta bani ke Aisha, ita ce tayi dalilin da ki ka
sallama min kanki.
Ita ce ta biyo mu Dabai da umarnin da take
147
bayarwa ne na samu nayi sa'ar samun zaman lafiya
a gidana don haka ni a wurina ita ce ta ba ni ke.
Muka yi sallama ya kama hanya ya tafi nima na
dawo dakin Goggon in da ake sha'anin suna,
Goggo sai bina da kallo take yi tana kokarin ganin
idona, ko me take son gani oho?
Suna da kwana biyu Ado ya dawo yana
dawowan yaje ya sayo wani katon rago ya kawo
gida aka yanka yasa aka soya ya zuba shi a cikin
kwalla wacce itama sayota yayi ya hada da katon
din minti na malta sweet.
Da katon din cingam Bazooka 200 da goro dan
takarda biyu da dabino mudu biyar da shadda yadi
goma-goma, guda hudu da atamfofin super guda
uku ya tashi Bala ya ce mishi yayi wa Sa'adatu
rakiya zuwa gida gaba daya kayan ya ce a kaiwa
Baba a gaya mishi shaddojin guda hudu.
Shi daya Baba Yahya daya, Mallam Liman
daya, Mallam Harisu ma daya, atamfofi kuwa
Mama daya Innata daya, Zubaida ma daya, sauran
kuwa akai mishi a gaya mishi na haifi Umahmah ga
kayan suna nan a rabawa Jama'a.
Sannan itama Sa'adatu yayi mata tata tsarabar.
Kwanan Bala uku a can maimakon daya ko
biyun da Adon ya ce mishi ya yi ya kuma dawo da
148
shatara ta arziki.
Jego mai kyan nayi mai kuma dadin gaske na
murje nayi gwanin sha'awa in ban da ina lissafin
kwana kin tafiya ta gida ma ina jin da nafi haka
morewa jegon nawa.
Rannan Ado ya dawo gida daga Danja a
lokacin nan kuwa kwanana arba'in ne har da uku.
Yana shigowa dakin ya nemi wuri a bakin gadon
da nake zaune ya kama kallon yarinyar da ke ta
faman bacci.
NI wannan yarinyar da wa tayi kama ne? nayi
murmushi na ce wah yasan mata, wasu suce da ni,
yayi maza ya galla min uban harara wadanda basu
san ka ma iso ba ko?
Nayi shiru naci gaba da abin da nake yi, to wai
ni ba kin yi arba' in bane me kuma kike yi a naan
dakin? Nayi murmushi na ce to ai ban gama
wankan ba Goggo ta ce sai na kara.
Wai wata biyu ba kwana daya zan yi zamu bar
wankan yau ne gobe mu tafi gida. Ya tsuke fuska
ya ce a'a ban yi miki wannan alkawarin ba, na dai
ce in kin yi wata biyu za ku tafi amma ai ba daga
nan dakin za ki tashi kiyi tafiyar ba.
Nayi maza na ce ban gane ba, ya ce to kar ki
gane, kina nufin haka zan yi ta zama? An gama
149
hakurin tsohon ciki an yi na zaman jego sai kuma
in yi ta zama ina jiranki sai kin dawo daga tafiya?
Ki gayawa Goggo za ki koma dakinki yau sai
muyi ko kwana bakwai ne tare in yaso rana itayau
ma kiyi tafiyarki, na sunkuyar da kaina kasa na ce
ba zan iya ba.
Ya ce