Showing 15001 words to 18000 words out of 48659 words
Chapter 6 - Salon So Book Hausa Novels By Hadiza Salisu Sharif.txt
ce, "Au ta zo ne?
"Uhm wai rigima suka yi da mijin nata ta taho.
Ya ce, "Ikon Allah ai ni ban ma sani ba bari na
tambaye ta
Ya dau waya ya kirawo momy ta yi sallama ta shigo ta nemi waje ta zauna. Ya kalle ta ya ce, "Ina jawahir
take?
Momy ta ce, "Tun da aka yi auren ta ba ta zo gidan
nan ba. Wani abu ne? "Wai sun yi rigima da mijin ta
taho.
Momy ta ce, "Oh ni 'yasu, yara ne ka haife su ba ka haifi halinsu ba, yanzu duk fadan nan da aka yi wa
jawahir sai da ta sabawa nijinta.
Aunty ta ce, "A'a ai ba laifinta ba ne, da ai lafiya
suke zaune auren nan da ya rakitowa kansa duk
shi ya hargitsa musu zaman."
Momy ta ce kin ji irin shashancin ko, ai komai na Allah ne, namiji da aka halicce shi don mata hudu
ka hana shi kara daya.
Aunty ta ce, A'a ba ta fa da laifi ko ke da kika girma
da Yaya ai ce zai kara aure da sai kin hana mu
sakewa bare ita da ga yin aure shekara daya a ce
namiji zai maka kishiya, ai dole a ji kanku. Dady ya ce, Ai kun san ma ba za ta zo nan ba tun da
ta san ba goyon baya za ta samu ba. Tana gidan
Inna, tun da ta je hannun Inna kuwa kwato ta sai
wani ikon Allah. Aunty ta ce, "Ai maganinsa kenan
wallahi gwanda
ta hora shi tukunna. Momy ta ce, "A'a ni dai ba na son son kai don dai
kin ga 'yarki ce kawai kuke son ga sa masa gyada
a hannu.
Dady ya ce, Ba me wahalar min da da, duk zan tara
su na san meye matsalarsu. Hankalin Haidar ya kara
mummunan tashi yayin da ta bayyana cewa jawahir ba ta gidansu. Goma na dare Haidar ya isa
gidan Inna a gigice yana neman jawahir din.
Inna ta fututtuke ta ce ita yaushe rabon da ta ga
jawahir ma? Wallahi ya je duk inda jikarta ta take ya
nemo mata ita in ba haka ba kuwa ya gamu da
fushinta. Haidar kamar zai yi kuka magiya yake yi wa Inna
idan ita ta boye jawahir ta fito da ita don ya ga
motarsa a gare jin gidanta wadda da ita jawahir din
ta fito. Inna ta ce, To sai dai in zuwa ta yi ta ajiye
motar ba ta shigo ba ta fice, "Ta ce, "Na gaya maka
wannan kame-kamen ba zai yi maka ba, ka je ka nemo min jikata. Sha daya na dare ya bar gidan
Inna ya isa gidansa.
Ikon Allah ne kawai ya kai shi gida, amma haka ya
kwana yana juyi da tunanin inda za a ga jawahir.
Ga yunwa ta gallabe shi ga ba abinci, shi kuwa ko
ruwan shayi be iya dafawa ba, bare ya dafa ya sha. Haka ya yi ta juyinsa har aka yi, sallar asuba. Daga
masallacin gidansu ya taho a motarsa. Abba ya yi
mamakin ganinsa inda yake tambayarsa, "Lafiya
haka da asuba.? "To Abba ina zan iya samun
sukuni ba a fa ganta
ba. "Ba ka ce ka ga motar gidan Inna ba.?"
"Ai Inna ta ce ita ba ta shigo mata ba ajiye motar ta
yi ta san tana waje.
Allah ya kyauta, Abba ya lallaba shi ya yi wanka
suka yi
break tare. Abban ya dauko shi suka yo gidan Inna wai ko za su ga jawahir din. Amma Inna tana jin
tsayuwar mota ta tura ta wani dan daki ta yi
zamanta a falo.
Abba da Haidar suka shigo duk yanda suka yi don
su bigi cikin Inna su ji ko jawahir tana gidan Inna ta
fututtuke ta ce ba ta zo mata ba. Dole suka hakura suka yi mata sallama suka fita.
A mota kawai Haidar sai ya sawa Abbansa kuka,
"Don Allah Abba ka tainaka min a ga jawahir,
yanzu in ban gan ta ba ai na shiga uku ya zan yi da
rayuwata?
Ya dafa kansa ya ce, Ka yi hakuri Haidar za a ganta ne insha Allahu.
Bayan fitarsu Inna ta yiwa danta Aminu da yake
Abuja waya ta gaya masa komai ta ce tana so ta
turo masa jawahir nan kada ya sake ya ce tana
gunsa. Aminu ya amsa da to! Ya ce da kansa zai zo
tararta filin jirgi. Jawahir ta gama shirinta a boye direban Inna ya kai
ta filin jirgi ta hau zuwa Abuja sai da ya ga tashinsu
sannan ya dawo ya shaidawa Inna.
Can kuwa Uncle dinta yana Airport yana zaman
jiranta. Yana hango ta ya taro ta da murna suka
rankaya zuwa gidansa matarsa Maryam ta yi farin ciki da ganin jawahir, don Maryam mace ce mai
faran-faran da son jama'a ga ta wayayyiya. Irin
gogaggun matan nan ne wadanda suka san
makamar kama da namiji. Ba bata lokaci Uncle ya
karbi takardun makarantar
jawahir ya samar mata University of Abuja. Ba bata lokaci jawahir ta zamo daliba a jami'ar.
Jawahir an shiga cikin wayayyun 'yan matan jami'a
ta goge ta kile, ta kara kyau da girma babu yanda
za a yi wanda bai yi mata cikakken sani ba, ya gane
ta, don yanda Maryam ta ke gyara ta kamar 'yar
cikinta don wani magunguna da tsumi na mata da take dibga mata tana sha. Sai maganin ciko da
nono da tsaitsayar da su don har ya zube, shi take
ba ta tana sha.
Kasancewar hankalinta a kwance yake ta yi 'yar
kiba ta murje jikinta mulmul kamar na jariri, sabon
haihuwa. Kirjinta ya cika fam yana tsaitsaye ba shi da alamar rankwafawa, duk wanda ya kalle ta sai
ya juya ya kara kallonta saboda tsabagen haduwa
da wani shirtaccen kyau da ya kara bayayyanar
mata.
(((((((SALON SO)))))))
((((PART 19 TO 20))))
:
BY SULAIMAN MUSA MUHAMMAD (BOMBOY).
.
HAIDAR ya kasa samun nutsuwa dole ya nufi gidan abokinsa Faruk don yanke shawarar da za ta
fisheshisu. Yana zaune a falo Faruk ya hada kai da
guiwa yana ta tunani tare da karanta wasikar jaki.
Faruk ya shigo falon tare da yin sallama. Bai jira an
amsa sallamar ba don ya san ba zai samu ba ya
karaso ya dafa kafadar Haidar ya ce, Me yake faruwa ne da kai aminina? Wace matsala ce kuma
take kokarin danno maka kai ne? Kai da za ka yi
auren ke ce raini.
Ya ce, "Kyale ni Faruk abin duniya duk ya dame ni,
ko ka san jawahir ta gudu ban san inda ta nufa ba.
Faruk ya dafe kirji ta gudu fa ka ce? Me ya hada ku, ko na ce me ka yi mata? "Uhm kai dai a yi sha'ani,
wai daga na yi maganar aure zan yi sai yarinya ta
gudu.
Faruk ya ce, "Ai madallah ka ga irin abin da nake
jiye maka ko, to ai ga irin ta nan yanxu sai ka je ka
bunciko ta a duk inda take. Haidar ya ce, "Wallahi ni dai ina zaton tana gidan Inna don mota ta da ta
dauko ta taho da ita, na ganta a gidan Innan. Sai
dai amma Innan ta kafe ta ce jawahir din ba ta
gidanta.
Faruk ya ce, Ka ga taso mu kaje kawai mu
shammace ta ba tare da munyi sallama ba mu shiga kawai in tana ciki za mu gan ta. Suka mike suka yi
gidan Inna Haka suka danna kai falon Inna babu
sallam abun mamaki ba jawahir sai Inna da ta yi
zumbur za ta tashi ta ce ni har kun tsorata ni lafiya
kuka shigo min haka babu sallama? Faruk ya
durkusa yana gaishe ta Haidar kuwa zubewa ya yi a kasa yana yi wa Inna magiya inna
don Allah don Annabi Inna ki taimaka ki fito min da
jawahir.
Inna ta ce, Haidar me kake fada ne? Ni na san inda
jawahir take ne? Faruk ya ce, "To ai ni abin da ya fi
ba ni mamaki ya a ka yi motar ta zo nan gidan, "Inna ta ce, "Ni dai ina zaune aka aiko min da
mukullin motar na ajiye na zata ma ko tare suke da
Haidar din motar ta lalace musu suka ajiye ta, su je
su dawo. Ta mike ta shiga dakinta ta fito ta ce ga
mukullin motarka nan kada ku sake zuwar min
idan ba jikata kuka gano min ba. Haidar cikin marairaita kamar zai yi kuka ya ce, "To
yanzu Inna ya za a yi da neman jawahir din.?
Cikin fada ta ce, To ya za a yi kuwa? Da ka rike ta
hannu bibbiyu ai da haka ba ta faru ba ko? Yanxu
da ka yi sakaci da ita ta bata ai ko wa sai ya huta. A
dauki yarinyar nan cikin girma da mutunci 'yar uwarka ta jini a baka amma ka rinka wulakanta ta.
Ya yi saurin cewa, "Wallahi Inna ba wulakantata
nake ba wai don kawai na ce, zan kara aure shi ne
ta yi tafiyarta.
Inna ta ce, "Uhm ai ka ga yanzu ta bar maka filin
gidanka ka fi sakewa kai da Amaryar taka sai ka je kai ta yo auren.
Faruk ya ce, "Inna hakuri za a yi in dai an san inda
take din a fada mana.
Ta ce, "To ban sani ba ku tashi ku ba ni waje.
**** ****** ****** Maganar jawahir kuwa tana
gidan Ankul dinta ta dage da karatu don makaranta biyu zan ce take yi.
Tana zuwa jami'a yayin da kuma Ankul dinta ya
daukar mata lakcara guda yake dada tunasar da ita
da nusar da ita halayyar dan Adam, yanda ake iya
zama da su sannan yana koya mata dabaru na iya
kasuwanci da yanda za ka sarrafa kudi duk kankantarsu don juya su.
Ta bangaren jawahir kam ma iya cewa
Alhamdullihi, don komai a ka gaya mata ya zauna a
kwalkwalwarta kenan da yake yarinya ce me kaifin
basira da kokari. Jawahir ta gama nazarin abun da
aka yi musu lakca a yau ta mike a gajiye ta shiga toilet ta yi wanka ta
gama shirinta ta fito falo ta samu Auntynta a zaune.
Maryam ta kalle ta tayi murmushi, "Tubar kallah 'yar
gidan Ankul ba dai kyau ba, zo ki zauna na dora
miki inda muka tsaya don so nake yi ki mallake
Haidar tsab yanda ya raina ki yake kiranki da tatsitsiya ko kwaila to yanzu ki zame masa dan
hakin da ka raina.
Yanzu abin da zan fara miki da shi shine zan koya
miki kissoshi kala-kala don haka dauko littafi da
biro ki rubuta komai don gudun mantawa. (Saboda
haka idan kuna so nima na fada muku to kowa ya/ ta dauko biron shi/ta domin nima saida na rubuta
sannan na iya kawo muku badon haka
ba........hmmm. Gani nan ina zagayawa fa. Hhhhh su
o'o akwai akwai tsoro ji harda rawar jiki kar na
ganta ba paper). Jawahir ta mike ta dawo da littafi
da biro, "To yanzu za mu fara da kissar tsafta don ita ce kan gaba a kan
komai. Ki kasance mai tsaftar gidanki ko da yaushe
cikinsa da wajensa. Kicin dinki ya zamo a gyare a
share, a goge ki turara masa turarukan wuta me
dadin kamshi. Toilet dinki ya zamo kullum cikin
gyara idan kika wanke kika goge komau kika cire yana ki masa nasa turaren wutar na musamman ya
kasance cikin kamshi wanda mutum ya yi bahaya
wannan kamshin zai kashe masa jin warin bahayan
nasa, idan ba ki da lokacin yin wanki da kanki to a
ajiye almajiri idan sun kai kala biyu zuwa uku ki ba
shi ya wanke ya goge miki, idan kin tashi sai ki turare kayan naki da turaren kaya sannan ki jera a
kwaba. Sai kuma kwabar ki sa mata turaren kaya
don gudun warin ruma da dai sauransu. Ki kasance
mai kwasar shimin mijinki, gajeren
wandonsa, hankijinsa da dai wani karamin abu da
yake amfani da shi ki wanke, ki goge su ki turare su da turaren kaya ki adana masa su. Idan kin
shiga wanka ki rinka amfani da daddadan sabulu
me kyau da dadin kamshi. Ki rinka cuda
hammatarki, kasan nonuwanki, matse-matsin
cinyarki, ki rinka wanke gabanki sosai da sabulu
me kamshi, duk wani lungu da sako na jikinki ki wanke shi ki gyare shi fes in da ko ina mai gida ya
sa kansa zai ji kamshi.
Ki kasance ko yaushe cikin gamsasshiyar kwalliya,
ki daure da asuba idan kun yi sallah me gidanki zai
ja ki ku koma gado ku kwanta, to ki yi kokarin
hana kanki bacci. Har sai shi ya yi sai ki janye jikinki a hankali ki tashi ki nufi kicin don hada muku karin
kumallo.
Kada ki yi masa break kala daya saboda saurin
ginsa ki yi masa kalolin break kowanne ki zuba a
fulas gudun kada ya huce. Daga nan ki jere su a
tebir ki gyara wajan ki da turare ko ina da daddadan kamshi me sanyaya zuciya, sai ki je ki yi
wanka ki bata lokaci wajen yin kwalliya wannan fa
kwalliyar safe ce ta barka da tashi me gida. Za ki
saka les ko atamfa ko shadda ko boyal duk
dai wanda ya samu, za ki feshe jikinki da kalolin
turaruka masu kyau da dadin kamshi wanda har za a kasa tantance wane irin kamshi kike yi, to sai ki
nufi dakin maigida. Ba a tashin miji da hayaniya ko
surutu ko ki yi ta jijjiga shi kina kiran wane! ka tashi
lokaci ya yi, in kika yi irin haka za ki bata ran
maigidanki.
Abin da kawai za ki yi shine da kin shiga dakin mijinki kin ga yana bacci ga lokacin tafiya Office ko
kasuwa ya kusa, to sai ki zauna a gefen gadon ki
sa hannuwanki kina shafar fuskarsa kisa bakinki
kina hura kunnunsa a hankali kina shafa fuskarsa
tare da dan jan karan hancinsa. Ko ki fara shafar
kasan mararsa kadan-kadan. To za ki ga ya tashi a nitse ba tare da magagi ko tsaki ba, da ya mike ya
shiga toilet ko kafin ya fito sai ki yi saurin gyara
gadon ki debo masa kayan da zai sa hade da best
da gajeran wando da dan hankici duk kuma ki
feshe su da turaruka masu dadin kamshi ki
debomasa takalmansa ki goge su fes, da ya fito daga toilet ki yi gaggawar daukan tawul ki rinka
tsane masa ruwan jikinsa sannan ki debo mayukan
da yake amfani dasu ki rinka shafa masa a hankali
kina yi kina ba shi labari na ban dariya a hirar
nishadi. Ki taimaka masa wajen sa kayan nasa, ki sa
karamin kum ki taje masa sumar kansa, ki dada dauko turaruka ki kuma feshe shi da su, ki sa masa
gilas idan yana da ra'ayi. Ki riko hannunsa ku taho
zuwa kan tebir kuna tafe a hankali kina yi masa
rausaya tare da yawan shigewa jikinsa har ku iso
tebir din. Ki rinka zuba masa komai kina turo masa
gabansa kada ki damu da sai kin ci a lokacin, ki rinka hada
masa abinci me yawa a gabansa ki rinka tura masa
kina yi masa shagwabar bai ci da yawa ba, ko ki ce
ke ba ki yarda ba sai ya cinye da sauran abubuwan
da za su ja hankalinsa ya saki jikinsa sosai ya ci
abinci ya koshi. Idan ya mike don ya tafi office ki roko masa jakarsa
kina yi masa 'yar shagwabar Honey da ka tashi
daga office ka yo gida kada ka tsaya wani wajen ka
ji. Honey idan ka isa office ka tsaida hankalinka ka
yi aikinka a nitse kada ka yi tunanin komai bare ya
sa min kai a damuwa. Za ki ga ya rungumoki tare da shi miki albarka duk kuma inda yake hankalinsa
yana kanki Allah Allah zai yi ya dawo gida don ya
tarar da ke.
To da ya tafi office ke kuma a wannan lokacin za ki
samu ki yi baccinki kafin lokacin girkin rana ki kula
me mijinki ya fi so, me ya fi sha awar ci don ki kiyaye wajen girka masa su, shinkafa da miya, ko
tuwon shinkafa da miyar taushe, ko danyar
kubewa, ko miyar agushi, ko miyar wake da
ganye, ko tuwon dawa, ko na masara, tuwon
semovita ko ki daka masa sakwara, ko ki dafa
kuskus ko taliya, zaki hada masa da soyayyen naman kaji ko gasasshen naman kasuwa ko
farfesun kayan ciki, ko farfesun kan rago ko na
jelar sa ko farfesun naman karamar dabba, ( A nan
ana magana ne idan mijinki mai hali ne, idan kuwa
ba mai hali ba ne sai ki yi masa abin da kika
tabbatar yana jin dadinsa dai-dai rufin asiri) To idan kika duba abin da ya fi so a cikin yi masa
kika gama komai kafin ya dawo, ki dada gyara
gidanki ki turare shi da nau'in kamshi kala kala, ki
shiga aiki sake fesa wanka sai ki yi kwalliya ki hade
da siket ko riga da wando ko doguwar riga ko
dinkakken shadda, ko atamfa, boyal, yadi, material, da dai sauransu, to ya kasance karamin dinki ne
dai-dai jikinki ki saka wanda da zarar maigida ya
dawo za ki tafi cikin salon murna ki ringume shi
kina me yi masa barka da zuwa. Ki fara raka shi
dakinsa ki cire masa kayan jikinsa ki hada masa
ruwan wanka da turaren wanka a ciki da ya shige tolet sai ki kwashe kayan da ya cire ki
rataye masa a anga. Ki fito masa da kanana na shan
iska. Da ya gama shirnsa ya fito sai ki zo a nitse
cikin dabara ki rinka loda masa abinci yana ci kina
fara loda masa wani yanda zai ci ba tare da ya gane
ya ci da yawa ba. Kina zuba masa sanyayyen abin sha yana ci yana sha, har sai ya koshi ya yi kat sai ki
jawo shi ku baje kan kafet ko kujera kuna wasanni
da hirarraki masu dadi ko kallo ku, ki rinka karanta
masa labarai masu dadi, amma ki kasance ko
yaushe kina manne a jikinsa ki rinka yi masa
shagwaba kina mai da kanki karamar yarinya a gabansa kina zama doluwa marar wayo ki rinka sa
yin dan sokoncin zai rinka sa mijinki dariya, to
yawaita masa irin wannan abubuwan shi zai kara
muku shakuwa da fahimtar junanku, za ku
kasance cikin bege da son junaku ko da yaushe.
Idan kin tabbatar kin wa mijinki lodi da abincin rana to yunwa ba za ta gallabe shi da dare ba, don
ba a so da daddare a ci abu me nauyi an fi so a ci
irinsu hadin salak, sharfar taliya me romo
gasasshen nama, ko hanta ko zaka, farfesun kayan
ciki ko na naman romon kai, ko na jelar sa ko
naman karamar dabva, kai da dai duk abin da Allah ya hore muku marar nauyi.
To kinga wadannan duk inya ci va za su yi masa
bauyi a ciki ba bare su hana shi su kuni su takura
shi wajen aiwatar sa sunnah Jan
hankalinsa ta suffofin kwanciya kala-kala. Duk abin
da kika kula ya fi so to ki lakanci abun duk sanda kuke tare ki rinka kirkiro wasu abubuwan ma da
bai san da su ba. Ki saki jikinki da shi ki cire kunya
ki rinka sarrafa shi kina dan kukan kissa tare da
kiran sunansa a hankali kina hadawa da kalaman
soyayya don tafiyar da imaninsa. Ki kasance cikin
yawan shan kunun aya, shan zuma, shan rake, lemon zaki, kankana, gwanda,
abarba, nono, dabino, cukwi, tufa, inibi, kin ga
wadannan ki kasance cikin yawaita cin su ko da
yaushe don suna karawa mace ni'ima da amfani
sosai a jikinta. Ki nemi garin bagaruwa gwangwani
daya, garin kurna gwangwani uku, garin habbatus sauda
rabin gwangwani, garin dakakken dabino ki rinka
samun busasshiyar aya ki daka sai ki hada su waje
guda