Advertisement
Showing 36001 words to 39000 words out of 48659 words

Chapter 13 - Salon So Book Hausa Novels By Hadiza Salisu Sharif.txt

wallahi ina sonka ina kaunarka zuciyata tana son
kasancewa tare da kai koda yaushe.
Ya yi mata kyakkyawar runguma yana sumbatarta
da haka suka je suka yi kataccen break.
Ya dauko abayarta ya sa mata ya rufe mata kanta
da karamar hijabi fari mai kyau yaja hannunta suka fice yawon zaga gari.
Hakika ta sha kallo ta yaba da tsarin kasar London
gari ne me kyau da ban sha awa. Ita dai ba don
tunanin iyayenta da 'yan uwanta ba, da ta roki
Haidar su dawo kasar nan da zama sai dai ba za ta
iya ba saboda kulafucin iyaye da 'yan uwanta. Sun zaga sosai daga nan suka dire a wani
hadadden gidan abinci girke girkensu sun kayatar
da jawahir ta ji dadin abincin sosai har ta rinka
santi. Sai yamma likis sannan suka koma
masaukinsu.
Washe gari ma wajen sga biyu suka fita, ya rinka zagayawa da ita suka dire a wasu kamfani na kera
akwatuna ya zabo mata set biyu masu kyau sabon
dizayin don a lokacin ma ba su zo nan ba. Da masu
ruwan zuma da masu ruwan toka. Daga nan suka
wuce wani tafkeken
shago na saida gwala gwalai, tare suka rinka zagayawa, duk
in da ya hango me kyau in dai ta bashi sha'awa ba
ruwansa da tsadarta sai ya dauko mata sarkar kafa
me kyau ya kara a kafar jawahir tuni ya ga sun
kara haskakat kafar tata
Ya kuma dakko sarkar hannu itama ya kara mata
subuhanallah tuni yaga kyakkyawar matar tasa ta
sake fitowa sosai
Abin ya ba wa jawahir mamaki, yanda ta ji an buga
kudin mai yawa taga ya biya duk tsadarsu bata re
da ya damu ba. Ta matso dab da shi ta kwantar da kanta akan
kafadarsa ya sa hannu biyu ya rungmeta "My love
don Allah ka daina yawan kashe min kudi don
hidimar da kake yi min ta yi yawa.
Ya dada rungume ta yana dan bubbuga bayanta
kada ki damu bebyna komai na mallaka a duniyar nan naki ne ki daina damun kanki don na kashe
miki 'yan kalilan din kudi."
"To Yayana na gode Allah saka da alheri Ubangiji
ya kara budi.
"Yauwa Bebyna, amin"
Ta rada masa a kunnensa "My love" mu koma gida abincin jiya."
Cikin dariya ya kama bakinta wannan bakin ya iya
kwadayi ko, ta manne kanta a kirjinsa tana
murmushi suka wuce gidan abincin.
"Yan kwana biyun nan jawahir tana fama da yawan
kasala da lalaci ga yawan bacci, yanxu basu fi ya dadewa hira ba sai jawahir ta kama bacci.
❤❤❤SALON SO❤❤❤
❤❤❤ PART 36 ❤❤❤
.
By Sulaiman Bomboy.
.
Abin da Haidar yake dauka yawan gajiyar da ita da
yake yi ne shi yake yawan sa mata kasala.
Yau ma tare suka shiga toilet wanka suka yi suka
cuda junansu cikin farin ciki tare da wasanninsu na
ma'aurata. Ya kinkimota ya fito da ita ta zille daga
cikin sa ta koma daya dakin don ta shirya. Haidar ya gama shirin cikin wando iya gwiwa wato tree
gwata da riga marar hannu me kyau yana ta kyalli
don shima fatarsa ta kara gogewa. Kowa ya kalli
shi yasan fatarsa ta kara goge da hutu da jin dadi
irin na masu da shi.
Jawahir ta gama shirinta wani mini siket iya cinya da ya matse mata cinyoyi sai dai yana da tsaga
gaba da baya.
Rigarta iya kirjinta ta tsaya cibiyarta a waje ta ke
fuskarta ta kara haske da kyau da kuruciya
yarintarta ta kara fitowa fili. Jikinta sai fitinannen
kamshi ne yake tashi me ta da sha awa. Ta dawo dakin da ta bar shi saboda zazzabi da ta
ke ji ga ta shin zuciya, yana tsaye yana fesa turare
ta zo ta kwanta a bayansa tare da zagaye shi da
hannuwanta ya kamo ta ya zagayo da ita gabansa
tare da cewa "Bebina lafiya me yake faruwa ne da
ke, jikinki duk ya canja ga yawan lalaci da bacci.? Ya dauke ta suka koma kan kujera suka zauna
yana lallatse jikinta don ganin ta kamaimai me yake
damunta, duk ta narke a jikinsa ta langabe tana ta
zuba masa shagwaba tare da marairaita.
"Bebina muje asibiti a duba min ke don na san me
yake damunki. Cikin ma rairaita ta ce "My love ni bana so muje
asibiti don kada suyi min allura idan na sha fanadol
ma zan samu sauki" Ya ce "Haba bebyna ya za ayi
na barki haka kin ji jikinki kuwa yanda ya dau zafi
ya kama lallatsa wayar likitan Hotel din ta rike
hunnansa kamar za tayi kuka. Don Allah "My love kada ka kirawo shi wallahi na
sha magani zan ji garau. Ya ce ke dai kin fiye tsoron
Allura."
Ya hada mata break yana bata a hankali tana kau
da kai alamar ba ta so don bata jin dadinsa ya rinka
lallaba ta yana ririta ta har ya samu ta dan ci. Ya bata magani ta sha ta kwanta a jikinsa tana dan yi mata
tausa tare da mammatsa mata jikinta.
Bacci ya kuma dauke ta ya gyara mata kwanciya a
jikinsa lokacin da ta tashi jikin nata da sauki daga
nan London suka wuce kasar America jawahir tayi
mamakin yanda taga Amerika ashe itama haka take da kyau gaskiya kasar ta bata sha awa.
Nan ma Haidar ya bude bakin aljihu yai ta narka
mata kudi kamar vai san zafin nema ba. Watan su
daya a Amerika suka dire kasar Saudiya jawahir
tayi kyau har taga ji da kyau ta kara haske da
kuruciya, duk wanda ya kalle ta zai gano yaron ciki a jikinta don wani dan ya cewa da ta yi da wani
shirtaccen kyau da ta kara, nonuwanta sun sake
cikowa suna tsaye kyam da su. Haidar yana ji da ita
yana lailanta duk da canjawar da jawahir ta yi
hakan bai sa Haidar ya gano ajiyar da ya yi a jikinta
ba, bare ita da kuruciya ta yi mata yawa ita dai tana jin canji a jikinta amma bata dauke shi a komai ba,
bare ta kula.
Suna ta shirye shiryen dawowa gida sun sayi
tsaraba ta 'yan uwa da abokan arziki kamar masu
shirin bude kamfanin sutura, da kayan kyale kyale.
Jawahir tana kwance lamo a kan gado zazzabi ne me zafi ya rufe ta lokaci daya Haidar ya shigo ya
zauna gefen gadon yana cewa kasa uwar bacci ba
dai daga wannan 'yar fitar tawa har kin koma
baccinba.?
Ya sa hannu zai dago ta ya ji jikinta da zafi. A gigice
ya dako ta ya rungume ta a jikinsa yana jero mata tambayoyi "Bebina me ya same ki daman vaki da
lafiya, baki gaya min ba daurewa kawai kika yi?"
Bai jira amsar ta ba ya sabe ta a kafada ya yi waje
da ita, motar Hotel din ya yi amfani da ita ta xuwa
asibitin.
Likita Bilkisu muhd Adam ta karbe ta cikin gaggawa ta shiga yi mata tambayoyi da gwaje
gwaje a lokacin ta yi mata sukanin ta hango
karamin ciki dan wata uku a jikinta.
Haidar ya
juyo cikin farin ciki ya dako kan jawahir yasa
harshensa yana lashe hawayen nata. Yasa hannunsa kasar mararta yana dan shafawa ya
rada mata a kunnenta babyna mu duka mun yi
kuruciya da wauta sai dai mu kiyaye gaba sai dai mi
ta addu'a Allah ya raya mana Bebinmu Allah ya fito
mana da shi lafiya."
Ta ce, "Amin cikin shagwaba ta ce ka huce my love."
Ya sake rungumarta na hakura bebina tun da ke
ma ba laifinki ba ne na mune da rashin kulawarnu.
Nan fa sabon tattali da ririta suka tashi don Haidar
daga kansa yake yiwa jawahir wanka wai don
kada ta wahala duk wani abu da take yi masa yanzu shi ya dauke mata nauyinsa. Ita kuma ta kan
shagwabe masa ta ce yana ta aikin lada haka yake
so ta zauna ba nono.
Ya ce "Ai aikin lada da yawa yi min kiss shima lada
zaki samu. Ya turo mata kumatu ta cije shi ya da fe
wajen a'a a'a bazan yarda ba sai na rama. Da ya yi kanta zai turmusheta sai ta daga hannu
sama tana cewa bebinka bebinka zaka wahalar
dashi ya yi dariya ya dumgure ta."
Ta yi dariya don Allah yaya mu goma gida mana.
Ya zaro ido "Ke yaushe zan yarda mu shiga jirgi da
wannan dan ta yin cikin nawa." Salon kisa wabi abun ya faru da shi ai mu da mu
koma gida sai kin haihu su ganmu da bebinmu. Ta
marairaice ta fada jikinsa ta saka kuka ya dagota
yana dariya to to sarkin shagwaba yi shiru da
gangan nake yi rana ita yau jirgin mu zai daga
zuwa Nigeria Ta kuma kankame shi tana kyal kyala dariya,
Haidar ya gama luguiguita jawahir dukjansu zube a
gado suna mayar da numfashi.
Hannun Haidar yana kasan marar jawahir yana
shafa bebinsa.
Ya ce ko kin san wani abu? Ta girgiza kai ya ce sai da likitan nan ta fara gaya min kina da cikinsa nan
na gani alamomin hakan daga jikinki. Ga shi yanzu
har ya fara fitowa kamar ba dan wata hudu ba, ta
marairaice murya cikin shagwaba ta ce wallahi ni
kunya nake ji su ganni da cikib nan ai sai suce vani
da kunya daga zuwa jinya, na koma da dan rakiya. Haidar ya dada jawo ta jikinsa yana shafa bayinta
tare da dariya yace in banda abinki ni shi ne shedar
na warke.
"Kinga duk wanda ya kalle ki ba sai ya tambaye mu
an samu nasarar aiki ko ba'a samu ba, ta dada
shigewa jikinsa ta ce yanzu shi kenan kowa yasan abin da muka yi ko?
Ya kara tun tsirewa da dariya yanzu bebina in
banda abin ki akwai wanda ya taba sha a ruwa
ne?" Kowa kika ganshi da ciki ai ta haka ya samu ta
ce "Na shiga uku yanzu momyna da Dadyna da
Anty da Inna da Abbanka haka za su ganni da ciki gaskiya zan sha kunya kai ku wa ka yi min wayyo
babu ruwanka ko?
Washegari jirginsu ya daga zuwa Nigeria da yake
an san da dawowarsu 'yan uwa iyayensu sun zo
taryarsu babu wanda yasan jawahir tana da ciki sai
dai idonsu ya gane musu. A cikin jirgi, jirgi yana jama'a aka fara sakkowa,
Haidar ne a gaba jawahir tana biye da shi sun yi
kyau sun dade kara ja da fari jin dadi da hutu ya sa
sun haske wajen kowa ya kalle su sai ya sake
duban su ba don murmushin da su ke dokawa ba,
da iyayensu basu gane su ba. Suna sakkowa jawahir zata kwasa da gudu ganin iyayenta Haidar
ya riko ta yana ce matw ki kula kada ki yi min
ganganci da ciki."
'Yan uwa suka yunkuro gaba daya suka taro su
jawahir ta durkusa kasa ta kama kafar babanta ta
rike tana me jin dadi da murnar ganinsu. Ya sa hannu ya dagota yana kallonta fuskarsa cike
da murmushi na yanda yaga 'yarsa ta kwantar da
hankalinta gashi yanda ta kara kyau da haske
kamar balarabiya.
Inna ta dafa kafadarta jawahir ta juyo ta rungume
ta tana murna Inna ta dako ta cikin dariya ta ce ke taurin me nake ji haka? Ko dai kin samo mana dan
London? Kai amma abu ya yi kyau."
Dady ya ce "Menene?"
Inna ta ce, "Ciki ne da ita da sauri jawahir ta fuzge
jikinta cikin jin kunya taje ta rungume Mominta da
Antinta, ta je ta gaisa da Abban Haidar. Nan fa sukai ta gaisawa da 'yan uwa ana murnar
ganin juna. Daga nan suka rankaya gaba daya don
raka su gidansu. Jawahir ta yi mamakin canja
fasalin gidan nasu da aka yi, ya yi masifar tsaruwa,
don ya fi na da ma kyau, tsadaddun kujerun da
kayan kyale kyalen da suka suyo a kasar waje. An kawata babban falon da su, sai ka ce falon
sarauniya America don tsananin tsaruwa da kyau
da ya yi sai da aka ci aka sha sannan iyayensu suka
taya su murnar samun lafiyar. Haidar da karuwar
da suka samu.
Kowa ya fashe, sun tattafi ma'aikatan gidan suka kara gyara gidan ko ina ya kara yin fes sai sheki da
kyalli ne yake tashi da hadadden kamshi.
Da daddare "Faruk ya zo suka rungume juna shi da
Haidar suna murnar sake ganin juna.
❤❤❤SALON SO❤❤❤
❤❤❤ PART 37 ❤❤❤
.
By Sulaiman Bomboy.
.
Jawahir ta shigo masa da kayan ciye ciye suka
shiga gaisawa. Faruk ya ce "Mutumin lallai naga
alamar ka warke har da tsarabar dan london ne ko jafan ko dan ijift ne ko America? Naga alamar
kamar jawahir tana da ciki ko?"
Haidar ya yi dariya ya ce "Ai ma ganinku nayi masu
tambaya yanxu kuwa kowa ya kalle ta yaga
shedar aiki ya yi kyau.
Suka kyalkyale da dariya tare da tafawa Faruk ya ce, "Bakinmu da nayi muku dai ya kama ku to Allah
ya raba lafiya, Ubangiji ta sa masu amfani ne ya
bamu masu albarka, don Hafsat tana can da nata
tsohon cikin.
Kai mutumin lallai kayu aiki, to Allah ya inganta
mana, Ubangiji ya raba su lafiya da shi. Bayan sun nutsu sun huta suka bude tsarabobi suka rinka bin
'yan uwa da dangi suna rabo kowa aka bashi
tsaraba sai ya jinjina kudin da aka kashe masa.
Jikaken abu mai muhimmanci da tsaraba da mutum
sai yaga kamar shi suka yiwa tafiyar. Anty Maryam
ma da Uncle har gida suka zo yi wa su jawahir barka da kuma yi musu sannu da zuwa.
Da yake hutun su suka dakko zasu dade a nan a
gidan Ankul din suke zaune wanda ya zauna farkon
aurensa kafin aiki ya maida shi Abuja.
Jawahir ta
sha murna da ganin Antyna Maryam ta rungume ta suna ta dariya cikin jin dadi da walwala kamar sa
hadiye junansu.
Anty ki ce kin kusa haihuwa don naga cikin naki ya
yi tsini da yawa."
Ta ce "Haka Ankul dinki yake cewa wannan cikin
ya fiye girma da yawa wai yana takura shi don na fiye langwai.
Jawahir tasa dariya ai gaskiya Anty sai yanzu na
gano sirrin da ya sa Ankul ya ke manne miki ko, na
ce ku ke manne wa juna, ashe haka rayuwar aure
take?
Hakika jawahir rayuwar aure aba ce mai dadi da nishadantarwa kwanciyar hankali da samun
nutsuwa. Amma fa duk wa 'yannan abubuwan
basa samuwa sai ka yi da ce da abokin rayuwa
nagari."
Haidar ya yi sallama ya shigo tare da cewa da
Maryam "Antynmu ai kin yi nauyi da yawa, da kin hakura da zuwan da sai muzo har gida mu gaishe
ku."
Ta yi dariya tare da cewar ai bazan iya jure rashin
ganin diyata ba, yanda ake yi min zuzutun kara
kyan da tayi amma da nazo ai na gani idona ya
gane min kyakkyawar kulawar da ka yi ma 'yata. Ya yi murmushi ya kalli jawahir ya ce, "Bebina zamu
fita da Ankul xuwa dare zamu dawo." Ta
marairaice fuska kamar mai shirin kuka ya dafa ta
"Haba bebina mene ne kuma bana so ki bata ranki,
ba ga Antynki nan zata taya ki hira ba, sai mun
dawo zai dauke ta su ta fi. Ta yi murmushi yayin da ta juyo ta kalli Anty maryam. Ta ga ita ba ta saurari
su ma, hankalinta yana kan littafi tana karantawa.
Haidar ya riko ta suka yo falon tsakiya ya zauna a
kujera ya dorata kan cinyarsa "Meye damuwarki
babyna?
Ta yi rau rau da ido har sunkawo kwalla ta ce "Ni ba komai va ne ina tsoron kada Ankul ya sake
cewa ka dawo da Kausar ne, ba zan jure ganin
kana yi mata magana ba bare har ka shiga dakinta
ka kwana mun zama mu biyu da matsayi daya a
wajenka ta saki kuka.
Haidar ya rungume ta yana rarrashinta. "Kar ki damu Bebyna, daman can kaddara da
sha'awar kare kaina daga zina ita ta sani auren
Kausar, ki sa a ranki tsakanina dake mutu ka raba ne
takalmin kaza aurenmu auren zobe ne ba saki
ba yaji ba kishiya har avada.
Kuma na ji wai SULAIMAN BOMBOY za ta aura. Ta ce, "waye kuma SULAIMAN BOMBOY?" Ya ce wani yaro
ne dan karami amma ya nace wai shi a lallai sai ita.
Ta ce, "Um. Ta dako kai da sauri "Allah yayana?
Ya ce, "Sosai ma kuwa ta yi saurin kankame shi
tana sumbatarsa, cikin murna ya dako ta yana
dariya muje kada Ankul ya gaji da jira. Suka fito babban falo jawahir ta ce "Ankul ka bar
min Anty ta kwanar min anan." Ankul ya girgiza kai
ya ce, jawahir kenan har yanzu
dai kina tare da kuruciya, to idan haihuwa tazo
kuma cikin dare ku yi yaya da ita, ku da kuke duk
farin shiga? Gaba daya suka sa dariya suka fice ita kuma ta
koma gun Anty maryam suka bude shafin hira. "Kin
gane ne Anty ni fa yanzu abun da nake tsoro
kada Haidar ya dawo da kausar don ban san yanda
zan yi ba, a da ban damu da aurenta sosai ba don
sannan ban damu da Yayan ba, amma anya yanzu yanda nake son Yaya Haidar muka shaku da shi
yake sona yana ririta ni yana tarairayata kamar kwai,
zan juri ganinshi da wata matar, wai! Naga
mace a rungume a kirjin Haidar, subhanallahi Allah
ma ya kiyaye, Anty ai wuka zan soka mata ta mutu
nan take. Maryam ta tuntsire da dariya ta ce "Allah ya kiyaye
jawahir," Anty maryam ta ce "Ai na gaya miki wasu
matan su suke jawowa kansu ake yo musu kishiya,
na farko akwai matan da girman kai da ji da kai
tsabagen muskilanci ya yi musu yawa, to yawanci
masu irin wannan halin sai ki ga har mazajensu na aure su ke yiwa ko suna mantawa a karkashin
mazajen su suke? Dole mazan su ne gaba da su, dole
ne duk matsayinki da jin kanki, ki sauke su ki
yiwa mijinki biyayya ko dan ki samu tsira ma ranar
gobe kiyama, domin aljannar mace ta na tafin kafar
mijinta sai ya daga zaki shiga. Abu na biyu kuma shine, kazanta, sai ki ga mace awaje dagwas
dagwas da ita amma da zarar ta yi aure ta haihu sai
kiga ta zama kazama. Ba za ta tsaya ta tsabtace
kanta ba bare abincinsu ko abin shansu.
Wasu matan za ki ga kudin da aka ba su na cefane
a ciki zasu raga su boye baza su yo cefanan na duka ba bare su sarrafa girkin yanda zai yi dadi. Sai
mace tai abinci garau garau ba wadataccan kayan
miya bare mai kiji abinci kadas babu dadi abinci
babu kyau a fuska.
Bayan ta gama girkin ba ta san tai wanka ba ta
gyara jikinta, a'a sai ki ganta daga ita sai daurin kirji tana ta fama da kaurin wuta. Da kin doshi dakinta sai
zarnin fitsarin da warin dauda. Kin kai wa namiji
abinci ya yi cokali biyu ko uku ya ji ya kasa ci ya
ture saboda rashin dadi.
Baruwanki da kwantar da murya bare ki bincike
shi me ya hana shi cin abincin, a'a ke babu ruwanki sai ki ja kwanon gabanki ki kama ci ko ki kirawo
yaranki ki ce kuzo ku dau abinci babanku ya rage,
babu ruwanki da damuwarsa.
Idan dare ya yi kina kwance cikin yaranki kin saki
baki kina munshari kin bude nono kin saka wa
yaron da kike goyo a baki kin riga kin sabar masa, sai da nono a bakinsa zai yi bacci, da maigidanki ya
zo ya taba ki don ki taso yana da bukatarki ki kama
miya kina faman zumburar baki ke an takura miki
kin gaji, daren ma ba za'a barki ki huta ba, saboda
Allah mijin nan naki waliye ne da ba zai bukataci
mace ba in har Allah ya kare shi daga sharrin zina? Ai kuwa dole ya yi kokarin karo aure ko dan ya
samu me debe masa sha'awa.
Jawahir ta ce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login