Showing 12001 words to 15000 words out of 48659 words
Chapter 5 - Salon So Book Hausa Novels By Hadiza Salisu Sharif.txt
Abba suka tafi America karatu.
Bayan dawowarsu ne da za a bikin bude masa
kamfaninsa da mahaifinsa ya bude masa to sai ya
tafi garin mashi ya lalubo Faruk. Bayan bude
kamfanin nasa ne dai suka ci gaba da zumuncinsu.
To faruk din yayi aure yana zaune kusa da iyayensa
Yau Haidar bai samu zuwa office ba don Abuja yake
shirin tafiya, don haka tun tara na safe ya kammala
duk shirye shiryensa ya nufi hanyar Abuja. A hanya
ya lodar musu tsaraba. Bai samu matsala
dangane da kwantaccen da ta yi masa, tun da ya san unguwar da suke zaune fitacciyar unguwa ce
ta manyan kasa masu fada a ji ne.
Kausar kuwa a na can an gama duk wani shirye
shirye na taryar gwarzon masoyi. An gyara falo an
kayatar dashi, ana jiran masoyi. Kausar ta yi wanka
ta sha kwalliya da dandatsetsen less. wanda za mu iya cewa kwalliyarta ce, ta fito mata da kyau.
Don kun san ba a mummunar mace sai marar
gyara. don duk munin mace kwalliya sai an ga
kyata. Don naka gyara da kwalliya shine mace.
Kausar baka ce amma a yanzu da yake durfafi yin
shafe shafe da mayuka 'yan kanti za mu iya cewa ta koma fara.
Doguwa ce, tana da kiba da fati. ba ta da wani
girman nono, kanana ne wanda har sun riga sun
zube, amma wayayyiya ce ba ta shiga abin da be
shafe ta ba akwai hutu da jin dadi rayuwar duniya.
Haidar ya iso lafiya. "Ya kuke murna da rawar jiki a wajen Kausar. Tuni ta sa a ka shigar da Haidar
dakin da aka wuni ana gyarashi don zuwasa. Tuni
aka gama cika gabasa da kololin abubuwan ci da
na sha. Can Kausar ta shigo cikin washe baki tana
fara'a
don bakin yaki rufuwa ta ta ho ta saurin ta ta zauna kusa da shi a guje ta rirrike hannuwansa, "Oh ni
'yar nan! Allah na gode maka da ka sake hada ni
da abun sona, burin zuciyata wato Haidar, ubangiji
yanda ka hada mu a nan yanzu ubangiji Allah ka
hada mu a gidansa a dakinsa, a matsayin matar
aurensa,. Ta shafa. Haidar ya ce, "Irin wannan doguwar addu'a haka
to kada ki yi wacce za ki rike ni a gidanku na kasa
komawa gida.
Ta kyalkyale da dariya ta rinka zuba masa girke
girgen da aka yi masa kamar ta ba shi a baki haka
ta rinka yi masa. Suna dade suna hira duk wani dan gidasu sai da ya zo suka gaisa. Haka ya shiga ciki
ya gaida Babarta da kishiyar babarta.
Ta hau da shi falon sama har wajen babanta sai da
ya ce, Baban nata yayi murna da ganin shi don ya
yaba da hankain haidar a kan zai turo iyayensa
don a yi maganar aurensu da Kausar. Babanta ya yi ta sa masa albarka inda Haidar din yake ta malala
masa godiya.
Haidar sun sauko daga saman sun dawo wajen
hirarsu Kausar sai munrna take kamar ta goya shi.
Ya sa yaron gidansu ya kawo musu tsaraba a but
din motarsa ya yi wa kausar sallama don yana so ya tafi gida kada dare ya yi masa a hanya.
Da kyar ta kyale shi ya tafi don gani take yi kamar
in ya tafi ba zai dawo ba. Haidar daga Abuja duk
dumbin gajiyar da ya kwaso bai wuce gidansa don
hutawa ba sai ya zarce gidansu, yanda ya shiga a
hargitsensa Abba da Aunty suka san ba lafiya ba. Bayan sun gaisa ne ya koma gefe daya ya yi zugum
da shi yana tunanin ta ina zai fara ne.
Abba ya shi, "Haidar lafiya? Me yake faruwa ne?
"Wallahi Abba abun da yake damuna ne na rasa ta
inda zan bullo masa bare na gaya muku
"Ba komai gaya mana ko meye, kana da wadanda za ka gayawa ne wandada suka fi mu? Ai ka ga
babu ko?
Gaya mana menene damuwarka?"
"Wato Abba tun muna America akwai yarinyar da
muka yi alkawarin aure da ita, to bayan mun gama
na taho gida Abba kuka tayar min da maganar auren jawahir. Abba don kada na bata muku rai ne
shi yasa ban yi muku maganar kausar din ba. Ita
dai na gaya mata, na ba ta hakuri, to ta tashi
hankalinta sosai, to shi ne na kwantar mata da
hankalinta da cewar zan aure ta bayan shekara
daya. da kyar Babanta ya amince mata shi ne yanxu
kuma uban nata ya takura mata da maganar auren,
nake so don Allah Abba ku bar ni na aure ta.
Aunty kuwa ta mike tsaye cikin fada take nuna shi
da yatsa, "Kai ka kiyaye ni, wallahi ka shiga
hankalinka. A aura maka 'yar uwar tawa auren naku shekara daya ka ce za ka yi mata kishiya, to
ba ka isa ba ka yi kadan jawahir ta fi karfin ka
wulakanta ta."
Abba ya daga mata hannu ya ce, "Aisha ya isa
haka. Haidar tashi ka je gida tukunna sai mun yi
shawara za ka ji komai. Ya mike, "To Abba na gode ku tashi lafiya. Aunty
sai da safe ya wuce sukuku kamar wanda kwai ya
fashewa a ciki
Abbansa ya ce, ba a yin haka Aisha ki duba ki gani
yaron nan ya yi mana biyayya lokacin da muka
tursasa shi auren jawahir yanzu bai kamata ya zo da tasa bukatar mu ki biya masa ita ba, kin san 'ya
'ya amana ne a hannunmu duk da cewar mu muka
haife su to idan muka zalince su Allah fa ba zai
kyale mu ba sai ya tambaye mu, to kin ga dai bai
kamata da farko mun bi son rainmu mun yi masa
aure ya hakura sun zauna sannan yanzu ya kawo bukatarsa mu bi son zuciya mu hana shi, aikin ga
ba mu dai dai ba bare lamarin aure da ba ayi masa
katsalandan.
Abun duniya duk ya dagulewa haidar duk dai da
ya ga alamun nasara a wajen Abbansa, to Aunty fa
Ai ita za ta zamo babbar matsala. Yana zaune a falon kasa jawahir ita ma tana waje
daya zaune kan kujera tana yi wa Sayyid karatun
Alkur'ani yana biyawa.
Wayar Haidar ta fara ruri ya daga, "Hello Kausar ina
gajiya.
Ba gajiya sweety, yaya ka dawo gida? "Lafiya lau kausar ai na sha wahalar tafiya dag
kano zuwa Abuja a mota kuma a dawo a ranar, ai
akwai wahala. Ko da yake ba komai tun da
Hausawa sun ce garin masoyi ba ya nisa, duk ranar
da Allah ya mallaka min ke na fanshe wahalata......
Wani katutun bakin ciki ne ya tsayawa jawahir a zuciya, rainin hankali wato a gabana ma yake yi wa
mace waya? wallahi bai isa ya yi min wulakanci ba,
ina zaman dole a gidansa 'yar sakin fuska ba yayi
min bare mu yi hira amma shi ne yake kyalkyala
dariya da budurwarsa, kawai sai ta mike a fusace
ya riga ya shagala da yin magana a wayar ta fizge wayar daga hannunsa ta doka ta da kasa.
Wayar ta tarwatse sai ta ya daki a guje ta rufe kofa
duk da haka sai ta fada gado ta sa kuka.
(To in banda abun jawahir kukan me kike)
Bari dai mu ci gaba labari mu ji me yake faruwa a
zukatan guda biyun. Haidar ya bi wayarsa da take tarwatse kan kafet da
kallo, "To me jawahir take nufi da za ta fizge masa
waya? Kishi take yi ko kuma dai ta fara raina shi
ne?
Lallai zai yi wa tufkar hanci kada nan gaba abin ya
shafi aurensa. Da safe ya gama shirinsa ya sauko ya nufi tebir don
yin break ya ga wayam babu break bare alamarsa.
Ya kwallawa sayyid kira ya fito da gudunsa, "Ina
Antinka?"
"Tana daki."
"To je ka ka kirawo min ita." Ya kirawo ta ta fito yayin da ta durkusa, "Ga ni."
Ke me ya hana ki yin break? Kina nufin haka zan
tafi office da yunwa.?
Kanta yana sunkuye a kasa ta ce, "Ai ca nake za ka
biya ta wajen masoyiyar taka ka ci a can.
Ke ba na son shirme kin ji ko, tashi ki je ki hada mana break. Bakin ciki ya ishe ta ba abin ta ce ba za
ta yi ba ta sabawa ubangijinta. kawai sai ta mike
tana kuka ta nufi kicin din. Sai tausayinta ya kama
shi yarinyar tana burge shi ko don biyayyarta.
Ta gama soya dankali da kwai ta dafa ruwan shayi
sai dammaman kunun gyada da ta yi masa kofi daya kamar yanda yake sha lokaci lokaci. Za ta
wuce daki ya yi kirata, "Ke zo nan. Ta dawo ta
durkusa. Ya ce, "Ta so ki yi break. Ta
girgiza kai na koshi. Ya daka mata tsawa. "Ta so
mana jinkinta na rawa ta mike ya hada mata ruwan
tea me kauri ya mika mata. Ya tura mata dankali da kwai da biredi gaba ya ce, "Ki ci da yawa ko yanzun
nan ranki ya baci. Haka ta rinka ci ana hawaye yana
kallonta sayyid
kuwa ya tafi wajen Dela za ta yi masa wanka.
Haidar ya gama break dinsa ya mike ya nufi office
jawahir ta kifa kanta a kan tebir din ta ci kukanta ta koshi ta gama ta shafe hawayenta ta koma daki.
Sayyid ya shigo an yi masa wanka ta shirya shi ya
rinka jijjiga ta dole ta fito ta hada masa break ta
koma daki.
Zuciyarta tukuku take yi mata sam ta kasa samun
sukuni a zuciyarta tun daga wayar nan da ta ji haidar ya yi, "Wato ma ina ruwanta ne da wayarsa.?
To me yake neman faruwa da ita ne? ke wallahi na
gaji da zaman banza a gidansa ya zo mu yi duk
wace za a yi, na cire tsoronsa da shayin komai don
ni mutum ce ba dabba ba yanda yake da a gidansu
haka nima nake a gidanmu. Yau ma dai haidar daga office da ya tashi gidansu
ya kuma waccewa a kan maganarsa ta jiya.
Abbansa ya ce, Ka kara hakuri Haidar a bi komai a
hankai ba a son gaggawa don gaggawa tana daga
shaidan.
Aunty ta ce, Alhaji ka rabu da yaron nan, nema yake ya tozarta mu ya bata mana zumunci to
wallahi ba ka isa ka shiga tsakanina da dan uwana
ba.
Abba ya ce, "Haidar tashi ka je gida zan je na nemi
Daddyn jawahir din na yi masa bayanin komai, na
san shi mutum ne me fahimta ba zai kawo komai ba to daga nan sai mun shirya ranar da za mu je
Abujan wajen iyayen yarinyar. Haidar ya rissina,
"To Abba na gode Allah ya saka
da alheri, ubangiji ya kara girma.
Ba komai haidar kai dai ka rike amana kuma ka
sawa zuciyarka adalci ya yi musu sallama ya tafi. Yau a falo ya samu jawahir tana kallon wasan
Hausa. Be kalli inda take ba ya haye samansa. Ita
kuwa daman a cike take ta shi jira take yi ya dawo
su yi wace za su yi don ta gaji da zaman gadin
gidansa.
Sai da ta bari ya kammala dun wani abu dayake yi ya dawo falon kasan ya zauna yana duba jarida
sannan ta fara magana ba tare da ta kalle shi ba.
"Yaya yau dai magana nake son mu yi da kai.
Ba tare da ya dago kai ba ko ya bar karatun jaridar
ya ce, Uhm ina sauraronki.
Ta ce, "Wai menene matsayina a gidan nan ne? "Bai dago kai ya kalle ta ba ya ce, "Matsayinki kike
son sani? Ta ce, "Kwarai kuwa."
"Ya ce, "In dai ba mantawa kika yu ba matsayinki
yana na kanwata da kuma wai matata ta aure, don
wai zance.
Ta ce, "To in haka ne me zai hana ka sake ni ko ma huta daga ni har kai da wannan daurin da bai
bayin da aka yi mana.
Ya ce, mata, "Ai dama ba ni na gayyato ki ba in
wanda ya kawo ki ya gaji da zaman naki za ki ga ya
zo ya dauke ki.
Zumbur ta mike tsaye ta rike kugu ta nuna shi da dan yatsa, "Kai bari ka ji, ni ba irin ballagazayen
matan nan ne da ka saba wulakantawa ba, ni na fi
karfin wulakancinka, ina bin ka ne gudun kada na
sabawa ubangijina da kuma gudun wargajewar
zumuncin iyayenmu da nake yi wa biyayya, to
yanzu na gaji da zama da kai don ka san ba na son ka a ka ba ni kai, na yi hakurin zaman shekara a
gidanka, to yau hakurina ya kare ba zan sake
kwana a gidanka ba dole ne ka sake ni.
Tana rike da kugu tana yamutsa fuska tare da
girgiza jikinta na jin bala'i.
Ya kalle ta daga sama har kasa, dariya ce ta kwace masa ya dai daure ya gintse dariyar ya ce, "Ni nan
da kika ganni ba zan taba sakinki ba, in kin ga
dama ki zauna in baki ga dama ba ki je duk inda za
ki amma maganar rabuwa babu don ni ba wawa
ba ne.
Idan ba ki sani ba ma ki sani aure zan yi kwana nan. Ta dafe kirji, "Aure! Aure fa ka ce? Da gaske
kake
yi?
Wallahi ba zan zauna a gidanka ba bare matar ta zo
ita ma ta raina ni, ban da kaddara ma me zai sa na
aure ka? Ni me santalelen saurayi da yanzu ina gidansa.
Ya mike kuwa cikin sauri zai kai mata mari ta yi
saurin kaucewa ya ce, "Ki yi a hankali duk san da
kika sake fadar wani namiji a gabana da sunan
yana sonki sai kin raina kanki. "Ya yi hayewarsa
sama ya bar ta tana kuka. Haka kawai be yi min abun da na nema ba sannan
ya ce aure zai yi, wallahi ba zan zauna ba tafiyata
zan yi, duk abin da ma zai faru ya faru. "Da sauri ta
fada dakinta ta kama hada kayanta tana zuvawa
cikin akwati ta turo akwatin da kyar ta kirawo Dela
ta ce ta bawa yaron gida ya sawa Haidar a but din motarsa. Cikin rawar jiki ta karbi aiken uban
dakinta duk abin da ta san za ta bukata ta sa an kai
but. Ta fito da shirinta za ta fita lokacin Sayyid ya
tashi daga bacci ya ce, "Aunty ina zaki? Ni ma zan
biki. "Ta shafa kansa, "Ka yi hakuri Kayyid zan siyo
maka jirgin sama me tashi. Ya makale kafada alamar bai yarda ba.
Ta ce, "To je ka dakin Yaya ka ce ya zo mu tafi.
Ya ce, "To Ya hau san a guje.
Ita ma saurin ta yi ta fice ta shiga motar Haidar ta
tashe ta ta tafi ba ta taba tuka mota da kanta ba sai
yau, amma ta iya don duk sanda za su fita da direba sai ya koya mata.
Haidar yana jin tashin mota ya turo Sayyid daga
jikinsa ya mike zumbur sai sannan ya tuna ya bar
mukullin motarsa a falon kasa. Ya gangaro falon
kasan da sauri yana salati, "Inna lillahi wa inna
ilaihir raji un. Hankalinsa ya yi mugun tashi. "Na shiga uku.
Kadda yarinyar nan ta yi wani wajen yanzu idan
wani abu ya samu yarinyar nan yaya zan yi da
rayuwata?
Ga Sayyid ya ishe shi da ihun kuka yana kiran
"Aunty Dole Haidar ya dauki wani mukullin motar ya saba Sayyid a kafada suka fita. Ya shiga mota a
hankali yake tuki yana kallon hanya ko zai hango
motarsa da jawahir a ciki.
Jawahir kuwa cikin nutsuwa da tsoron ta gudanar
da tukinta har ta zo kofar gidan Inna tayi hon
megadi ya bude mata ta shiga ta yi parking ta sa shi ya jidi kayanta da yake but ya shigar mata da su
cikin falon Inna.
Inna ta ce, Lafiya na ganki da kaya?
Ta ce, "To lafiyar kenan.
Inna ta ce, "Me yake faruwa ne na gan ki da kaya
kuma kin rame a kan san da kuka zo, ko ba ki da lafiya ne?
Ta ce, "To ba dole na rame ba an aurawa wanda ba
ya so na ni yana ta gasa ni ga shi nan ai yau ya
koro ni gidanmu ko.?"
Inna ta dafe kirji ta ce, "Shi da kansa ya ce ki taho
gidan? "Shi ne mana Inna kullum sai dai ya kira ni da tatsitsiya ko
kwaila, ya mai da ni 'yar aiki na girka masa ya ci ya
koshi wallahi sai kwanan nan ya fara yi min
magana amma da ko meye sai dai ya rubuto min a
takarda sai ni ma na ba shi amsa a rubuce sai ka ce
kurame. Inna ta saka salati, "Au ni ina ta murna na zata ciki
ne da ke ashe ba wani bayani.
Ta ce, "Uhm inna ke nan, to ko matsayin
kyakkyawan kallo ba na samu a wajensa duk na yi
hakuri na jure to wai yanzu aure zai yi. Inna ta ce,
"Aure, lallai ma yaron nan ban ni da shi boye ki zan yi, zan gyara ki na kula da ke har sai
kin zama cikalkiyar mace zai raina kansa ne da ni
yake zancen.
Duk waigen da Haidar yake yi bai hango jawahir ba
har ya iso gidansu. Aunty ya samu a falo tana
kallon labarun kasa ya sauke Sayyid ya tafi da gudu ya fada jikin Aunty yana kuka.
Aunty ta rungume shi tana cewa, "Haba Auta me
aka yi maka kake kuka.?
"Bayan Auntyn gidan Yaya ce ta gudu ta bar ni.
"To yi hakuri tun da an kawo ka wajena ka ji." Ya
daga kai Ta kalli Haidar, "Ina jawahir din take?"
Ya ce, "Wallahi ban san inda ta tafi ba, kawai na ji
karar mota, ashe ita ta fice ta yi tafiyarta.
Aunty ta dafe kirji, "Ita kadai ta ja motar ta fita?
Wato ka yi mata maganar auren naka ko? To
wallahi tashi ka fita duk inda take sai ka je ka nemo ta.
Abbansa ya shigo, "Lafiya na gan ku haka?
Aunty ta ce, "To ba dole ka ganmu haka ba, ya
salwantar min da 'ya.
"Wa ce 'ya?" Jawahir mana, wai be san inda take
ba. Abba ya yi saurin zama don jin faduwar gaba da ya
yi, ya kalli dan nasa, "Haidar me ya hada ku har ta
fita?"
Haidar ya ce, "Ni kaina ban san abun da na yi mata
ba, ta ji dai ina waya ta kwace wayar ta tarwatsa ta
sai na mike na hau sama, to ban ankara ba na ji tashin motata.
Aunty ta ce, "Uhm ka ji ba, in ban da rainin hankali
yaushe zai je gabanta yana waya da budurwa suna
hirar aure. Ni na san wannan rawar kan da kake yi
sai ka jawo mana tashin hankali, ka ga in ka ga ba
hali ka sakar min 'ya mu ba neman kai muke yi da ita ba.
Abba ya ce, "Duk haka ba ta taso ba, ku kwantar
da hankalinku da safe zan je gidan na su sai na ji
dalilin tahowar tata. Yanzu tashi ka tafi gida.
Aunty ta ce, "Ba fa tabbas din gidan ta tafi dole ne a
yi binkicen ta tun daga yau." Ta dauko mayafinta ni bari na je gidan na su yanzu.
Ta shiga mota direba ya ja ta suka nufi gidansu
jawahir. Tana shiga gidan ta tarar da mommy da
Nasir da su Auwal da Sani. Aunty ta zauna duka
suka gaishe ta cikin fara'a ta amsa tana wasa da
dariya ta su. Suka gaisa da momy da tsokana irin wasan nan na
kannan miji. Ta ce, "Yaya kuwa yana nan?
Momy ta ce, "Eh yana sama. Auwal je ka gaya masa
Aunty ta zo, "Ya hau da saurinsa ya sauko ya ce, "Ki
hau saman Ta hau.
Bayan 'Yan gaishe gaishe da suka yi sai ta gyara zama ta ce, Yaya ina Jawahir din?"
Cikin mamaki ya
