Showing 3001 words to 6000 words out of 35296 words

Chapter 2 - MIJIN TACE Book 3 Hausa Novels by hafsat Sodangi.docx

in rada mishi cewar ni fa ba

16

da gaske nake yi ba, zabin da nayi na cewar zan bi

Ado nayi hakan ne kawai don in sanya Mama bacin

rai, amma babu wanda zan iya fuskanta da maganar

tawa ya saurareta."

Gaba daya wuri ya hargitse, hankula sun kai

matuka wajen tashi, Baba Yahya da Babana sai

faman rirrike su ake yi saboda Babana ya koma

taya Mama zagin Inna da danginta da take yi, yana

tayata kiransu munafukai masu raba dan uwa da

dan uwa, shi kuma Baba Yabya yana rama musu

To ma na fasa tunda akan wannan..

Cikina ya bada wani irin sauti na kulułulu!!!

saboda tsoron kalmar da zai karasa zancen nashi da

ita, sai naji ya katse zancen nashi ya ce, na fasa ba

in da zata zabin da tayi zabin banza ne, ban yarda

ba, ba za ta bishi ba, a zuciyata nace tafi nono fari,

Baba da haka kayi tun farko ma da ba a tsaya

wannan kace-nacen din ba, tunda dai ni din ai

mallakinka ce.

Zancen Baba Yahya ya katse ni da na ji yana

fadin, wannan ai shi ne karya ba za ta zabi mijinta

ka hana ta bibn shi ka kashe mata aure ba, saboda

kawai matarka tana son ganin hakan, in zaurawa ka

ke son gani a gidanka ai gasu nan ka samu."

Mama ta sake kurma wani uban ihun, wai Baba

17

Yahya ya yi wa 'ya'yanta gori, bai saurare ta ba

balle Babana, ganin shi kawai naga yayi ya damko

hannuna yana jana zuwa inda Ado ke makure a

jikin bango.

"Yau ka ce kana son tafiya da matarka?"

Da sauri Ado ya ce mishi "Eh." Baba yana jin

haka yayi maza ya danka mishi ni a hannunshi, tare

da fadin "Gata nan Ado na baka ita ku tafi, ka ike

min ita amana ka sani iyayenta ma hakuri da su

muke yi, to balle kuma ita yarinya ce yar karama."

Ado yayi maza ya kama hannun nawa ya rike

da iyakacin karfinshi, tanfar yana tsoron kar a

kwace mishi ni.

"Wuce ku tafi." Ya bani umarni mai karfi,

daidai lokacin da Babana yake ta sakin wasu

maganganu masu tsanani su Mallam Harisu suna ta

faman bashi hakuri, na kalli Baba Yahya ina kuka,

na ce mishi "Ba zan bi shi ba Baba, ba zan bishi ba,

ni dama ba da gaske nake yi zan bi shi..."

Wani irin gigitaccen mari ya dauke ni dashi, sai

da naga waikiya ta haske ni gaba daya, Ado yayi

maza ya kankame ni a jikinshi da sauri yana baiwa

Baba Yahya hakuri.

"Kayi hakuri Baba, kayi hakuri." Yana kuma

tattare ni da fadinshi don gudun kur hannun Baba

18

Yahyan ya sake kawowa gare ni, gigitaccen marin

da Baba Yahya ya kifa min ya katse min komai,

hatta kukan da na dade ina yi, na daina shi na koma

zare ido saboda ban taba jin mari mai tsananin

wannan ba.

Ado ya tasa ni a gaba, muna fita daga gida ina

jin Baba Yahya yana fadin, "Ai ko za ki shide ba

shure-shure ba sai ya tafi da ita, ai ba zai zabe ta ya

bar ki ke da mijinki da duk abinda ki ke ganin kun

mishi ya ce ita kadai yake so sannan ku hana shi ita

ba, yana sonta tana son shi ke ki ka kulla auren da

nufin sharri don ki cutar da ita, kisa shi ya

wulakantata.

Amma' abin mamaki sai gashi zaman da yayi da

ita na kwanaki tamanin da bakwai kacala sun sa shi

ya zabe ta ita kadai ya barku ke da mijinki da duk

abin da ku ke ganin kuna dashi.

A kofar gida Ado yana kokarin shigar da ni

cikin motar da ke tsaye tana faman jiranshi wadda

shatarta ya dauko, sai ga su Liman da Mallam

Harisu, har da Baba Yahya sun fito. Mallam Harisu

da Limar suka wuce, Baba Yahya yana yi musu

godiya.

Shi kuwa Baba Yahya yazo ya tsaya jikin

motar hannayenshi duka biyu ya saka cikin

19

aljifayen shi ya fito da duk abinda ke ciki ya

mikowa Ado tare da fadin sai kayi hakuri da

wannan baka ba da lokacin da za'a yi maka shirin

tafiyar taku ba.

Hannu biyu Ado ya saka ya karbi abin da aka

bashin cikin ladabi na gode Baba, Ubangiji ya kara

girma."

Baba Yahya yana tsaye a kofar gidanmu har

motarmu ta bace daga unguwarmu, Ado yana ganin

motar ta bar kan titinan daga cikin gari ta fada kan

babbar hanyar da ta nufi Kano ya saki wani irin

sansanyar ajiyar zuciya tanfar dai da a tsorace yake,

ko yana tunanin za'a biyo shi ko a tare shi a kwace

ni.

Lokaci mai tsawo yana cikin wata irin

matsananciyar natsuwa kafin daga bisani naga ya

shafa fatiha, don haka na gane addu'a yayi yana

shafa fatihan kuwa ya juyo gare ni, kamo ni yayi da

hannayenshi duka biyu ya jawo ni ya kwantar da ni

kan kirjinshi, ya kuma dora hannunshi guda daya a

jikina don ýa tilasta ni kwanciya kan kirjin nashi.

Cikin natsuwa ya soma yi min magana.

"Kin taba ganin wanda ya zabi yin aure ya

tozarta? Ai abubuwa guda uku Aisha, Ubangiji ba

ya tozarta mai yin su, alkawari ne ma yayi cewar

20

zai taimaki mai yin su, na farko a cikin su shi ne

aure, sai Jihadi sai kuma bawan da aka rubutawa

biyan wata ka'ida don ya samu 'yanci ya zama da,

don haka babu abinda zai same ki sai alheri.

Wata irin tafiya muka Yi wacce bazan iya

tsayawa ina bada labarinta ba saboda tsananinta, ya

kai duk in da ya kai, daga ni har Ado babu wanda

bai wahala ba, iyaka dai shi ya yi tashi wahalar ne

cikin farin ciki da gamsuwar samun yanda yake so,

babu kuma wata alama ta damuwa a fuskarshi,

yayin da ni kuma nayi tawa wahalar cikin

matsananciyar damuwa ga bacin rai ga ciwon ciki

mai tsananin gaske.

Ado ya rarrashe ni ya gaya min duk wata

magana da zai gaya min, har ya gaji yayi shiru ya

zuba min ido, amma ban daina kukan da nake yi ba,.

babu abin da yafi damuna irin tafiyar da nayi na bar

Innata da na san haka zabin da zan yin zai zama daj

ban yi shi ba.

Na za6i bin Ado don in batawa Mama ita kadai

rai daga baya in an tashi in sulale in yi tafiyata in ki

komawa gidanmu, sai na tabbatar ya bar garin

tunda nasan ba zai sake zama ba, gashi hakan ya

jawo min al'amura masu tsananin gaske, na farko

ya haddasa 6acin rai mai tsanani tsakanin Babana

21

da Amininshi Baba Yahya, a dalilin furta kalmomi

masu zafi da Baban nawa ya fusata yayi tayi a

kaina da mahaifiyata, da ma danginta gaba daya.

Hakika nayi wauta mai tsanani da nayi nufin

6atawa Mama rai ba tare da na tunawa kaina cewar

bacin ran Mama yana nufin ɓacin ran Babana ne

ba, sannan hakan yayi sanadin da ni din zan bi Ado

kauyensu alhalin m din ban san komai game da

zaman kauye ba, ba kua duk wadannan ne suka fi

kuntatawa zuciyata ba, irin tafiyar da nayi na bar

Innata, ko a wane hali take ciki ko a wane matsayi

ta dauki tafiyar tawa? Wannan shi ne abinda yafi

damuna.

Motar ta sake yin tsalle ta sake faduwa cikin

wani ramin a karo na biyu, nima na sake yin maza

na kankame marata da hannayena duka biyu tanfar

dai yanda nayi a farkon fadawar nata, haba Malla

Haruna a rinka kokarin kaucewa ramukan nan

mana.

Mallam Haruna ya dan yi tsaki kadan alamar

shia ba a son ranshi ba ne hanyoyin namu ne sai

hakuri in ban da haka da gangan ai mutum ba zai

rinka fadawa cikin ramukan ba don Sukurkuta

mishi motar zasu yi babu halin kayi ƴar tafiya sau

daya sau biyu sai ka raba abin da ka samu tare da

22

makanikai.

Ni kam Suna maganarsu ina jin su ina kankame

da cikina ina sauraron abinda zai sake faruwa,

tunda daga sanadin fadawa ramin farko ne cikina

ya urda ya kama ciwon da nake ta fama da shi.

Da kaina na lallaba na sake jingina jikina a

jikin Ado, maimakon jawo nin da yake yi ina ki

saboda dunkulewar da naji marata tayi a wuri daya,,

da sauri Ado ya dora hannunshi a jikina ya kara

tallabe ni na kwantar da kaina a kirjinshi ya cusa

hancinshi da bakinshi a kan nawa ya dan sumbace

shi kadan.

A hankali kuma cikin natsuwa da kuma sanyin

murya ya soma yi min magana a hankali.

"Ina son ki Aisha." karo na biyu kenan da na

taba jin sunan nawa sak a bakin Ado kafin yau, bai

taba ba da Humaira ya saba kirana, ban damu ba

duk abin da za a fada a fada, in ma dandani

haukaci akayi min oho, ni kam ina so, ina sonki ban

kuma zabe ki don in 6atawa wani rai ko don in ba

wani haushi ba.

Ban zabe ki akan lalura ko akan kuskure ba, na

zabe ki ne don ina sonki don na riga na gane

rabuwa da ke ba zai haifar min da da mai ido ba,

don haka na zabi rabuwa da komai da kuma kowa

23

don in same ki ke kadai, don nasan abinda kawai

zan yi kenan in samu kwanciyar hankali da

nutsuwar da nake bukata.

Don haka ban ga dalilin wannan bakin cikin da

ki ke tayi ba, in don tsoratarwar da aka yi tayi miki

ne a kan kauye da kuma gidanmu ni din ai namiji

ne Humaira, nayi miki alkawarin babu wata wahala

da zata dunfaroni in barta takai ga taba min ke face

sai nasa dantsena na tare miki ita.

Ai ban rabo ki da gidanku da iyayenki don in

wahalar da ke ko don in zama sanadin wahalarki

ba, na rabo ki da su ne don ina son rayuwa tare da

ke, ina son ganinki a tare da ni, ina son mallakar

jikin nan naki, tó a na menene za ki yi ta wannan

6acin ran?

Ko kina so ne ki nuna min cewar ke din ba kya

sona? Ko kuma ba kya bukatata? Tabbas na sani ba

zan iya amsa wadannan tambayoyin na Ado da

kalmar eh ba, in dai har gaskiya nake nufin fadi. To

amma iyayena fa? Musamman ma Innata, Inna tuna

girma da darajarsu da kullum mai babban allo yake

gaya min da kashedin da yake yi min a kansu, na ba

a karo tsakanin kwai da dutse.

Sai in ga don in zauna da su lafiya in rabu da su

kuma laiya zan iya hakura da duk wani abinda

24

nake so amma ina amfanin wannan abin da ya faru

tsakanina da su a yau? Na tafi Babana yana ta furta

munanan kalamai a kaina, Inna kuwa ko sallama

bamu yi ba balle in san halin da take ciki, amma

Ado wai kar in tsananta bakin ciki.

To me zan yi? dariya? Nan da nan naji haushin

shi ya kama ni saboda ganin da nayi tanfar kanshi

kawai yake so..

"Dan sha ruwan nan ki jika bakinki, in ma ba

za ki ci wani abu ba kin ga ai tunda ki ka yi amái ba

ki sake cin wani abu ba, na ce uh'uh.

Kalaman Ado a kowane lokaci na rarrashi ne

da fadin maganganu masu dadi, don dai ya samu

yaga hankalina ya kwanta, ni nasan babu abin da

kalaman Baba zasu yi miki don kuwa baki yi mishi

komai ba, fushi yayi da fushin wani, Inna kuwa

nasan ba za ta taba jin zafinki ba, balle tayi fushi da

ke, balle har taje tana yi miki wasu munanan

kalamai.

Nayi Imani a daidai wannan lokacin da take jin

kalaman dan Baban yake fadi a kanmu ita tana yi

mana addu'a ne tana neman mana kariya daga duk

wani sharri ko wata fitina, tana kuma neman mana

alheri wu Ubangiji shi ne kuma abin da zai same

mu Humaira."

25

Mun iso Kano ne misalin karfe shida da kwata,

shirye-sbiryen saliar magriba ake tayi don a

wannan lokacin ita magriba din ana yinta ne shida

da rabi a mafi yawancin wurare.

"Samu wuri mai kyau ka tsaya Mallam Hlaruna,

sai mun yi sallar magariba da Isba'i mu wuce."

Mallam Haruna yayi maza ya ce, "Kai a'a

Mallam Ado, kar muyi haka don kuwa muna da

sauran tafiya mai tsawo ban da haka ma ina ganin

tanfar gara wannan hanyar da muka baro a

bayanmu, kan wanda zamu hau nan gaba."

Ado yayi murmushi ya ce, "Ina ganin dai ka

dade baka je Katsina ba Mallam Haruna, in ba haka

ba ai mu hanyoyinmu masu kyau ne."

Kofar wani gida Ado ya kai ni, sai da yayi

sallama da mai gidan suka gaisa sannan ya roke shi

in shiga wurin iyalinshi in yi sallah, don a kan

hanya muke, ya ce babu komai. Na shiga shi kuma

ya koma sai da na idar da sallar naja carbina na jira

nayi Isha'i bai dawo ba, na huta naji dadi sosai don

ban saba irin wannan doguwar tafiyar ba, bas taba

yin ta ba.

Iyakacina giyade, ban taba wuce nan ba, sa

zuwa can maigidan ya shigo yana gayawa iyalinshi

wadanda suka yi matukar karrama ni cewar

26

bakuwar nan ta fito suka ce to, suka rako ni har

kofar zaure sukamiko min leda mai dauke da robar

da suka cika min da kunun aya, nasa hannu biyu na

karba nayi musu godiya.

Ado ya tasa ni a gaba zuwa in da motar mu

take, ina shiga ciki na zauna ya miko min wasu

kwayoyi guda biyu tare da kwalbar Coke ya ce

"Karbi ki sha saboda aman da kike yi." Ban yi

mishi musu ba na karba nasha, ya fita akan zai

maida kwalbar, bai dawo ba sai bayan minti ashirin

da biyar.

Mallam»Haruna yayi tsaki har ya gaji.

"Dabai fa mutumin nan ya ce zamu je, amma

yake yi mana irin wannan bata lokacin." Gabana ya

yanke ya fadi jin sunan garin da Mallam Harunan

ya ambata, ban taba jin sunan garin ba, iyaka kuma

dai ban ce mishi komai ba, tunda ba abokin magana

ba ne.

Ado ya dawo rike da ledoji guda biyu ya mika

wa Mallam Haruna daya, ya ajiye mana daya

Mallam Haruna ya karba yana godiya, yana ganin

dankwaleliyar kazar da ke ledar tashi ya mance

abin bacin ran da Adon yayi mishi, duk da tabbacin

da Adon ya bani na ba zan sake yin amai ba komai

naci, ban yarda naci koman ba, in ban da kunun

27

ayan da mutanen nan suka bani wanda yayi min

dadi ba kadan ba.

A wannan lokacin na dan samu natsuwa da

kuma saukin da nayi bacci, wata kila don sanyin

dare da ya sauka wata kila kuma don saukin aman

da na samu, gashi har na samu nasha kunun aya ya

zauna amin.

Ban sha wahala ko naga tsananin tafiyar ba

kamar yanda direban ke ta magana don kuwa na

farka ne a inda naji Ado yana ce min "Kin faraka a

daidai Humaira, daga wannan garin da ki ka ga

muna wucewa sai kaute guda daya ne a gabanmu

(Tukunya) daga shi sai (Dabai).

Can baya kuwa in da muka baro, kin yi bacci

ne a kusa da garin (Dayi) daga nan sai Malumfashi

sai Kafur sai Sabuwar Kasa, sai Gozaki sai Dabai,

to amma kin san akwai kananan kauyuka a

tsakanin garuruwan sai a hankali za ki san su."

A zuciyata na ce, in na zauna a garin kenan,

don ni kam a zuciyata ina ganin tanfar babu abin da

ya dace dani irin komawa gida in je in roki Babana

da Innata gafara kan bacin ran da na san na sanya

Su.

Ado ya saki wani lallausan murmushi bayan

yayi ajiyar zuciya, tare da hamdaia ga Ubangiji.

28

"Ga Dabai Humaira mun iso." A hankali ya soma

rada min a kunnena, bude ido ki ga garin mijinki

Humairah gari da zai zamo shi ne garin 'ya'yanki,

ina son Dabai Humaira, ba wai don garina ba ne

kawai, a'a mutanen garin mutane ne masu neman

na kansu, masu karamci da ganin girman juna.

Mutanen Dabai jarumai ne manoma ne wasu da

yawa kuma 'yan kasuwa, in ta fannin ilimi ne kuwa

muna da manyan Malaman addini a ta bangaren

bokon ma ba a bar mu a baya ba, mutanen mu da

yawa suna nan warwatse cikin ma'aikatun

Gwamnati suna aiki tun daga LocalGovernmnent

har zuwa State da kuma Federal.

A daidai lokacin da Ado ke ta faman wasa min

garin nasu na bude ido tarwai, wai domin in ga

abinda yake gaya min din, tunda an yi sa'a farin

wata ya haske ko ina. Ban ga komai ba in ban da

dogayen bishiyoyin da ya ce min na kuka ne, sai ko

filayen da yake ta nuna min yana fadin duk nan da

ki ke gani ba jeji ba ne, gonaki ne na mutane. Bari

damuna ta zauna sosai ki ga abin mamaki, a

zuciyata na ce ka gani dai.

Shi garin Dabai gari ne da yayi sa'a babbar

hanya ta ratsa shi, ta ko ina kin ga wannan hanyar

da muka biyo'ai kin ga garuruwan da muka baro a

29

bayanmu, to» näii gabanmu in ta wuce Dabai zata

wuce, mararrabar Danja ta tafi har Hunkuiyi taje

Basawa ta isa Zariya, kin ga ta tafi har Kaduna

kenan.

In kuwa a mararrabar Danja ki ka tsaya ki ka bi

hanyar da tayi dama, to za ki isa kauyen Dan Mai

gunta ki wuce kije har Danjan, in kuma ki ka nufi

hagu to zaki je garuruwan Kudan daga nan kije har

Makarfi in ki ka fada babban titi ma sai ya maida

ke har Kano, ita ce ma hanyar da yan kasuwanmu

suka fi amfani da ita."

Ya sake kallona cikin murmushi yana fadin

"Ba za ki gane dadin Dabai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login