Showing 48001 words to 48659 words out of 48659 words
Chapter 17 - Salon So Book Hausa Novels By Hadiza Salisu Sharif.txt
biyu a tsakani jawahir ta ba wa direbanta waya
sabuwa da kudi dubu goma a ciki da lambar wayar iyayen Kausar ta ce ya kai wa Kausar.
Direba ya kama hanya ya kai wa Kausar ta rinka
murna tana kwarara wa direba godiya ta ce ya
mika mata godiya wajen jawahir din kafin tazo.
Direba yana tafiya, Kausar ta kulle dakinta ta buga
wayar bugu uku ana hudu aka dauka. Muryar babanta ta ji ta fashe da kuka, "Dady, Dady
nice Kausar kun gudu kum barni cikin halin kunci
da wahala.
Tana kuka tana gaya masa halin da ta ke ciki da ita
da mijinta tace yanzu mijinta bashi da komai suna
cikin kuncin rayuwa hatta lokacin da ta haihu bai yi mata komai ba, da yunwar da ta sha da bautar
girkin da take yiwa matan gidan da irin tsangwama
da cin mutuncin da ake yi mata har kawo irin
taimakon da jawahir take yi mata da binkicen da
jawahir ta yi ta samo mata lambarsu ta kawo mata
sabuwar waya da kati na dubu goma a ciki duk ta gama gaya masa.
Hankalin
babanta ya tashi ransa ya damu ya ce mata kiyi
hakuri da man kwanan nan muke son mu zo mu
duba ki ganin mun shekara daya da baro Nigeria.
Amma kisa idonmu a cikin satin nan muna tafe." Hankalin babarta da 'yan uwarta ya yi masifar tashi
da jin halin da Kausar ta ke ciki, ai basu iya hakuri
ba kwanakin ba cikin kwana uku suka dira a
Nigeria.
Iyayenta da 'yan uwanta har kuka suka yi jin halin
da Kausar ta shiga, nan fa aka shiga bata kashi tsakanin Bomboy da iyayen Kausar da kyar
suka samu ya sake ta.
Bayan ya sake ta ne, ya shiga daki yai ta kuka har
da ihu shi ya shiga uku. Yanzu yaya za ayi ya kuma
wani auren?" Da kyar su Amal Junior da Jauhar M.
Nas suka rarrasheshi. Suka zo suka ta yiwa jawahir godiya tare da sa
mata albarka.
Suka roki kuma Haidar gafara a bisa abin da Kausar
ta yi masa ya ce "Ba komai ai ya yafe mata.
Nan fa kyakkyawar alaka da zumunci ya kullu
tsakanin jawahir da Kausar da kuma iyayensu. Satinsu uku a Nigeria suka daga da Kausar da
'yarta da iyayenta zuwa America.
Cikin lokaci kankani Kausar ta murmure ta murje ita
da 'yarta ssuka shiga shafe shafen da ya bayyanar
masu da kyansu. Bata dade da gama idda ba
manema suka fito mata in da ta sake auren wani mai mata daya da 'ya'ya uku.
Ya riki kausar da 'yarta cikin gaskiya da amana in
da suke zaman lafiya da abokiyar zamanta.
Haidar da jawahir linkafa ta ci gaba sun zamo abin
kwatance da sha awa a Nigeria suna da 'ya'ya biyar
kenan 'yan uku Salma, Sadat, Salim sai Nana khadija da Mohammad auta.
Rayuwarsu me burgewa da ban sha awa kowa ya
shiga gidan baya son fita don ganin irin
rantsattsiyar SALON SO, ya yarda suke shimfidawa a
gidan.
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
KASH DAMA ANCE LAIFIN DADI KAREWA.
DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA UBANGIJI DA YA BANI DAMAR KAMMALA KAWO
WANNAN LITTAFI KAMAR YADDA MUKA FARA.
TSIRA DA AMINCI SU KARA TABBATARWA GA SHUGABA
ANNABIN RAHMA (S.A.W), ALAYEN SA DA
SAHABBAN SA. DA FATAN MUN KARU DA DARUSSAN
DA MUKA GANI A CIKIN WANGA LITTAFI, ALLAH YASA MUYI KOYI DA MASU KYAWAWAN HALAYEN
DAKE CIKIN SA YA KUMA TSARE MU DAGA AIKATA
MUNANAN AYYUKA MAKAMANTAN NA WASU DA
MUKA JI A CIKI. TOHHH!!! INA FATAN NIMA XAKU
TAYA NI ADDU'AN SAMUN WATA MATAR TUNDA
MAFARKI NA TA SUBUCE MIN WATO KAUSAR. SAI MUN HADE A WANI SABON LITTAFIN INSHA ALLAH..
WASSALAM.