Showing 18001 words to 21000 words out of 35296 words

Chapter 7 - MIJIN TACE Book 3 Hausa Novels by hafsat Sodangi.docx

sosai da sosai, to ya ya

zan yi? Iyayenmu ne in naji maganarsu ko naji

tsoronsu nayi hakan ne saboda girma da darajarka a

wurina ba zan 1ya jayaiya da su.

Goggo ta ce, "Ci gaba da kin shiga girkin nawa

zai zamo sanadin da kowa zai 1ya warewa ya ce

83

baya ciki, in nayi haka kuma ban kyauta musu ba,

don wannan girkin nasu yana cikin alamomin hadin

kan gidansu.

Gaba daya suna ci daga tukunya guda, to sai

kuma in ce mata ba zan yi ba?

Shiru Ado yayi cikin nazari da tunani kafin

jimawa can ya dago ido ya kalle ni ba za ki iya

aikin ba Humaira ba, kuma zasu taya ki ba don

wannan haduwar da ki ke ganin suna yi kowadanne

suna taya 'yan group din su ne.

Ke kuma ba kya cikin na kowa, sannan cefanen

gidan nan ba karamin abu ba ne, ni kuma a halin

yanzu ba zan iya ba saboda a halin da nake ciki

kina gani sarai kullum kara maneji nake yi.

Ban yi miki bayani ba ne, don,ba ki yi magana

ba, ba ki kuma nuna min damuwar ki ba duk wani

abin da nake kashewa yanzu ba nawa ba ne,

rancensu nayi.

Hannu biyu na dora a kaina na ce rance? Bai

kula ni ba sai yaci gaba, to zan rinka cin bashi ne

ina yin cefanen da bai zaa min wajibi ba?

In suka yi hakuri ma ai nima ba zan bar abin

haka kawai ba, tunda duk masu cin abincin nawa ne

ba sai an ce min in yi ba.

Ni kam kuka na rinka yi saboda na tsani bashi,

84

gai nake tankar shi ne karshen fitina tunda naji

Malla mai babban Allo yana yawan neman yin

magans kan Hadisan da suka yi mini da gaggauta

biyanshi in har mutu ya cilka ana bin shi, kai ni kam

ban son bashi.

Kukan da nake tayi yasa Ado tsayawa yi min

bayani Ke bashin fa ba wanda za'a matsa min ba

ne wurin Haruna naje na karba wannan abokin

nawa da nace miki tare muka yi Secondary School.

Yana gamawa shi ayayenshi suka yi mishi aure,

har na ce miki yanzu matanshi uku da 'ya'ya birjik

yana kuma ta hidimarshi.

Duk da Ado yasha bani labarin abokinshi

Haruna na rowan bargo ban ji dadin bashin da yace

min yaje ya karba a wurinshi ba da nayi tunani

sosai ma sai na gane har 'yan atamfofin Nicharm

din da ya sayo min guda biyu yazo min dasu a

dinke, wai in dan sabunta a kudin da ya rantan ya

sayo min su.

Ke ba fa ni kadai ne nake cin bashi ba utane da

yawa ana bin su bashin da bai dadi shi ne wanda ka

karba bayan kasan baka da hanyar biya, ni kuwa

ina da shi.

Damuwar da ya gani a tare da ni ce tasa shi yi

min wannan bayanin, tabbacin da Ado ya bani na

85

bashi da halin da zai yi cefanen gidan nan in girkin

yazo kaina yayi matukar tayar min da hankali.

Duk da ni din ba mai yawan yin addu'a ba ce,

sai na dukufa nayi ta karanta wata addu'a da mai

babban allo ya bani ita, ya ce min addu'ar Nana

Aisha' ce (R.A) a kowanne lokaci.

Wani lokaci ma in na zauna ina yi na rinka

kenan sai Ado ya gaji da ganina a zaune ya sure

ya dora a katifa yana daiyar cewar da nayi mishi

mai babban allo ya ce min mai yawan karanta

addu'ar baya talauci.

Shi kuwa Ado sai ya ce nin, in ya kama sana'a

ko? Ko kuwa haka kavwai za su Zubo mishi? Ban

kula shi ba, iyaka dai ban daina ba.

Rannan mun tafi Makaranta da safe shi kuma

ya wuce gonarshi kan hanyar tatiyar tamu dai ya

bani tabbbacin a satin nan zai fara dibar masararshi

ya sayar ko da bata gama karasawa ba, tunda ba zai

sake zuwa wurin wani neman wani rancen ba.

Na ce mishi, to in dai ba ya zama dole ba kar

ya yi hakan, ya kara hakuri kawai

Na shiga aji ya wuce ya tati, ina aji ina tunanin

Ado, irin wahalar da ya yi wa gonarshi ya sonmna

diban masararshi a yanzu ba karamin asara ba ne

tunda ba duka ne tayi ba wacce tayin ma bata yi

86

wani kwari ba.

Ana tashinmu na fito ban ganshi a inda yake

jirana ba, na dan tsaya kadan ko zai karaso ban gan

shi ba naga za'a watse a bar ni ni kadai nia na biyo

hanya na dawo.

Ina bullowa lungun gidan mu naga wata

lafiyayyar mota a tsaye a kusa da Masallaci mai

lambar Abuja, ban sake kallonta ba, na wuco na

nufi cikin zauren gidanmu muka yi kaci6is da shi

Na daga ido na kalle shi har ya dawo yayi

wanka yasa T-shirt da wandon shi masu kyau

wadanda ma ba kasafai yake sanya su bayana kuma

kamshin turarenshi.

Ban san dalili ba sai naji haushinshi ya kama ni

nan take na soma yi mishi kuka, shi ne baka biyo

min ba ka dawo gida?

Ina kukan ina tambayarshi, to kiyi hakuri mana

Humaira, ki tsaya mana kiji abinda yasa nayi hakan

in ban da uzuri ba ki gamsu ba sai kiyi hakan ki.

Daga cikin dakin zauren nan na jiwo wata

murya tana tambayar Ado to kai tsoron kukan nata

ka ke yi ne?

Da gudu na fada dakin jikin mai babban allo na

kwanta shi da Baba Yahaya ne a ciki.

Mai babban allo ya ture ni yana fadin "Ke

87

matsa can ja'ira, shagwababbiyar wofi, kar ya baro

ki a makaranta ya dawo shi kadai akan me?

Duk tsiyarki da wayonki mata hudiu zai yi ba

da ke kadai zai zauna ba, nayi murmusha na cee

oho, ni dai nayi gaba, Baba Yahya ya taya ni

murmushin tare da fadin gaskiyarki Aishatu.

Na gyara zama na gaida Baba Yahya cikin

ladabi da girmamawa, yana kallona sai murmushi

yake yi alamar dadi ya kama shi.

"Karatu ki ke yi?" Na ce mishi "Eh Baba." Ya

sake wani murmushin ya kalli Ado Ubengiji ya yi

muku albarka ya rufa muku asiri ko in e ya kara

don ya riga ya rufa sai neman kari. Ado ya ce amnin

Baba.

Na kalli mai babban allo ina murrmushi "Ina su

Hajiyoyinki?" Ya taya ni murmushin tare da fadin

kalau din su, ba su ma san zamu zo ba."

Na sake kallon Baba Yahya na ce "Baba ba ku

gaya wa kowa ba ne? Baba Yahya ya ce, ai babu

wanda ya sani jiya da daddare ma da Yayanku yazo

nan gidan shi da Atika nayi kamar in gaya musu sai

kawai na fasa.

Nayi murmushi na ce dukansu lafiyarsu kalau

Baba? Ya ce kalau dinsu Aliya dai zata tai aikin

Hajji ita kuma Atika cikin dake gare ta yasa ba a yi

88

maganar tafiyar tata ba. Dadi ya kama ni jin alherin

da 'yan uwana suke ciki.

Na sake kallon Baba Yahya cikin natsuwa na

ce mishi oh Baba, ashe zaku zo dubani da sauri ya

ce zamu zo mana Humairah, zamu zo mana mu gan

ki.

Na kuma ji dadin zuwan da nayin ba kadan ba

nazo na same ki kina karatu, mijinki ya maida ke

makaranta don kiyi ilimi shi kuma naje gonarshi na

gani wannan noma da wannan yaro yayi ya wuce

abin mamaki sai abin tsoro.

Zuciya dai ita ce mutum, shi yasa Manzon

Rahma (S.A.W) ya ce, in ta gyaru dukkan jiki ya

gyaru, in kuma ta Baci to dukkan jikin ne ya baci.

Na dan yi murmushi saboda jin dadin

gamsuwwar da ya ce sunyi na ganinmu cikin natsuwa

na ce mishi Baba har kun je gonar ne?.

Mai babban allo ya ce ai mu ta can muka fara

don da muka yi tambaya gonar tashi aka kaimu, ai

mijinki ya zama sarkin noma.

Na sake wani murmushin daidai Ado ya sake

shigowa da wani kwanon a hannunshi.

Baba Yahya ya kalle shi cikin natsuwa daidai

yana ajiye kwanon ya ce mishi kai mu fa mun riga

mun koshi, wannan gaudan da ka kawo mana ba

89

cin wasa muka yi mishi ba.

Ai rabon ma da in ci gauda mai dadin na yau

har na manta matanmu na can ba su iya irin wannan

girke-girken ba.

Ina jin sun tsunduma hira da Ado akan maganar

gonar tashi nayi maza na nemi izininsu na shiga

gida naje na tube uniform dina na daura sabuwar

atamfata.

Na gyara nayi tsaf, na yafa sabon gyalena na

dauko abincin da na tanadan mana muci, in mun

dawo. Na hada da abin shan da nayi na ajiye cikin

randar kasa na dora a tire na hada dasu plate

cokali da kofuna, na dawo nayi sallaa a bakin kofar

suka amsa.

Na shiga na tsuguna na ajiye tiren mai babban

allo yana kallona yana cewa, amma ai kina jin

Babanki yana cewa sarkin noma mun koshi ko?

Ban asa mishi ba, na kalli Baba Yahya cikin

yanayin da zai tausaya min, na ce mishi Baba

wannan abincina ne da nayi da hannuna, kuci ko ba

yawa.

Nan da nan ya ce, zuba mana muci Aisha, nayi

maza na jawo plate-plate zan fara zubawa, mai

babban allo yana fadin "Ka ji wai tana jaddada da

hannunta tayi kamar hannun nata ya wani iya ko

90

kuma dabanne.

Ado yana murmushi yana fadin, kai dai bari ka ji

kawai Mallam.

Ina zuba musu abincin, Baba Yahya yana

kallona. Burabuskon gero ne da miyar taushen da taji

busasshen kifi da tantakwashi, sai kamshi suke yi

daga shi har miyar.

Na zuba musu a plate na zuba musu miyar sosai

na mika musu, Baba Yahya ya kai lomar farko ya

tsaya ya sosa kunnenshi da dan makullin motarshi

kafin yaci gaba da kai loma bakinahi.

Jimawa can, sai naji yana tambayata Ke da ki ke

sammakon zuwa makaranta Aishatu, da wanne lookaci

ki ke wannan girkin?"

Kan in yi magana Ado ya soma yi mishi bayani

har yana ce mishi ban cika gane ina wahala mai yawa

ba Baba, saboda Humairah wata irin yarinya ce mai

hakuri da juriya.

Duk abin da zata ji ta taimaki abokin zamanta shi

take yi, babu yanda za'ayi in dawo gida bata gamsar

de i ba, tana kuma tsusayin wahalata.

Matsalarta daya ce, Baba kullum a kanta muke

fada da ita, Baba Yahya yayi murmushi saboda ganin

rin kallon da Adon yayi min yasan zolayata yake so

yayi.

Ya ce, kishi ne da ita Baba kishin ma na rashi

91

hankali, in ba haka ba.... Mai babban Allo ya karbe

maganar, don haka Adon yayi shiru shia yana

sauraron shi.

Yayin da Baba Yahya yake ta faman murmushi,

ni kam tsuke fuska nayi na sunkuyar da kaina kasa, ai

duk tsiyarta sai kayi hudun nan don kayi biyu ma'ai

ba wani kokari kayi ba.

Kana girbe amfanin nan naka, ka samu wata

santaleliyar fara ka hada, kaga sai ya zama kana da

baka ga kuma fara ka kawo.

Baba Yahya yayi dariya ya ce rabu da su kin ji

Humairah ke dai ki kara kokari akan wanda mijinki

yake bada labari kin ji ko? Na ce, to Baba.

Na kwashe kwanuka na fita dasu na dawo don

yin sallama da su, ina durkushe Baba Yahya sai

faman sanya mana albarka yake yi, zan je in baiwa

uwarki labarinlku.

Na sake wani murmushin, kudi ya miko bandir

din Naira hamsin-bamsin guda biyu sababbi, "Rike

wannan ki rinka zuwa makaranta da su."

Nasa hannu biyu na karba nayi mishi godiya,

suka fita suka tafi ina leke ina ganinsu tsaye tare da

su Baba Tanimu da sauran mutanen unguwa.

Na koma na shiga gida ina ta murnar kudin da

Baba Yahya ya bani cikin zuciyata, ina fadin shi

kenan ajiye su zan yi in girkin ya zo kaina Ado ya

92

samu abin da zai yi cefane dashi.

Jimawa can sai ga Ado ya shigo murmushi yake

tayi, na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi sun tafi?

Ya sake wani murmushin ya ce sun tafi Humairah, ni

a rayuwata ko me zan cewa Baba Yahya? Oho! Nayi

murmushi na ce mutumin kirki ne amma Baba Yahya

kadai mai babban allo fa?

Yayi murmushi ya ce, dukansu Humairah, amma

Mallam ai kin san ganinki yazo yi, na ce ai haka

kace? To bari sai na gaya mishi.

Yayi dariya ya ce, "Yi hakuri." Na mika mishi

kudin da Baba Yahya ya bani, ina murmushi ""Ga shi

nan ka samu kudin cefane in girkin ya zo kaina.

Wani irin lallausan murmushi ya sake kafin ya

daga gefen katifa ya rinka fiddo min bandir din dari

bibiyu sai da ya ajiye guda biyar,

Zubawa kudin ido sosai nayi ina kallonsu, a ina

ka same su? Ya ce a ina na samne su kuma? Ban da

wurin Baba Yahya. Sannan ko mai babban allo bai ga

lokacin da ya bani ba.

Baba wani irin mutum ne mai iya martaba

mutum ya sake kallona cikin murmushi mashin zan

je in sayo mana don in hutar da ke tafiyar kafan da

kike yi zuwa makaranta kullum da dawowa.

Asabar da Lahadi kuma in dan rinka daukanki

muna fita kina ganin kauyuka da kasuwanni.

93

Na kalle shi cikin natsuwa na ce, ni na yafe kaje

ka biya bashin da ka karba in sun ragu ka rike don

cefanen abincin gida.

In gonarka takai kayi girbi in ka gama biyan

sadakin aurarrakin da zaka yi in wani abu ya ragu ka

sayi mashin din.

Yayi dariya ya ce, wai wa ya ce miki zan yi aure

ne? Na galla mishi harara na ce, uhun ba ina jin mai

babban allo yana ce maka kar ka yarda in tsufar da

kai ni kadai ba? Yayi dariya mai karfi ya ce, kai

Humairah! Ke kam ban san iyakacin kishinki ba.

Don haka yau bari in yi miki wani alheri tukuicin

zuwa mai babban allo gidana, in hutar da ke in

kwantar miki da hankali, don ki sakata ki wala kiyi

abin da ki ke so, aure ko?

Ya zuba min ido yana kallona cikin natsuwa da

walwala kafin ya ce a yanzu a wannan halin da muke

ciki ba zan yi shi ba, ban ce miki kwata-kwata ne ba

zan yi ba, a'a a wannan lokacin ne ba zan yi ba.

Don haka kar wata ta sake ce miki an ganni wani

wuri bani ba ne, in kuma lokaci yayi na in yin to ni

da kaina ne zan gaya miki.

Don ina fatan in yi ne a lokacin da ke da kanki za

ki gamsu da cewar eh, ya dace in yi in ba, wannan

halin na samu ba, ba zan yi miki kishiya ba Humairah

to me zan yi da ita?

94

Duk da cewar da nayi wa Ado kar ya sayi mashin

sai daya saya don irin na matasa, yana kawo mashin

din gida su Baba da su Goggo suka sa albarka ya

shigo ya ce min ki shirya in rana tayi sanyi za ki raka

ni Ruwan bago muje in kaiwa Mallam Haruna

kudinshi.

Daga nan kuma tunda yau ranar Lahadi ne sai mu

tsaya a kasuwar "Sundu' muyi sayayyar abin da ba

mu dashi na kayan abinci, na ce mishi to.

Da yamma na shirya nayi kwalliya da daya

atanfar tawa itama Nicharm ce amma nayi kyau

sosai, na yi wa mutanen gida sallama naje na dale

bayan mashin din Ado, wanda tunda na gan shi nake

ta faman murmushi.

"Ke ba ki san yanda tafiyar kafan nan da ki ke yi

yake ci min rai ba ne." Abin da yake gaya min kenan,

lokacin da na sa hannu biyu na kankame shi kamar

yanda ya yi min umarni.

Muka fara tafiya, sai da muka tsaya a Sundu

muka yi sayaiya muka ajiye a wata runfa muka wuce

zuwa Ruwan Bago.

Gidan Mallam Haruna, ni na shiga wurin

iyalinshi na shiga wurin uwargidan Hannatu, don

Ado ya ce min ita yafi sani, nan sauran matan suka

same ni muka yi hira da su, sai da ya gama ya aika a

kira ni.

95

A hanya muna dawowa Ado yana bani labari, kai

biyan bashi da dadi Humaira, kai da ka biya ka ji

dadi shima wanda ka baiwa ya ji dadi.

Balle shi Mallam Haruna ma bai dauka zan

maida mishi da kudin ba. Nayi maza na ce don me?

Ado ya ce mutanen yanzu fa ba wani damuwa da

biyan bashi suka yi ba.

Na ce, hu'un, ai kuwa dai suna daukarwa kansu

jidali.

"Kinga iyalin Haruna ko? Ga gidanshi ga

ya' yanshi gashi yana noman nan, yana kuma taba

kasuwanci. Komai nashi gwanin sha'awa ko? Na ce

ni ban sani ba, na dai san kawai bai fika komai ba.

In dai ba yawan matan nashi ba ne yake ba ka

sha'awa, to, to shi kenan mu bar maganar, na ce eh

gara mu bari.

Ana cikin haka rannan girki yazo kaina, kafin

zuwan ranar kuwa babu abin da Ado bai tanada ba na

kayan amfani, tunda ga bokitaye, robobi, kwanuka,

kore, ludaya, cokala suna kammale.

Ina tashi da safe na kammala ayyukan wurina,

nayi duk abin da zan yi na jira Ado ya dawo kamar

yanda yayi min umarni, gabana sai faduwa yake yi,

ina dai ta faman addu'a.

Kar fa ki ce za kije kiyi wahala mai yawa ga

buhun shinkafa can na kawo, in kinga ba za su

96

taimake ki ba sai ki juye ta kawai gaba daya, ki juye

mata abin hadinta akai in ta nuna za'a ci.

Nayi murmushi na ce mishi, to na fita. Ina fike

da tsintsiyar zabori a hannuna don share wurin yin

girkin, da kuzarina na fita sai dai ina dosar wurin na

susuce.

Tun daga nesa dai na hango buhun shinkafar da

Ado ya kawo a kwance a kasa, ga kwandon tumatur,

attaruhu, albasa da tattasai, ga galan din man gyada

da ledar maggi da su kori da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login