Showing 33001 words to 35296 words out of 35296 words
Chapter 12 - MIJIN TACE Book 3 Hausa Novels by hafsat Sodangi.docx
to shi kenan ni zan koma duk ranar da ki
ka gama wanka ki ka koma dakin naki sai in zo
muyi kwana bakwai tare kafin ki tafi, in kuma naga
raina ya 6aci da yawa ma sai in fasa tafiyar taka
gaba daya.
Da sauri na kalle shi "Me nayi maka?" Hawaye
suka soma ganagarowa daga idanuna, saboda
fargaba. Na matsa na matsu in je gida in ga Innata
da Babana dama sauran dangi baki daya.
To tun yaushe muke zaune ni da ke a haka
Humaira? Sai kuma ace ba za ki tausaya min ba ai
babu son kai a tsakanina da ke.
Goggo ta shigo ta same ni ina kuka ta soma
salati ina dalilin wadannan hawaye da suke zuba,
kai Ado me kayi mata? Ban yi mata amai ba
Goggo wai babu hali ne kawai ta ce ga yanda
za' ayi in ce a'a.
Ai kuwa dai ba zai yiwu ba. Goggo ta soma yi
min fada bakin cikin Ado ya kama ni don haka ma
150
ban sake daga ido na kalle shi ba balle in san
maganar da yake yi min.
Kwana uku bayan nan ya sake baro Danja ya
dawo gida ina ganinshi na tsuke fuskata, amma bai
hana shi yin magana ba. Wurinki nazo saboda naje
nayi wani sabon tunani.
Wanda zai yi mana amfani dukanmu, ki rinka
zuwa kina samuna adalci muna hira da daddare in
su Goggo sunyi bacci.
Na girgiza kai nuna alamar rashin yarda tare da
fadin ba zan...tun kafin in karasa maganar tawa ya
katse ni da wata irin rantsuwa na kuma san ba
dabi'arshi ba ne yin hakan.
To na rantse miki babu inda za ki in dai ba ki
yarda da wannan ba gaba daya na fasa tafiyar ki
zauna kawai tunda ni dama ba don ke na shiryata
ba, don nna ce nasan yanzu haka tana son ganinki
balle taji kin haihu.
Zata zo ta gan ki taga abin da ki ka haifa amma
duk da haka nasan in nayi waya na ce mata tayi
hakuri wani uzurin ya hana ki zuwa, ai zata hakura
tunda ita ba irin ki ba ce, ace mata baka da ikon
sarrafata.
Ba ka da halin ka ce mata ga yanda za'ayi ta ce
maka to sai a'a? sannan a rinka yimaka karyar
151
ladabi da biyayya ta musu? A haka fa muke zaune
ni da ke in kin yi min alherin kwana bakwai to sai
kin yi dalilin 6acin raina na kwanakin da ban san
adadinsu ba.
Cikin zuciyata kalaman Inna suka fado min
game da muhimmancin mijinka yasan alherinkato
ni yaushe ne Ado zai san alherina da kokarina akan
shi ya rike wannan yabon guda daya a mafi
yawancin lokaci yakan yabe ni ne a daidai lokacin
da abin yabon ya faru.
Amnma 'yan mintoci kadan bayan nan da zan yi
mishi wani kuskuren musamman ace kan abin da
ya shafi kankanshi ne ba zai tuna kokarina na baya
ba don haka naji hawaye sun fara zuba a idona a
dalilin zuciyata ta kuntata na fara kukan kenan sai
ga Goggo ta shigo.
Ni fa naji abinda ya ishe ni wai ina dalilin
wannan kuka ne na iya shege? Kai Adamu yayi
maza ya ce na'am Goggo ta ce na roke ka ka yi wa
yarinyar nan abinda take so.
Ya ce mata to Goggo ya tashi ya fita ya bar mu
ni da ita a dakin tana ta mita dama kin yi a hankali
namiji ne in ki ka zauna ki ka yi jegonki na gaskiya
ma ina ruwanki da shi yaushe za ki je kina daga ido
kina kallonshi.
152
Balle ki san abinda yake ciki ranki yana baci a
banza, taja tsaki ta wuce ta fita taje sanya mana
ruwan wankan yamma.
Mun kammala komai muna shirin kwanciya
Goggo kam ma tuni take ta faman gyangyadi jira
kawai take yi in gama baiwa Umahmah nono in
mika mata ita suyi kwanciyarsu da tuni tayi
barcinta, don tare suke kwana.
Muna cikin haka sai ga Ado ya shigo, Goggo
sai da safe ta ce mishi to sai da safe, ta amsa daidai
ta karbi yarinyar sunyi kwanciyar su.
Nan da nan ta soma minshari, ya mike tsaye
yana kallona muke ko? Nayi kamar ban ji shi ba, na
ce muke ko? Ko kina son yi min wulakanci ne? na
mike tsaye na fita na nufi wurin namu gabana sai
faduwa yake yi, shi kuma ya tsaya yana jawowa
Goggo kofarta wacce dama ba sakata take sanya
mata ba.
Ina shiga dakin na shaki wani irin kamshi mai
dadi ga kayaiyakin ciye-ciye iri-iri ya ajiye ga wasu
dunkakkun zannuwan da ban san da su ba a gefe.
Yana shigowa yayi murmushi, kici wani abu
mana ga kuma dinkunanki nan ki duba, na ce uh'uh
ai ba dadewa zan yi ba.
Bai kalle ni ba ya ce min dama kin saki ranki
153
don ba zan yarda da wannan dari-darin ba kin
gane?
A kan dole na saki jikina da Ado na bar shi
yayi abin da yaga dama, kuma wai maimakon yayi
la'akari da halin da muke ciki na satan jiki muka yi
na kawo mishi kaina bai damu be, bai yarda ya
hakura dani ba sai wajen karfe biyu na dare.
Ya rako ni na dawo dakin Goggo na hau gado
na kwanta yayi min sai da safe yaja kofar ya koma
wurinshi don yin wanka tunda ni kanm na riga nayi
nawa.
Na fara bacci kenan, Goggo ta tashen a dalilin
yarinya ta tashi na karbeta na bata nono.
Washegari da safe Ado ya shigo bayam munyi
wanka daga ni har yarinyar Goggo tana wurin
kosanta, zama yayi a bakin gadon yana wasa da
kafar yarinyar dake faman shan nono.
Zan fita amma ba zan dawo da wuri ba in na
dawo zan zo in sanar da ke don ki zo ki same ni, na
ce mishi kai...yayi maza ya katse ni da kin koyi ce
min to don ki rinka sarun cikakken lada.
Da daddaren kuwa sai da ya dawo ya zo yaja ni
muke je. Washegari ma haka tun ina tsoro sai kuma
na saki raina, rannan ina tare da shi mun yi matkar
sakin jiki mun shagala cikin al'amuranmu.
154
Gaskiyar magana ita ce daga ni har shi muna
Son juna, muna son kasancewa tare da juna, nakan
dai jawa Ado raine kawai in yi mishi yanga saboda
kawaici da kuma jan aji irin namu na mata.
Amma in ba haka ba kasancewa tare da shi
yana sanya ni jin dadi, ya sanya ni farin ciki da
nishadi, ya sanya ni in rinka ji da ganin tanfar
bayan ni din to babu wata. Barin komai yake yi ya
tarairaye ni ya gaya min kalmomi mnasu sanyaya rai
da tofar da zuciya.
Ya maida kanshi zama tanfar wani dan yaro ko
wani mara yawo a gabana, bai kuma gajiya kullum
muka shiga cikin irin wannan halin zai nanata
kalmarshi guda daya da ya saba gaya min ita ce ke
din matata ce Humnairah.
Ke ce matata kar ki taba ganin nayi aure a wani
lokaci kiyi tunanin zan mallaka mata kaina kamar
yanda nake mallaka miki ko zan zauna in yi mata
shagwaba da sakarci irin wanda nake yi miki.
Muna cikin wannan halin ne kawai naji Goggo
Ayalle tana kwala min kira a tsakar gida da
iyakacin karfinta, a cikin kua wannan tsohon daren.
A kidime fwarai nayi maza na bude baki da
nufin amsawa don in hutar da ita wage bakin da
take yi tuna yi min irin wannan kiran a cikin
155
wannan daren wanda nasan da wuya kwarai ace
akwai wani cikin mutanen gidan nan da bai ji kiran
da take yi min din ba, tunda dare ne, dare kuwa ba
raina motsi yake yi ba.
Ado ya yi maza ya dora tafin hannun shi akan
bakin nawa ya rufe da iyakacin karfinsh1, don hana
sautin maganar tawa fitowa sosai.
Ganin hakan ya sanya ni kokarin kwatar kaina
a hannunshi, tunda shi da kanshi ya ji kiran da ake
yi min daga inda muke din kuma muna jin muryar
Umahmah da ke ta faman canyara kuka.
Amma hakan bai sanya shi ya hakura ba, sai da
ya natsa don kan shi sannan ya kalie ni cikin wani
yanayi da yafi kama da na tsananin gajiya.
A hankali ya bude baki yana yi min magana, ke
ba ki da wayo ai shiru za ki yi abin ki sai ta gaji ta
koma daki sai kiyi fitowarki, na ce mishi to.
Amma duk da haka jikina ya kai matuka wajen
tsorata sai bari nake yi, ya zuba min ido yana
kallona ke menene haka? Na fa zunubi muka yi ba
ni mijinki ne ke matata ce.
Na ce mishi uhun, ai ni babu abin da yafi
damuna da tsayuwar min a rai irin bazuwar
maganara cikin gidannan da yanda za'ayi ta yadata
ana cancanzata, cikin sauri ya ce min ke kar ki
156
nemi ki maida mutane wadansu iri mana. Goggo
Ayallen da girman shekarunta ne ki ke cewa za ta
yada wannan maganar?
Kina so ki ce ita din bata san girma da lalurar
aure ba ne? nayi kamar in ce to ai a sanin girma da
lalurar auren nata ne taja ta tsaya a tsakar gida a
cikin tsohon daren nan ten wage balkinta tana
kwalawa sunana kira tanfar wata yarinya yar
Karama.
Bayan kuma tasan karamin mnotsi ma dare bai
raina shi ba, balle wannan ihun da ta rinka yi
wanda ba mutanen da ke cikin gidan nan ne kadai
za su jiwo ta ba, har makwabta sai sun ji.
Sai kuma na ce uhun, bari dai ma kawai in
kama bakina in yi shiru, kar in jawowa kaina wata
magana tsakanina da shi a wannan lokacin da na
san ba karamin abu zan fuskanta a cikin gida ba, in
fadi wata magana ya ce na yi wa matar Baban shi
rashin kunya.
Rako ni yayi nayi wanka yana tsaye yana jiran
fitowata sannan ya tasa ni a gaba ya kai ni har
kofar dakin Goggo Ayalle. Ya kalle ni cikin
natsuwa da murya mai sanyi ya ce min shiga kiyı
kwanciyarki na sake daga ido na kalle shi.
Fuskata ta bayyanar da alamar tsoro yayin da
157
zuciyata ke ta faman harbawa da sauri ya sake
kallona fuskarshi ta bayyanar da murmushi mai
yawa daina jin tsoro Humairah.
Ai ni mijinki ne ba wurin wani kika je ba kin
amsa umarnina ne na kuma gode miki iyakar
abinda Goggo zata yi in ma ranta ya baci ta ce ki
koma dakinki gobe shi kenan, amma ba za ta je
tana yáda wannan maganar ba.
Ai ita babbs ce, in kuwa haka zata yi to ai ai
yafi min na riga na gaji da wankan naki, lin gane?
Na gyada kai nuna alamar eh, don ni kam ko bude
bakin nawa in yi magana bana iyawa, saboda
kaduwar da nake yi.
To shiga mana, na kaile shi cikin natsuwa a
hankali cikin muryar da tafi kama da rada na ce
mishi, to jeka ka kwanta zan shiga.
Ya ce uh'uh ai ba zan bar ki cikin daren nan a
waje ba in haka yasa na tura kofar a hankali na
shiga. Cikin sa'a gaba daya dakin a duhu yake nayi
matukar jin dadin hakan don haka na lallaba a
hankali na dale kan gadona, ina shirin kwanciya
kenan sai kawai naga Goggo ta hasko ni da
tochlight dinta.
Ashe wai duk abin nan da ake yi duk da
dadewar da nayi ban baro wurin Ado ba, duk da ita
158
yarinyar tuni ta hakura da kukan nata ta koma
baccinta.
Ita Goggo bata hakura ta kwanta ba, tana nann
zaune dingir a tsakar dakinta bata ma yarda ta hau
gado ba, don kar tayi gyan-gyadi da bacci zai
dauke ta har in shiga bata sani ba.
Don haka tayi zaman dirshan a tsakar daki tana
Jiran sai taga zuwana wai ita nan a dole sai taga
KWALUWAR DAKA'.
"Ina ki ka fito? Ruwan me ke diga a jikinki?
Jegon kenan? Dama damuwarki kenan yasa kika yi
ta tasa yaron nan a gaba da koke-koke? Haba ni
fa...kuka na soma yi wa Goggo kuka kuma mai
tsanani, saboda tambayoyin nata sun yi min tsanani
da yawa.
Kukanki din banza da na woff? Ina...daga waje
Ado yayi gyaran murya mai karfi, wai dai don
Goggo tasan shi din bai yi nisa ba yana wurin ko
zata yi hakuri ta bar maganar tata.
Ban sani ba ko bata gane abinda gyaran muryar
tashi ke nufi ba ne ya hana ta saurarawa ta ci gaba
da fadin ina amfanin ace mace ita ce fitinanniya?
Namiji bai damu ba sai kece...
Uh'uh Goggo, uh'uh Goggo, abinda ya ci gaba
da fadi kenan don kara yi wa.Goggo Ayalle
159
kashedin maganar tata, yayin da ni kuma gabana ke
ta faman harbawa saboda tsoron kar ya ce zai tanka
mata.
Gaba daya fatana da burina bai wuce ya bar
wwrin tsayuwar tashi yayi tafiyarshi wurinshi, ba
Care da ya bude baki ya ce mata komai ba.
Saboda nasan yin maganan nashi ba zai taba
haifar mana da da mai ido ba, fin barin maganar da
Goggon tayi shi ne ya hassalar da Ado har yayi
dalilin da ya toro kanshi cikin dakin ya ce mata ba
ita na ce Gogggo ni ne, ba ita ba ce kyale ta kawia
ni ne.
Abinda kawai naji Ado ya gayawa Goggo
Ayalle kenan sai kawai naga ta fashe da kuka tare
da salati mai tsananin karfi.
Mu tafi littafi na hudu don jin yanda za'a kare
tare suke'.
Fatan alheri gare ku dukanku taku,
Hafsat Chindo Sodangi
(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)
24 ga watan uku 2013
07035586299
160