Showing 45001 words to 48000 words out of 48659 words

Chapter 16 - Salon So Book Hausa Novels By Hadiza Salisu Sharif.txt

da
Abbansa ya daka masa tsawa ya nuna masa bacin
ransa a zahiri sannan ya bari aka tafi da su jawahir
da yaran gidansu.
Shi kuma Haidar ya yi fushi ya yi nasa gidan ransa a
bace, yana shiga gidan yaga bakinsa yau ba jawahir a ciki can kuma ya rinka hango ta tare da
'ya 'yansa 'yan uku, haba wa, tuni wani sabon farin
ciki ya sake mamaye shi ya shiga wanka ya sake
sabon wanka ya zira farae shaddarsa sabuwa kal
mai laushi sai sheki take yi kamar boyel.
❤❤❤SALON SO❤❤❤
❤❤❤ PART 41 ❤❤❤
.
By SULAIMAN BOMBOY
.
Ya debi makudan kudi wanda ba zan iya cewa ko
na wane ba ya zuba a jaka ya fice ya kulle ko ina na
gidan ya fito ya kara gaya wa megadi ya kula da
gida sosai
Ya shiga mota da kansa yake jan motar cikin farin
ciki da annushuwa wani tsadaddaen hadadden kanti yaje wanda duk kayansu da ga waje suke
shigowa da shi. Nan da bude bakin aljihu ya runka
jidar kayan jarirai su tawul, da shawul da riguna
famfas su safa da takalman jarirai komai iri daya
guda uku yake kwasa, sai da ya cika but da kayan
jarirai har da gadaje set me uku na jarirai. Haidar ko ya manta ne da dinbin siyayyar da suka
yo daga kasar waje ta jariran ne? Oho.
Ya je ya siyo katon ragonsa wanda za a yanka
saboda naman gashi ya siyo kwandunan tattasai
da tumatir da attaruhu albasa da kaji da zabi
saboda girkin 'yan barka ya yiwa direbansa waya ya taho da wata motar kwashe wasu kayan suka
nufi gidan su jawahir.
Tirkashi! Wani aiki sai masu da shi, aka rinka jidar
kayan da Haidar ya kawo ana kaiwa sashen momy
Haidar ya shigo yana ta gaisawa da jama'a suna yi
masa barka. Ya karasa falon Momi ya gaida su Momi su Anti
Babarsa da su Inna da kannansa 'yan biyu. Dangi
dai rankacakaf kowa ya zo, jariran suna hannunsu
sun sha ado, da tsadaddun kaya 'yan kantuna
masu kyau.
Sayyada ce take gaya masa ai jawahir tana sashenta ta ce kada abar kowa ya shiga bacci zata
yi, shi yasa aka kwaso jariran ma aka yo nan da su,
saboda yan barka.
Haidar ya ce ai suma jariran suna bukatar hutu da a
kyale su aka yi a jikin uwarsu suna jin diminta suma
suyi vaccin iya in an jima su ka tashi duk me son ganinsu sai ya gansu.
Anty babarsa ta watso masa harara yayin da ya
mike sum-sum ya bar falon ya nufi sashen da aka
ware wa jawahir.
Ya tura kofar falon ya shiga ko ina a gyare sai uban
kamshi da yake tashi, yana kai cikin dakin wani kalar kamshin ya ja mai dadi da sanyaya zuciya.
Ya hangota kan makeken gado tana ta baccinta
hankalinta kwance.
Ta yi kwanciyarta cikin jar sup me zanen ganye ta
kara kyau da haske sai dai ta rame. Ya karasa bakin
gadon ya sumbace ta yana shafa fuskarta tare da hura mata iska a kunnanta.
Ta bude ido
tare da fadada murmushinta "Lah, Honey ka daina
fushin ka zo? Ta tashi ta jingina a jikinsa ya
rungume ta yana shafarta tare da shakar
ni'imtaccen kamshin da yake jikinta. Ya ce "Bebyna ai ba zan iya fushi da ku ba, ina zan
iya bacci ba tare da naji diminki ba, ai ba ni da
kwanciyar hankali in banga 'yan ukuna ba.
Aka kwankwasa kofar jawahir ta yi saurin kwace
kanta ta matsa can gefe, ta yi izinin a shigo.
Inna ce da sajida suka shigo dauke da kwanukan abinci.
Inna ta sakko mata da filo kasa ta ce zauna anan ta
bude mata kwanon tuwon dawa yana turiri ta
bude miyar kubewa danya da aka burge kaza ciki.
Daya kwanon kuma gasasshen nama ne ya ji
kayan kamshi da yajin daddawa. Sai kunun kanwa a kwanon sha Inna ta debo man shanu ta zuba
mata amiyar ta ajiye mata yajin daddawa, ta ce
"Sakko ki zauna maza ki cinye."
Idon jawahir ya yi rau rau zata yi kuka, Haidar ya ce
"Haba Inna daman dan ki yi mata izaya da badin
tuwo da kunu shi yasa kika dage sai ta taho nan.? Inna ta ce, "Da Allah i min shiru ku me kuka sani
wannan ai shine gatan me jego shi zai sa mata
koshi ta sami wadataccen ruwan nono da 'ya 'yan
zasu sha su koshi ko kasan har yanzu yaran basu
sha komai ba sai zam zam da dabino?
Cikin tashin hankali Haidar ya ce "Inna saboda me? Bayan an siyo musu katon din madara.? Inna ta ce,
"Ai duk wani abu da za'a basu shi yanxu shirme ne
in dai va su fara shan nonon uwarsu ba, nonon
uwa shi ne abu mafi mahimmanci ga jariri. Don shi
yake sa su kuzari yake kara musu lafiya kuma don
haka ki sauri ki ci ga ruwan wanka can yakusa tafasa, idan an daki nonon da ganye zai temaka
wajen zuwan ruwan nonon da sauri
Haidar ya ce "A to ta so maza ki ci tuwon nan ki sha
kunun.
Jawahir ta kalli Haidar a marairaice alamun tsoro a
faskarta. Haidar ya kamo hannunta "Yi hakuri ta so na taya
ki ci kin ji kada ki damu.
Ta zauna kan filon shi kuma ya zauna kan kafet din
suka zuba yajin daddawa da man shanu suka fara
cin tuwo.
Yanda suka za ce shi ba haka suka ji ba, ashe dai shima tuwon dawar da dadi.
Tun suna ci suna hira har abin ya kaisu da shiru sai
dai gyada kai, kawai suke yi suna kai loma tare da
zuba santi.
Inna tana zaune tana kallon su sai da suka kusa
cinye tuwon nan, Inna ta zazzuba musu kunan a kofina ta tura musu gasashen naman shima sun ci
amma ba da yawa ba saboda koshin da suka yi.
Cikin kwana biyu ruwan nonon jawahir ya watada
tana shayar da 'ya 'yanta su koshi sosai.
Daddare dai ba sa shan nono sai madara yau
kwana hudu da haihuwar an kawo kayan barka akwati biyar na me jego da jirajirai.
Bayanin kayan da suke ciki zai cika min dan lattafin
nawa ban gama ba, hade da mukulun dankareriyar
mota jif, me ruwan ganye wadda Haidar ya yiwa
jawahir kyautarta da takardun dankareren gida da
yake a Nasarawa GRA shima gift ne ya bata duk saboda haihuwar 'yan uku.
Sai takardun filaye guda uku kowacce da sunan
yaran mallakarsu ce kyautar ubansu Haidar da
yake ba su.
Kowa ya kalli kayan sai ya yi murna tare da son
barka da wannan hidima da Haidar ya yi. Ranar suna an sa wa jariran mazan sunan baban
Haidar da baban jawahir macen kuma an sa mata
sunan Inna.
Amma duk an boye musu sunan ana kiransu da
Salim, Sadat, Salma, Alhamdulillahi taron suna ya yi
kyau ya kuma kayatar ya burge kowa da yamma aka je dan Haidar da jawahir sun yi shigar kaya iri
daya jawahir ansha gwala gwalai hannu da wuya
da kunne har da sarkar kafa, sai sun jero a gurin
fatin suna rike da hannun juna suna tafiya sannu
sannu suna murmushi tare da hira kasa kasa a
tsakaninsu sai sheki suke yi kamar taurari, Bayan su
kuma Sayyada ce da Sajida sai Auwalu a tsakiyarsu
suna dauke da jariran yaran an yi musu kwalliya ta
ke ce raini Salma ta sha adon gwal har da siririyar
sarka ta kafa da ta hannu masu bidiyo da hoto sai
haskasu suke yi Sa'adu Bori ya saki kida yana wake su cikin wakar soyayya ta yi dadi Jawahir da
Haidar.
Allah ya raya Salim, Salma, Sadat, 'yan uwa kuwa
suka balle bakin jaka sukai ta yi musu ruwan kudi.
'Yan uwa da abokan arziki suka rinka ba wa
jawahir kyauta iri iri ta kayan jarirai da kudi da sauran su da haka taro ya watse.
Kowa ya nufi gida, jawahir tana zaune a gidansu ita
da jariranta da Inna sai kakar babarta wadda ita
take yi mata wanka.
Anty Maryam kuwa ta dage da sake hada wa
jawahir sababbin sinadarai na matse 'ya mace da kara mata ni'ima mace ta koma kamar bata san
namiji ba.
Haidar kuwa kwana kawai yake yi a gidansa da
safe da ya gama shirinsa gidan su jawahir zai taho
ita zata hada masa break ya ci ya dauki yaransa ya
yi musu wasa sannan ya tafi office. Haka in ya dawo ma nan zai zo jawahir ta shirya
masa abinci ya ci ya yi kat yai ta rainon 'ya 'yansa ya
na yi musu wasa sai shadayan dare sannan zai
koma gidansa.
**** **** *****
Bari mu waiwayi Kausar don muga wace rayuwa take y ne."
Kausar tun ranar da ta bar gidan Haidar ta sauka a
gidansu Abuja.
Iyayenta sun tare ta da murna amma ganinta da
shirmin akwatuna sai jikinsu ya yi sanyi suka shiga
tambayarta da lafiya? Kausar ta gaya musu karya da gaskiya na ciwon
Haidar sannan ta mika musu takardar sakin da ya yi
mata. Ba su ji wani zafin sakin da ya yi mata ba don
su a ganinsu gwanda hakan da 'yarsu ta takura,
'yan aikinta suka shiga gyara mata wajen zama.
Kwanaki kalilan a tsakani mahaifanta suka tura kano gidan Haidar don kwaso kayan Kausar suka
tarar da gida a kulle sai megida ne yake yi musu
bayanin ai ba kasar, sai gidan su Haidar din suka je
suka yi wa Anty bayanin zasu kwashi kaya.
Anty ta yiwa Yaya Abba waya yazo ta bashi
mukullayen ta ce ya je ya bude musu gidan ya tsaya su kwashi iya kayansu.
Haka kuwa aka yi, ya je ya bude musu ya jira suka
gama kwasar kayansu ko tsinke basu bari ba,
bayan yin iddar Kausar ta bude shafin zawarci in da
manema kuwa suka yo mata ca! Ganin ta fito daga
gidan mekudi ga ta kuma 'yar mekudi. Kausar abinka da goggiyar tuni ta kuma wanke
fata ta tsunduma cikin zawarci. Manema da yawa
sun firfito mata sai dai rashin sa'ar da ta yi, duk
cikinsu babu saurayi, daga me mata daya sai me
mata biyu.
Hakan ne yasa ta riki Bomboy dinta. in da ya fito ya kawo
kudin aurenta ba dadewa ba aka sa ranar biki an
sha shagali da casu kamar na budurwa.
Ta tare a gidan ta dake nan K/Maiyaki. Bomboy dai ya dauki matar sa kauthar kamar wata sarauniyaba abin da be ajiye mata ba na jin dadin rayuwar
dan Adam. Ba ruwanta da girkin gidan kullum sai
dai ya dauke ta zuwa hotal su ci abin da ransu yake
so, ruwa sai da na roba wato swan.
Kowanne lokaci firji dinta cike yake da kalolin
abincin gwangwani da kalolin lemummuka. Tuni Kausar ta kara gogewa jin dadi da hutu ya
kara samun mazauni kome sai dai 'yan aikinta su yi
mata bata katabus koda yaushe aikinta kwanciya
ko ci.
Ana cikin haka ne aiki ya kuma mayar da iyayen
Kausar kasar America. A lokacin kuwa Kausar da Bomboy ba sa kasar don haka bata sani ba
don iyayen nata sun ta lalubenta a wayarta ba su
same ta ba, sai sallahu suka bar mata gun 'yan
aikinta suka daga zuwa America.
(((((( SALON SO ))))))

:
KARSHE!
.
BY SULAIMAN BOMBOY
.
KARSHE!
.
Ranar da Bomboy da Kausar suka dawo da
ga tafiya, 'yan aikinta suka gabatar mata da sakon
iyayenta. Kausar har kuka ta yi don bakin ciki gashi wayarta da lambobin iyayen nata suke ciki ta fadi a
wannan tafiyar da ta yi, don haka ba wata hanya
da zata ji su ba damar ta yi musu waya kenan, ko
su yi mata?
Ga shi bata san address din su a American ba, bare
wata rana ta kai musu ziyara dole ta dauki dangana da hakuri ta na me fatan Allah sa su zo nan kusa
don ta ji cikakken address dinsu ko ta bisu su tafi
tare. Ba dadewa Kausar ta gama da laulayin ciki me
wahalar gaske bata iya cin abinci sosai ga azabar
ciwon ciki da ciwon kai. Hankalin Bomboy
ya tashi da ganin rashin lafiyartata. Ya kwashe ta suka nufi asibiti akayi mata tes da
gwaje gwaje daga karshe likitan ya dauki fitsarinta
ya ce, gobe a dawo a karbi ruzol suka taho a hanya
ya yi mata siyayya fal irin na marasa lafiya ya dawo
da ita gida.
Da gari ya waye Bomboy da kansa ya je ya karbo sakamakon gwajin da aka yi mata hankalin
Bomboy yayi fari da ganin wannan sakamakon
Murna a gun shi da Kausar kuwa kamar su hadiye
juna don murnar samun ciki Kausar ta fara
kawowa Bomboy tsarabe-tsarabe, ta ce
wannan ta ce wannan haka Bomboy zai je ya kwaso mata. **** **** ****** *****
Sannu sannu rayuwa ta juya ta juyawa
Bomboybaya domin kudin hannunsa tas sun kare
'yan aikinta wuya ta ishe su duk sun gudu sun
barsu, sai ga Kausar ta je ta na rokon matan yayun
Bomboy da su taimaka su rinka sammata abincinsu, su kuma suka ce muddin tana so ta
rinka cin abincinsu sai dai ta fito ta rinka girkawa
don babu bawanta da zai rinka dafawa yana bata
tana ci.
Dole Kausar ta fito tana girkawa da safe koko ne
za'ayi shi tsilulu saboda babu wadatacciyar gasara, rafin kofi ake rabawa kokon ga ba kosai da rana a
jika garin kwaki a yayyafa a kasan roba yaro ma
baya koshi bare babba.
Da daddare datsar dawa za a tuka bakikkirin da
koriyar miyar kuka wadda daga daddawa sai
barkono a ciki. Kausar ga fama da ciwo ga shi yanzu cikin nata ya
kai wata shida ya yanzu cin abinci ne da ita saboda
cikin yana sata masifaffiyar yunwa. Ga abincin da
ake bata baya isarta, ga rashin dadi haka take
hakura ta tattura, ga shi duk ta yi baki ta rame ta
kanjame ke ba kya ce 'yar hutu Kausar din da ba ce.
Duk ta bushe sai kashin wuya da tsinin ciki gashi
bata iya yin tuwon ba duk ranar da ta yi sai yai
danye ko ya yi gudaji.
Ga matan yayye da 'yansu si yi mata masifa sun
dungure mata kai suna yi mata ba la'i, dole ta jure ta hakura take zaune don bata da gurin zuwa in ma
ta fita ga iyayenta har yau bata samu labarin su ba,
to ina zata samu kudi xuwa American ma bare ta
binciko in da suke.
Don kayan dakinta kaf ta sai da su ta ci abinci
duniya kenan me juyi juyi. **** ****** ****** Jawahir watanta biyar kenan da haihuwa ita da 'ya
'yanta sun kara kiba da haske sun yi kyau jajir da
su kamar 'ya 'yan Turawa. Kowa ya kalle su sai ya
yi sha'awar cewa da ma dai iyalinsa ne.
Haidar arziki ya ci uban na da, ya tanfatsa musu
wani tsantsareren gida na gani na fada wanda duk wanda yaje gidan kallo abinda yake fadan shi ne
aljannar duniya.
Gidan ya
tsaru iya haduwa ya hadu, yanda Haidar ya
hadewa jawahir falonta da dakunanta ko na
sarauniyar indiya albarka Dakin 'yan uku kuwa ke kya ce kamfani ne
tsadadde na kayan wasan yara saboda kayan alatu
da suke ciki, Haidar ya kara girman da murjewa ya
zama Alhaji me tsananin kyau da kwarjini.
Jawahir ta zama big madam cikakkiyar mace ga
kyau ga hutu ga kwarjini 'yan 'ya'yayansu guda uku abin sha'awa tubarkalla, bul bul da su jajir da
su gashinsu akanannade kamar 'ya'yan turawa.
Mijinta ya sakar mata naira sosai don duk wasu
takaddun kamfanoninsa da gidajensa da filayensa
da duk wasu kadarorinsa suna hannunta. Baya yi
mata geji akan komai duk wani abu daya kamata ya yi na game da biyan ma',aikatansa
albashi na kamfanoninsa zuwa na gidajensu, ya ce
Abbansa ya kwanta ya huta shi yake komai na
gidansu.
Jawahir ta kasance me taimakon talakawa da
kaskantattu wadanta basu da watada, don haka gidan nasu kullum yake cike da 'yan neman
alfarma.
'Yan uku suna da shekara daidai ta yaye su sun yi
girma sunyi wayo gudunsu suke yi ko ina ga
surutu kamar Aku. Suma hadadden falonsu duk
sun ci kwalliya kamar masu shirin zuwa fati, Haidar yana ta wasa da 'ya
'yansa ya ta da kai da cinyar jawahir Salim da Sadat
shiga iri daya akayi musu ta jins da T shirt fara da
aka yi rubutu da ruwan gwal a gaban rigar.
Salma ma tana sanye da dan jins dinta da 'yar riga,
kunnanta da wuyanta yana sanye da yari da sarka kirar daimond 'yar xire, kanta ya sha kananan
kalba da kanan ribon a jiki yaran sun yi kyau
kamar 'ya 'yan turawa.
Gaba daya yaran suna kan Haidar suna ta tsalle
tsallensu a jikinsa, wayar ku sa da jawahir ta yi kara
ta daga ta kara a kunnenta, "Hello yauwa Anty jawahir wallahi wata bakuwa ce tazo ta kafe lallai
tana son ganinki.
Jawahir ta ce "Okey ba damuwa kawo ta muna
falon sama
Ta dire wayar, bakuwar da tun shigowarta ta saki
baki tana ta kalle kalle a cikin gidan babu abin da ya fi kayatar da ita irin tsantsara tsantsaran falon da
suka rinka wuce su, jikinta bai kara yin sanyi ba, sai
da suka shiga wani tsantsareren falo wanda ya
hadu da kayan kyale kyale sai wata hadaddiyar
matattatakalar bene wadda aka yi ta kamar da
ruwan gwal. Kasan matattakalar shimfide yake da kafet, suka
hau suka yi sallama falon suka shiga.
Jawahir ta dago kai tare da amsa sallamar ta zuba
wa matar ido, tana tunanin ina ta santa. Matar ta
zube a gabansu tana kuka Haidar kuwa yana ta
wasa da 'ya 'yansa be ma dago kai ba bare yasan wacece.
Jawahir ta ce a'a baiwar Allah me kuma yake
faruwa daga zuwa sai kuka ba tare da kin yi wani
bayani ba."
Ta kwanto yan kwananniyar'yarta daga baya
wadda shimi ce kawai a jikinta saboda rashin sutura matar kuma atamfa da take jikinta duk ta
kode ta jeme ga hadin baki a jiki matar ta ce "Ban yi
mamakin yanda baku gane ni ba ni ce Kausar.
Jawahir ta
yi zumbur ta mike tana rike da baki cikin mamaki ta
ce "Kausar ke ce rayuwa ta maida ki haka me ya faru dake Kausar ina iyayenki da mijinki.?"
Kausar ta goge hawayenta ta shiga basu labarin
iyayenta da halin da take ci, ta juya tana kuka tana
rokon Haidar gafara Haidar ya ce "Ni wallahi ba
komai don rabuwa da ke alheri ya zamar min don
da ina tare da ke da ban sami zaman lafiya da kwanciyyar hankali haka ba." Ya mike goye da
Salma ya dauki Salim da Sadat a kafadarsa ya shige
ciki.
Kausar ta bisu da kallo tana me sha'awarsu shi da
'ya 'yansa da matarsa da ta yi hakuri da yanzu
itama tana cikin wannan daular. Jawahir ta girgiza kai zuciyarta cike da tausayin
halin da ta ga Kausar. Lallai duniya zancan banza ce
kana takama kai wani ne lokaci daya sai Ubangiji
ya mayar da kai ba komai ba.
Jawahir ta ce Kausar "Ki yi hakuri lamarin duniya
kenan don haka ba a son daukan duniya da zafi. Ta mike ta shiga daki ta debo sababbin riguna kala
takwas da turamen atamfofi kala hudu da
dinkakku kwance kala shida, da kudi naira dubu
hamsin ta kawo mata ungo wa'yannan kije ki yi
amfani da su zan kuma sa abinciko min koda
lambar wayar iyayen naki ne kin ji ko." Kausar ta rissina ta rinka godiya tana kukan murna.
Jawahir sai da ta sa aka hada mata kayan abinci fal
bayan but din mota tasa direba ya kaita har gida.
Kausar tana komawa ta sai rishonta ta sai kananzir
galan guda ta kai dakinta take girkinta ita kadai ita
da mijinta suna ci ta daina kula abincin gidan Nan fa matan gidan da 'ya'yan gidan suka tusa ta
agaba da habaici da bakaken maganganu ita dai
bata kula kowa sai ta rinka kulle wajenta ma ta
daina sauraronsu.
Sati

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login