Showing 12001 words to 15000 words out of 35296 words
Chapter 5 - MIJIN TACE Book 3 Hausa Novels by hafsat Sodangi.docx
da dinner set da kuma
wasu kwanuka.
Ga bokitaye da randa da dai wasu tarkace, ga
kuma kayan abinci dan daidai gwargwado ko a ina
yaké samun kudin da yake kashewa? oho!
tambayar da na.yi wa kaina kenan, a zuciyata dai
nasan babu abin da yafi min ban dakin nan dadi,
don na samu kebabben wuri har da bayan gidan
hadakan da ban saba da shi ba yake sani jin kiyan
yin wanka.
Nayi maza na kammala abubuwan da zan yi
nayi wanka saboda jin dadin ganin bandakin na
zauna na shafa mai nayi gyara irin yanda na saba yi
a gida, gaba daya dakin ya gauraye da kamshin
kayan shafan da nayi amfani da su.
Ado bai shigo ba sai da yayi sallár Isha'i shima
57
yana shigowa bandakin naji ya shiga yana wankan,
Cikin zuciyata na ce ashe shima da kwiyan wankan
yake ji, don tunda muka zo ban gan shi yana
wankan dare ba, yana shigowa dakin ya sanya
hannayenshi duka biyu ya sure ni.
"Kina lissafin kwanakin aiko? Kina lissafin
kwanakin da nayi ina hakuri ina fama da shan jar
kanwa da lemon tsami? Tuni na langabe mishi na
sa shi ya mance duk wata damuwa in har yana da
ita da kuma wahalar da yake wuni cikinta, wanda
nasan ya manta rabon da yayi irinta, duk wani abin
da nasan zan yi wa Ado rannan da zai sa shi jin
dadi ko farin ciki nayi mishi.
Na kuma yi matukar yin hakuri da shi, ban
Duna mishi gajiyawata ko korafi kan al'amuranshi
ba, ba don komai ba sai don zuciyata ta riga ta
yarda ta amince da cewar Ado mijina da na kuduri
aniyar zama dashi a kowane hali yake ciki in
taimake shi, in ba shi hadin kan da da yake nema a
tare da ni, in jiyar da shi dadi gwargwadon abin da
zan iya yi.
Saboda na yarda na amince sona yake yi da
zuciyarshi guda daya dawo da ni kauyensu da yayi
kuma ba laifi ba ne gurinshi na asali yazo da ni
mafi yawancin wahalar da yake yi kuma na yarda
58
mati yawancinta tawa ce.
Sallar Asuba ya fita yayi ya dawo ya same ni
nima ina sallar, nayi zaton komawa zai yi ya dan
kwanta kafin ya fita tunda ni dai nasan kashi uku
bisa hudun daren idonshi biyu ne, amma sai naji ya
ce min ni na tafi bai ma jira amsawata ba.
Na idar da sallata na koma na kwanta, sai da na
dan yi bacci kafin na tashi na duba abin da muke da
shi na abinci na gama gyaran wuri da tsabtace shi,
nayi wanka nazo na shirya abin karyawa, na karya
na gyara jikina na jawo kofar wurina na rufe don
kar kaji su shiga suyi mana ta'adi.
Na fita naje na gaida manyan gidan duka kafin
na wuce can tsakar gida wurin haduwar matan
gidan. inda ake da babban fili sosai da ke dauke da
wurin girki a can nesa ga runbuna a can wani gefen
ga in da ake aikace-aikacen wanki ko wanke-
wanke, wani gefen can kuma daka ake yi da nika
ga kuma wata katuwar rumfa da ke tsakanin wasu
manyan bishiyoyi in da ake zama ana yin hira.
Zaman tsakar gidan nan yafi komai dadi, don
wuni ake yi ana raha ana barkwanci ana kwashewa
da dariya, shagala nayi a cikinsu ana tayi ina kallo
har ina taimakon masu daka da yin tankade, ban
ankara ba sai naji ana kiran sallar azahar.
59
Gaba daya aka watse kowa ya nufi wurinshi
don yin sallah, kofata tana rufe kamar yanda na
barta a zuciyata na ce yau ma Ado bai dawo ba
kenan, na idar da sallah naje na karbo fura nazo na
dama na ajiye mishi na koma wurin matan gida, na
ce ba zan iya zaman kadaici ba, in ya dawo ya kira
ni ko kuma ya sha furarshi ya tafi.
Ado bai shigo ba sai bayan 'sallar magariba, ban
taba ganin tashin hankali da bacin ranshi irin na
rannan ba, kina nufin ba za ki iya zaman wurinki
ba? To me yasa ki ka yarda ki ka dawo? Kina nufin
ai ba zan dawo gida in same ki a wannan dan
tsukakken dakin namu kina zaman jiran dawowana
ba?
Sai in ina son ganinki in biki cikin mata ina
kwala miki kira? Ke ba ki san hakkina ba? Ba ki
san abin da za ki taimake ni da shi ba? Fura ce zan
rayu a kanta Humaira? ba ki ga kamar dandanon
abincinki a bakina zai yi matukar yin amfani a gare
ni ba?
To bari in gaya miki dama kin bi a hankali
wannan taron nasu da ki ke gani-randa suka tashi
tambayar junansu gulma suka sa dake a ciki abin
zai baki mamaki, ke baki taba zaman gidan yawa
ba duk fitinar da ki ka sani a gidanku wasan yara
60
ne.
Gabana ya yanke ya fadi, jin da nayi Ado ya
kira fitinar gidanmu wasan yara na ce to ai gara ka
maida ni gidan namu, abin da kawai na fada kenan
Ado yasa hannu ya make ni, kina hauka ne? Na ce
kina hauka ne da kullum za ki rinka kallona kina
cewa in maida ke gidan naku ke kina da gidan
zuwa ne?
Ko ba ki ji abin da maigidan ya fada ba sanda
ki ka zabi biyo ni? Ya ce kar ki sake taka gidanshi
saboda ya yafe min ke bai da sauran bukatarki."
Dukan da Ado ya yi min bai 6ata min rai ya
daga min hankali irin wannan maganar da ya soka
min ba saboda gaskiyar abin da Babana ya gaya
min ya gaya min. Nayi kukan bakin ciki har na gaji
a kasa da kwanaki talatin na barin iyayena da nayi
na biyo shi har ya fara goranta min abin da ya
farun.
Tabbas Ado namiji ne dama kuma nasha jin
Mama tana cewa shi namijin ba dan goyo ba ne, a
gabanshi kuma ma ta fada ta ce namijin ai ga ki
nan gashi nan.
Rannan dai kam kwanan da muka yin ba mai
dadi bane, don haka yana fita sallar Asuba na duba
inda 'yan kudina da nake tarawa suke, don yau kam
61
nayi niyya ko ba za su kai ni gida ba in dai za su
raba ni da garin Dabai, to zan tafi in yaso nasan
yanda nayi na karasa gida.
Ban ga komai a wiirin ba sai nera hamsin saura.
ya kwashe kwana biyu muna cikin wani hali ni
dashi, rannan ya dawo da yamma ya same ni, kin
gani Humairah mu biyu ne ni da ke a nan, ya
kamata in wani abu ya faru a tsakaninmu na rashir
jin dadi in na ba ki hakuri ki hakura, ba zai yiwu
ace kullum sai na kai wa Inna maganar za ki hakura
ba, in dai ba so ki ke mu rinka tayar mata da
hankali ba.
Kuka na soa yi sosai da sosai, kiyi hakur na
sani ban kyauta ba da nayi miki gori, to amma ke
kin ga yayi miki daidai kan maganar da ba ta taka
kara ta karya ba ki rinka cewa in maida ke
gidanku? Ai ya kamata ace ni da ke mun fahimci
wani abu a tsakaninmnu, shi ne zaman namu bana
rabuwa ba ne ba kuma na wulakanta juna ba.
Tsawon lokaci yana yi min maganarsu na
rarrashi da ban baki har dai ya samu ya gawo
kaina na hakura, muka shirya.
Tun daga wannan lokacin na rage shiga can
cikin gida don yin hira da matan gidan sai dai kawai
in gari ya waye in shiga in gaishe su dukan su in
62
dawo wurina in gama aikina in gyara komai in yi
wanka in gyara jikina, duk da 'yan kayan nawa har
yanzu guda uku ne sai lodin rigunan baccin da babu
damar in sanya su da rana sai da daddare in yi
mana abin karyawa irin wanda naga ina, so don
komai na abinci Ado kawowa yake yi, komai
tsadarshi kuwa.
Agada, Doya, Dankali, Wake, Kuskus,
Indomie, kwai, manja, Mangyada, Manshanu,
Shinkafar tuwo saboda masa da kuma ta wara duk
ina da su ina kuma da kayan tea zan kuma tashi da
safe in je in kar6o kunu da kosai, don ko ban je ba
za a biyo ni da shi, don haka nake girmama su in je
da kaina.
Shi kuwa Ado ka'ida ne kome nayi na karyawa
to sai na karbo mishi dumame wurin Goggo Ayalle
ya fara dashi kafin ya ci wani abin.
Kullum zai baro gonarshi sha daya ya dawo
gida, yana dawowa zai tube kayan jikinshi ya shiga
bandaki yayi wanka, ni kuma sai in tsoma su a
ruwa in wanke su in shanya in wanke mishi ranbut
din nashi na hannu da na kafan in jefa su kan rufin
dakin namu su sha rana, sai da yamma in kwashe
su.
Yana fitowa daga wankan zan sanya mishi
63
tabarma a inuwan dakina ya hau kai ya zauna in
gabatar mishi da abin da na tanadar mishi.
Yana ci muna hira yana bani labarin gonar
tashi, mafi yawancin lokaci in muka zauna a wurin
zai yi wuya mu tashi bai nanata gaya min maganar
da ya saba gaya min ba, ina so in samu damar dda
zan nuna miki halarcina Humaira, ina so in samu
damar da zan nuna miki cewar ni din da namiji ne.
In ya gama abin da zai yi ya kama hanya ya fita
sai kuma in sake zama in shirya mana abinda zai
dawo da azahar ya ci, hakan kuma bai hana ni
tanadar mishi furar da zai sha bayan yaci abincin."
Da daddare kuwa food flaks din mu nake
dauka in kai wurin da ake kwashe tuwon darea
zuba mana namu in yi musu sannu da aiki in dauka
in kawo mana in zuba mana manshanu da yaj1 muci
ba tunda ya hana ni cin abincin hadaka da su ba,
ban dai kara tsinkewa na lamarin gidan yawa na
kara tsorata da zaman gidan yawa ba irin ranar da
aka wayi gari a gidan ana tuhumar Ade 'yar dakin
Yaya Furera wai tayi gulma.
Ade kuwa kishiyar, Ruwailah ce ranar ne na
gane su matan gidan ba shugabancin matan sasansu
suke yi ba, a'a group ne kawai daga kowane sasa ka
ke in kana so zaka shiga kan hakan ne ma nake
64
ganin tanfar gaba dayansu kowacce kokari take ta
janye ni in shiga nata group din.
Ni kuwa kashedin da Ado ya yi min da kuma
ganin abinda ya faru a ranar don ma anyi sa'a Yaya
Baidu yana gida, shi ne ya fito yayi tsawar da
kowacce ta shiga taitayinta da ba a san abin da zai
faru ba, yasa na kara tsorata na kara kama kaina.
Sannu a hankali ma sai na daina zuwa karbo
mana tuwon daren, ina yi mana namu saboda
kullum Ado yana yi. min maganar ke ba taya su
aikin komai ki ke yi ba, amma sai kin je kin karbo
musu tuwon su, in nayi abincin daren dai ban sawa
kowa, amma na rana gaba daya tsofaffin gidan
nake sanya musu, su kuma yaran matan wacce ta
aiko danta ko tazo ta ce in zuba mata in zuba mata,
wacce bata aiko ba shi kenan. Don abin da ya ce
kenan, sai ko yaran gida da na gama suna wurina.
Yarda da bin ka'idojin Ado da nayi sai suka yi
dalilin da na samu wata irin rayuwa a tare dashi
wacce ta fahintar dani cewar ita mace ba wai tarin
dukiya ko wani kyale-kyale ne yake samar mata
farin ciki da kwanciyar har kalin rayuwarta ba, a'a
mijinta kawai.
Kullum ni da Ado a cikin tarairayar juna muke,
yana gudun bacin raina ina gudun nashi, yana
65
tattalin farin cikina kamar yanda nima nake tattalin
nashi, duk da matsanancin aikin da yake fama da
shi a gonakin shi ramar shi tayi matukar raguwa,
saboda yana da kwanciyar hankali a gida ina kuma
tarairayarshi da abinci mai kyau.
Rannan muna daki da daddare ni da shi, hadari
ne ya taso a gari ganga-ganga, tuni na fara sabawa
da irin wannan hadarin mai yawan iska da rugugi
gami da tsawa, shafa maina nake yi ban fasa ba, na
ce mishi kai-kawo hadarin nan ba irin namu ba ne
na can.
Idon shi yana lumshe ba tare da ya yarda ya
bude su ba, ya ce min eh ai ko ruwan ma ba daya
ba ne, in kin lura ai mun baro can ne damuna ta
riga ta kankama sai muka zo nan muka tarar
lokacin ake shuka.
Na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi idon
naka yana ciwo ne? Bai yarda ya bude suba ya ce
min to ko ba sa ciwo Humairah tunda ki ka zauna
kika bar kirji a waje ai dole in yi maza in rufe su in
dai ba so ki ke in kasa cika alkawarin da nayi miki
na cewar shekaran jiya waccan da wacce ta wuce
da jiya da yau da gobe duk za su zamo ranakun
hutu ne a gare ki ba, don ki san in aka yi min alheri
nima na iya irin nawa alherin.
66
Nayi murmushi na ce eh, gaskiya ne kar ka
bude kai dai to dan bani hannunka in sa shi yayi
min wani aiki.
Ba tare da ya bude ba yayi maza ya miko
hannun yana laluben in da nake tare da fadin ungo
shi Humairah ungo hannun nawa karbe shi ki sanya
shi hidimar da ki ke ganin ta dace da shi ina kama
hannun nashi na ji Ado ya yi wani irin ajiyar zuciya
mai sanyi ban sake ganin yanda aka yi ba sai
ganina nayi a gefen shi a kwance ya zagaye ni da
hannayen shi duka biyu tare da yi min tambayar.
"Kin san wani abu ne Humaira?" Bai jira na ba
shi amsar na sani ko ban sani ba, sai ya soma
rattabo min bayaninshi, ke din mai alheri ce,
alherinki kuma yawa ne da shi saboda kina da kirki
ga ki da abin arziki iri-irni, in ki ka ga dama sai ki sa
mutum ya rinka ganin tanfar babu ma wanda ya kai
ki abin arziki, balle ya iya fin ki.
Ban kula zancen na Ado ba, iya ka dai nasan in
dai barin shi ya yi yanda yake so shi ne kirki, ko
alheri to na yi mishi.
Muna cikin irin wannan zaman mai dadi ni da
shi wara magana ta taso a cikin gida, Ruwaila ce
take yawan yi min magana akan kankane ni da Ado
yake yi, yana hana ni mu'amalla da kowa cutata
67
yake so yayi dama haka tsofaffin maza suke yi ma
matansu, don su hana su fahimtar komai.
Shi Adamu ai ba yaro bane ga sa'o'inshi ne da
ke garin nan suna shirin yin surukai, ko ma daukan
jika kwanannan, don haka ga adashe nan na kafa ki
zo ki shiga, na ce ai ba zai bar ni ba, ta gallà min
harara "Ke ko iya zama da miji baki yi ba? Ai
kamewa za ki yi daga gare shi ba a sakan mishi jiki
haka sakakaka ba, in ki ka ga ya matsa sai kema ki
bijiro mishi da taki bukatar.
u da muke da shashun kishiyoyi ma muke yin
hakan muci nasara balle ke ke kadai? In ki ka saban
mishi da yanda ku ke din nan ai wahala za ki sha
tunda in ke kin yarda da hakan wata ba za ta yarda
ba, kin kuma san ana yin kaka in ya saida amfanin
gonarshi kishiya zai yiwo miki."
Kirjina ya bada sautin rugugugu! ban sani ba
ko itama ta gane tsananin tsoratar da nayi ne yasa ta
yin murmushi, ta ce "Lah, to wannan ai ba wani
abu ba ne, mu nan ai haka ake yi kaka tana yi in
aka cika runbuna da hatsi, to abinda yai saura sai
akai kasuwa a sayar sai ki ga an kawo miki wacce
zaku ci hatsin tare shi kenan."
Ta sake kallona ta ce min, to balle ko mijinki
da wahalar damunar nan bata hana shi manne miki
68
ba, ai kuwa kin san ya huta da kaka akwai magana,
na kuma ji Yayanshi yana cewa yayi noma ba
kadan ba, in kaga irin aikin da yake yi ma sai ka ga
tanfar da gayya yake yi.
Sammako yake yi ya riga kowa tafiya, sannan
duk a can ake baro shi, na ce mishi babu wata
gayya so yake yi yayi gini ya kuma kara wani
auren, ai kuwa dolen shi yayi aiki tukuru." Na zuba
mata ido kawai ina kallonta don kuwa ban taba jin
maganar da ta dame ni ta daki zuciyata ba irin
cewar wai Ado zai yi min kishiya, to ni kuwa
kenan ribar me naci a biyo shin da nayi?
Ta salke kallona cikin natsuwa ta ce, yarinya
kamar ki ya kyale ki kina yawo cikin wasu
zulunbun dogayen riguna da tun suna baiwa
mutane sha'awaa har sun daina sun maida ke kin
zama tanfar wata tsohuwar Babarbariya."
Kalaman na Ruwailah sun yi matukar yin tasiri
a zuciyata, musamman da ta tabbatar min da cewar
su al'adar mazansu ne ma in sun cika runbu da
hatsi, to abinda ya saura in an kai shi kasuwa aure
ake yi.
Don haka nan na kame sosai daga yawan
sakewa Ado fuska, al'amura suka yi matukar
sauyawa a tsakaninmu, da yazo zai taba ni sai in ce
69
mishi cikina na ciwo, sai yayi maza ya kyale ni.
Rannan dai ta kure, mun kai wajen sati uku a
haka tunda safe Ado yake yi min magana,
rarrashina yake yi a dalilin bai son tilasta ni saboda
abin da ya taba faruwa a tsakaninmu, ganin da nayi
ya matsu kwarai mu fahirnci juna ya sani bijiro
mishi da maganar adashen da ake yi a gidan, wanda
ni kadai ce bana yi.
Cikin natsuwa ya kalle ni ya ce, "To kina da