Showing 6001 words to 9000 words out of 35296 words
Chapter 3 - MIJIN TACE Book 3 Hausa Novels by hafsat Sodangi.docx
karamcin mutanenta
ba sai na gaya miki cewar mutanen da suka san
Dabai din da irin halinta suna yi mata kirari da
cewar ce Dabai dabaibaye bako, maida bako dan
gida ya manta garinsu, ta magaji mai alamar samu.
Ban taba tankawa Ado maganganunshi ba
tunda muka baro gida, don haka wannan ma ban
amsa ba, na dai san kawai yana son garin nasu da
kuma jihar tasu ta Katsina don yanzun nan ne zan ji
ya ce wa Mallam Haruna a'a ai mu nan Katsina
babu wannan, to ban tsananta jin mamakin shi ba,
don kuwa nima ina son jihata ta Bauchi da garinmu
na Giyade da kuma unguwarmu ta Nasarawa
30
Jahun.
"Rage tafiya sosai Mallam Haruna ka kumna
sanyawa na baya alamar barin hanya nan gabanka
kadan ta gefen damanka akwai hanyar da ta shiga
ciki, ita za ka bi." "Yan daidaikun mutane ne a waje
saboda dare ya riga yayi nisa, amma mafi
yawancinsu Ado yana shaida su alamar dai bai taba
rabuwa da al'amuran garin nasu ba.
"Bi ta nan gefen kayi dama sosai, akwai
katuwar bishiyar kuka, ta gefen ta zaka wuce kiyi
yamma irin bayanin da Ado ya rinka yi kenan har
muka iso inda yace to, ga Masallaci can fari nan
kawai zaka tsaya.
Muna tsayawa Mallam Haruna yayi murmush
ya ce, "Kai Mallam Ado kasan garin nan Ado ya
taya shi murmushin ya ce, garina ne fa, ga ruwa
nan a randa ga lbandaki can gefe in zaka taba ruwa
bari mu shiga in fiddo maka da abinci."
Mallam Haruna yayi maZa ya ce, kai ai ni a
koshe nake, a dai bani wurin kwanciya kawai.
Ado yasa hannu ya dauki jaka guda daya dakke
bayan motar ya rataya akan kafadar na kuma san da
ita kadai ya iso garin ya tasa ni a gaba muka nufi
cikin gidan, muna fita daga zauren wanda babba ne
sosai ga kuma wani daki a cikin shi.
31
Sai ga wani shamaki da ya shiga tsakanin
mutanen zauren da ganin cikin gida daga bayan
shaakin hanyoyi ne da suka nufi sasan da ke gidan,
gaskiya ne girman gidan su Ado ya wuce a tsaya
yin bayani.
SW Kinga ga hanyar sasan u nan, wancan sasan
Baba Halliru ne shi da 'ya'yanshi wancan na Baba
Ubangida shima shi da nashi ya'yan wancan nasu
Baba Tukur ne shima da nashi iyalin mu dai je
kawai yanzu ba za ki gane komai ba sai an kwana
biya kin gane kan gidan da mutanen ciki tukuna. A
zuciyata nace hu'un.
paR Muna dosan sasan da ya ce min shi ne nasan ya
kwala sallama sai kawai naji wata murya ta asa
daga cikin wani daki tana kuma tambayar Adamu
ne a cikin tsohon daren nan? Yayi murmushi ya ce
mishi eh Baba, mutumin da Ado ya kira da sunan
Baba ya fito rike da sanda a hannunshi ba dai don
tsafi kam sai dai ko don wani dalili don da
karfinshi na ganshi.
Yana ganina yasa hannu ya rufe baki nuna
alamar mamaki da wannan yarinyar ku ke tàfe? Ya
ce mishi eh Baba, sannu da zuwa Aishatu, nima
nayi ta amsawa don girmamawa.
Kaga halin mata ba? Sufa babu wani babba
32
babu yaro a cikinsu, in ka biye musu kunya za su
baka. Ado yayi murmushi ya ce, me ya faru Baba?
Ya ce to ai uwar taku bata nan tana can taje
Kauyensu na Tukunya zata kwana saboda yau ana
kamun wata jikar su, in ban da rashin hankali irin
nata da nima na biye ta shi babba yana yin nesa da
wurinshi ne tunda ya san yana da baya da yawa.
Ado ya ce, ai babu komai Baba, Baba yaja tsaki
ya ce, in ban da lalura irin ta girma me za'ayi da
zaman mace daya ne?
Ado ya sake wani murmushin ya ce ai
Humairah ba gobe zata tafi ba, ba kuma jibi ba,
zata dawo ta same ta babu damuwa, ya ce auto shi
kenan amma ai ba dai haka aka so ba.
Makullin dakin nan a kusa yake ni ko Baba?
Baba yayi maza ya ce, eh ai cikinshi nake wuni
tunda sorona ya fadi, ya ce haka ne fa Baba an gaya
min soronka ya fadi ya bude dakin muka shiga,
komai a gyare yake a kintse, dakin yasha leda ga
katifa timemiya a shimfide ga kujerar kwanciya
can gefe akwati ne shia mai kyau a rufe na tabbatar
komai na cikin dakin na Ado ne.
Muna shiga ya sauke jakar kafadar shi ya bude
ta ya fiddo fitilar chaji ko batir ya kunnata ko ina
ya dauki haske sosai.
33
A to, tunda ka ki ka sanya mana wutar lantarki
a gida mu ma mu rinka ganin haske irin naka na
birni, ai ka rinka yawo da fitila a Jaka, wata mata
ce da ta ja ta toaya a bakin kofa tayi wannan
maganar tana ganin dakin ya gauraye da haske
kuma ta karasa shigowa cikin dakin ta durkusa
kamar wata karamar yarinya.
Da gefen Adon ya harareta ya ce, mijinki fa me
ya hana shi jawowa? Tayi murmushi tare da
langabar da kai ta ce waiyo bai da shi ne, ya ce eh
bai da shi, amma ai a hakan yake iya karo aure ko?
Ta sake wani murmushin kafin ta sake cewa
waiyo!! wannan ai rabo ne.
Ado yayi maza ya ce, haka ne. Tayi maza ta
kalle ni cikin fara'a, kin ga rabu da mijinki kin ji ke
dai sannu da zuwa abinki na ce mata yauwa, na
kuma fara gaisheta saboda ganin zata iya girmana
da shekarun da suka kai tara ko ma goma.
Kai gani kafin ki fara tambayar mutane abin da
za su ci don ke aikinki kenan tayi maza ta sake
langwabewa ta ce ehhhyi, ni ai cin ne sna'ata, sai
in ga kamar kowa ma haka yake.
Yayi maza ya girgiza kai ya ce a'a ke kadai ce,
ta ce au to, to na ji to ku da wanne ku ke farawa?
Ya ce wanka don ba ki iya karbar baki ba ne yasa
34
ba ki gane hakan ba, ta ce au to to naji zan gyara ko
da yake dai munan da yake mu yan kauye ne ci ne
gaba da wanka ya ce, eh to ai kin san mu 'yan birni
ne, ta ce haka ne.
To bari in samo ruwan zafi nan da nan ta fita,
tana barin dakin ya daga ido ya kalle ni cikin
natsuwa ya ce min Ruwailah kenan, matar yaya
Jafaru ce ai kin san yana yawan zuwa wurina, na
gyada kai nuna alamar na gane shi, ya ce to shi ne
babban wanmu a nan sasan shi ne dan Baba
Tanimu na farko wanda yaje ya karbar min aurenki
amma ai kin san ni ni kadai ne wurin mahafina ko?
Na girgiza kai a hankali, nuna alamar ban sani
ba, ya ce to ni kadai ne. Ya ci gaba da abinda yake
yi na kaye-kaye da gyare-gyare tanfar dai ba a cikin
dare muka shiga dakin ba.
Ruwailah ta dawo da ruwan zafi a bokiti da
wani kuma a flaks dinta da ta dauka a dakin, ga
kuma wani kunshi cikin leda da ta ajiye a gefe, wai
yana yi muku sannu da zuwa.
Ado ya yi tsaki ya ce, kai ke kan ba ki da kirki,
yanzunnan sai da ki ka tashi bawan Allahn nan a
cikin tsohon daren nan ki ka yi sanadin fitarshi
waje? Ta ce, oh oh, ba ma a wurina yake ba, to
amma da bai fitan ba da wa ya sauke maka
35
mutumin da kazo dashi din?
Ado ya rike baki nuna'alamar mantuwa, ya ce
na shagala ina kallon Humaira, kin san ni in ina
tare da ita to sunana ne kadai ban iya mancewa da
shi.
Ruwaila ta kyalkyale da dariya ta ce, ai kuwa
dai ma kayi kokari tunda ba ka mancewa da sunan
naka a nan sanu.
Sabon soso da sabulu da brush da abin wanke
baki da sabon tawul ya fiddo daga cikin jakar tashi
ya miko min na karba nabi bayan Ruwailah da ta
daukan min ruwam muka je ta nuna min ban dakin.
Na dawo daga wankan na samu kwanukan
abinci iri-iri, ya kalle ni ya ce min wannan kunshin
na gasasshen nama ne Yaya Jafaru ya sayo miki, ga
furar da Baba ya bayar da nono Ruwailah ta dama
miki, ga kuma tuwon dawa miyar kuka shima mai
dumi ne ta dumamo da wanne za ki fara?
Na ce kowanne, ya kalli Ruwailah da ke ta
faman bubbude min kowanne in gani ya ce mata ba
kin gama naki ba, to kije mana kuma sai da safe, ta
ce am wai jira nake yi ta gama mu tafi can wurina
ta kwanta.
Yayi maza ya ce, wasa kenan, tabar dakin
mijinta da mijin nata a ciki taje ta kwana a wannan
36
tsohon dakin naki? Ta ce, to ai shi kenan sai da safe
Amarya. Nayi murmushi na ce mata to ki huta
gajiya.
Tana fita Ado ya kalle ni ya ce wannan
atishawan da kike tayi fa don kin yi wanka a bayan
gidan da babu rufi ne baki saba ba, ban amsa mishi
ba amma cikin zuciyata nima na yarda hakanne don
maimakon in ji dadin wankan da nayi sai naji
kamar sanyi ya kama ni.
Naci tuwo sosai don yayi min dadi laushinshi
da dankonshi yayi banban da irin tuwon da na saba,
nasha ruwan tea mai cçitta naci nama kadan na
gyara na kwanta bayan na shafa mai nasa rigar
baccina wanda itama shi yazo da ita.
Na kalle shi cikin natsuwa nayi mishi magana
wanda tun fitowarmu ban yi mishi ba saboda na
gane babu komai cikin jakar tashi in ban da
kayayyakin amfanin da ya saya saboda ni na ce to
da ban biyo ka ba fa yaya zaka yi da kayan nan?
Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce, ban taba
daukar za ki iya kin bina ba, na dauka ke ma kina
sona.
Muna kwance ni da Ado akan katifar yana
gefenshi ina nawa sai dai mu dukanmu babu wanda
ya samu yayi bacci, ya daga ido cikin natsuwa ya
37
ce min Humairah ba ki ga kamar kasa yin baccin
nan da muka yi alama ne na muna jin marmarin
juna ba?
Nayi maza nace mishi, a'a bana ji ya sake daga
ido ya kalle ni ya ce, to ai ni ina ji, nayi maza na
tsuke fuska na ce mishi ba fa na zabi biyo ka da
nufin in biyo ka ba ne.
Cikin natsuwa ya ce min ai na sani, na sake
tsuke fuska na ce, to ko da na biyo ka akan
kuskuren ba zaa zan yi ba, komawa zan yi. Ya sake
cewa na sani, ya sake saurarawa ko zai ji zan sake
fadin wata magana, sai yaga nayi shiru.
Sai naga yayi murmushi kafin ya ce min to
amma ai ko za ki koman tunda ba ki kai ga tafiyar
ba ai ina ganin ba zai hana in nace nayi marmarinki
kiyi min yanda ki ka saba yi min bä ko kuwa. Nayi
maza na kara tsuke fuska, kafin na ce mishi a'a, ya
ce to shi kenan sai da safe.
Washegari tun safe Goggo Ayalle ta dawo
gidan a dalilin aiken da Baba Tanimu yayi na a
dauko ta, tana dawowa kuwa ta maida ni dakinta,
wunin ranar har dare ban gane na gama gaisawa da
mutanen gidan nan ba saboda yawansu.
Don haka kowa na gani kawai sabuwar
gaisuwa nake yi mishi, sai in shi ne ya ce min ai
38
dazu mun gaisa in ce mishi to.
Karba sosai Goggo Ayalle tayi min, ta yi ta ina
taka saka dani, komai hannunta ya kai kan shi in
dai ta daga taga naci ne miko min shi take yi, ungo
ki ci, sai in ni ce naga zan kwari kaina in ce mata
na koshi.
Sau goma kuma in ta kalle ni zata yi murmushi
ta ce, oh haka rabo yake har da rabon aurenki cikin
al'amuran da suka kai Adamu garin nan suka
zaunar dashi, kin san shi rabo ba karamin al'amari
ba ne.
Sai kawai nima in taya ta murmushin da take
yin sai dai ban ce mata komai, can anjima kuma sai
ka ji tana sake tambayata in ce ko dai manyan duka
lafiya? In sake cewa lafiyarsu kalau, tamfar dazu
bata tambayí lafiyar tasu ba.
A haka muka wuni har dare ina idar da Sallar
Isha'i ta kalle ni ta sake nuna min gadon da na wuni
akai ta ce min hau kiyi barcinki ki huta gajiya, kar
yan hiraa suce zasu dame ki, na ce to. Na sake
dalewa gadon nayi kwanciyata, zuwa can naji Ado
yana kirana, nayi kamar ban ji shi ba, ya matso
kusa da kofar Goggo yana tambayarta.
"Goggo Humaira tana kusa ne?"
Goggon tayi maza ta sauka daga nata gadon ta
39
leka tana tambayarshi wani abu ka ke so ne
Adamu? Ya ce a'a Goggo, sai da safe. Abin da
kawai ya fada kenan sai na jiwo Baba Tanimu daga
dakinshi yana fadin "Yau ga wani al'amari, wannan
fa shi ne girman kwabo.
An gira ba ayi hankali ba, yaro yana kwalawa
matarshi kira kina ji tayi shiru ba kiyi mata magana
ba, ya taso yazo har kofar dakinki yana tanbayarki
ita kin ce wai in wani abu yake so ya gaya miki, to
in ita yake so fa?
Na ce in yana da bukatarta ne ma ya gaya
miki? Goggo tayi maza ta ce au, to ai bangane ba
ne. Ke Aisha tashi-tashi je ki maza mijinki yana
kiranki."
A kan dole ta fito da ni daga dikin na shiga
dakinmu na samu Ado yana zaran jiran shigowan
nawa, gasasshiyar kaza ne a gabanshi, a gefenta
kuma flaks ne na ruwan zafi, ban kalle shi ba na
wuce na hau katifa nayi kwanciyata, ya biyo ni da
kallo fuskarshi ta bayyanar da rashin jin dadin shi
kan yanda nayi.
Yayi karfin hali ya hadiye fushinshi tashi mana
Humairaa nayi kamar ban ji ba, yayi tayi min
magana nayi shiru kamar ba dani yake yi ba, ke ni
fa kin san bana son irin wannau wulakancin na ayi
40
tayi miki magana kina yin banza da mutane, ban
tanka mishi ba, ban san yanda aka yi ba sai kawai
naji ya cafko hannuna ya murde.
A firgice na kwallara kara saboda zafin da naji,
na kuma yi maza na kame bakina nayi shiru saboda
funawar da nayi cewar a bakon wuri muke ko kuma
ni din ni bakuwa ce.
Daga cikin dakin Baba Tanimu da ke
makwabtaka da namun naji an yi gyaran murya
alamar dai yin kashedi.
Ado ya hakura ya gyara ya kwanta, ni kuwa
naci gaba da zama a kan katifar ina kukan sharbe
tare da shisshika a hankali sai dai shi Ado shiruu
kawai yayi amma yana ji na.
Ana cikin haka wani irin hadari ya taso mai
matsanancin iska da guguwa da rugugi mai
tsananinn firgitarwa har wani bai iya cin motsin
wanda suke tare, sai in yayi motsi ne da karfi nayi
maza na gyara na kwanta da nufin yin shiru kamar
yanda shima Adon yayi, sai kawai naga ya juyo
gare ni.
"Kin fasa kukanne?" Nayi kamar ban ji shi ba,
Ni fa yau ba zan iya irin kwanan da muka yi jiya
ba." Ya miko hannu zai taba ni, nayi maza na ce
mishi "Gaskiya ni fa ba zama nazo.yi ba, ko yau
41
dinnan da ina da kudin mota da tafiyata nayi."
Ina gama fadin hakan ya cafke ni, bai saurari
ihun da nake yi mishi ba saboda yasan ba zai kai ga
kunnen Baba Tanimu ba. Sabuwar iskar da ke
kadawa ga tsawa da rugugi, watakila ma ya dade
yana baccin shi, gane hakanne yasa ni barin ihun na
koma yi mishi bayani.
"Ni gaskiya tun da muka zo fa cikina yana
ciwo, ban gaya maka ba ne kawai." Bai saurara ba.
Na kwana da matsanancin ciWon cikin da yay
dalilin da na kwana ina murkususu daga kan katita
in koma kasa, na rasa in da zan sa kaina in ji dadi,
nayi kuka har na hakura nayi shiru.
Ado yayi nadamar abin da ya faru tsakanina
dashi, yayi nadamar tilasta min da yayi a haka
muka kwana daga ni har shi babau wanda ya samu
runtsawa.
Ana fitowa daga sallar Asuba muka kama
hanya zuwa asibiti da ni dashi da Yaya Jafaru da
Ruwailah, saboda tun dare ya shaidawa Baba
Tanin halin da nake ciki, tun daren kuma Yaya
Jafarun yayiwo aron mota wurin wani abokinshi
don ma Baba Tanimu ya hana tafiyar daren ne yaa
ce a hakura ayi sallah tukunna.
Asibitin Malunfashi ya kai mu, shi ne wai yafi
42
girma a nan kusa, gwajin farko da Likitan tayi min
tayi bayanin ciki ne ya lalace ya fita daga cikin
mahaifa, sai dai bai shiga ya fadi ba, saboda haka
zasu wanke shi ya fita don in ba haka zan yi ta
wahala da shi kafin ya kai ga fita.
To amma me ya kawo haka Likita? Ado ya
bukaci sani, tayi ta lissafo dalilai ciki har da tafiya
mai tsanani ko kuma bacin rai ko aiki mai wahala
shi yasa yawanci muke hana mata masu karamin
ciki ko kuma cikin da ya riga ya kai watanni
bakwai yin irin wadannan abubuwan, ku kuma
maza muke rokonku da ku rinka tausaya musu.
Daga Ado har Yaya Jafaru da Ruwailah sun
gamsu da jawabin nata.
Aka yi min wankin ciki aka sallamo mu bayan
La'asar, duk da Ado yaso a bar ni in kwana wai a
kara kulawa dani sosai aka ce babu gado.
Mun iso gida gab da magriba, kai tsaye dakin
Goggo Ayalle aka kai ni, wacce ta yi fada mai
tsanani akan wankin cikin da taji an yi min, ina
dalili yarinya ko haihuwar fari bata yi ba za aje ana
kakaba mata karfen nasara