Showing 24001 words to 27000 words out of 35296 words

Chapter 9 - MIJIN TACE Book 3 Hausa Novels by hafsat Sodangi.docx

anje gida anga

Sa'adatu balle kuma aje ana mafarkin anje gida Baba

yayi kora da sanda.

Tsuke fuska nayi na ce, ai ni ba zan taba

mancewa da garinmu ba, kuma ma ai ta nan wurin ne

in da ba kauyen ba ne ta can wurinku ku kauye nel?

kan mu karasa gida muka yi fada da Ado, don haka

nan da na ganshi ya kafe mashin din a kofar gida na

ce ba zan sauko daga kai ba sai ya juya ya maida ni

Tukunya kamar yanda yayi alkawarin kai ni.

Ya soma rarrashi yaga alamar ba zan yarda ba,

sai kawai naji ya ce min, kine dai so ne kawai ki nuna

wa mutanen da suke zaune gindin bishiyoyin can

cewar eh da gaske ne kin fi karfina.

Kin ga sai suma su yarda da magánar da matan

cikin gida suke yadawa cewar ni din MIJIN-TACE

ne, ban sani ba ko Ado ya gane irin dukan da wannan

kalmar ke yi wa zuciyata ne in an fade ta yasa ya

gaya min hakan, don a firgice na sauko daga kan

mashin din na shige cikin gida, naje na tsaye bakin

kofa ina jiran yazo ya bude min in shiga.

Sai dai a gidan ban yarda kun zauna lafiya ba,

110

saboda na riga na gaji da yanda yake tsattsare ni yana

kokarin hana ni mu'amallah da kowa da kowa, har da

mutanen da nake tare dasu, wadanda matan yan

uwanshi ne.

Muna cikin wannan rikicin, Ado ya samu aikin

koyarwa a Makarantar Secondaryiyanmata ta

DANJA', shi kenan sai murnan samun aiki yasa

muka shirya.

A farkon samun aikin murna nayi ba kadan ba,

saboda ni da shi addu'a sosai muka yi akan aikin,

saboda irin bayanin da ya rinka yi min cewar, aikin

koyarwar shi ne aikin da yafi so a wannan lokacin,

saboda irin alherin da ke cikinshi.

Za ka koyar da yara mutanen da suke sune za su

girma, su zama al'uma ta gama shi a wurinshi babu

wani aiki da yafi koyarwa dadi, da kuma

muhimmanci aikin ne mai lokaci ga kuma. lokuta

daban-daban na hutu wanda zaka iya aiwatar da wasu

l'amuran naka da basu shafi Makaranta ba a lokacin.

Koda dai a wannan lokacin da muke ciki, ba

wani muhimmanci hukuma da wasu Jama'ar gari

suke baiwa Malami ba, shi a wurinshi darajar Malami

ba sai wani ya ce gata.ba, tunda Ubangiji da kansa ya

girmama shi.

Irin wadannan kalaman nashi ne suka kara cusa

min son aikin nashi, amma yana farawa ba a dauki

111

wani lokaci mai tsawo ba na gane ba sakandaren

'yanmata ba ne ta kamata a tura min mijin mawa ba.

Don ba a je ko ina ba na soma gani wasikun

yanmata da hotunansu a cikin Jakarshi ga waya akai-

akai, ga text na kalamai masu dadi irin ma wadanda

ban taba jin su ba.

A farkon al'aarin yana rarrashina ya gaya min

kalamai masu dadi da yake rage min 6acin raina,

amma daga baya sai kawai ya daku wai shi ba zai

dauwama kan rarashi da ban baki kan matsala guda

daya ba.

Don haka hanya mafi sauki ta neman zaman

alfiya kawai in daina yi mishi bincike in daina taba

mishi jakarshi ta zuwa aiki da kuna wayarshi in ban

taba su ba ai ba zan ga abinda ke ciki ba.

Kan ka ce meye wannan kuma sai ya fito da wata

ka'ida ta cewar, wai shi din tafiya tana yi mishi

yawa, kullum sai yaje Danja yayi aiki ya dawo

Dabai.

Don haka ba zai juri hakan ba, wahala tana yi

mishi yawa, maimakon ace kullum yana zirga-zirga

kan hanya da safe da yamma zai maida tafiyar tashi

ta zaa ranar Litinin da safe.

Ba zai dawo ranar ba sai ya kwana ya bada

darussanshi na ranar kala ta in an tashi sai ya dawo

ya kwana a gida, sai washegari aba ya koma da

112

safe ya kwana ranar ya wayi gari a can Alhamis in ba

shi da wani darasi na ranar Juma'a to ranar zai dawo.

Ba zai sake komawa ba sai ranar Litinin in kuma

yana da shi Juma'a to sai in yi hakuri sai Juma'ar zai

dawo.

A farkon bayanin nashi banga wani abin damuwa

a ciki ba don yayi min bayani sosai kan wahalar

zirga-zirga a hanya amma yana fara aiwatar da abin a

haka mutanen gida suka gane shi kenan sai aka soma

kace-nace.

Ya samu wata a can kenan ya ajiye, nan da nan

hirar gidan ta koma hirar mazan da ke ajiye mata a

waje, wato matan banza.

Cabdi! Ai gara mana irin namu mazan da ke

shigo mana da abokan zamanmu cikin gida suci daga

abinda muke ci, shi din kuma gashi nan a tsakaninmu

ya dai ishemu muna kuma kallonshi.

Amma matan banza hidimar da ake yi musu ai ba

irin ta nmatar gida ba ce, ga kuma ciwace-ciwacen nan

na zamani."

A wannan lokacin in na ce bana cikin tashin

hankali to nayi wa kaina karya, gashi dai a wannan

lokacin nayi matukar wadatuwa da abubuwan

rayuwa, komai da Ado yasan zan bukata ko zai yi

min amfani kawo min yake yi.

Albashinshi na farko ma da aka fara bashi saboda

113

anyi mishi biyan na wata uku ne gaba daya kamar

yanda all'adar aikin Gwammati take, kananan atamfofi

masu saukin kudi masu kyau turmi goma ya saya

min.

Ya bayar duka aka dinke min, dinki kuma mai

kyau ga takalma da gyalulluka da under wears, a

wannan lokacin kuma tuni ya canza min tsarin

abincina, a kowane lokaci ban rabuwa da madarar

fulani da shi yasan inda yake zuwa ya samo ta.

Bana rabuwa da naman kaji, bana rabuwa da

kayayyakin itace dangin kankana, gwanda, inabi,

lemo, ayaba, in zai kawo kumá masu kyau zai kawo

min. gashi kua ya tsare mnin girkin gidan.

Kullum ya zagayo kaina ko baya nan Furerah

zata yi don zai sa a kawo mata kudin cefanen ya ce

tasa a sayo wanda ta mafi son hakan.

Jikina yayi matukar yin kyau saboda yana samun

nau'o'in abincin da ya dace ya samu, amma na kasa

yin kiba in maida jikina ya zama kamar asalin yanda

nake kafin zuwan mu.

Sai ma kara ramewa nake yi saboda kullum a

cikin fargaba nake. Ni kuma gashi duk da wadatar da

Ado ya samu ban koyi adana ko kwabo a dakina ba,

hamsin-hamsin din da su. Baba suke bani yana ganin

sun taru zai sa hannu ya kwashe in ma bai diba ba in

dai ana zaune kalau ni da kaina ma zan ce mishi ga

114

Su.

Sai a lokacin da raina ya soma baci ne zan rinka

ganin ina ma adana abina nake yi da nayi amfani

dasu na tafi gidanmu.

Rannan abin ya ishe ni, bakin cikin Ado yana

nema ya maidani wata iri Alhamis ya zo bai dawo ba

na zuba ido ban gan shi ba cikin zuciyata na ce to

watakila sai Juma'a kenan.

Yayi sammakon dawowa don wani lokaci yakan

yi hakan sai kawai naga Bala da sassafe ya kawo min

cefane wai a gaya min sai gobe zai dawo ya tsaya

daurin auren Jalo.

A zuciyata na ce tafdijam! Wato ni babu abin da

nasan darajarshi irin ciki, don haka cefane na gashi

nan an kawo min babu fashi shi sai sanda yaga dama

zai taho.

A cikin gida kuwa rannan maganar da su

Ruwailah suka wuni suna yi kenan, amma akan wai

ban da ni ake yin hirar ba tunda ni da 'yan dakinta

ma ba wata doguwar magana ke hada mu ba.

Don ko nayi musu a lalace suke amsa min, ko a

yanzu da rashin Ado ke sani zaman cikin gidan wani

lokaci da sauran mutanen gidan muke hira, amma

yan dakinta ta hana su kula ni.

'Ko da yake dai nima ko da baya nan din na stare

dokarshi ta shiga dakin mutane, bana shiga dakin

115

kowa. Ina jin ta a gindin bishiya tana fadin au, to shi

namiji don ka tsare shi ka hana shi yin aure ai ba

wata birgewa ba ce.

In har baka hana shi ganin na banza ya ce yana

So ba, ta tsirtar da yawu nuna alamar kyaa, ta ce ni a

yanda nake da kyaman nan ai ba zan 1ya zama da

manemin mata ba.

To me zan yi da shi? Ai komai zai bani gara ya

bar shi ya tsare min mutuncin kanshi kawai yafi min,

ni nayi sana'ata in nemi abin da zan rufawa kana asiri

dashi.

Sannan abin tsiyar shi ne, sma kara kullewa a

can tana karakwace maka shi. In a farko kana

ganinshi şau uku a sat sai a koma biyu sai a koma

daya wani satin ma sai ka ji shiru.

Ai gara a hada mu mu hudu a gida kishiya dai

kowacce tazo Ubangiji zai bani hikima da basirar

zama da ita, in ta kunso wani abin tsiyarta ma a wayi

gari ya koma mata kanta ko ya kare tsakaninsu can

musu ita da wanda ya kawo ta, aifa kam- aifa kam

abin da yan amshin nata suke fadi kenan.

Rannan da daddare Inna ce na runtsa ta karya na

yi wa kaina. Washegari tun safe Ado ya dawo ya yi

sa'a kuma a wurina yazo ya same ni ban riga na rufe

na tati wurin hira ba.

Karbar da nayi mishi bata wani ba shi sha'awa

116

ba baki da lafiya ne? na kalle shi da gefen ido na

tambaye shi me ka gani? Yanayin ki ne na ganshi

wani iri.

Na ce ta dauro ne ka ganshi a haka ka kuma san

daurowa take yi a daure AIkali. Ya ce haka ne, to ga

leda nan nazo da shi juye abin da ke ciki don ba zai

juri zafi ba.

Na mike kamar zan juye abin da ke ledar na

wuce na tafi tsakar gida abin ban sake dawowa dakin

ba. A tsakar gidan kuma sai tambayeta ake yi ana

fara'a ashe maigidan ya dawo?

In ce eh sai ace kai madallah, hannunshi da

zuwa. Ina nan wurin a. zaune sai ga Ado ya shigo

suka gaisa da matan duka ya kalle ni cikin natsuwa

ya ce min zo mana Hunmaira, na ce to.

Na tashi na bi bayan shi don komai yaya ba zan

iya wulakanta mmijina a gaban wani ko wasu ba.

Muna shiga ya kalle ni ya daga ido ya kalli

agogo sannan ya sake kallona ya ce min, kin ga

wannan abinda ki ka yi min na farko kin yi min kuma

na karshe kin gane? In dawo daga wani wuri baki

karbe ni ba baki yi mi abida ya dace kiyi min ba.

Ki tafi ki bar ni awa guda minti sittin ina zaman

Jiranki, na yau din ya zama na karshe kar ki sake. Na

ce Inna sake din me zai faru? Ko me zaka yi?

Ya ce to ki sake mana ba ga ki ba gani? Na juya

117

da nufin sake fita, yayi maza ya kamo ni ya murde

min hannu, nayi karfi hali ban yi irin ihun da nakan

yi ba alamar na riga na saba da wannan wahalar.

Kar ki neme ai da fitina Humaira, bana so. Yana

ta nanata kalmar alamar bai son fadan da ya gane ina

so muyi. A zuciyata na ce ya san ba shi da gaskiya.

In wani abu nayi miki a laifi ki gaya min bai

zama min komai ba in ba ki hakuri ke kin san na saba

hakan bani da wannan girman kan me nayi miki?

Kullum naje aiki na dawo sai kin yi min sanadin

bacin rai?

Saboda kawai bana gida kina shiga cikin matan

da suke cusa miki ra'ayin da ba naki ba suna koya

miki abinda bai dace ba, wanda ban taba zaton zaki

yi haka ba, ke da ki ka girma a gida irin naku ki ka yi

karatun boko da na addini har yanzu ma kina yi.

Amma wai wadannan matan ne suke koya miki

abinda za ki yi wa mijinki.

Kalamanshi suka sanya ni bude baki na ce mishi

ni babu wata wacce take koya min wani abu,

halayenka da dabi'unka ne kawai suka gundure ni.

Ya dan saki fuskarshi kadan alamar bacin ran nashi

ya dan ragu.

Yana kallona cikin natsuwa ya ce wadanne a

Ciki? Ko duka? Ban amsa ba, sai ya ce to tunda ma

halayena ne matsalar ai duk ta kwana gidan sauki,

118

tunda ba cusa miki wani ra'ayi a kaina ba

Magana kawai zaki yi ki ce min Ado ko Kawun

da ki ke kirana halinka kaza-kaza da dabi'arka iri

kaza da iri kaza basu min ba, ka canza sai in ce miki

to.

In kuma canzan tunda ke ma sheda ce ni mutum

ne mai saurin canzawa daga wani matsayi in koma

wani ko daga wani hali zuwa wani duk ina iyawa,

don haka mu bar wannan maganar yanZzu anjima sai

muyi ta.

Yanzu zo kiyi min tausa in dan ji dadi in

wastsake gajiyata ta wannan satin kin kuma san

wannan karon kwana hudu nayi bana gida,

maimakon daya ko biyu da nakan yi.

Ko kallonshi ban yi ba kaina a sunkuye na ce

mishi can inda ka baro ba. ayi maka tausar ba ne?

maganar da nayin tayi matukar dukan Ado watakila

bai taba zaton ina yi mishi irin wannan zargin ba, ni

ayi min tausa a inda na baro Humairah me ki ke nufi?

Kina yi min mummurian zato ne? na ce kana yi

wa kanka, dai in ba haka ba me yake zaunar da kai?

Me yake tsareka daga dawowa gidan ka? Rikici sosai

muka yi saboda ranshi ya kai matuka wajen 6aci da

zargin da nayi mishin.

Amma duk da haka yayi kokarin hadiye fushin

shi ya zaunar da ni don yayi min bayani.

119

Tafiya nake yi Litanin in dawo T'alata in koma

Laraba in dawo Alhamis ko Jumaa in kin yi lissafi

da kyau za ki ga sau biyu ne kawai ko uku ba na

kwana a gida a sati.

A haka kuma kullum kina ganina ko kuma kiyi

fashin ganina sau daya to menene? Na kuma gaya

miki a gidan abokin aikina iro nake kwana wannan

satin kuma jalo ya kara aure na tsaya tunda mune

abokan ango.

Na ce gaskiya ban yarda ba sai dai cikin biyu ka

zabi daya ko dai ni in bika mu koma can ko kuma

kullum kaje ka dawo cikin natsuwa ya ce min ba zai

yiwu ba.

Humaira kina karatu kina aji shi da ba za ki bar

karatunki ba, sannan a can din ma ai ba ni da in da

zan ajiye ki sannan ni in yi ta wahala ina ta zirga-

zirga akan hanya ba za ki tausaya min ba, saboda wva

nake aikin nan ne? nayi maza na ce mishi idon ni ne

ka daina.

Gaba daya ban karbi rarrashin da Ado yayi min

ba, ban kuma yarda mun shirya ba, naja na tsaya kan

cewar sai lalle wannan karon nima ya bar ra'ayinshi

ya dawo nawa, tunda ni nayi mishi hakan wane dubu

wane dari bafulatani ya ce wai cabiyar din cegiya?

A haka yayi kwana biyunshi ya koma ban yarda

ya taba ni ba.

120

Ranar da ya tafi Litinin na zuba idon ganin

dawowarshi da yamma don in ga ya bar nashi ra'ayin

ya bi nawa, ko bai bi ba? Bai dawo ba talatan ma da

ya saba dawowa da yamman bai dawo ba, bai kuma

aiko da cefanen da ya saba kawowa a ranar ba.

Kamar yanda ya saba yi in zai yi fashin zuwa sai

ya tashi wani ya ba shi duk abinda ya saba zuwa min

dashi ya kawo mnin, ya kuma yi min bayani. To

wannan karon shiru ban ga Ado ba.

Sai ranar Alhamis da yamma, don haka ni kuma

ina zaune a dakin ina jin shigowarshi, amma ban

daga ido na. kalle shi ba, balle in yi mishi wata

magana. Tun bayan sallamarshi da na amsa wacce

itama don nasan amsatan wajibi ne yasa' nayi hakan.

Ban sake daga ido na kalle shi ba, balle in ce

mishi kaci kanka, kusan minti goma yana zaune bai

ce min ba ban ce mishi ba, sai naga ya mike ya fita

kamar zai je ya dawo ne.

Nima na mike nayi abubuwan da zan yi, ban

shirya ba shi abincina ba don haka ban ma shiga

kicin don yin girki ba.

Shiru ban sake ganin Ado ba har wajen karfe

takwas na dare, sai kawai ga Bala da manya-manyan

ledoji guda uku rike a hannayenshi, wai gashi ki duba

abinda babu ki fada aje a kar6o.

Na leka cikin ledojin, daya kayan shafe-shafena

121

ne sai su Sheltoze da Room freshner da su izal da

Detol, kayayyakin amfani dai da suka dangane

wannan, daya ledar ta kayan Tea ne madara Nido

babban gongoni da Bounvita shima babba sai kwalin-

sugar guda biyu.

Dayar kuwa nama ne da kifi, na kalle shi cikin

natsuwa na ce mishi shi fa? Wai don in san in da ya

tsaya yaje na raka shi yaje ya duba aikin lambunshi

daga can sai ya ce in raka shi tasha ya shiga mota ya

tafi Danja.

Kan uba, abin da nasan na fadi kenan, kafin nayi

maza na rufe bakina, saboda tsayuwar Bala a dakin.

Za'a karbo miki wani abu ne? na ce mishi a'a, jeka

kawai.

Yana fita na ce me zan yi in ba kuka ba? Kwana

nayi idona biyu ban runtsa ba, nayi kuka har na gaji,

nayi bakin ciki irin wanda ba zai kwatantu ba, wunin

rannan ban fita ko 'ina ba, ina kwance a dakina ko su

Goggo ban je na gaishe su ba sai da suka ga shiru ne

suka biyo suka gaishe ni a cewar bani da lafiya.

Sauran matan gidan ma suka yi ta zuwa, amma

don fitina wai sai da Ruwaila ta gane lafiyata kalau,

ina jin ta tana gayawa wata da suka zo duba ni tare

cewar, kalau dinta, bakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login